Skip to content
Part 15 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Tsabar ɓacin rai muryasa har rawa ta ke yi ya ce “Yanzu abincin da zan ci ɗin shine kika zubar Amera? “Ai muddin ka ce bazan ci abinci a gidan nan ba to sai dai kowa ya huta wallahi “Ameera ta ƙarasa tana miƙewa zata bar gurin. Adam ya ce “Haka kika ce ko? Ta juyo ta ce “Eh haka na ce babu wanda zai ci komai yau. Tana faɗa ta ci gaba da tafiyar ta cike da jin haushin rashin dafa mata Ɗanwaken da take son ci. Sai da ta shige ɗakinta sannan Adam ya iya miƙewa daga gurin ya nufi ɗakinsa da niyyar ɗaukar key mota ya fita waje ya naimi abinci domin ba zai iya kwanciya bai ci abinci ba saboda wata iriyar mahaukaciyar yunwa da yake ji. Ɗan makulli kawai ya ɗauka sai ATM dinsa yana tafiya yana jin har yanzu jiri na ɗibansa.

Sai da yazo bakin ƙofar palon ya ganta tsaye da makulli tana masa wani irin kallo. Lokaci ɗaya gabansa ya faɗi domin bai tsammaci ganin ta a gurin ba. Bai ko iya mata magana ba shima ya tsaya yana kallonta kamar yaga wata halittar. Kallon-kallo kawai suke wa juna kamar wasu abokan karawa. Shi Adam yana kallonta ne cike da mamakin yadda a ka yi Ameerar sa ta dawo haka, domin ya lura wannan halittar da ke gabansa mai amsa sunan Ameera wallahi kashe shi take son yi, domin shi dai zai iya dafa Alqur’ani mai girma a kan cewar wannan ba Ameerar sa ba ce, kallonta yake yi sosai yana son ya gano wata sheda da zata nuna masa cewar ba ita ɗin ba ce, amma babu alama sai wannan ƙaton cikin dake jikinta wanda izuwa yanzu babu abin da ya tsana kamar wannan munafikin cikin.

Ita kuma Ameera tana mamakin ƙarfin halin sa ne ganin shi yaƙi ya dafa mata nata abincin amma shi ya zo zai fita ya je ya ci ita kuma ko ohoo ko! Dama ta yi wannan tunanin hakan ya sa tana shiga ɗaki ta yi saurin ɗaukar kii ta fito domin tare shi. Sun kai kusan minti biyar a haka kafin Adam ya ce “Ba ni hanya zan wuce? “Babu inda zaka je na faɗa maka, idan kuma kana son fita to ka tsaya ka dafa min abin da na ce maka sai ka je duk inda kake so ka sayo abincin ka.

Adam yayi shiru ya na tunani. Baida ƙarfi a jikinsa badan haka ba da sai yai mata dukan raba raini kafin ya fita abinsa, ga kuma yunwa da ke ta kiɗan amaja a cikin sa, ga har yanzu gabansa zafi yake masa. Sake kallonta ya yi ya ce “Dan Allah wace ce ke? Cike da mamaki Ameera ta ce “Ban gane ba wai ni ka ke tambaya? Adam ya ce “Dan Allah ke wa ce ce? Mai nai miki kike son kashe ni? “Cike da takaici da mamaki ta ce “Wai ko ka fara shan ƙwayoyin gusar da tunani ne? Au wai kai dama kallon da kake min kenan? To ni ce dai Ameera wacce ka sani. Cikin rashin sanin abin yi Adam ya juya ya koma ɗaki harda hawaye. Sai da ya shiga ɗaki amma ya fito ya sameta har lokacin tana Palo a zauna da alamar dai shi take fako, bai ce mata komai ba ya shige kicin ya tsaya yana tunanin dame-dame ma a ke buƙata idan za a yi Ɗanwake!

