Sosai dambe ya kacame tsakanin Nana da Nasiru kowa na furta duk abinda ya zo bakin sa, al’ummar dake gurin ne suka yi nasarar raba wannan rikicin, Nasiru ya shige motar sa ya barta a gurin, itama ta tare mai ɗan sahu ta shiga ta bar gurin cikin ɗacin rai!.
Bayan tafiyar su Kadija likitan ya ƙara ma Adam allura sannan ya sanar da Najib cewa in sha Allah zuwa jibi jikin zaiyi sauƙi sai a sallamshi. Najib ya amsa da ok Allah ya kaimu lafiya. Bayan likitan ya fita Najib ya tsaya ya na tunanin maganar Haura ta ɗazu. “Kenan da gaske itace ta soka masa wuƙa! Idan kuwa itace to gaskiya a kwai matsala domin wannan abun nata zai iya zama hauka. Haka dai ya yanke shawarar idan an sallami shi kawai gidansa zai wuce da shi har ya ƙarara warkewa.
Su Haura suna isa gida Ameera ta wuce sashinta cikin sauri domin har lokacin abun da wannan yaran ya mata bai bar kanta ba, wanka ta fara yi kafin ta saka wata doguwar riga wanda cikinta ya fito sosai a rigar. Ɗakin Haura ta nufa kanta tsaye domin ta sama musu abun da zasu karya da shi. Babu ko sallama ta tura ƙofar ɗakin haɗi da ambatar sunanta. Sai dai taga wayam babu kowa a cikin ɗakin, har zata juya sai kuma taji ana ƙoƙarin buɗe toilet hakan yasa ta tsaya ta na jiran fitowar ta.
Kallonta ta ke yi babu ko ƙifta ido tsabar mamaki. Tsawar da ta buga mata ne yasa ta saurin kwaɗa wani uban ƙara na tsoro domin sam bata lura da ita a ɗakin ba. “Ke dan ubanki haka ake fitowa daga toilet a garinku? Ko bakiga tawul a cikin toilet ɗin da zaki rufe jikinki bane? Haura ta rikece ta kasa magana sai ihu ta ke yi. Ganin haka yasa Ameera riƙo mata hannu ɗaya ta juyo da ita da kyau sannan ta sauke mata marin da yasa ta dawo hankalin ta. Ai kuwa cak ta tsaya tana zaro ido. Cike da umarni Ameera ta ce “Daga yau karki ƙara fitowa wanka tsirara? Haura ta ɗaga kai. Ta ƙara cewa “Sannan karki ƙara kwana bakiyi wanka ba? Nan ma dai ɗaga kai ta yi. Sannan Ameera ta riƙe mata kunne ta muɗa ta na faɗin “Daga yau babu ruwan ki da shiga lamarin gidana a kan komai, yanzu kuma na baki minti goma ki sama mana abin kari, saura kuma ki dafa mana ɗan wake dan ubanki. Cikin kuka Haura ta ce “To me zan dafa? “Ki soya doya da ƙwai sai ki haɗa mana shayi ina jiranki yunwa nake ji. Ta ƙarasa tana barin ɗakin.
Tana fita Haura ta share hawayenta sannan ta samu ɗaya daga cikin kayan da aka saya mata ta saka, lokaci ɗaya ta saki dariya ganin yadda rigar tai mata chas-chas a jiki kamar dama ita ake jira tazo ta saya. Sosai ta shagala da kallon kanta a madubin ɗakin sai ɓaɓɓaka dariya take yi kamar wata zararriya. A haka dai ta fito tana ta dariya ta shiga kicin. Ameera kuwa sai da ta koma ɗaki ta tuna ashe fa basu da ƙwai s kicin ya ƙare hakan yasa ta riƙe kai ta na sakin gajeran tsaki a ranta, juyawa ta yi da nufin komawa ta sanar da ita cewar ta dafa wani abun sai kuma kira ya shigo wayarta. Ganin sunan Umma ne yasa ta tsaya tana kallon wayar har ta tsinke, tana tsinkewa wani kiran ya biyo baya hakan yasa ta ɗaga haɗi da sallama. “Gani nan a hanyar gidan ki idan ma ba kya gidan to ki dawo yanzu” Umma tana faɗa ta kashe wayarta. Ameera ta saki tsaki ta nufi ɗakin Haura. Kafin ta ƙarass ta hango Haura a gurin daining tebul ta gama jere komai tana goge-,goge na kayan cikin palon. Cike da mamaki ta nufo gurin ta bude kular farko taga doya da ƙwai a soye a guri ɗaya, kula ta biyu kuma zallar ƙwai ne a ka soya da yawa shima da ban. Kula ta uku kuma miyar ƙwai ce da naman kaza ya sha suya har wani ɗaukar ido ya keyi. Sai kuma plas na ruwan zafi sai gwangwanin madara da na suga da na baumbita. Sosai Ameera ta ke mamakin komai hakan yasa ta kai kallonta ga Haura wacce ke ta aikin ta. “Ke Haura zo nan” Ameera ta faɗa cikin tsawa.
