Skip to content
Part 4 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Ya fara magana cikin sanyi-sanyi kamar mai tsoron kar wani ya ji. “Ba daɗewa zan yi ba yanzu zan dawo dan Allah ina so kema ki shirya mutafi tare nasan idan ta ganki zata ji daɗi shima Najib zai gane cewar ba laifinki bane please Honey?. Adam ya ƙarasa yana riƙo hannunta kamar zaiyi kuka. Yana gamawa ta zame jikinta batare da tace masa komai ba ta juya ta nufi ɗakinta ta barshi baki sake yana kallonta. Haka dole ya haƙura da zuwa gurin Kadija ya dawo Palo ya zauna yayi tagumi yana tunanin lokacin baya tsakanin sa da Ameera, lokacin da suke soyayya irin soyayyar da zakaga masoyan har kama da juna suke yi, tsaɓar soyayyar da suka sha a baya shine yasa ake kiransu da Ameera ta Adam, ko kuma wasu suce Ameera da Adam. Yana cikin wannan tunanin sai gata ta fito cikin shigar kayan bacci.

Kallo ɗaya yayi mata ya kawar da kansa gefe. Ta na zuwa ta ce “Honey ta shi muje mu kwanta na kasa bacci ne? Ta faɗa da ɗan rigima a muryarta. Ta shi yayi ba tare da yace komai ba ya nufi ɗakin yana shiga ya kwanta kansa na kallon sama. Itama irin kwanciyar da yayi tayi tana kallon gurin da idonsa ke kallo.

“Honey na dameka ko? Baka san yadda za ka yi da ni ba ko? Tayi maganar ba tare da ta kalle shi ba.

Sai a lokacin Adam ya juyo ya kalleta ya sauke ajiyar zuyace kafin ya ce “Wai duk abinda da kikeyi dama kina sane kenan? Jin haka yasa itama juyowa sukayi ido biyu kasancewar basu kashe wutar ɗakinba. “Meye nake yi wanda bai dace ba ko kuma nayi laifi? Itama ta tambaye shi tana jin yanayinta na sauya wa . “Babu komai” ya faɗa sannan ya sauƙa daga kan gadon ya kashe wutar yayi shirin bacci ya haye katifar ba tare da ya ko ƙara bi ta kanta ba, itama daga haka bacci yayi wuff da ita.

Washegari da wuri Adam yayi shirin zuwa aiki daga nan kuma zai biya ta gidan Najib ɗin. Sosai yake sauri yana Allah-Allah kar wannan matar ta kawo masa wata matsalar da safen nan, tsabar sauri ma bai ko tsaya ya karya ba ya nufi kicin gurinta yana sanar da ita ya shirya zai tafi. Yana shiga ya tatdata kwance a cikin cikin ɗin tana baccinta hankali kwance yaso juyawa ya fita amma dai ya ƙaraso yana kiranta. “Honey Honey lafiya kuwa kike? Jin haka yasa Ameera farkawa tana sauke idonta a kansa. Kafin tayi magana ya ce “Idan bacci zaki yi ai da kin tsaya a ɗaki amma sai kizo kicin ki kwanta. Yana faɗa Ameera ta fashe da kuka tana faɗin. Indomi da ƙwai nakwson ci kuma nazo naga babu ƙwai shine bacci ya ɗaukeni kuma ni yunwa nake ji sosai. “Ok tom yanzu dai bari na aiki mai gadi ya sayo mana ƙwan sai ki dafa ko? Ameera ta ɓata rai sannan ta tsayar da kukan shagwaɓar ta ce “Wai dan Allah dole ne sai kaje gurin wannan yarinyar ne, to ni dai wallahi yau bana jin daɗi ina son zama da mijina a gida, kuma gashi cikina ma yana ɗan murɗawa haka kawai ka tafi ka barni ni ɗaya a gida ai kuwa ba zai saɓu ba. Cike da mamaki yake kallonta ya ce “Me kike nufi? Da sauri tun ma kafin ya rufe baki ta bashi amsa “Abun da kaji shi neke nufi. Jin haka yasa ya ce “Ai kuwa baki isa ba, dele na tafi gurin aiki, zan ajiye miki kuɗin ƙwan a ɗaki sai ki ba mai gadi ya sayo miki ban yarda ki fitaba na faɗa miki. Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga kicin ɗin cikin sauri. Ai kuwa tabi bayansa tana masifa. Ganin yaƙi tsayawa ne sai ta bishi da gudu. Shima yana juyawa yaga ta nufoshi sai kawai shima ya saka gudun. Sosai take jin bata so ya tafi ya barta a gida, ganin ya sa gudu yasa ta ƙara dagewa. Har cikin harabar gidan bata dai binsa ba, ganin haka yasa bai ko bi ta kan motarsa ba ya na zuwa ya nufi gurin get.

Shi kuwa Baba mai gadi cikin mamaki ya hango amarya da ango suna tseren gudu, hakan yasa ya saki baki ganin uban gidan nasa ya dage da gudu. Kasancewar get ɗin a rufe yake yasa ko da Adam ya ƙara so gurin yayi-yayi ya buɗe taƙi har saida Amera ta cim masa. Tana zuwa ta riƙe masa riga tana haki!.