Ruwa ya fara ɗorawa sannan ya buɗe buhun fulawar da ko taɓawa ba’ayi ba, Nan take ya ɗaibi daidai da yanda ya ke tunanin zai masa, sai da ya juye a wata roba sannan ya zuba ruwa sai kuma ya fara tunanin anya ba’a zuba wani abu bayan fulawa? Shiru ya yi yana tunani, gashi kuma ya bar wayarsa a ɗaki kuma baya so Ameera ta taya shi. Gashi yana bukatar sanin wani abun, shi tun da kaye bai taɓa ko gwada yin ɗanwake ba, bai ma san dame-dame ake buƙata ba. Kaman zai yi kuka ya shiga tunani, lokaci ɗaya Haura ta faɗo masa arai ya ce “Ina ma tana nan! Ya daɗe a haka har ma ruwan ya fara zafi sai ya shiga dube-dube a cikin kicin ɗin, ganin babu sarki sai Allah ne yasa shi dole fita domin ɗauko wayarsa ya kira Khadija. Daidai zai fita ita kuma Ameera ganin ya daɗe a cikin ɗin sai ta biyo bayan sa ta gani ko ya fara yin ɗanwaken ne. A bakin ƙofar kicin ɗin suka haɗu ya wuce ba tare da ko yayi mata magana ba. Ita kuma ta ce “Ko ɗanwaken kake dafawa ne? Ta yi tambayar ta na shigewa ciki. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauki wayarsa ya kira Kadija amma ba’a ɗaga ba, yana ƙara kira ta ɗaga ta na faɗin “Yayana na kaina barka da dare? “Lafiya alhamdu lillah ya jikin na ki? “Jiki da sauƙi “

“Ok please ina so na tambayeki ne cikin gaggawa “

“Ok Yaya ina sauraronka Allah yasa na sani”

“Adam ya ɗan sai ta muryasa ya ce “Please dan Allah ya ya ake haɗa ɗan wake?

Shiru Kadija ta yi ta na jin tausayin yayan nata domin tasan wannan aikin Ameera ne a wannan daran da kowa ke so ya huta amma ita ta wani haɗa shi da yin ɗanwake. Afili ta ce “Yaya bari yanzu na dafa sai Najib ya kawo maka kaji? Adam yayi ssurin cewa “No har fa na ƙwaɓa fulawar kawai ki sanar dani ɗin yanzu pls. Kadija ta ce “Ok zan turo maka yanzu ta message. Ta faɗa ta na kashe wayar Adam kuma ya nufo kicin ɗin yana yi yana duba wayar tasa.

Yanzu ma daidai zai shiga itama zata fito riƙe da kofi ɗauke da tea mai zafi. A hankali ta ce sannu da aiki domin ta yi mamakin ganin yadda ya daɗa ƙwaɓar ɗan waken bai yi ruwa ba kuma bayi tauri ba. Ba tare da ya tamka mata ba ya shige yana jin ƙarar saƙo a wayar tasa. Kafin ya buɗe ya kalli gurin da fulawar take sai yaga an ƙwaɓa daidai yadda kawai sai dai a fara zubawa a ruwa. Kallon hanyar waje yayi yana jin taikaicin taimaka masa da ta yi. Haka ya shiga jefa ɗanwaken har ya gama sannan ya soya man gyaɗa, dama suna da yaji mai daɗi a ajiye, lokaci ɗaya shima abin ya shiga ransa ga wani ƙamshi dake tashi daga cikin man da ya sha albasa, a gefe guda kuma ga ɗan ƴen tumatur da albasar da ya yanka, sai kuma soyayen naman da ke cikin firiza shima ya ƙara soyawa. Tun tana Palo ƙamshin man da na naman ya cika mata hanci, har wani leƙe take yi tana Allah-Allah ya fito ta fara kaiwa bakinta. Haka ya fito da gabaɗaya abincin Palo sannan ya koma ya ɗauko mai da naman, sannan ya ƙara komawa ya ɗauko fleet da cokula masu yatsu. Sosai yake yin komai cikin sauri saboda yunwa da ke ta hautsuna halittun cikinsa. Sai da ya gama zubawa yana nufin miƙa mata amma tayi wani saurin fusgewa saura kaɗan ya zube tana ce ko nasa ne. Ita kanta sai da taji kunyar abun da ta yi.