Da sauri ta ƙara so fuska cike da fara’a. Sai a lokacin Ameera ta kalli shigar da tayi. Rigar tai mata kyau amma rashin iya sakawa yasa basu zauna mata da kyau ba. Cikin sanyin murya ta fara cewa “Keda wa kuka dafa wannan abincin? Haura ta ce “Ni ɗaya ce”
“A ina kaka samo ƙwai har kika yi amfani da shi?
“A kicin na samu, ai a kwai da yawa”
Ameera ta saki ajiyar zuciya ta ce “Yaya ma sunan garin ku?
Haura ta amsa da “Garuk”
“Kince ku ba musulmai bane ko? Haura ta ɗaga kai.
Ta ce “To kuna yin tsafi ne! Ko dai aljannune ku? Haura ta ce “A’a ba aljannu bane. Kuma bama… Kafin ta ƙara sa an turo ƙofar palon an shigo haɗi da sallama. Umma ce sai Nana a bayanta fuskokinsu babu sauƙin kallo ga mai laifi. Da sauri Ameera ta nufi Uama tata cikin fara’a da ɗoki tana ƙoƙarin rungume ta amma Umma ta daka mata tsawa tana faɗin “Sannu shaffiya da mai, wato dan tsabar rashin hankali da gidadanci irin naki sai da kika san ta yadda kika yi har kika raba wannan auran ko? Auran da ya rage wata ɗaya amma yazo kin haifar da tashin hankali a gidaje guda biyu, yanzu ga shi yazo wai dole sai an bashi kayan sa, shi kuma Abbanku yace sai ta samu wani kafin a ba shi kayan sa hakan ya haifar da faɗa harda manya a ciki kuma duk kece kika haɗa a wannan ban zar halayyar taki ta shirme wacce bamu san daga ina kika aro kika yafa ba.
Cike da mamaki Ameera ta ce “Ma sha Allah tunda an fasa auran yanzu kowa sai ya huta! Ta faɗa ki a jikin ta. Umma ta kai mata mari amma amma ta kauce ta ce “To Umma dan Allah kuma ku manta da lamarin wannan yaron wallhi ɗan iska ne, hannu fa ya ƙe riƙe mata a cikin mutane fisabililahi! Kuma ma ai indai faɗan Nana da Nasiru ne kowa yasan zasu shirya kawai ku barshi da kansa zai dawo idan har da gaske son nata yake ba iskanci ya kawo shi ba. Cike da takaici Umma ta ce “Allah dai ya wadai wallahi idan ma hannu ya riƙe mata sai ki fara zaginsa ba nasiha ba, haka ake gyara! To yanzu haka Abbanku yana police station duk a dalilin ki. Ameera ta ce “Police station dai? To a kan me?
“A kan ya ce ba zai bada kaya ba sai ƴarsa ta samu tsayayye ba.
“Cicin faɗa Ameera ta fara “Wallahi wannan mutanan basu da mutunci yanzu a kan kayan lefen da kwata-kwata guda nawa suke da sadakin da ya kawo shine zasu kai Abba police station, to wallhi basu isaba ni dama nasan wannan yaron ba ɗan arziki bane, wallhi ɗan iska ne. Cike da zafin zuciya da Nana ta gama ƙunsa a gurin yayar tata ta ce…
“Wai kina ta cewa ɗan isa, me yayi na is kanci ne? Saboda ya riƙe hannuna ne ko? Ta ci gaba da faɗin idan sabo da haka ne to ke lokacin da Adam ya ke nemanki meye bakuyi ba? Ina ce har kowa sai da yasa muku ido tsabar zallar iskanci da kuke yi, wacce irin runguma ce baya miki a gaban mu, ko kina ce mun manta ne, to a gurin ki na koya. Take Ameera ta fara masifa “Yanzu Umma a gaban ki yarinyar nan take faɗa min irin wannan maganar ko? Wato har raini ya shiga tsakanina da ke har haka ko, ni zaki wa sharri, to idan ma haka ne ai ni ya aureni dan uwarki. Umma ta ce “Gani nan uwar tata zage ni yadda kikeso. Haura dai abincinta ta ci sannan ta miƙe ta bar palon.
