Skip to content
Part 16 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Kallon abun nasa ta tsaya yi ganin yanda suka koma kaman na yaro ƙarami, sai kuma ta kalleshi ganin yadda ya rufe ido alamun kunya. Afili ta ce “Wai mai nake gani haka ne Honey? Tana faɗa ta sakko daga kan gadon ta na jin haushin abun da ta gani ɗin. Ganin ta fita daga ɗakin ne yasa Adam mayar da kayansa ya kwanta yana jin kamar ba daidai yake ba. Sosai ya kwanta yana tunanin abubuwan da Ameera tai masa daga samuwar wannan cikin kawo yanzu.

Ya tuna dukan da yasha a hannun soja, ga wuƙa da ta soka masa, gashi yanzu ta kashe masa gaba, ga abun da taiwa Khadija, ga kashe mahaifiyar Haura da tayi, ga dukan ita Hauran, ga ƴan aiki biyu da suka gudu daga gidan tsabar masifa da bala’i. A haka har barci ya ɗaukeshi ba tare da ya sani ba.

Da safe tunda ya tashi Sallah ya shiga haɗa kayansa a cikin ƙaramar jakarsa, sai da ya kwashi duk abun da yake so sannan ya zuge jakar ya ɗauka ya kai bayan motarsa, sannan ya dawo ya ƙara duba duk abin da yake buƙata. Sai da ya gama koshe komai sannan ya ɗaura alwala ya fara nafila kafin lokacin sallar ya ƙarasa. Bayan ya idar ne ya ɗaga hannu yana riƙon Allah ya raba shi lafiya da wannan cikin na Ameera, Allah yasa ta haife cikin yau. Sosai tsabar ruɗewa ma har bai ma san abun da ba zai yiwu ba ma yake roƙon Allah.

Bayan ya gama ya ɗauki biro da takarda ya rubuta mata message ya ajiye a bakin gado sannan ya je gaban hotonsu shida ita dake cikin ɗakin ya ɗauka ya zubawa ido yana jin hawaye na zubowa daga cikin idanun nasa.

Gogewa yayi kafin ya bar gurin ya nufi hanyar fita. Sai da yazo palo sai kuma yayi tunanin zuwa ya duba ta, amma sai ya tuna cewa yanzu haka ta tashi kuma baya so ta ganshi. Hakan yasa kai tsaye ya fita daga gidan yana zuwa ya nufi gurin mai gadi dake alwala ya ce idan ya idar ya bude masa get.

Bayan ya sanar da shi ya dawo cikin motar ya zauna yana tunanin ina zai je. Lokaci ɗaya tunanin zuwa garin su Haura ya faɗo masa, sai kuma ya girgiza kai domin bai san hanya ba. Sai kuma tunanin zuwa hotel, shima yaga hakan bai masa ba. Yana cikin wannan tunanin yaji mai gida ya na buɗe get d’in. Sai da ya tashi motar yazo har bakin get kafin ya ƙara juyowa ya kalli gidan yana jin wani irin kewar gidan nasa na ƙara kamashi, a haka ya bar gidan saida yayi nisa sosai kafin ya tsaya a wani masallaci ya bisu Sallah kafin ya ɗauki hanyar barin cikin gari.

Ɗanwaken jiya ta ɗauka da niyyar ɗumamawa amma ko da tayi ido biyu da shi sai taga ya fita a ranta, ga kuma yunwa da da take ji. Palo ta fito tana addu’ar Allah yasa Adam yayi musu girki, sai dai tana zuwa taga babu komai a gurin cikin abincin. Ganin haka yasa ta nufi cikin ɗakin nasa ranta a mugun ɓace. Tana shiga ta fara kiran sunan sa amma jin ba’a amsa ba ne yasa ta nufi cikin toilet tana ɗan kiran sunansa. Sai da tazo bakin gadon zata zauna sai taga takarda hakan yasa ta ɗauka gabanta na faɗuwa. Kasa buɗewa ta yi sai ta tsaya tana kallon ɗakin ganin an kwashi kaya da dama a cikinsa. Juyawa tayi ta bar dakin izuwa nata ɗakin tana tafiya kamar mara lafiya. Sai da taje ɗakinta sannan ta zauna tana tunanin mai Adam yake nufi ne? Ya saketa kome! Sosai ranta ya ƙara ɓaci hakan yasa ta nufi ƙofar gida tana kiran Baba mai gida. Yana isowa ta ce “Yaushe ya fita daga gidan nan? Baba mai gida ya ce “Ai hajiya tun da asuba ya bar gidan da Mota, domin yau ba a yi sallar asuba da shi ba. Cike da ɓacin rai Ameera ta lailayo zagi ta maka wa Baba mai gida. Ta ce “Ɗan kaza-kazan ka shine baka zo ka sanar da ni ba har ka barshi ya tafi? Ta shi daga gabana dalla Malam. Ameera ta ƙara sa tana barin gurin cikin ɓacin rai. Sosai baba mai gida ya ji zafin zagin da Ameera tai masa, hakan yasa ya fara kuka, da zarar ya tuno irin zagin da tai masa wanda tun da yake ba’a taɓa masa irin su ba, sai hawaye ya zubo masa.