Girgiza kai kawai Adam ya yi shima ya shiga haɗa nasa. Sai da ya gama zuba komai yana ƙoƙarin ƙara yaji yaji tana faɗin ƙara min wannan yamin kaɗan.

Kafin ya ce komai ta ƙara ɗauke na gaban nasa domin kuwa ɗanwaken yayi mata daɗi sosai. Ta ce “Ai dama kai taliya za ka ci ko? To kawai ka bar min sauran gobe da safe zan ci, in yaso Kai yanzu sai ka shiga ka dafa taliyar ta ka yanzu ka ji? Ameera ta ƙara sa ta na rufe sauran ɗan wake dake ruwa a robar. Cike da mamaki Adam ya ce “Ban fahimta ba, yanzu kina nufin sai na ƙara shiga kicin nayi girki bayan ga wannan da yawa? Ameera ta ɗago kai baki ce ke da ɗan wake ta ce “A’a dan Allah kar mu yi haka da kai! Kai fa ka ce taliya kake so ni kuma na ce ɗan wake kuma ni yanzu gashi ka min nawa ba sai kama ka yi naka ba. Adam ya kalli robar ɗan waken ganin ga ɗan waken da yawa ya ce “Na fasa cin taliyar tunda ai ke ce kika zubar da wacce na dafa ɗin nima yanzu wannan ɗin zanci. yana faɗa yana ƙoƙarin jawo robar gaban sa, amma Ameera ta yi saurin ɗora hannunta a kan robar ta ce “A’a kar mu yi haka wannan shine zanci har safe please kaima dafa naka ko kuma ka fita kaje ka sayo. Sosai Adam yake jin yunwa domin yana daidai gurin da zai iya sumewa tsaɓar yunwa. Haka ya na ji yana gani ya mike ya ɗauki wayarsa da makullin Mota ya fita cikin daren domin nemawa cikinsa abun da zai ci.

Yana tafiya hawayen azaba da na taikaci na zuba a idanun sa har bai san lokacin da ya bigi motar wani ba. Ai kuwa da sauri mutumin ya fito yana faɗa da zage-zage shima Adam ya share hawayen sa ya fito yana bawa mutumin haƙuri wanda ya haƙura badan yaso ba. Allah ya taimakeshi bai sha wahala ba domin gurin cin abinci ɗaya ya je ya tarar basu tashi ba. Sai da ya zauna ya cika cikin sa, kafin ya sayi wani ya nufo gida da shi.

Daidai yazo gurin da ya haɗu da su Haura wancen karan ya hango mutane biyu zaune kamar kuma mata. Kamar ba zai je gurin ba ya fito daga motar ya nufi gurin yana ɗan tsoro. Sallama ya yi yaji an amsa masa yana son ya ga ko dai Haura ce. Wasu ƴan matsan mata ne waɗanda baza’a kirasu yara ba kuma baza’a ce musu tsofi ba ne su biyu ya gani wanda hakan ya bashi mamaki ganin dare yayi. Adam ya ce “Bayin Allah me kuke yi anan a cikin wannan daran? Ɗaya daga ciki ta ce “Ai anan muke kwana bamu da gurin zuwa, muna da yawa harda yara yanzu haka wasu daga cikinmu ana zuwa ne a ɗauke su sai a dawo dasu da asuba.

