Skip to content
Part 5 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Cike da tabbacin abun da za ta sanar ɗin Ameera ta fara ce wa “Karki ƙara tsayawa wani ƙaton banza ya ɗora hannunsa a jikinki da sunan duka wai saboda ya kai sadakin ki, idan har ya dake ki kema ɗaga lafiyayyun hannayen da Allah ya baki ki daki ɗan banza, ai ke ɗin ba jakarsa ba ce dan uban sa da zai dinga jibga tun ma kafun ayi auran, Idan kuma ya ce ya fasa auran kema Ki ce kin fasa ai shi ɗin ba autan maza bane. Nana dai ta yi shiru ta na sauraron yayar tata cike da mamaki, sai da ta gama tsaf kafin Nana ta ce “To Anty Meera in sha Allah hakan za’ayi ai dama kinsa bana raga masa tun ma ba yanzu ba, idan yamin ramawa nake bana tsoron da. Bari na tafi gida Umma ta ce kar na daɗe. Nana ta faɗa ta miƙe da niyar tafiya har ta fara barin cikin palon sai ji ta yi Ameera na faɗin “Ke kinsan bana so ina magana ban ƙare ba mutum ya tashi zai ta fi, wannan ai raini ne, dan ubanki yaushe har na fara sakar miki ido har haka da ina miki magana zaki tashi ki tafi? To wallahi idan kika bar gidan nan to kar ki sake dawowa, idan kuwa na sake ganin ƙafarki a gidana Allah sai na karya miki su. Nana tayi mutuwar tsaye tana kallon Ameera cike da mamaki domin da farko ta yi tunanin wasa take yi sai yanzu da ta juyo ta kalli fuskanta sai taga yanda ta ke haɗa rai, kuma cikin fushi take maganar. Ganin haka Nana ta ce.

“Haba Anty Meera Umma ce fa ta ce kar na daɗ…”Inji uwar ki itace ta ce haka? Idan baki barmini gida ba sai na ɓallaki banziya munafuka, ai dama nasan munafunci ya kawo ki gidan kuma kin gama. Jin haka Nana ta ƙara ɓude baki zata yi magana amma Ameera ta bita da gudu wanda yasa ta fasa faɗin abun da ta yi niyya ta yi waje tana ihuu! Sosai Ameera ta ji haushin abun da Nana tai mata, bata so a gwale ta haka, tana magana a tari numfashin ta ko a tashi a tafi ko aƙi sauraronta abun na ɓata mata rai sosai da sosai.

Tun daga wannan lokacin Ameera ta ƙara zama masifaffiya ta bugawa a jarida, sosai masifar tata ta wuce gona da iri, domin kowa yazo gidan basa wanyewa lafiya, haka ma Adam ya kawo mata mai aiki amma tsabar masifa da bala’i mai aikin ta gudu da kanta, domin har duka take mata, shi kansa Adam yanzu bai cika zaman gida ba saboda rashin son zaman lafiya irin na Ameera. Kadija ta warke amma bata ƙara zuwa gidan ba domin ta ce idan kuka ganta a gidan to Ameera ta sauƙa ne. Yanzu haka Ameera ce ta ce da Adam dole ya ƙara samo mata ƴar aiki domin bazata iya komai na gidan ita ɗaya ba. Jin haka yasa shima ya ce “Sai dai ta nema da kanta amma Ameera ta da me shi da tashin hankali kala-kala har sai da ya je ya samo wata ƙaramar yarinya wacce kana kollonta kasan baƙauyiya ce, Adam ya yi hakan ne ko zata jure abun da Ameera ɗin za tai mata. yanzu haka cikin Ameera watansa biyar harda wasu kwanaki, kana kollonta zakaga ɗan cikin yayi kamar an kifa ɗan ƙaramin ƙwarya.

