Skip to content
Part 20 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Lokacin da ka shigo rayuwar su sai Hatta ta yi amfani da tsafin ta domin ka dinga jin tausayin su, sosai kuma hakan ya yi nasara a kan ka. Tun daga lokacin ne kai kuma ka fara sintirin zuwa kai musu sadaka. Ganin haka ya sa ta ƙara ƙarfin tsafin nata a kanka har watarana da kanka kazo akan zaka ɗauki Haura a matsayin ƴar aiki. Lokacin da suka zo gidan sai suka tarar da matar ka na ɗauke da ciki, kuma cikin nata irin mai saka mace ƙunci da masifu ne. Sosai Hatta tayi niyyar hallakar da cikin jikin matar ka domin ta lura bata son zaman Haura a cikin gidan. Duk abun da matarka take yi babu sa ka hannun kowa domin kuwa dama laulayin ciki na iya zuwa da hk, sai dai wasu lokutan Hatta na tura mata aljannu domin su ƙara birkitata.

Duk wannan abun Ɓultuwa bata da labari domin Hatta ta ɓoye komai.  Ganin irin azabtuwar da Haura ta ke yi a gurin matar ka yasa Hatta dawowa cikin gidan ka, daga nan kuma ta fara kwaɗaitawa ƴarta auran ka, sai ta fara amfani da kai wajan dai na jure komai na matarka, abu kaɗan sai kaima ka ɗauki zafi. Ana cikin haka Ɓultuwa ta gano komai. Sosai hankalin ta yayi mugun ta shi jin wai Hatta ta samu wanda ya taimake su. Daga lokacin Ɓultuwa ta biyo iska tazo gidan domin hallaka mutumin da ya shiga gonar ta. Ko da tazo sai ta rasa ta yaya zata aiwatar da komai domin jikin ka da na matar ka a kwai aljannun Hatta kuma hakan ba mai yiwuwa bane itama ta tura nata aljannun. Duk wani abu da a kayi tana cikin gidan tana kallo. Ranar da abun ya faru kuwa ita da kanta ta shiga jikin matar ka ta ture Hatta, bayan faduwar ta ta shaƙeta batare da kowa ya sani ba har ta mutu. Bayan mutuwar Hatta kafin labari ya sa me mu ita ce ta fara zuwa ta sanar da cewar kune kuka kashe ta. Sosai muka zo da niyyar ɗaukar fansa amma ganin irin mutuwar da ta yi sai sarki ya ce dole sai an bincika dalilin mutuwar.

Haka muka ɗauki gawarta aka fara bincike. Lokacin Haura ta dawo gida sai sarki ya yafe mata komai amma da sharadin bazata ƙara barin cikin garin Garuk ba. Daga lokacin Ɓultuwa ta saka Haura a gaba akan idan har tana son auran ka to zata yi iya mai yiwuwa har ka aureta. Daga nan ta hure mata kunne har suka ƙara barin cikin garin Garuk suka dawo niman, Ɓultuwa ce tai maka kiranye har sai da kazo inda suke ka tafi dasu. Daga nan ta ci gaba da wasan kura da kai har ka furta musu zaka auri Haura. Daga nan kuma ta ci alwashin sai ta rabaka da matar ka. Sai dai hakan ba zai yiwu ba sai idan sun san idda Hatta ta binne sihirin da tai maka wanda idan matar ka ta haihu komai zai wargaje. Baka san komai ba domin har kayan ɗaurin Aure ka yi, wanda da an ɗaura wannan auran da shikenan kun gama shiga hannunta daga ku har ita Haura ɗin. Hakan yasa da muka gano sai muka cire aljanin jikin matar ka domin shine ya tare cikin, cikin ikon Allah kuma ta haihu lafiya.  Sosai Haura ke kuka tana zagin Ɓultuwa da yaran Garuk. Ita dai Ɓultuwa bata cikin yanayin daɗi domin har yanzu jini ne ke zuba a jikinta domin kuwa ta a zabtu.