“Biyoni mutafi cikin ruwan sanyi” Ta faɗa ba tare da tunanin mai gadi na kallonsu ba.

Jin haka yasa Adam fara lallaɓata babu yanda baiyi ba amma ta kafe akan ita Allah yau ba zai fita ba. Jin haka yasa ya haƙura suka koma gida. Suna shiga ta sake shi ta nuna masa kan kujera tace ya zauna, ai kuwa babu musu ya zauna. Itama zama tayi tana kallonsa ta ce “Na faɗa maka ƙwai nake son soyawa da indomi kuma kasan bamu da ƙwai a cikin ko? Cike da ɓacin rai ya zaro kuɗi yace gashi kije ki ba mai gadi ya sayo. Ai kuwa cikin masifa ta ce “Ni zaka wulakanta akan na tambayarka kudi Honey? Shine har da watsomin wato irin ga matsiyaciyar nan ko? To wallahi nafi ƙarfin wulaƙancinka akan wasu banzayen kuɗinka kuma bana so. Tana gama ta tashi fuuu ta nufi ɗaki ta ɗauki kuɗi ta fito ko hijjabi babu ta nufi hanyar waje. Tana zuwa ko takan mai gadin bata ko bibi ta nufi hanyar waje da kanta, kasancewar a kwai wani mai ɗan shago inyamuri a ƙasan layin nasu.

Tana zuwa cikin fushi ta ce abata ƙwai kret ɗaya. Ya ƙarɓa ya fara suba mata a leda sai taga wani ɗan ƙarami tace a sauya mata yayi ƙarami. Shi kuma yace ai ba’a sauya wa sai dai idan kiret ɗin gaba ɗaya za’aa sauya. Jin haka Ameera ta ce “To wallahi sai ka sauya mini, na sayi abu da kuɗina amma kace wai ba’a sauyawa kai ɗin banza. Tana faɗa ta sa hannu ta ɗauki guda ɗayan zata sauya da kanta, ai kuwa malam inyamuri ya yi sauran mayar mata da wanda ta saka masa yana cewa “Hajiya nace miki ba’a sauyawa sai dai idan wani kike so gaba ɗaya amma dai bazamu zake ko ɗaya daga ciki ba. Ai kuwa cikin tsananin ɓacin rai da masifa Ameera ta ce “To wallahi sai an sauya min ko kai ɗan gidan uban waye, kai ɗin banza ni da kuɗina amma na bari a cuceni. Tana faɗa ta zagayo ta gaban shagon da kyau sannan ta nufi gurin ƙwan. Kallo ɗaya za kaiwa wannan inyamurin ka gane ba ƙaramin ƙaton mutum bane amma tsaɓar ƙarfin hali na Ameera sai take ƙoƙarin ture shi ta ɗauki ƙwan, ganin yaƙi turuwane sai kawai ta ɗauki nata kiret ɗin ta watsa masa ƙwan a fuskar sa tana faɗin”Tsinane kaine matsiyaci gasunan gaba ɗaya kaje ka dama da shegiyar matarka.

Adam da ya saci hanya zai gudu ya hango abun dake faru da matar tasa. Da gudu ya ƙara so gurin yayi saurin shiga tsakaninsu ganin inyamurin ya dososa cikin ɓacin rai. Ita kuwa ganin Adam a gurin sai ta ƙara ƙaini gurin zagin mai shagon. Sosai Adam ya ba shi hakuri sanan ya biya shi kuɗin ƙwan wanda da kyar ya haƙura domin kuwa ta masa wanka da ƙwan gabaki ɗaya jikinsa. Haka Adam ya kamo hannunta suka nufi gida.

Suna shiga palo ya juyo da ita ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu. Sai dai kamar walƙiya kuma kamar a mafarki yaji sauƙar maruka fiye da guda biyu a kumatunsa wanda yasa bai ko iya tsayawa ya duba daga ina marin suka fitoba. Ta gama zuwa har ƙarshe ta gaji bazata iya ba ta gaji. Cikin mamaki da tsoron Adam yake bin ta da kallo ya riƙe kuncinsa, kasa yin magana yayi sai kallonta da ya keyi. Jin yaƙi cewa komai sai ita ta fara magana cikin tsananin ɓacin rai da fitar da abun dake ranta.

Dama cike take da abun da yayi mata na jefa mata kuɗi ga kuma rashin shigar mata faɗa da bai yi ba sai wani haƙuri yake bayarwa shine kuma yanzu tsabar samun guri zai wani mareta. “Wallahi nafi ƙarfin a wani ya wulakanta ni koma a inane, ka fita ka tarar ana faɗa da matarka kai baka shigar mata ba sai kawai kai ma kazo gida ka hau dukan jaka ko? Ai iyayena jaka suka ajiye maka da zaka daka alokacin da kake so to wallahi baka isa ba. Cikin ƙarfin hali Adam ya ce “Ni kika mara Ameera? Yanayin yanda yayi maganar sai da gabanta ya faɗi amma ta dake ta ce “To laifin waye? Mai yasa zaka mareni a kan waccen wawan arnen? Ba tare da yace komai ba ya nufi ɗaki ya shiga toilet ya sake wanka ya sauya kaya ya fita daga gidan gaba ɗaya.

