Ɓultuwa ta yi tambayar cike da nunu ɓacin ran da suke ciki. Da sauri Adam ya juyo yana bin su da kallon mamaki domin shi harga Allah ya manta da su. Haura ya kalla ya ga tana wani cin magani sai kawai ya ce “Ku yi hakuri na manta ne, amma yanzu kuzo mu shiga ciki. Haka Adam ya buɗe get ɗin suka shiga shima ya mara musu baya da motar tasa. Su na shiga Ɓultuwa ta ce da Haura “Kinga yanzu ke matarsa ce, sabo da haka ki je ɗakinsa ki yi wanka idan yaso sai ku fara maganar kafin na zo, kar ki ji tsoron waccer matar ta sa domin yanzu duk ɗaya kuka kin ji dai ko? Haura ta amsa da kai. Hakan kuwa aka yi, ɗakin Adam ɗin ta shiga cikin sanɗa dukda tasan baya ciki amma sai ta tsinci kanta da fargaban aiwatar da hakan. Tana shiga ta ga babu kowa a ciki, ga kuma ɗakin ba’a gyare yake ba kamar ma dai yau ba’a kwana a cikinsa ba. Haka ta shige toilet duk jikinta na rawa, ta na shiga ta fara cire kayan ta, sai da ta yi tsirara kafin ta sakar wa kanta ruwan sanyi ta na lumshe ido gami da sauke ajiyar zuciya ta na godiya ga Allah da yasa yau ta zama matar Adam.
Yana shiga palon gidan nasa ya nufi ɗakin Ameera domin a ce yake so ya yi wanka, sai dai yana shiga ya fito dalilin ganin ɗakin ba’a gyare ba, nasa ɗakin ya nufa cikin farin cikin yau ya zama baba. Yana shiga ɗakin ya shiga cire kayan sa sai da ya gama yin zindir kafin ya tura ƙofar toilet ɗin ya shiga ɗauke da addu’ar shiga bayan gida (“A’uzu bika minal kubusu wal-kaba’isu)
Ɓangaren Malam kuwa ganin har zuwa lokacin Adam bai dawo ba ne ya sa ya ce “To ko wani zai karɓa masa wakilcin yarinyar a ɗaura suran ne?, sai kuma Malam ya tuna bai san sunan yarinyar ba. Haka dai akai ta jiran Adam amma shiru, ga kayan ɗaurin aure amma babu ango kuma babu wakilin sa, haka dole Malam ya bada haƙurin cewa ina ga dai ba lafiya ba ne. Haka kowa ya watse ba tare da ɗaurin auran ba.
Yana shiga toilet ɗin Haura ta juyo a tsorace dalilin jin karatun da yayi, hakan yasa shima saurin tsorata dalilin da yasa suka haɗa goshi bata tare da kowa ya an kara ba. Ganinsa tsirara yasa Haura saurin juyawa ba tare da itama ta rufe komai daga jikinta ba. Shima Adam ɗin cikin tsoro da mamakin ganinta a cikin toilet ɗin sa ya sa ya yi kamar zai rusa ihu! Sai kawai bakinsa ya shiga furta “Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raju’un! Yana faɗa yana kallon yadda ta juya masa baya, shima.
Sai neman shagala da kallon bayan ta da yaso yi, amma jin ya na ƙoƙarin kasa saita kansa ne ya sa ya juya ya fita daga toilet ɗin ba tare da ya biyewa ɗaya gada cikin zuciyar tasa dake angiza shi taɓa wani sashe na jikin ta ba. Tana jin ya fita ta sauke a jiyar zuciya tana ɗaura tawul da niyyar fitowa. Sai da ta fara leƙowa ta ga baya cikin ɗakin kafin ta fito da saur ta buɗe ƙofar zata fita shi kuma ya kama zai buɗe ya shigo. Tana buɗewa suka ƙara cin karo har sai da tawul ɗin jikinta ya kunci, amma ta yi saurin taro kayan ta tsaya ta na kallon sa ganin sa shima ɗaure da tawul ya na kallonta da duk ta rikice. “Mai ya kawo ki cikin toilet dina yin wanka? Adam ya watsa mata tambayar yana bin jikinta da ke rawa da kallo. Sai yanzu yake ƙara tunano lokacin da ya fara ganinta tsirara, sai yau da ya ƙara ganin ta. Jin ta yi shiru ne ya ƙara ce wa “Tambayar ki na ke” Haura ta ce “Wanka nazo yi saboda naga nima matarka ce yanzu shi ne kawai. Cikin ɗan mamaki ya ce “Mata kuma matar wa?! To ya kika zama matar ta wa? Lokaci ɗaya gaban Haura ya fadi domin ba yadda ya saba mata magana ya ke yi yanzu ba, wannan karan Adam ne a gaban ta. Ganin haka yasa kawai Ɓultuwa ta ke son gani domin ita tasan san abun yi. Hakan yasa ta raɓa ta jikin sa har suna gogar juna ta nufi ɗakin su.