Adam ya ce “A’uzubillahi! Almajiran ma haka ake muku? Ta ce “To yaya zamuyi haka rayuwa tazo mana da shi” Adam ya ce “Karki wa rayuwa ƙarya baiwar Allah kuma ai da goyan bayanku a keyin komai daku, idan baku yarda ba baza’a mu ta ƙarfi ba ko. Sai matan suka yi shiru.

Adam ya ce “Ina wata mata tsohuwa da ƴarta ana cewa ƴar Haura, kwanakin baya ina ganin ta anan amma yanzu bana ganinsu lafiya dai ko? Ɗaya matar da bata ce komai ba ta ɗago ta kalli Adam ta ce…

“Itace kaɗai yarinya mai hankalin da bata yarda da bin kowa amma itama wani mai mota yazo ya tafi da ita wanda itama tun lokacin babu wanda ya sake ganin ta, daga baya ma mahaifiyarta ma ta fita, to har yau bamu ƙara jin ɗuriyar su ba. Adam ya ce “To Allah ya ƙara tsarewa. Suka amsa da Amin sannan ya ɗauko wannan abincin ya ajiye musu ya zaro kuɗi ya miƙa musu yana tausayin irin wannan rayuwar. Azuciyarsa ya ce to ina yaransu! Ko ba su da ƴaƴa ne? Haka dai ya ƙara so gida yana saƙe-saƙe a game da rayuwar waɗannan bayin Allah, wanda ya gudurta a ransa cewar zai taimakesu.

Wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin kayan barci, sai dai yana kwanciya Ameera ta shigo ta na faɗin “Tun ɗazu ina jiran ka a Palo amma dan wulaƙanci shine kana ganina zaka shareni ka wuce ko Adam?” Adam ya bita da wani irin kallo domin kuwa babu komai a jikinta daga ita sai wandon ciki sai rigar mama ga ƙaton cikinta da yake jin kamar ya soka masa wuƙa ya sace kowa ya huta! “Aiyya sorry ban kula da ke bane”

“Ai dama ba zaka kula ba tsabar wulakanci ai ko baka ganni ba zaka shiga ɗakina ka duba ko lafiya nake. Ta ƙara sa tana hawowa kan gadon, ta na zuwa ta faɗa kansa wanda cikin nata ya tokare Adam ɗin. Kwantawa tayi a jikinsa ta ce “Honey ina fa buƙatar ka sosai a tare dani Allah”

Cikin sauri Adam ya ce “Amma kinsan dai bana da lafiya ko? Kuma ke ce kika jawo komai. Ameera ta ce “Ba ka da lafiya na me? Wai har yanzu abun bai ware ba ne? Ta faɗa tana miƙewa daga jikin sa ta na ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ta gani. Da sauri Adam ya miƙe zaune ya ce “Please honey wallahi babu abun da zata iya, rokon Allahn da nake yi Allah yasa baki jawo min wata matsalar a gurin ba. Ameera ta ce “To wai ka tsaya na gwada dabara ko zata tsaya mana. Ta ƙara faɗa tana ƙara kai hannu a karo na biyu gabansa. Adam ya ƙara rike hannunta ya ce “Babu abun da zan iya wallahi har yanzu zafi yake min ba na ko so a taɓa please kiyi haƙuri. Cike da ɓacin rai ta ce “To ai laifinka ne ka bari na kwada ka gani ƙila ma idan aka yi shikenan ta ware kuma ka samu sauki kawai bari ka gani Allah zaka iya ai ba komai ba ne. Ta ƙarasa tana cire masa kayan jikin sa, sai da tazo kan wandon Adam ya ƙara cewa “Please honey please?” Ameera ta kawar da kai ta na faɗin “Wai wannan wani irin abun kunya ne dan Allah Honey, kaman wacce zata yankaka ko zan maka kajiya? Kawai fa raya sunnha zamu yi. Tana faɗa ta cire wandon wanda sai da Adam ya saki ƙara domin yaji zafi sosai…

<< Ameera Da Adam 13Ameera Da Adam 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×