Itama Amera wayarta ta ɗaga ta kira Umma ta ce abawa Nana ƙanwarta kuɗi ta sayo mata ƙwai tazo mata da shi yanzu tana son cine kuma na gidan ta ya ƙare ne ga kuma Adam baya gida. Ai kuwa babu jimawa sai ga Nana ta kawo mata ƙwan. Koda nanar tazo taga yanayin yayar tata sai take tambayar ta lafiya kuwa. Ameera ta sanar da ita babu komai amma nanar ta so dagewa son jin komai. Nan take Ameera ta hauta da masifar cewar ina ruwanta, ko itama ta zama magulmaciya ne. Jin haka yasa Nana yin shiru da bakinta. Ameera ta ce ta shiga kicin ta dafa mata indomin ɗin. Kawai sai taji komai ma baya mata daɗi, sosai take jin ƙunci a ranta idan ta tuno da abun da ya faru ɗazu. Cikinta taji ya murɗa alamar yunwa sai kawai ta kwaɗawa Nana kira . “Nana wai har yanzu baki gama dafa indomi ba kawai? Ko rufe baki batayi ba sai ga Nana ta fito da alamar ta gama. Nan suka zauna suna ci Nana tana bata labarin saurayin ta wanda a ka saka musu rana da shi ta ce “Anty Meera kinsan Allah Nasiru bai da kirki kumafa tsabar rashin Kunya har cikin gida ya shiga da kansa wai ya fasa auran, Allah ma dai yasa Baba baya gida ai da anyi abun kunya. Ameera ta ce “Ni ban taɓa ganin soyayya irin wannan ba kullum faɗa kullum kuma sai wani daga cikinku yace ya fasa, an ya a haka aure zai yiwu kuwa Nana? Nana tayi dariya ganin ta fara cin nasarar sakƙo da yayar tata ta ce “Waifa kawai dan an faɗa masa cewar an ganni da wani a tsaye kuma wallahi ƙaryane shine shi kuma yana zuwa ya hauni da masifa kamar wata matarsa ko ƴarsa, shine nima na kasa jurewa har sai da muka yi dam e shine ya ce wai ya fasa, amma jiya ya dawo zance dake baida kunya.

A kwanakin baya idan Nana tazo wa da Ameera da irin wannan maganar haƙuri take bata domin babu wanda bai san irin soyayyar Nana da Nasiru ba soyayya ce wacce su kaɗai suka san nufinsu, in dai yazo zance tofa sai sun raba gari, amma zuwa gobe kamar ba’ayi ba. Sun kai shekaru biyu a haka har dai a ka saka ranar, wacce yanzu haka kullum idan yazo ko ita tace ta fasa ko shi ya faɗa, to shekaranjiya ne abun ya girma domin har cikin gida ya shiga yana faɗin ya fasa. Shi Nasiru bashi da haƙuri kamar yadda itama Nana haka, amma duk da haka wani irin so sukewa junansu wanda basa iya yin fushi mai tsayi da junansu.

Ameera ta ce “Buɗe kunnuwanki da kyau kiji abun da zan sanar miki. Nana ta ɗaka kai ta kalli yayar tata ta ce “Ina sauraronki. Lokacin da Adam ya isa gidan su Najib ya tarar da Najib ɗin shima a gida domin har yanzu ba shi da lafiya. Da kunya ya ƙarasa ciki yana senne kai! Ganin yadda suka tarbe shine yasa yaji daɗi domin basu nuna masa komai ba daga kadija har NAJIB ɗin. Zama yayi a gurin da kadija ke zaune yana kallon bandejin dake ƙoshinta, kafin yayi magana itama take tambayarsa ciwon fuskarsa. Nan take ya zauna ya faɗa musu komai irin dukan da ya sha a gurin soja, sannan ya tambayi kadija abun da ya faru. Itama haka ta kwashe komai ta sanar masa bata ɓoye ba. Sosai Adam yaji tausayinta ya sanar mata cewar wallhi itace duk ta hana shi zuwa da masifa iri daban-daban. Sai a lokacin NAJIB ya ce “Maganar gaskiya Ameera ba da sanin ta take yin wannan abun ba, wallhi cikine yake sakata duk wannan abun, lokacin da kadija ta faɗa min farko nima na ɗauka rainine da iya shege sai da na tsaya nayi bincike sosai nagano abubuwa da dama akan masu ciki, hakan yasa nayi mata uzuri, to kaima dole sai ka ƙara hakuri kuma ka bita a hankali. Yanzu dai ka samo mata ƴar aiki domin samun sauƙin wasu abubuwan. Adam ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Najib jin wai harda yin bincike.

<< Ameera Da Adam 3Ameera Da Adam 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×