Sosai Nana ta furta abubuwan da ke ranta ita kuwa Umma bata hanata ba domin itama abun da Ameera ta yi ya ɓata mata rai sosai. A haka Umma ta bar gidan ita da Nana tana sanar mata kar ta ƙara shiga sabgar Nana da Nasiru ko da Allah yasa abun ya shiryu. Amma Ameera ta ce “In sha Allah ma ba zai shiryu ba. Hakan yasa itama ta yi fushi ko irin Allah ya tsare hanya ɗin nan ma ba tai musu ba bare ma aje ga batun rakiya. Suna tafiya ta dawo kan Haura ta sauke mata gaba ɗaya baƙin cikin da ta ƙusa, domin kuwa duka tai mata babu laifin fari bare na baƙi, dukda abubuwan kirkir da tai mata.
Haka suka cigaba da zama da Haura kullum cikin sabon abun mamaki take yi, har yanzu bata ƙara leƙewa asibiti gurin Adam ba haka bata kira su Umma taji a wani hali suke ba, ko da kuwa jin an saki Abba ne ko har yanzu yana ƙullen ne. Kullum kwanan duniya sai ta daki Haura duk da irin ƙoƙarin da take yi, komai na gidan itace amma kuskure ɗaya zata yi ta sha duka. Izuwa yanzu ta daina mamaki da lamarin Haura domin ta gene cewar su din matsafa ne.
Tana kwace a palo kan kujera tana karatun littafin da ta siya na Batul Mamun mai suna uwa uwa ce wanda labarin ya ɗauki hankalin ta sosai, sai murmushi take saki ta na sake juyawa dags kwancen da ta ke. Sosai take mamakin halin yaran innayo, ace yara mata kusan guda shida amma duk babu wacce take taimaka mata gashi kuma mazajensu masu hali.
Kwana huɗu kawai ta ɗan ƙara kumbura cikin ya ƙara fitowa ga ƴar ƙiba da ta yi. Sosai ya tsaya ya na ƙare mata kallo daga ƙofar ɗakin duk yayi kewaarta barinma cikin dake jikinta, hakan yasa lokacin da Najib ya ce su wuce gidansa ya ce a’a shi dai yana son zuwa yaga halin da matarsa ke ciki. A hankali ya isa saitin kanta yasunkuyo kusa da kunnenta ya ce “Honey I’m back” Zumbur ta meƙe har tana sakin wayar, ganin sa yasa ta saki tsaki ta na kawar da kanta. Cikin murmushi ya ce “Please Honey I miss you and my baby. Ya faɗa ya na son shafo cikin nata. Da sauri ta ture hannunsa ta na faɗin “Ba kai kace baka son ganinmu ba, kawai kaje ka zauna da su Kadija da abokinka tun da mu bamu da wani amfani a rayuwarka. Ta ƙara sa tana jin furicin da yayi tun a lokacin yana dawo mata sabo. Adam ya ce “I’m sorry honey ba haka nake nufi ba baki fahimce ni bane please I’m sorry.
Ya ƙara sa yana kamota ya haɗe jikinsu guri ɗaya. Take ta saki kukan kewarsa da tayi. Soyayyar Adam ta daban ce a cikin zuciyarta ita kadai tasan irin wahalar da tasha na rashin sa. Adam ya shiga shafa cikin nata yana faɗin I hop baby yana lafiya dai ko? Shiru ta yi tana ƙara lafewa a jikin sa. A hankali ta ce “Ya jikin naka ? Ta faɗa tana ɗagowa tana kallon gurin da ya warke sai tabo kawai. “I’m fine jiki yayi sauƙi sai godiyar Allah, ina fatan dai lafiya kike zaune da wannan ƴar aikin ko? Ameera ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Hakan yasa ya jata suka shiga cikin ɗakin yana riƙe da ita. Suna shiga toilet ya jata suka yi wanka tare sannan ya shafa mata mai itama ta shafa masa cike da farin ciki. Kayan ƴan boooll na Chelsea mai ruwan blue mai ɗauke da sunan Yokohama a gaban rigar suka saka, sai kuma bayan rigar mai ɗauke da sunan Hazard mai labba goma a baya kasancewar Adam na son mutumin. Sosai cikin nata ya ɗaga rigar har ma rigar na neman yi mata ka ɗan. Nan ya shiga ɗaukar su hotuna wanda sun kwana uku basu yi ba. Sosai Adam ya rungumota a jikin sa yana faɗin Ameera ta Adam ikon Allah! Ameera ta saki murmushi ta ce Adam na Ameera sai ikon Allah! Duk dariya sukayi domin tunawa da lokacin baya da sukayi. Nan take wasan ya sauya kowa ya shiga faranta wa ɗan uwansa, wanda kowa ya nunawa ɗan uwansa yanda yayi kewar ɗan uwansa. Adam sai saka mata albarka yake yi kamar ba gobe. Haka suka sake yin wani wanka suka ƙara saka irin kayan amma wannan karan masu ruwan kunun ɗorawa (yalo). Haka ya kamata suka fito Palo tana manne a jikin sa.