Ya na kan hanyarsa ta dawowa daga gurin aiki ya ga yarinyar tare da mahaifiyar ta suna bara a kan trefik (kan titi) hakan yasa ya tsaya ya kirasu bayan sun zo ya basu sadaƙa sannan ya sanar da su cewar yana so ya ɗauki wannan yarinyar zata dinga ta ya matarsa aiki a gida. Jin haka yasa suka amince kasancewar ita uwar ba wai makanta ce tasa suke yin barar ba, domin kuwa idanunta ƙalau suke, haka ma ƙafadunta, su dai san dalilin su na yin barar, amma dai lafiya ƙalau suke, hasalima ba wani tsufa ita uwar yarinyar ta yi ba. Haka Adam ya sa su Amota har gidansa kafin ya sallami uwar ta koma gurin barnta shi kuma ya shiga cikin da yarinyar. Tun kafin ya shiga ciki yake tsoron abunda zai faru domin kuwa Adam yasan bata shiri da ƙazama ko yan ƙauye. Da sallama ya shiga cikin palon ita dai yarinyar sai binsa a baya ta ke tana kalle-kalle ganin haɗuwar palon da ta shigo. Ganin babu kowa a palon ne yasa ya nufi ɗakinta yana kiranta. Yana shiga ɗakin ya sameta ta a kwance riƙe da waya tana fama da karance-karance littafi, domin yawanci yanzu abun da ta ke yi kenan, idan kuma taso ayi zaman lafiya to Adam ɗin ne ke karanta mata ita kuma tana zaune ta hakince kamar sarauniya, idan baya yi da sauri ta ce ya dinga sauri idan kuma yayi a hankali nan ma tayi ƙorafi. Idan kuwa a kazo gurin dariya tsabar dariya har marinsa take yi wai duk a cikin dariya ne, sai tai ta dukansa tana ƙyaƙyata dariya kamar taɓaɓɓiya, sannan bai isa ya tsaya ya ce ya gaji da kansa ba sai dai idan har itace ta ce ya isa haka. Tana karanta littattafan marubuta da yawa amma tafi son littafin Khadija Candy da Batul Mamun da S Reza. Tabbas idai sun fitar da sabon labari to sai ta karanta domin tana ƙaruwa sosai da littatafan su, yanzu ma haka littafin Khadija Candy ta ke karantawa na WANI GARI, sosai karatun ya ɗauki hankalinta harma bata san ya shigo ɗakin ba. Har saida Adam yazo har kusa da ita kafin ta ɗago kai ta kalle shi. Ai kuwa cikin masifar ƙatse mata karatu da yayi ta fara faɗin.

“Yanzu fisabililahi haka addini ya ce a shigo ɗaki babu sallama? Kana babba da kai amma har yanzu baka iya yin sallama ba idan zaka shiga guri, ni bana son irin haka dan Allah a koyi sallama kafin dai yara su taru su ɗauki irin wannan ɗabia’ar. Girgiza kai kawai yayi domin izuwa yanzu ya saba jin kalamai masu tsauri fiye da wannan daga bakinta. ya ce “Na samo miki ƴar aikin tana Palo ki fita ki ganta ni zan fita? Kasancewar tana cikin karatu yasa ta ce “Wai dai tazo gidan ba? To wani irin gani kuma zan mata, haba dan Allah wai mai yasa kullum Adam baka son ganina cikin farin ciki ne, saboda ka kawo ƴar aiki sai kawai na bar abun da na ke yi na zo ganinta wato itace ma matar gidan da har sai nazo na gai data. Tana faɗa ta ja tsaki ta koma ta zauna. Ganin bai ce komai ba ne kuma zai juya ya tafi cikin masifa domin bata so tayi masifa bai tanka mata ba, ta fi son ya dinga tanka mata yanda zata sauke masa na yau gaba ɗaya. Ta ce “Malam kazo ka fassara mini wannan yaran da wannan rayinyar take yi a cikin wannan littafin wai yaran Garuk ne.

Ta faɗa tana zaune a gurin ta na jira ya zo gurin. Cike da dauriya Adam ya ce “Ban iya ba” yana faɗa ya juya ya bar ɗakin. Ai kuwa ta ce “Wallahi sai ka fassara mini kama isa ka ce baka iya yaran Garuk ba. Ta na faɗa ta biyo shi a baya da gudu har cikin palon ta miƙa masa wayar ta ce

“Duba ka fassara min yanzu. Adam ya ce “Wai ke mai yasa baki da hankali ne ba kya ganin baƙuwa ne? Kuma na ce miki ni bamma san wani yare yaran Garuk ba bare ma har na iya fassara wa. Jin haka yasa Ameera kallon yarinyar da aka kawo mata a matsayin ƴar aiki, taso yin magana amma maganar da Adam ɗin yayi mata na cewar bata da hankali yasa ta ji zafi harma hakan ya nuna a fuskanta.