Wayarta ta ɗauka ta shiga kiran sa amma bata shiga, sosai take mamakin abun da Adam ɗin yayi, takardar da ya ajiye ta ɗauko tana son buɗewa ta karanta amma tana tsoro. Nan take ta shiga boɗewa zuciyarta na tabbatar mata da cewar Adam ba zai iya sakin ta ba, ko dan wannan cikin dake jikinta. Tana fara buɗe wa taci karo da jan rubutu hakan yasa tayi saurin ruɗewa ta ajiye takardar tana riƙe ƙirji. Take ta tuno watarana da Adam ya taɓa sanar da ita cewa baya yin rubuta da jan biro idan kuwa yayi to tabbas ba abu mai daɗi zai rubuta ba. Lokaci ɗaya taji ta daina jin yunwar sai ta koma ɗaki ta zauna tayi shiru! Chan ta miƙe ta saki wasu lafiyayyun tsaki tana fadin “Aikin banza duk nabi na damu kaina, ai nasan Adam ba sakina yayi ba, kuma zai dawo ya same ni sai ya sanar dani ina ya tafi bai sanar min ba. Sosai ta dawo da walwalarta kamar da, ta shiga kicin ta ɗauko supar commando mai sanyi haɗi da Keck ta zauna ta sha kayanta sosai.

Wasa-wasa har bayan sallar la’asar babu Adam babu dalilin sa, hakan yasa ta ƙara gwada layinsa a karo na uku amma bata shiga ba. Tun safe babu abun da taci sai kayan sanyi tsabar ƙyuiwayr yin girki. Haka dai Adam har dare layin sa baya shiga shima bai dawo ba. Bata gama shiga mamaki ba sai da taga har dare babu Adam. Nan fa hankalin ta ya tashi domin bai taɓa yin irin hakan ba, duk yanda ta kai da ɓata masa rai to a gida zai kwana. Sosai take ta faman kiran lambar sa amma a kashe. Tana son kiran Najib ko Khadija ta tambayesu amma duk ta goge lambobin su a wayarta a cewar ta wai bata da amfani domin su din munafukai ne.

Haka Ameera ta kwana cikin zulumi da fargoba, da safe ta fito tana ƙwadawa mai gida kira kamar ita ta raɗa masa sunan, sai dai har ta ƙara sa bataji an amsa mata ba, hakan yasa ta tattaro duk wata ɓacin ranta ta shiga dukan ƙofar da ta gani s a rufe. Ganin kamar babu mutu a cikin ne yasa ta juya a fusace zata koma sai idonta ya sauƙa a kan wata ƙaramar takarda a danneta da dutse. Cike da mamaki ta ɗauka ta fara karantawa (“Na so ace na tafi ba tare da na sanar wa da kowa ba, amma naga yin hakan bai da ce ba,shine yasa na samo yaro ya rubuta muku wannan takardar, ngd da komai, amma ba zan iya zama ƴar cikina tana zagina saboda ina neman a ƙarƙashin su ba. Saboda da haka na tafi na barwa Allah komai shi zai taimaka min, ina godiya wa Alhaji) tana gama karantawa ta saki murmushi haɗi da faɗin. “To dama ni banga wani amfaninka a gidan ba, wai shine harda bayarwa a rubuta saƙo dan rashin kunya. Take ta yayyaga takardar ta koma ciki tana mamakin wannan tsohon.

Kwana huɗu kenan yau babu ko labarin Adam ita kuma ta kasa sanarwa da kowa hatta iyayenta, gashi a cikin kwana huɗun nan sai taji kamar ana mata motsi a cikin gidan hakan yasa yau ta shirya domin zuma gidansu Khadija daga nan ta je gidansu. Sosai take damuwar rashin mijin nata, kana kallonta zaka hangi damuwa cike fall a fuskar ta. Tafiya ta ke yi tana hawaye har ta zo bakin get ta tsaya tana kallon get d’in dake rufe wanda tasan ko me ta ci bazata iya buɗewa ba. Ƙaramar ƙofar ta buɗe ta fita sannan ta rufe ta waje, mai keke napen ta tsayar ta shiga tana sanar da shi gurin da zai kai ta. Bayan an kawo ta gidan su Kadija ne ta biya mai keke sannan ta nufi cikin gidan. Ƙaramar ƙofar gidan a buɗe take hakan yasa kawai ta shige ciki ba tare da ta iya ko sallama ba. Maigadi na ganinta ya taso ta sauri yana tambayar wace lafiya.

