Ɓangaren su Kadija suna isa asibitin suka samu taimakon gaggawa kasancewar har zuwa lokacin da suka isa bata farka ba. Shi dai Najib ya na ta mamakin abun da ya samu matar tasa, tsabar tashin hankali ma bai ko tsaya ya tambayi mai gadin abun da ya faru ba. Ya kai kaman awa ɗaya a tsaye yara jira kafin wata daga cikin likitocin ta fito ta kira shi. Ko da ya iso sun gama shiryata an saka mata bandeji agurin sannan an saka mata ruwa ta na barcin wahala. Kallo ɗaya yayi mata yaga yanda ta rame ga kuma a lamar rashin jini a jikinta domin kallo ɗaya za kai mata kaga tayi fari. Nan likitan ta sanar masa akan za’a ƙara mata jini bayan ta farka, kasancewar jininsa group O ne yasa ya je a ka ɗiba a nasa. Bayan an gama ne ya fito yana son kiran Adam domin sanar da shi halin da ake keci ganin har lokacin bai ga Ameera ko Adam ɗin ba. Haka ya kira numbar Adam ɗin amma ba’a ɗagawa ya masa kira har sau huɗu amma babu amsa, hakan yasa ya bari zuwa an jima. Ko da ya koma ɗakin da Kadijan take kwance ya ga har yanzu barci take yi sai kawai ya fita izuwa masallaci.
Ko da ya dawo ya sake kiran Adam amma yazu yaji number a kashe, sosai yanzu abun ya fara bashi tsoro. Sai yanzu kuma ya tuna cewar Adam fa a gida ya bar wayarsa, har ya yanke shawarar zuwa gurin aikin Adam ɗin amma yayi tunanin kar kuma ya tafi ita kuma Kadijan ta farka baya nan, hakan ne ma yasa ya zauna har sai ta tashi ta sanar tashi abun da ya faru.
Koda mai keken ya sauketa bata tsaya bashi guɗi ba tayi hanyar shiga gida da gudu, tana zuwa ta tura ƙaramin get ɗin ta shege ciki da gudunta. Mai keke kuwa ganin haka yasa ya biyo bayan ta yana masifar bata isa ba wallahi. Mai gadi dake zaune yaga ta wuje da gudu ya bita da mamaki baki a sake yana ganin ikon Allah na sauya rayuwar wannan baiwar Allahn cikin lokaci kaɗan. Yana cikin mamakin yaga mai keken ya shigo har cikin gidan yana zage-zage. Mai gadi ya tare shi yana tambayar sa. Nan mai ɗan sahu ya sanar da shi cewar kuɗi zata bashi. Dama a kwai sauran canjin kuɗinta a gurin mai gadin na ƙosan ɗazu hakan yasa ya tambaye shi nawa ne kuɗin sai ya cira ya ba shi. Ita kuwa Ameera ta na shiga palon ta fara sauke ajiyar zuciya ta cire ɗan kwalin a bayar da ke kanta sannan ta samu guri ta zauna tana riƙe bayanta gurin da ta bugu. Firiza ta nufa domin ɗau kan ruwa mai sanyi sai taga frizan a dungware a ƙasa socket ɗin ma baya jikin wuta, ga kuma babu komai a ciki, sai yanzu ta tuna da cewar a shefa kayan freza ɗin suka tafi sayowa. Komawa ta yi ta zauna ta ciro wayarta ta latsa kiran numbar Honey, amma taji wayar a kashe, sai ta tuna da cewar a she fa ita ce ta ka she masa wayar. Sai kuma tunanin Kadija ya faɗo mata kasancewar saboda su Kadijan ta kashe wayar.
A fili ta furta “Oo ni Allah na Ameera me yake faruwa da ni ne! Yanzu fa sai ace wannan duk laifinane bayan kuma ni duk ba laifina bane. Sai kuma ta miƙe tsaye ta fara ƙoƙarin kuka tana kiran sunan Adam.