Koda suka iso sun samu Haura tana gyara palon hakan yasa ta gaisar da Adam haɗi da tambayarsa ya jiki. Adam ya amsa da sauƙi yana kallon yanda itama ta sauya sosai. Afil ya ce “Hony ke ce kika siya mata kaya ne? Ameera ta taɓe baki ta ce “Yaushe zan iya zama da tsama-tsama, ai ya zame mini dole na saya kafin ka dawo kar a kashe ni da tsami. Ya ce “God bless you my beautiful wife, kinyi ƙoƙari gaba ɗaya ma ni na manta ne da batun tafiyar, yanzu kalla yanda ta yi kyau ba kamar lokacin da tazo ba. Ameera ta kawar da kai tana faɗin “Kin gama abincin ne? Tayi tambayar duk da kuwa tasan abinci kamar ma ba girkawa a keyi a cikin gidan ba.
“Eh na gama tun ɗazu kafin Yallaɓai ya shigo” Bata ƙara cewa komai ba suka nufi gurin abincin. Nan Ameera ta zuba musu a flet ɗaya suka fara ci. Suna cikin ci ne Haura zata wuce wa ta kusa da su zata shiga kicin Adam ya bita da kallo. Sosai hankalin sa yayi gurinta wanda ya manta da cewar Ameera na kallonsa. Kallon gurin da yake kallo tayi sai taga Haura na tafiya, tsabar mamaki sai taga kamar tana karkaɗa masa ƴan ƙananan mazaunan ta ta ke yi! Take taji gabanta ya faɗi, lokaci ɗaya wasu banzayen tunani suka fara zuwar mata. Ɗan buka cokalinta tayi a cikin flet ɗin wanda hakan ya dawo da Adam daga kallon tv dan ya tafi. Bai san lokacin da ya furta “Kisa saka kaya “
Cike da mamaki Ameera ta ce “Wani kaya kuma zan saka?
Adam ya waske da faɗin kisa ke kaya mu je mu sayo abubuwan da babu a gidan, in yaso itama wacce yarinyar sai a ƙaro mata kayan ko? Ameera ta yi shiru tana kallonsa har sai da ya tsargu. “Lafiya dai wannan kallo Honey karfa ki hango muni na? Afili ta ce “Ka bari sai gobe yau bana jin daɗi sosai”
“To Allah ya kaimu lafiya matar Adam ita kaɗai babu ƙari” Kafin Ameera ta ce wani abu sai ga Haura ta sake fitowa daga kicin riƙe da flet ta nufo gurin da suka. Tun daga nesa ya kafeta da ido har bai san yana sakin murmushi ba. Shi tun lokacin da ya ganta tsirara to koda yaushe idan ya ganta to a haka yake ƙara kallonta, ga kuma dama ita bata saka hijabi gashi doguwar riga ce mara nauyi siririya a jikin. Ameera ta saci kallon Adam ai kuwa ta ga harda murmushi yake saki, sannan ta kalli Haura sai taga kamar itama murmushin take masa harda ma huro masa isa da su kanne ido ɗaya. Take Ameera ta ƙware tana ta famam tari! Hakan yasa Adam jawota jikinsa yana mata sannu. Haura kuma ganin haka tayi saurin ajiye abincin da ta kawo ta tsiyayo mata ruwa ta zo ta kusa da Adam tana miƙa masa ruwan ya bata. Lokacin da Adam zai karɓi ruwan sai taga kamar murmushi suke yi, sai taga ya riƙe hannunta ɗaya ya jawota jikinsa yana ƙoƙarin hade bakin nasu.