Sosai Adam da Ameera ke mamaki wanda ita Ameera harda hawaye. Shima Najib dai sai kallon Ɓultuwa da haura ya ke yi kaman yaga wasu halittun da ban. Khadija kuwa ji take kamar ta kamo shigiyar Ɓultuwa ta lakaɗa mata nata dukan ko zata huce.  Ameera ta miƙe tare da baby ɗaya ta shige ɗaki, itama Khadija ta bita da namijin.  Haka mutanen garin Garuk suka tattara suka tafi da Ɓultuwa Adam ya ce abar masa Haura zai zauna da ita , zai ɗauketa kamar ƙanwaraa, lokacin da ya tambayi Ameera itama ta ce duk abun da ya ce ta yarda. Khadija dai ta ce wallahi ita tsoron su ta ke yi, idan zasu biye nata karsu ƙara yarda da su. Amma Adam da Ameera su ka ce karta damu Haura mutuniyar kirki ce.

Haka ranar suna yara suka ci sunan su na Hassana da Husaini. Amma za’a dinga kiransu da Salim da Salma. Sosai Haura ta kama kanta a gidan bari na bari yi nayi. Sai yanzu take ganin asalin halin Ameera wanda ta cika da mamaki abun da ya komar da ita masifaffiya. Ameera ta ce “Ai shi ciki babu abun da bai sakawa amma irin nawa shine mafi muni, ya Allah karka ƙara jarabtata da irin wannan laulayin da zan adabi kowa. Haura ta amsa da amin. Sai da su kayi wata ɗaya da haihuwa Adam ya saka Haura a school bayan shawarar da su ka yi da Ameera. Sosai kuwa take ƙoƙari dudda yanzu babu asiri ko tsafi a jikin ta, komai da ƙwaƙwalwar ta take yin sa.

Ɓangaren Nana da Nasiru kuwa duk ta inda Nasiru ya biyo Nana ta ƙi yarda su aikata abun da ya ke so.ga shi har yanzu babu wanda yasan suna tare. Ameera ce ta kira Nana ta ce “Nana kina son Nasiru har yanzu? Nana ta fa she da kuka tana cewa Wallahi ina sonsa sosai, kuma yanzu ban san abun yi ba. Ameera ta bata haƙuri akan zata gyara mata komai kamar yadda ta ɓata.

Haka Ameera ta taka taje ta samu Umma da Abba ta fara basu hakuri akan a warware komai na tsakanin Nana da Nasiru. Amma Abba ya ce idan bata bar gaban sa ba zai saɓa mata. Baba ya ce “Koda Nasiru shine kaɗai namiji to sai dai kar Nana ta yi aure. Sosai Ameera ta dingi sintiri daga gidan ta zuwa na su. Ta kai sati ɗaya kafin Abba ya haƙura. Haka ma taje gidan su Nasiru su kuwa ana zuwa suka ce dama su ai yaran su na so, kuma su duk abun da yaran su ke so to suna mara masa baya. Daga nan aka je kotu aka warware sharadin da a kayi a ka ɗaura auran Nana da Nasiru. Sosai Nasiru yazo har gida yana ma Ameera godiya da bata haƙuri a kan duk abun da ya faru. Wata uku da haihuwar Ameera itama Khadija ta haifo nata ɗan ƙato Namiji mai kama da uban sa.