“Allah dai yasa Honey ya ƙwace ya gudu daga hannun wannan mugun, Allah yasa bai ji masa ciwo ba, waiyo ni Allah Honey na mai ya kaika faɗa da sojoji! Sosai kuka ya kufuce mata tana yi tana kiran sunan Honey ganin kukan ba zai kaita bane yasa ta fita waje da sauri sai kuma ta dawo ta ƙara surar jakarta da ɗan kwalin ta har ta kusa isa ƙofar waje sai kuma ta dawo da baya ta zauna ta dafe bayanta da yake mata wani ciwo. A fili ta ce “Allah ya isa tsakanina da wannan Hanifah ɗin shegiyar yarinyar, kimin laifi amma saboda ubanki soja ne sai kawai baza’a hukunta ki ba, ai kuwa wallahi ƙaryane sai dai idan ba Ameera kika taɓo ba.
Ta shi tayi ta leƙa wajen cikin gidan ta ƙwaɗawa mai gadi kira, bayan yazo ta sa ya kwashe abincin da tayi tace yaje ya cinye. Da murna mai gadi ya kwashe abincin ya fita da shi ya na godiya. Ɗaki ta koma da niyyar sake wanka tayi alaula kafin Honey ya dawo ganin magrib na dosowa.
Ɓangaren Adam kuwa ana zuwa da shi asibiti bai ko yarda an kwantar da shi ba ana gama wanke masa ciwon bakinsa ya sallamesu ya fito daga asibitin bayan sun rubuta masa magungunan da zai siya, sai da ya biya ya sayi maganin kafin ya koma ya ɗauki motarsa ya nufi hanyar gida. Yana cikin tafiya ya ɗauki wayarsa domin kiran Najib yana danna kiran sai yaga kiran ya dawo. Sai da ya duba yaga wayar a jirgi. Sosai yayi mamakin hakan domin dai shi da kansa bai sa wayarsa a jirgi ba, Nan take Ameera ta faɗo masa, girgiza kai kawai yayi yana kiran numbar Najib ɗin bayan ya cire wayar daga jirgin.
Tana shiga Najib ya ce “Hello Adam”
shima ta ɗaya bangaren ya amsa da cewar “Kana gida ne? Cikin ɗacin rai da ɓacin ran da Najib ɗin ke ciki dalilin jin duk abinda ya faru daga gurin Kadija ya ce “Wallahi Adam ka bani mamaki, wato saboda kar ma na kiraka na sanar da kai abinda matarka taiwa Matana shine ka kashe waya, kuma tsabary rainin hankali kana iya kirana ka tambaye ni wai muna gidane ko? To kaje gida ka ajiye mini motana kuma wallahi ka sani ba zan bar wannan cin mutuncin ba, ko mai ina za’a je sai dai aje. Yana faɗa ya kashe wayarsa yana jin wani ɓacin rai ganin irin halin da matar tasa ke t. Tsabar masifar dake cinsa ma har ya manta da cewar matar tasa ƙanwar Adam ɗin ce.
Cikin tsananin mamaki Adam yake sauraron abokin nasa jin abun da yake cewa, jin ya kashe wayar ne yasa ya fara salamulai a fili ya na cewa “Innalillahi wa Innalillahi raji’un! Meye Najib ya ke faɗa ne, wai Amera ce ta daki Kadija ko meye. Nan dai ya shiga kiran sa amma a kashe, haka ya nemo numbar Kadija itama a kashe, take hankalinsa ya ƙara tashi gabansa yana faɗuwa, domin tun da yaji muryar Najib a haka to yasan ransa ya ɓaci sosai. Gidan su Najib ɗin ya fara zuwa amma mai gida ya sanar da shi ai tun safe da hajiya Kadija ta fita shima Najib yabi bayanta basu dawo ba. Motar ya bari a gidan sannan ya nufi gidan sa cikin ɓacin rai yana jin yau sai ya ɓata wa Ameera rai, dan tsabar bala’i ma a ƙafa ya taka har zuwa cikin gidan.
Ko da ya tura get ɗin ya shiga sai yaci karo da mai gadi ya saka kulolin abinci a gaba yayi tagumi yana kallon cikin babbar kular kamar zaiyi kuka. Yaso ya wuce ciki amma ya ƙarasa gurin mai gadin yana tambayar sa Amera ta dawo ne? A tsorace mai gadin ya dawo hankalinsa yana miƙewa yana masa barka da zuwa cikin yanayin tsoron yanayin da ya tarar da shi.
“Eh Hajiya ta dawo tun ɗazu tana ciki ma yanzu haka”.