Ganin haka yasa kafin ta yi magana Adam yayi saurin cewa “Wasa nake miki Honey kawo na fassara miki, ai yaran Garuk ana mana sabjet ɗin sa a school kuma na iya sosai kawo nagani? Ya miƙa hannu ya amshi wayar yana kallon fuskarta ganin ta na murmushi! “Yawwa ko kaifa wallahi littafin ya na min daɗi ne to kuma ina so naji abun da yarinyar take cewa a gurin ni kuma ban iya yaran ba. Adam ya karɓa ya karanta gurin ya kai sau biyar yana so yasan wani irin amsa zai bata wacce zata yi daidai da gurin. Ita kuma ganin yayi shiru yasa ta ce “Allasarki ba dai shi ma likitan zaginsa ta yi ba dai ko? Ta faɗa da alamar tausayi. Jin haka yasa Adam samun madafa cikin yanayin tausayi ya ce “Eh wallahi nima abun ne yake ta bani mamaki irin zagin da take masa, sosai fa ta dinga zaƙulo manya-manyan zagi kala-kala wanda haramunne ma kayi zagi da yaran Garuk da irin wannan kalmomin. Kai allasarki likita ya zagu? Ameera ta ce “Kai amma Waira bata kyauta ba shi da ya taimaka miki mai ye na zagi, ni har ma littafin ya fita a kaina. Ta na faɗa ta fita daga cikin littafin tana jin babu daɗi. Sai a lokacin ta kalli ƴar aikin ta ce “Wannan mai zubin abun tsoron ce mai aikin gidan nawa? Dubeta fa ka ga kamar ta shekara bata yi wanka ba.

Cikin tsawa Ameera Ta ce “Dan ubanki ba kya yin wanka ne? “Cike da tsoro ta ce “I i ina ina ina yi! Ameera zata ƙara magana Adam ya ce “Please honey kiyi a hankali ƙaramar yarinya ce kibita a hankali. “Wannan ƙazamar zaka kawo mana gida Adam? Yanzu dan Allah kai sai ka yarda wannan yarinyar ta zama mai dafa maka abinci da share maka ɗaki da wanke-wanke? Ameera ta faɗa tana matsowa kusa da yarinyar harda toshe hanci. Ita kuwa yarinyar idonta ƙur a kan Ameera kamar mai kallon tv, sosai ta kafe cikin Meera da ido kamar mai gani har hanji, ita dai Ameera bata lura da kallon ƙurullar da take mata ba, shi kuwa Adam tsaf ya kulla harma ya fara tsoron irin kallon. Ganin har lokacin da Amera ta ke juya yarinyar bata daina bin cikin Ameera da kallon bane ya sa Adam saurin jawo da Ameera baya ya na cewa “Honey duk zata iya komai dan Allah ki barta. Ameera ta kalli yarinyar sai yanzu ta kula da fuskar yarinyar gata kyakkyawan gaske sai dai ƙazanta da ya bayyana a jikinta, Afili ta ce “Yaya sunanki? Yarinyar ta ce

“Haura”

Ameera ta kalli Adam ta ce “Meye kuma Haura kamar wani sunan yan kidnapping? Jin haka yasa Ameera bata sake cewa Kawai ba ta ce “Adam ya kai ta ɗakinta an jima zata kirata ta nuna mata aikace-aikacen da zata dinga yi, kuma tayi wanka yanzu! Shi dai Adam sai bin yarinyar da kallo ya keyi yana ta nazarin ta, sosai wani ɓangare daga zuriyar sa ya ke ƙoƙarin ƙin yarda da yarinyar. Bayan ya kaita ɗakin ne ya nuna mata komai da zata dinga amfani da shi harda toilet da dai komai, bayan ya gama nuna mata ne ya fito sai kuma wata zuciyar ta ce ya ɓoye ya ga wani abu yarinyar zatayi son tabbatar wa ya laɓe daga jikin ƙofa ta baya yana kallon yarinyar.

