Skip to content
Part 12 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Kasa ƙarasawa cikin palon ta yi ta tsaya tana kallon Haura da ta mai da hankalinta gurin cikin abincin ta. Najib ne ya yi ƙarfin halin magantuwa ya ce “Adam mai zan gani haka? Wannan ba wannan matar da ta rasu ba ce? Adam ya kalli Ammin Haura ya ce “Ba ita ba ce ƴar uwarta ce, ai waccar ta mutu ko dama ana mutuwa a dawo ne? Najib ya ƙurawa matar ido yana jin sam bai yarda ba wallahi waccer matar ce ga shi komai nasu iri ɗaya. Adam ya ce “Kaga nai mi guri ka zauna karka ruɗar da kanka. Najib ya ƙara so ya zauna yana son yin magana amma ganin idon Haura a kansa sai kawai yayi shiru, itama Khadija ta shiga ta zauna idonta a kan Haura da matar da Adam ya ce ƴar uwarta ce. Sai a lokacin Adam ya kai kallonsa izuwa ga Ameera wacce ta yi suman tsaye gabanta na faɗuwa tana jin kamar mafarki. Adam ya ce “Honey ƙara so mana kin tsaya kina ta kallon mu kamar kinga baƙi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Haura ta gefen ido sai ta ga yarinyar ta ƙara girma da haske ga kuma wani kallo da taga yarinyar na mata. Bata tsaya a palon ba sai kawai ta wuce ɗakin Adam ɗin tana zuwa ta zauna a bakin gado ta fashe da kuka. Sosai take kuka tana jin wani abu na kishi na sokar zuciyarta.

Acikin palo kuwa Najib ne ya sauya haurshe izuwa turanci ya ce “Wai Adam mai yasa baka da hankali da tunani ne? Yanzu me ye amfanin sake dawo da waɗannan mutanin cikin gidan ka, kai kasan halin matarka amma sam baka tsaron wani abun ya ƙara faruwa ko?

Adam ya ce “Ba zaka gane bane, yanzu haka yarinyar bata da kowa a duniya domin ƴan uwanta sun koreta, kuma wannan yarinyar mune sanadin rasa mahaifiyarta sai kuma mu barta ta shiga duniya ta lalace? Cikin ɓacin rai Najib ya ce “To idan taimakon su kake so ka kama musu wani gidan mana, dole ne sai ka kawo su cikin gidan ka, wai Adam mai yake damun ka ne, anya kuwa ƙalau kake Adam. Cikin nuna tabbacin zaman su Haura ya ce “Gida dai nawa ne ko? Kuma ni ke da ikon aiwatar da komai a ciki gidana ko? Sai a lokacin Khadija ta ce “Haba Yaya gaskiya hakan bai dace ba, mai laifin ka kai su wani gidan sai ka ɗauki nauyin su amma ba ka kawo su cikin gidan ka gurin da matarka take ba, kuma kai kasan halin da matarka take ciki please ya ya dan Allah ka duba wannan shawarar da Najib ya ba…” “Ya isa haka naji dan Allah ku tashi ku fita ina son hutawa, a kwai dalilina na yin hakan. Najib na jin haka ya tashi ya ce “Adam mu kake kora a gidan ka? In sha Allah kuwa ka kori ɗan halak. Yana faɗa ya bar gidan cikin ɓacin rai, itama Kadija tafi bayan sa ta na leƙen Adam kamar karta ta fi ta barshi. Suna fita ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune ya na tunanin hukuncin da yake so ya yanke.

Sosai yake ta nazarin komai yana jin wannan shine abun da zaiyi ya taimaki su Haura. Haura ce ta miƙe ta ɗauki jakar su itama matar ta miƙe suka nufi ɗakun Haura ɗin. Suna shiga matar tabi ɗakin da kallo cikin yaransu ta fara magana “Yanzu a nan zamu zauna? Dama anan kike tun tuni shine ba ku nemo ni ba. Ta yi tsalle kamar ƙaramar yarinya ta hau kan gadon tana dariya. Haura kuwa toilet ta shiga ta yi wanka ta fito ta saka doguwar rigar daga cikin kayanta sannan ta nufi kicin domin fara girki. Sosai take girkin tana hawaye, idan ta tuno da amminta. Lokaci yayi da zata aiwatar da burinta sannan ta bar musu gidan sai ta gama lalata komai tsakanin Adam da Ameera kafin ta tafi domin ba zata iya yafe abun da a kai musu ba.