Har Adam ɗin zai huce sai kuma ya dawo da baya yana kallon cikin kular abincin da kyau ganin abun da ke ciki. Ɗan wake ne a kayi amma ya dame ya zama kamar ƙullun tuwo, ko kyawun gani babu. Lokaci ɗaya Adam ya gane cewar abincin da tayi ne ɗazu kafin su fita. Zai magana mai gadi ya ce “Mai gida hatsari kayi ne? To Allah ya kiyaye gaba ya tsare tsau-tsayi da a’sara. Adam ya amsa da Amin yana nufar cikin gidan.
Ransa a ɓace ya tura ƙofar palon gidan nasa yana ƙoƙarin danne zuciyarsa akan abun da take saƙa masa game da matar tasa. Yana shiga ya fara kiranan sunanta cikin kakkausar murya. “Ameera “Ameera. Kafin ya rufe baki sai ji yayi an rungume shi ta baya tana faɗin. “Sannu da dawowa Honey ya jikin ina dai fatan lafiya kake ko Honey mai sukai maka? Ta dinga jero masa tambayoyi kamar zata yi kuka domin kuwa tun lokacin da ta dawo ta kasa sakuni sai kaiwa da komowa take yi tana jiran ya dawo duk ta damu. Cikin ɓacin rai ya ce “Bana son zancen banza Ameera me ya haɗaki da kadija ɗazu da tazo? Yayi tambayar cikin ihu da ta kaicin abun .
Ai kuwa Ameera jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa da kyau ta fara faɗin. Ni ina gida ina tunanin halin da kake ciki duk na kasa sakuni amma ka shigo kana mini ihu harda kiran sunana da Ameera a kan abun da ban san faruwansa ba, hasali ma ni a kaiwa laifi amma kazo baka ji kan zance ba ka hauni da faɗa wato kafi son ƴar uwarka a kaina ko?
Cikin sauri da jin shirmen zancen ta ya sake cewa “Mai ya haɗaki da ita?
“Ni fa ban san komai ba kawai dai ni naga tazo yin gulma ne shine kawai nace ta fita min daga gidan mijina tunda gulma ya kawo ta shine na turata waje. Da sauri Adam ya fincike ta daga jikinsa ya ɗan turata baya haɗi da faɗin. “Kadijan zaki kora daga gidana baki da hankali ne, kuma itace zata miki gulma har kina iya faɗa mini cewar gulma tazo, kuma wai gidana, to wallhi mutuƙar…”Ai kafin ya ƙarasa Ameera ta ƙwalla wani uban ihu sanadiyyar turata ɗin da ya ɗanyi ta faɗi a tsakar palon. “Waiyoooo allana Umma na! Waiyoooo cikina bayana ya kasheni! Inna’ilaihi na shiga uku!.
Sosai take kuka bilhaƙƙi da gaskiya harda hawaye. Ganin haka yasa Adam saurin ƙarasawa gurinta yana ƙoƙarin ɗagota. Take ta fara kai masa duka tana faɗin”Ni ka rabu dani ka barni ni dai sai ka kaini gurin Umma. Sosai ta burkice masa gashi taƙi ta barshi ya taɓata، sai faɗin cikinta da bayan take wanda hakan yasa Adam tsorata karfa wani abun ya sami cikin nata. Jin tunanin da yazo masa ne yasa gabansa faɗuwa, da sauri ya sunkuya ya kinkimota suka nufi ɗaki. Yana shiga ya kwantar da ita yana cigaba da bata haƙuri akan ba zai ƙara ba hakan ma kuskure ne. Lokaci ɗaya tayi shiru tana ajiyar zuciya, ganin haka sai kawai shima ya kwanta a kusa da ita ya ruƙo hannunta ya fara faɗin. “Kalli abun da kika ja a kai mini ɗazu duk a dalilin taurin kanki, dan Allah Honey ki rake wannan fushin wallahi ina cutuwa kinji? Shiru tayi tana kallonsa batare da tace komai ba domin ita har ga Allah bata ga wani abun da tayi na fushin ba, hasali ita batayi wani laifi fa. Jin tayi shiru ne yasa ya ɗaga rigarta yasa hannunsa a cikinta ya fara shafawa yana cigaba da faɗin. “Wannan Babyn yazo da rikici sosai, duk yabi ya sauya min mata kamar ba Ameera da Adam ɗin da suka kafa tarihin soyayya ba, dan Allah ki dawo kamar da kinji Honey? Ya faɗa yana kai idonsa ga fuskarta jin bata ce komai ba. Yana kallonta yaga tana lumshe ido alamun barci zatayi. Shi kuwa take yaji yana buƙatar ta jin yanda ta sake masa jiki. Sai kawai ya shiga rabata da kayan jikinta yana cigaba da shafa daga cikinta zuwa sama, sosai itama yanayin yayi mata daɗi sai kawai ta sakar masa jiki tana bashi dama. Sosai ta manta da komai ta saki jiki suka samu natsuwa domin itama tana buƙatar hakan. Bayan komai ya wakanane ya jawota jikinsa yana saka mata albarka sannan ya faɗa toilet yayi wanka haɗi da alaula ya fita Masallace. Ganin fitarsa yasa itama miƙewa ta shiga toilet ɗin.