Tana zuwa ta sanar da Ɓultuwa cewa ba’a fa ɗaura auran ba. “Cikin tashin hankali ta ce “Kamar ya ƙarya ne wallahi an ɗaura. Haura ta ƙara cewa “Babu alamar ma fa yasan da wani batun aure ma fa. Ɓultuwa ta kalli Haura ta ce “Ina ce dai ita shigiyar matar ta sa tana cikin gidan? Haura ta amsa da “Babu alamar tana cikin gidan, anya ma kuwa ba haihuwar ta yi ba. Da ƙarfi Ɓultuwa ta ce “haihuwar uwarki! Wallahi ba zamu ga wannan baƙar ranar ba, ta ma isa ta haihu ban sa ni ba. Haura dai ta shiga sauya kaya cikin rawar jiki. Ita dai Ɓultuwa sai sake-sake da kwance-kwance ta ke. Idan har haihuwar Ameera ta yi kenan shikenan asirin ya tonu kenan, ita Haura zata san gaskiya, kuma mutanen garin Ƙaruk ma zasu gano ta. Sanin dukkanin sirrukanta ya dangana ne da haihuwar Ameera, lokaci ɗaya ta fara tunanin kashe Adam ɗin shi da Haura sai ta gudu, amma sai ta tabbatar da cewar Ameera ta haihu.
Yana wanka yana tunanin maganar Haura wai ta zama Matarsa, ko mai take nufi ohoo! Bayan yayi wanka ya shirya ya fito daining tebul ya zauna ya na jiran fitowar Haura ta kawo masa abinci. Yana zaune sai gata sun fito ita da Ɓultuwa sun nufo gurin sa. Sai da suka gaida shi kafin Haura ta shiga kicin ta kwaso abun da suka dafa ɗin. Haka suka shiga cikin abincin su uku ba tare da kowa ya ce komai ba, sai Adam da ke dana waya yana murmushi! Ɓultuwa ce ta yi gyaran murya ta ce “Uhumm ahamm! Ya batun auran jinyan an ɗaura ko dai an ɗaga ne?. Adam ya kalleta domin maganar da ƙarfi ta yi. Adam da yake so sai ya gama cin abinci ya nai mi ƙarin haske sai kuma ga shi an hutar da shi. Ya ce “Wai wani aure kuke maga na a kai ne? Ban ga ne ba, munyi maganar aure da ku ne? Nan take Ɓultuwa ta rikice domin tabbas lissafi ya kwafce mata. Ta ce “Jiya kai ne ka kaimu gurin gyaran jiki ka ce zaka gurin ɗaurin aure idan ka dawo zaka zo ka ɗaukomu shi ne ba ka dawo ba.
Da ƙarfi Adam ya bigi teburin abincin wanda sai da duk sauran abincin da ke gurin ya zube. Ya ce “Karna ƙara jin wannan banzar maganar domin ban san anyi haka ba, kuma ni na ɗauki Haura domin na taimaka mata ne, muddin na sake jin wannan zancen sai kun bar min gida, wannan wani irin shirme ne haka. Haka Adam ya bar gidan cikin tsananin ɓacin rai. Koda ya koma asbintin Ameera bata farka ba, sai kawai ya nufi gurin yaran yana kallon su cikin so da ƙauna. A haka har Najib da khadija suka shigo ɗakin. Sosai Khadija ke murna tana kallon yaran nata. Adam ya kalli Najib ya ce “Wai Ka ji wani shirme da yarinyar nan dake aiki a gida na wai ni ne nai mata alƙawarin aure? Najib cike da mamaki ya ce “Eh ai gaskiya ne, nima nan kazo wai a lallai sai na mata wakilci, sabo da na ƙi ne yasa ka fara faɗa min baƙar magana. Adam ya ƙurawa Najib ido ya ce “Najib wallahi Allah ɗaya kenan ko? To na rantse da shi ban san aiyi duk wadannan abubuwan ba. Cike da mamaki Najib ya ce “Adam to wallahi ka kori mutanann daga gidan ka, idan ma taimakon zaka kai musu to karka barsu a kusa da kai. Haka dai Najib da Adam sai mamaki suke yi.
Sosai dangi da abokan arziki ke ta tururuwar zuwa asibiti, sai dai har zuwa yanzu mai jego bata farka ba. Najib ya sanar da Khadija komai da Adam ya sanar masa, itama dai mamakin ta yi ta na faɗin wallhi sai an kore su ko baya so.