Gani yayi ta zauna a kan gadon ta ɗaga kanta sama tana ta juya idanunta farare a saman ɗakin. Yana tsaye yaga ta miƙe kamar zata fito sai kuma yaga ta ƙara komawa ta zauna, ta daɗe a haka kafin ta miƙe ta shiga toilet, yana dai tsaye sai gata ta fito tsirara aihuwar uwarta, gashin kannan nata sun zubo mata har gadon baya sun zana kamar ba nata ba. Kallo ɗaya Adam yayi mata ya ɗauke kansa yana jin wani faduwar gaba, babu shiri ya juya ya bar gurin yana ɗan ƙoƙarin danne yanayin da ya shiga, sai haɗa hanya ya ke yi yana waigen baya kamar yarinyar ce ta biyo shi.

Misalin biyar na yammacin ranar Ameera ta je har ɗakin Haura ta kirata lokacin Adam baya gida. Zama ta yi a kan kujera ita kuma ta nuna mata ƙasa ta tsuguna kafin ta ce “Ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurareni, kar sai na gama kice baki gane wani abun ba. Kafin nan wannan kayan karki ƙara mayar da su, an jima ko gobe za’a sayo miki kaya suma koda an kawo miki ba’a maimaita kaya sau biyu kina jina ko? “Eh”

. Da farko dai kin iya girki? Haura ta yi shiru kafin ta ɗaga kai. Ameera ta ce “Dan ubanki magana za ki yi ba ɗaga kai ba. Cikin sanyin murya ta ce “Eh ina yi”

“Ok to daga yau girkin gidannan safe rana duk kece zaki yi, bama yin girkin dare, sannan kullum zaki share gidannan gaba ɗaya ki yi mofin ɗin ko ina, ki shiga ɗakuna suma ki gyara su, sannan bana son zama da ƙazanta kullum wanka sau uku safe rana da yamma, kina dai jina ko? Haura ta ce “Eh ina ji” Ameera ta sake cewa “Kin iya karatu da rubutu ko?

Haura ta ce “Wani irin rubuta da karatu?

Cikin rashin fahimtar tambayar Ameera ta ce “Rubutun Hausa da na Turanci mana.

“Na iya na Hausa da na garinmu amma ban iya na tauranci ba. Ameera ta ɗan ƙura mata ido ganin yadda ta kira turancin da tauranci. Ta so tambayar ta wani yarene na garin nasu amma tsabar jin kai yasa ta ce “To tunda kin iya na Hausa ai shikenan. Yanzu tashi ki shiga kicin ki dafa min indomin naji ko kin iya girki. Sannan ina ƙara jaddada muki wallahi wallahi Karki yadda na sameki da munafunci ko ƙarya ko gulma ko ha’incin. Tana faɗa ta buɗe wayarta tana shiga domin fara karatun sabon littafin da ta siya ɗazu na littafin UWATA CE SILA na S-Reza. Ko fara karatun ba ta yi ba tana dai karanta jawaban marubucin ne kafin a shiga cikin littafin sai ji tayi ance Anty na gama.

Cike da mamaki ta ke kallon indomin wanda sai tiririn zafi haɗi da wani irin ƙamshin daɗi ke fita daga cikin sa. Sosai take kallon Haura ka na ta kalli abincin. Lokaci ɗaya ta ji abincin ya shiga ranta sai ta fasa faɗin abun da taso faɗin kawai ta ɗauki indomin zata fara ci, sai kuma ta kalli haura ta ce “Ɗauki wannan wayar ki dinga karanta min wannan littafin afili ina saura? Ganin bata ɗauka bane yasa Ameera daka mata tsawa ta na cewa “Dan uwarki bada ke nake magana bane? Da sauri Haura ta ɗauki wayar ta ƙura mata ido.

“Wai dan ƙaniyrki ina wasa da ke ne? Bazaki fara karatun bane sai na watsa miki wannan abinci? Ta faɗa daidai lokacin da daɗin abincin ke ratsa ƙwaƙwalwarta.

Cikin muryar kuka Haura ta ce “Ban iya ba!