Amma ko ta kansa bata tsaya biba. Ganin da gaske tafiya take yasa mai gadin saurin shan gabanta ya na faɗin “Malama wace ce ke? Me kike nema? Ameera da bata jin zata iya masa magana ta ɗan raɓa zata wuce ya ƙara tare ta, ai kuwa ya buɗe baki zaiyi magana ta sauke masa yatsu biyar a kuncinsa wanda yasa shi saurin komawa gefe cike da mamaki, kuma sai a lokacin ma ya gane ta.

Tana shiga gidan taci karo da Najib ya na ƙoƙarin fitowa. Komawa da baya yayi ita kuma ta bi shi da harara. Daidai lokacin kadija ta biyo shi da hula tana faɗin “Yaya na zo ka sauya wannan hular zata fi dacewa da kaya. bata ƙara sa ba ta gansu tsaye curko-cirko hakan yasa ta ce “Ameera a gidan mu yau? Ta yi maganar cike da mamaki. Ameera da abun da Khadija din tayi ya bata haushi ta ce “Honey nazo nema ina kuka ɓoye shi? Najib da Khadija suka kalli juna kafin Najib ya ce komai kadija ta ce

“To fa sabon salo waye kuma Honey kamar sunan tsuntsaye? Cike da jin haushi domin tasan wa take nufi amma take faɗa mata magana, ganin kamar suna don raina mata wayo ne yasa ta tafi kanta tsaye ga abun da ya kawo ta. Ta ce

“Koma sunan tsuntsaye ne kona dabbobi wannan ke ya dama, yanzu dai abin da ya kawo ni shine ina kuka turashi yau kwana huɗu babu shi babu labarin sa, haka lumbsrsa itama bata shiga kuma nasan kune kuka zuga shi a kan ya bar gida, idan ma yana nan gidan ne to ku fito da shi mu tafi.

Najib ne yayi saurin faɗin”Wai Adam ɗin ne kwana huɗu baya gida kuma number sa bata shiga? Najib yayi tambayar cikin mamaki domin ko jiya sun yi waya da shi kuma ya ce ya na gida. Khadija ta ce “To Kinga laifin sa? Haka kawai ya tsaya a kashe shi babu laifin komai ba ƙara ma ya bar gidan yaje gun da zai huta ba. Najib ne yayi saurin dakatar da Kadija ya kalli Ameera ya ce “Kinga zauna muyi magana, bari na kira miki shi, mu ai bamu san baya nan ba.

Kira ɗaya Adam ya ɗaga yasa wayar a amsa kowa. Adam na ɗagawa Najib ya ce “Gani a ƙofar gidan ka Allah yasa kana ciki? Adam yayi jim ƙadan kafin ya ce “Eh shigo ina ciki. Sai Najib ya ƙara cewa “Ina fatan Ameera ma tana ciki ko? Adam ya ce “Idan ka shigo sai ka gani sarkin tsoro! Yana faɗa ya kashe wayar.

Ameera da ta yi mutuwar tsaye tun da a ka fara wayar ta ce “Wai yana gida da gaske? Khadija ta ce “Wai anya kuwa Ameera kanki ɗaya kuwa? Ko dai kin fara hauka ne, kai gaskiya inaga wallhi aljannu sun shafe ki ne, a she ma mijin naki na gida kika fito kina neman sa. Najib ya ce “Kinga ta shi muje gidan. Khadija ma ta yi wuf ta ce “Wallahi nima sai naje. Ameera kan ita birninta kawai tayi ido biyu da rabin ranta. Motar NAJIB ɗin suka shiga Ameera na jin kamar baya gudu. Suna zuwa bakin get d’in gidan Najib yake ta hom amma shiru, ita kuwa Ameera da tsabar zumuɗi ta manta da cewar babu ma mai gadi a gidan. Najib ne da kansa ya sauƙa ya buɗe get d’in suka shiga da motar. Abun da ya fara baiwa Ameera mamaki shine motar Adam da ta gani a fake a gurin fakin. Sai da ta rufe idonta ta buɗe kafin ta ƙara sa gurin motar ta shafa ta. Ita dai Kadija sai taɓe baki take yi cike da jin haushin Ameera ɗin.

Basu ƙara ruɗewa sai da tayi ido biyu da abun da ya tsayar da jin su da ganinsu na lokaci ɗaya daga Ameera har Najib. Suna shiga palon suka tarar da Adam zaune a ɗaya daga cikin kujerun cikin palon, sai Haura da ke kusa da shi ita da Amminta suna cin abinci cikin natsuwa. Shi kuma Adam yana latsa wayar hannunsa. Jin sallamar su yasa duk suka ɗago suna kallon ƙofar.

<< Ameera Da Adam 14Ameera Da Adam 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×