Ɓangaren Ameera kuwa tsabar kuka yasa kanta fara harbawa tana jin cikinta na juyawa kamar wanda zai fita. Ganin babu sarki sai Allah ne yasa ta kurma ihuu tana faɗin “Waiyoo cikinta. Da sauri ya faɗo cikin ɗakin yana kiran sunanta. Yana zuwa ya ƙara so kusa da ita yana tallafo ta da hannayen sa. Sosai Ameera ta fita a haiyacinta har bata san lokacin da Adam ɗin ya kinkimeta izuwa Mota ba. Asibiti suka nufa yana gudu yana mata sannu.

Zauna yake a gaban likitan bayan ya gama zaiyana maso komai na cewa a daure a lallaɓata domin idan ba haka ba za’a illata abun da ke cikin nata, domin ta kusa rabuwa da shi. Haka dai lokacin ya faɗa masa cewar ba komai bane kawai damuwa da tunani ne ya haifar mata da ƙunci har cikin nata ya mata wannan irin ciwon. Haka Adam ya fito daga gurin likitan yana jin cewar ko me zai faru sai ya faɗa mata burinsa domin shi yanzu harga Allah ta fita masa a kai kawai hakan za’a yi. A kan hanyarsu ta zuwa gida ne yaga taƙi ko kallonsa shima yayi kamar bai ma san da ita a gurin ba. Ita Ameera tana tunanin wai tun lokacin da ya tafi dama gurin su Hauran ya je ko yaya! To yanzu da ya dawo dasu mai yake nufi? To ita uwar yarinyar ma ba ance ta mutu ba me ya dawo da ita? Sosai kanta ya kulle ga wani haushin Adam ɗin da take ji, ji take tana buɗe baki uwarsa da take kushewa zata zaga.

Shi kuma Adam tuni ya faɗa tunanin yadda zai faɗa mata cewar yana son ya auri Haura ne domin shine kaɗai abun da zai mata ya biyata abun da sukai mata. Suna isa Ameera ta kama ƙafar motar da niyyar budewa amma ta jita a rufe, ta juyo ta kalleshi amma taga ya haɗe fuska ko kallonta baya yi, itama bata ce komai ba sai idonta da ya ciko da ƙwalla tana ƙoƙarin fashewa da kuka. Bai damu ba domin shi dai zuciyarsa ta cika da son auran yarinyar da take masa gizo a ko da yaushe. Ya ce “Magana nake so muyi? Ameera ta yi shiru. Ya ƙara cewa “Dake fa nake magana Ameera?

Da sauri Ameera ta ɗago ta kalleshi jin sunanta ɓaro-ɓaro a bakin sa. Take hawayen da take tarewa suka zubo ta ce “Ba na bukatar jin komai daga gareka, ka buɗe min ƙafa zan fita.

Adam ya ce “Ok tom bari mu shiga cikin gidan sai muyi maganar a can. Da sauri ta fito tana kuka sosai tana so tayi guda amma jikin ta babu ƙwari ga cikin ta da yayi nauyi. Tana shiga palon wani ƙamshin abinci ya daki hancinta wanda yasa ta saurin kallon hanyar kicin. Haura ce sanye da doguwar riga gashi kanta babu ko ɗan kwali sai dai ta yi pakin kan da ribob, hakan yasa ta yi wani kyau wanda ko ita Ameera ɗin sai da yarinyar tai mata kyau. Cikin ɓacin rai da kuka ta ƙara so gurin Haura ta chakumeta ta baya suka faɗi a ƙasa Amera ta fara kuka tana dukan Haura akan sai ta bar gidan mijinta. Ana cikin wannan halin Adam ya shigo da sauri ya ɗaga Ameera yana ture ta gefe ya ɗaga haura yana mata sannu.