Kallon ta ya yi ceke da mamaki ya ce “Haba honey yanzu fisabililahi kina kallo aiki fa na keyi shine zaki ce na zo na karanta miki novel? Ameera ta ƙwaɓe baki kamar zata yi kuka ta ce “Sabon littafin Khadija Candy ne fa please ni dai kazo kar a min nisa. Adam ya ce “To wai ko dai wani cikin ne shima mai hana mutum sakewa. Take Ameera ta gwalo ido waje tana dariya. Ta ce “No barshi zan karanta kayana ai bana addu’ar na ƙara yin ciki irin wannan. Adam ya ce “Allah dai yasa kar yaran su ɗauki irin wannan masifar. Ameera ta amsa da amin dai. Suna cikin hirar sai ga Haura ta dawo daga school. Ta na shigowa ta gaisar da su a tare ta na faɗin “Kai Anty yau fa bana gane kai na tsabar yunwa. Ameera ta ce “Gashi kuma ban yi komai ba a gidan, yaran nan sun hanani sa kewa sai yanzu ma na samu suka yi barci. Haura ta ce “Haba dai Anty Allah zan iya faɗuwa fa ko nayi kuka idan da gaske kike. Ameera ta ce “To yi kukan mana mu gani, kinga da sai naje na taso su suma su kalli ƙatuwar Antyn su ta na kuka ko. Sai lokacin Adam ya ce “Wasa ta ke miki abinci na kicin kuma irin wanda kike so.

Ba tare da tursasawa ba ko taƙuwara Haura da kanta ta ce tana son ta shiga addinin Musulunci. Ai kuwa Adam da Ameera sun yi murna sosai wanda sai da Ameera ta bata kyautar wata sarƙa mai kyau mai tsada.  Bayan musuluntarta aka ce ta zaɓi sunan da ta ke so sai kawai ta ce “A’isha. Sosai take jin daɗin zama a gidan itama kuma ta sake sosai kai ka ce dama a gidan ta taso. Nan dai Adam ya shigar da ita islamiyya sanna shi da Ameera suna ƙara mata karatun a gida.

Cikin ikon Allah Nasiru da Nana ko bayan auran babu wannan yawan fadan da su ke yi sai soyayya mai tsafta da suke shin fiɗawa kamar babu gobe.

“Zo na tuna miki da wani abu” Adam ya faɗa ya na kallon ganin ta ƙi ƙarasowa gurin. Ya ƙara cewa “Ranar da kika sa soja ya min duka ina kika gudu ne lokacin? Adam ya ƙara sa ya na dariya. Itama dariyar ta yi tana ƙarasowa ta faɗa jikin sa. Ta ce “Ni dai dan Allah a bar dawo da abun da ya wuce. Adam ya ce “To mai sayar da ƙwai fa na ƙarshen kayi? Ameera ta ɓata fuska ta ce “Allah zan yi kuka idan ka sa ke. Adam ya ce “To na ji yanzu babu ajiyar komai ne a cikin? Ya faɗa yana shafa cikin nata.  Ameera ta ce “Please Honey Dan Allah ka je ka nemo baba mai gida ya dawo aikin sa. Adam ya ce “Babu yadda ban yi da shi ba wallahi ya ce ba zai iya ci gaba da aikin a gidana ba, amma na ba shi jari kuma na roƙa miki yafiya kuma ya yafe. Ameera ta share hawaye ta ce “Tom Nagode Honey. Haka fara bata haƙuri har ya lallaɓata suka haura sama.

Alhamdu lilliha! Anan lissafin Ameera da Adam yazo ƙarshe. Nasan zaku sha mamakin yadda labarin ya zo a haka. To ba komai ba ne sai yanayin labarin. Ya Allah ka yafe mana kuskuren da ke cikin wannan labarin, alkairin kuma Allah ya sada mu da shi. Da wannan nake muka addu’a a duk inda kuke, ni S-Reza ina ƙaunar ku a duk inda kuke Allah ya barmu tare.

Albishirin ku masoya littattafan S Reza? Shin kun san wani irin labari zan fara rubuta muku? Hammm ba’a cewa komai. Shin ba dai kunce kuna son labari irin labarin UWATA CE SILA ba? To Tabbas wannan labarin sai ya taka shi chakwakiya da barikanci ta makirci. Ba zan faɗa muku sunan saba sai na gama shiri domin aikin na yi ne.

<< Ameera Da Adam 19

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.