Cike da mamaki Ameera ta ce “Baki iya me ba?

“Karatun” Haura ta faɗi iya gaskiyarta.

Cikin tsananin mamaki da rainin hankali Amera ta ce “To dan hancin uwar ki mai yasa da kika ce min kin iya?

Haura ta ce “Wannan ne ban iya ba. Ta faɗa tana nuna wayar.

Tsabar haushi da takaici yasa Ameera faɗin “To wannan ɗin yaran ubanki ne, ba kece kika ce Hausa kawai kika iya ba, to wannan menene?

Haura ta ce “Ai wannan ba Hausa ba ne”

Sai a lokacin Ameera ta ajiye abinci ta lailayo wani abun zagi da jin sama zunubi ne ta makawa Haura kafin ta jawo ta ta kwaɗa mata wani lafiyayen mari kafin nan ta ce “Idan ba Hausa bane da yaran ubanki S Reza yake rubutun littafi?

Cikin jin zafin marin da yasa saida ta fashe da kuka ta ce “Wallahi ba Hausa bane wani yaran ne da ban, kuma ki duba ki gani. Tsabar takaice sai da ta ƙara mata wani marin har tana ture ta kafin ta duba wayar da nufin dubawa.

Cikin tsoro da mamaki haɗi da firgici take kallon littafin da ta siya da rubutun Hausa amma yanzu ya koma wani irin rubutun da bata san ma ko na ina bane. Ga dai sunan littafin da Hausa amma komai da wani irin yare yake wanda bata ma san ta ina zata fara karantawa ba. Ta ke kuma ta yi wani tunani. Ɗazu kafin haura ta kawo mata abinci fa ta fara karanta jawaban marubucin na cikin littafin kuma da Hausa ya ke amma yanzu harda su ɗin sun koma wani yare da ban, sannan shi kansa abincin kamar bata yi minti biyu ba ta dawo wai ta gama, sannan kuma ita dai bata koya mata amfani da kicin ɗin ba duba da yarinyar kamar bata taɓa amfani da irin wannan kicin ɗin ba. Sai a lokacin ta kalli Haura ganin tana kuka ta daka mata tsawa ta na faɗin “Dan ubanki wacce ke? ina kika shiga min da littafina? Ni zaki rainawa hankali, yanzu na fara ƙaranta littafi lami lafiya daga zuwanki sai ya koma wani abun kamar yaran chana! Ina kika shiga min da littafi kuma wacce ke na ce!? Ameera ta ƙara sa maganar cikin ihu da ɓacin rai!

Haura ta ce “Wallahi Anty nima haka na gan shi ban san yaya a kayi b, kuma ni ba kowa ba ce Haura c… “Kafin ta ƙara sa sai ji kayi tass ta ɗauke bakin nata da mari. Ameera ta fita daga cikin littafin ta sake komawa, amma dai har yanzu haka yake, take ta kunna Data ta shiga Whasopp domin sake yiwa mai littafin magana ya turo mata wani. Ko da ya turo mata shima dai wanda ya turo mata ɗin haka ne. Hakan yasa ta tambaye shi wai da wani yare a ka rubuta littafin Uwata ce sila? S Reza yayi dariya ya ce “Ban gane ba Haujiya Ameera Ai da yaran Hausa nake rubuta duk littatafai na. Bata ƙara cewa komai ba ta sauƙa a online ta ce da Haura wannan wani yare ne? Ta kafe ta da ido.

Haura ta ce “Nima ban sani ba.

Cikin takaicin da yazo mata har wuya ta kamo haura ta fara jibgarta kaman an aiko ta, ta na faɗin “Karya keke tsinaninya wallahi kinsan komai wani guri kika shiga a wayar da rubutun ya zama haka kuma sai kin mayar min. Ana cikin haka sai ga Adam ya shigo gidan shima tun da ya fita yake ta nazarin yarinyar, sannan ga surar yarinyar da ya gani ya tsaya masa a rai, sosai yaso ace ya tsaya ya ƙare mata kallo amma ya kasa. Yanzu haka da sauri ya shigo gidan kasancewar tun daga waje yaje jin ihuu Haura.

<< Ameera Da Adam 4Ameera Da Adam 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×