Ganin haka yasa Ameera ƙara fashewa da kuka tana faɗin “Allah ya isa tsakanina da kai Adam, wallahi bazan yafe maka ba , mugu macuci azzalumi, ke kuma sai na ga bayan ki shigiya maiya. Ana cikin haka matar da suka zo da Haura ta fito da sauri tana tambayar Haura lafiya dai ko? Kafin kowa ya ce komai Ameera ta ce “Ubanki ne ya faru, ke ba kin mutu ba uban me ya dawo da ke? Matar cikin yaransu tayi magana tana kallon Haura wacce itama ranta ya ɗan ɓaci “Idan kin isa kiyi maganar da Hausa ko da turanci mana yadda zan ji, da na ci ubanki yanzu a gurin nan. Ganin haka yasa Adam saurin kama hannun Ameera suka nufi dakinsa yana bata haƙuri. Suna shiga matar ta hau Haura da faɗa cikin yaransu kamar zata mareta, ita dai Haura sai hakuri take bata, kai tsabar masifar matar harda murɗewa Haura kunne tana ƙara jaddada mata komai.

Suna shiga ɗakin ta ƙwace hannunta ta ce “Malam mutukar kana son zaman lafiya to ka kori wannan matar da uwarta, sannan tun ranar da ka bar gida ina ka tafi sai yanzu? Ba ka kirani ka sanar dani zaka tafi ba, sannan baka sanar dani dawowar ka sai kawai na ganka tare da su? Adam ya ce “In ji wa ban sanar dake ba, na ajiye miki saƙo kuma nasan kin duba, kuma ko mene ne ai ke kika jawo. Ba ni da lafiya amma kince sai na kusance ki fisabililahi kin kyauta min kenan? Ameera ta ce “To yanzu dai kawai ka kori wannan yarinyar please? Adam ya ce “Kin manta da cewar Ke ce kika yi sanadiyar mutuwar uwarta, idan na koreta ina zata je? Ameera ta ce “Nifa banyi sanadiyyar mutuwar kowa ba, sannan ita wannan matar wacece idan ba uwar tata ba?

Adam ya ce “A’a ba ita bace ƴar uwarta ce Kum..” kafin ya ƙara sa Ameera ta tareshi cikin mamaki ta ce “Ƙarya suke maka wallahi ita ce, na rantse da Allah waccer matar ce, karka yarda da su munafukai ne. Sosai Ameera take rantsuwa tana faɗin munafukai ne. Ganin haka yasa Adam faɗin to koma suwaye zan zauna da su. Ameera ta kalleshi ta ce “Adam ka dawo hankalinka idan ma baka da shi. Kafin ta ƙara sa ya ce “Auran yarinyar nake so nayi domin na taimakesu. Shiru ɗakin yayi Amera na jin Kamar ba daidai ta ji ba. Adam ya ci gaba”Dan Allah ki bani goyan baya , zan Auro tane domin ta dinga taimaka miki da aikace-aikacen gida please Honey Karki tada hankalin ki?

Ɓangaren Najib da Khadija kuwa suna isa gida Najib ya ce “Khadija tabbas Adam ba a cikin haiyacinsa yake ba, wallahi a kwai matsala ina tsoron ko ba wani abu su kai masa ba, naga gaba ɗaya ya sauya. Khadija ma ta amsa da cewar “Nima abun da ya ke ta min yawo kenan, shima yaya mai ya kaishi shiga sabgar su, yanzu Allah ne kaɗai yasan abinda sukai masa wallahi, ni harna fara tausayin Ameera kar su rabata da mijin ta. Najib ya ce “Nasan abun da zan yi ina zuwa. Yana faɗa ya fice daga gidan.

Ameera ta ce “Mai ma ka ce? Ya ce “Haura nake so na aura kuma cikin wannan satin, ba shawarki nake nema ba na sanar miki ne saboda kinada hakkin sanin hakan, idan kina da bukatar wani abu ki sanar dani domin ba niki za’a yi ba, mun gama magana da su.

<< Ameera Da Adam 11Ameera Da Adam 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.