Ɓangaren kotu kuwa sosai shari’a ta yi zafi inda a ka yanke hukuncin dole sai Nana ta samu miji kafin a baiwa Nasiru duk dukiyar da ya ka she mata, sannan kuma Abba ya shigar da ƙarar babu ɗan su ba ƴarsa, ya ce ya na so a shiga tsakaninsu. Nan ta ke alƙali ya shiga tsakanin Nasiru da Nana kar wanda ya ƙara shiga samgar wani kwata-kwata. Da wannan ƙara ta ƙare. Sai dai kuma Nasiru da Nana da bazasu iya rayuwa babu ɗaya ba. Kwana uku da yi musu iyaka da juna sai ga kiran Nasiru. Da sauri ta ɗaga cikin zumuɗi. Shiru yayi itama haka sai kawai taji ya na kuka, itama kukan ta kama kowa ya kasa magana. Cikin she-sheƙar kuka ya ce “Mai yasa Nana mai yasa ba zaki kira ni ki bani hakuri komai ya wuce ba? Mai yasa kike da taurin kai ne? Nasiru ya ƙara sa yana fashewa da kuka Kamar ƙaramin yaro. Itama cikin kukan ta ce “Mai yasa baka da haƙuri ba zaka manta da komai ba, mai yasa ka bari har a ka shiga tsakanin mu? Sosai suka sha kuka daga bisani Nasiru ya ce “Yanzu kina ina ne?
“Ina asibiti kasan Anty Ameera ta aihu ta haifi ƴan biyu Mace da namiji to nice ke zaune da ita.
Nasiru ya ɗan yi shiru kafin ya ce “Ma sha Allah! Allah ya raya. Yayi maganar kai da ji kasan ba har zuciyarsa ta ke ba, domin sosai yake jin tsanar Ameera domin ita ce ta yi sanadin komai.
Zaki iya fitowa mu haɗu yanzu? Nasiru ya tambaya cike da kewar ta. Itama babu wani tunani ta ce “Ok idan kazo ka kira ni. Ta faɗa tana jin wani irin wutar soyayyar sa na ruruwa a cikin tsakiyar magudanar zuciyarta. Ta na zuwa ta hango motarsa a wajan asibitin, tun kafin ta isa take sakin murmushi tana zuwa ta buɗe gidan gaba ta shiga.
Tana shiga Nasiru ya jawota jikinsa yana sakin nannauyar ajiyar zuciya. Itama ajiyar zuciyar ta sauke tana lafewa a jikinsa, a hankali ya fara shafa bayan ta har zuwa mazaunan ta, sosai yake kashe mata jiki har ya haɗe bakinsu. Itama cikin so da ƙauna ta fara mayar da martani domin kuwa ta yi kewar sa, sosai suka dinga tsotsar juna ba bu kama hannun yaro kamar wasu mayunwata. Cike da jaraba ya kai hannunsa gaban ta amma ta riƙe hannuna ta ƙwace jikin ta daga nasa ta na girgiza masa kai. Nasiru ya ce “No baby yanzu idan har ba haka muka yi ba to shikenan an rabamu, amma idan har muka nuna musu cewar muna son juna ta hanyar aikata hakan zai sa a warware komai a barmu ta re. Nana ta ce “No ba sai ta wannan hanyar ba, a kwai hanyoyi da dama da zaisa a warware ba sai mun aikata saɓon Allah ba. “To wacce hanya ce? Nasiru ya tambaya ya na kafeta da ido.
Misalin huɗu na yamma Ameera ta farka, ai kuwa nan kowa ya shiga barka. Sosai ta yi haske ta rame. Lokacin da a ka kawo mata yaran ta gansu sai kawai ta fashe da kuka, sosai take ƙara godewa Allah da irin kyautar da ya bata a lokacin da take buƙata. Sosai take son ganin Adam ganin baya cikin ɗakin. Haka duk wanda zai shigo idan ta a kan kofa ta na jira taga rabin ran nata ko yaya zata ga fuskarsa domin tasan zai fita farin ciki. Lokacin da ya turo ƙofar ɗakin zuciyarta ta tabbatar mata da cewar mahaɗin tane ke tafe. Ya na shigowa idonsa ya sauƙa a kan gabaɗaya rayuwar tasa. Sosai farin ciki da murna da zumudin sa suka baiyana, ya manta da kowa da ke cikin ɗakin ya nufi gurin matar sa ya rungumota yana jin wani irin farin cikin da ya daɗe bai samu ba. Sosai yake jin ɗumin zazzaɓin jikinta na sauƙa a kansa. A hankali ya ce “I love you my Honey” itama ta furta “I so much love you my Honey. Ganin dai abun nasu ba na ƙare bane yasa Nana ɗan yin gyaran murya. Hakan yasa suka dawo cikin duniyar mutanen dake cikin ɗakin. Ameera sai wani sunne kai ta ke yi lokaci ɗaya kunya ta rufe ta ganin ana ta kallonta.