Bayan sallar isha suna zaune a Palo suna kallo ta kwantar da kanta a kan cinyarsa shi kuma hannunsa na cikinta yana shafa ta ce “Honey wallhi gurin dana faɗi ɗazu har yanzu zafi yake min kamar ma fa karyewa nayi a gurin? Da sauri ya ce “Na gani?
Haka ta juyo masa kan kwankwason ta tana nuna masa. Ya ce “Sorry ba karyewa bane kawai dai kin ɗan bugu ne. Cikin shagwaɓa ta ce “Allah zafi fa yake min sosai bana iya ko sunkuyawa gaba ɗaya. Adam ya sake shafa gurin ganin bai ga alamar komai ba ya ce “To sorry zai dana in sha Allah kuma zan sayo miki magani gobe sannan zan samo miki wacce zata ɗan dinga tayaki wasu ayyukan na gida sai ke ki dinga hutawa ko? Dariya tayi tana faɗin amma dai ba a cikin danginka zaka nemo ba ko? Domin bana son raini Allah, kuma karka samo ƙazama Please. Sai a lokacin Adam ya tuno da kadija lokaci ɗaya ya saki salati yana faɗin Honey Kadija fa tana asibiti kuma bamuje ba? Take Ameera ta haɗe rai tana kallonsa. Take ya ɗauko wayarsa ya nemo number Najib kira ɗaya ya ɗaga haɗi da sallama.
“Najib kuna gida ne ko har yanzu kuna asibiti? Adam ya tambaya cikin harɗewarmurya?
“Mun dawo gida tun ɗazu. Najib ɗin ya bashi amsa kamar wani abun bai faru ba.
“Ok tom ina kadijan lafiya dai take ko? ganinan zuwa yanzu Please. Yana faɗa ya kashe wayar ya miƙe ya shiga ɗaki ya sauya kaya ya nufa hanyar fita daga palon yana sauri kamar zai tashi sama. Yana zuwa ƙofar palon yaga ƙofa a rufe, yana juyowa ya ganta tsaye ta riƙe ƙugu tana haɗe rai.
“Lafiya dai kika rufe ƙofar? Ya tambaya cike da mamaki.
“Babu inda zakaje a darannan ka barni ni ɗaya wallahi. Itama ta faɗa tana ƙara tsayawa a gurin da kyau.
“Gidan Najib fa zance dubo Ameera kuma kece silar zuwanta asibiti, kuma babu wanda yaje nidake, Please dan Allah zo ki buɗe min na tafi yanzu zan dawo. Cike da mamaki ta ce “Wato nice sila ko? To kai da kaje ka kai mata gulmar cewar Ina dukanka kullum, kuma ina hanaka sakewa a gidan kafa? ni bance komai ba sai ita magulmaciyar, to Allah komai dai me zakace bazaka tafi gidan ta a darannan ba. Jin haka Adam ya ce “To zo mu tafi tare Please bana son tashin hankali, naji har kin fara ce mata magulmaciya ce. Ameera ta tayi dariya ta ce “Babu inda zanje wallhi kuma kaima haka muna tare har gobe. Sosai ransa ya kai ƙarshe da ɓaci yana jin wallahi ko danneta sai yayi ya ƙwaci ɗan makulli ya tafi , bayajin zai samu sakuni idan baiga halin da kadija ke ciki ba. Kallonta yayi da kyau yana jin wani ɓacin rai na zuwar masa, da sauri ya ƙarasa gabanta yana tattaro natsuwarsa a guri guda ya ruƙota da ƙari ya mannata a faffaɗan ƙirjinsa ya matseta sosai.