Sai washegari likita ya sallmesu wanda suka tattara suka tafi gida. Sai dai suna shiga gidan suka tarar da wani sabon tashin hankali a cikin gidan nasu, domin an ɓalle get ɗin an ture shi gefe an shiga gidan. Mutanen garin Ƙaruk ne su sama da goma sanye da irin shigar ƴan garin wato suna suturta iya ƙirjinsu da da gaban su da wata fata mai kama da fatar damun daji. Lokacin da Ameera ta gansu sai da ta tsorata, ita kanta Nana da Khadija a tsorace suke, Adam da Najib ne dai suka yi ƙarfin halin tun ƙarar su suna tambarsu ba’a sin zuwa.
Cike da mamaki suka ji wani daga cikinsu yana Hausa. Haka ne yasa suka shiga daga cikin palon gidan da mutum uku daga ciki. Suna shiga suka tarar da Ɓultuwa an ɗaureta sai zubar da jini take ga wata ƙaramar randa a kusa da ita, wanda ruwa ne a ciki suna kallon abun da take faɗa ta yi ɗin kamar suna kallon Film. Shigowar su Adam abun ya tsaya cak!. Nan da nan mai jin Hausan ya fara magana ya ce “Ba matarka ba ce ta kashe Hatta (Wato Ammin Haura) kuma sannan ba ita ce ta soka maka wuƙa ba duk aikin wannan munafukar matar ce. Ya nuna gurin da Ɓultuwa ke daure. muma munyi-munyi da ita mun kasa, babu irin makircin da bata sani ba, duk abun da take yi bada sanin mu ba ne, sai yanzu da abun da ta yi ya ɓaci yasa muka yanke mata hukunci kisa domin ta shiga gonar da ba’a shiga. Cike da mamaki Haura take kallon Ɓultuwa jin cewar ita ce ta kashe Amminta. To ta yaya ita da bata gidan!. Sosai Haura ke son jin agarin yaya.
Mutumin ya ce “Hatta da Ɓultuwa uwa su ɗaya uban su ma ɗaya, sun taso masu son kansu wato suna son ace sun fi kowa, Hatta ita ce babba amma babansu yafi son Ɓultuwa saboda Ɓultuwa a kwai saurin sabo da mutum. Soyayya ya ce ta fara raba kawunansu, domin wanda Ɓultuwa ke mutuwar so shine yake son Hatta har a ka yi aure. Daga lokacin ta fara ƙulla mata sherri iri daban-daban har sai da a ka kori Hatta da ƴar ta bayan mutuwar mijin ta. Tun da Hatta ta tafi Ɓultuwa take bibiyar ta, duk wanda ya taimake ta kuwa sai Ɓultuwa ta kashe shi, koda kuwa waye. Ko sadaka ka basu a gurin bara to sai Ɓultuwa ta kashe ka domin kuwa ita ɗin tafi Hatta karfin tsafi, domin ita mahaifinsu ya barwa duk sirrin sa. Ganin haka yasa Hatta fara tunanin ko zata mallake wani ne idan yazo yi musu sadaka. Ana cikin haka wani yazo ta mallake shi , kullum sai yazo ya bata sadaka amma baifi kwana huɗu ba ta neme shi ta rasa. Daga lokacin ta fara tunanin ko dai akwai matsala ne. Hakan yasa tayi amfani da na’urar tsafin ta ta gano cewar wani ne ke bibiyar rayuwar ta, amma bata gane ko waye ba, daga lokacin ta fara bawa ƴar ta dukkan nin wasu sirrika na tsafi.
Sosai suke wahala har Allah ya kawo ka cikin rayuwarsu ashe kai ne mai taimakon su dukda cewar sun ɗan cutar da kai amma ba sun yi hakan da gaiyya bane domin Hatta mutuniyar kirki ce kowa ya shede ta, Hakan yasa lokacin da a ka ji labarin mutuwar ta sai da kowa yayi mamaki kuma daga lokacin ne a ka dukufa binciken dalilin mutuwar tata sai jiya gaskiya ta baiyana.
Ya a kayi Hatta ta mutu? Wani irin cuta su kaiwa Adam da Ameera? Ita Ɓultuwa me ye burinta? Shin yaya makomar Haura a wannan Game ɗin? Shi Ameera ta dawo haiyacin ta ko kuwa? Shin Nasiru da gaske son Nana ya ke ko dai lalata ya ke son yi?