Skip to content
Part 9 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Sunanta da Adam ya kira ne ya sa ta dawo hankalinta, sai wani zazzaro waje take yi kamar wata munafuka. “Sorry Karɓi ruwa ki sha Honey Please ki dinga cin abinci a hankali kinji? Adam ya faɗa ya na kai mata ruwan saitin bakinta. Babu musu ta karɓa ta kafa kai sai da ta shanye ruwan kafin ta fara sauke ajiyar zuciya ta na kallon Haura wacce tun ɗazu take fama da sannu-sannu. Ta shi ta yi daga gurin ta nufi ɗaki domin so take ta samu damar yin tunani. Sai da ta kusa shiga ɗakin sai ta juyo da nufin ganin yanayin da suke ciki. Ai kuwa ta na juyowa sai taga kamar Haura ta yi saurin sauƙa daga kan cinyer Adam ɗin ne, shi kuma taga kamar shima Adam ɗin gyara jikinsa ya ke yi. Haka ta shige ɗakin har zata zauna sai kuma ta fara leƙe daga cikin ɗakin kasancewar daga cikin ɗakinta ana iya hango wanda yake daining tebul.

Tana leƙowa sai taga Adam ne kaɗai a zaune a gurin, afili ta furta “Muna fiki Allah yasa na kamaka da laifin cin amana ka gani, wai ma to me yake nufi ne!.

Adam kuwa sai da ya tsaya ya cika cikinsa sosai har yana tambayar Haura a ina ta iya girki har haka mai shegen daɗi. Ita kuwa sai ta yi murmushi ta ce “Babu wanda ya koya mata da kanta ta koya. Adam ya kalleta ya ce “Da kanki kuma? “Haura ta amsa da kai. Haka har ya gama lokacin itama ta gama cin nata ta koma ɗaki. Shima yana gamawa ɗakin nasa ya nufa amma sai yaji kamar Muryar mutane biyu a dakin Haura ɗin, hakan yasa ya nufi ɗakin cikin sanɗa. Yana zuwa ya kara kunnen sa domin saurara, ya kai minti biyu bai ji komai ba hakan yasa ya fara shawarar buɗe ɗakin. A hankali ya tura ƙofar ɗakin yana leƙawa. Zaune ya hangota ta dafe kanta hawaye na zubowa daga cikin fararan idanunta, da a’lamar wanka zata shiga domin ɗaure take da wani ɗan ƙaramin tawul wanda tun ranar da Ameera ta ce ba’a fitowa wanka tsirara yasa ta fara ɗaurawa.

Da sauri Adam ya ƙara so gurin da take ya na tambayar lafiya? Da sauri Haura ta ɗago kai sai ga hawayen jini na fitowa daga idanunta ta. A ɗan tsorace Adam ya ce “Inna’ilaihi! Jini ne fa yake fitowa daga idon ki, ya faɗa yana ƙoƙarin komawa baya domin ya tsorata ainin. Da sauri ta fara goge jinin tana ƙaƙalo murmushi ta miƙe tsaye. Ai kuwa ta na miƙewa tawul ɗin ya kwance kafin ta tare shi ya dangane da ƙasa. Adam ƙamewa yayi agurin ya kasa kawar da kansa yayin da ita kuma Haura ta yi saurin shigewa toilet ta na barin tawul ɗin a gurin.

Sai a lokacin ya dawo hankalin sa ya sauke a jiyar zuciya yana juyawa ya bar ɗakin cike da rashin ƙwarin jiki.

Washegari ma kafin su ta shi Haura ta gama haɗa musu komai na kari, hakan yasa suna tashi daga barci suka nufo daining tebul ɗin suka zauna suna cin abincin cike da jin daɗin sa. Ameera ta ce “Honey zaka kaini gida yau idan ka dawo daga aiki sai ka biyo mudawo. Adam ya kalleta kafin ya ce “Kin ce yau zamu ƙarowa wannan yarinyar kaya ko kin manta ne? Ta ke ta ce “An fasa ƙaro mata kayan wanda ta samu ma ta gode. Adam ya ce “No ba za’a yi haka ba, idan na saukeki ni zan je na sayo mata kayan. Da ƙarfi Ameera ta ce “Na ce an fasa sayo mata kayan ko bakaji bane? Wai Adam me kake nufi ne da wannan yarinyar ne naga kana shishige mata da yawa fa, wallahi zaka yi mata sanadin barin wannan gidan.

Da mamaki Adam ya ce “Ina shige mata kuma? Haba honey me kike nufi da zantukanki, ashe baki yarda da ni ba har yanzu. “Eh! Wallahi ban yarda da kaiba in dai akan mace ne ban yarda da kai ba, kuma na faɗa maka karka kuskura ka ƙaro mata kaya, ni nasan kalan kayan da suka dace da ita. Adam dai bai ƙara cewa komai ba har ya kammala cin abincin sa kafin ya koma domin shirin tafiya aiki.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin ƙananan kaya sai zuba uban ƙamshi yake yi kaman anyi ɓarin turare a jikin sa. Ya yi nufin shiga ɗakinta ya kirata amma ya hango Haura ta na goge-goge a palon hakan yasa ya nufo ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna yana kallon ta. Haura kuwa da tun zamansa ta kula da shi sai gaba ɗaya ta kasa sakewa da irin kallon da taga yana mata, ita ta kasa gane masa, haka abun da ya faru tsakanin su jiya ya ƙarasa taji kunya sosai, hakan yasa ta miƙe zata koma ciki idan ya fita ta dawo ta ci gaba. Amma taku ɗaya ta yi ta tsinkayo muryarsa yana kiran ta da kee. A ɗan tsorace ta amsa da “Umhum” Sai kuma ta tsaya tana kallon sa.

“Nan zaki zo. Ya faɗa da ɗan ƙarfi wanda yasa ta ɗago ta saci kallon fuskarsa. A hankali ta ce gani.

Sai da ya gama kallonta sama da ƙasa kafin ya ce “Kije ki shirya zamu fita dake yanzu, kuma karki ɓata mana lokaci. Haura ta ce “Tom” Ta na faɗa ta miƙe daga zaman da tayi a ƙasa tana barin gurin. Bata daɗe da shiga ba sai ga Ameera ta fito cikin shigar wani Les uban su, domin kallo ɗaya ka ɗai less ɗin ke buƙata a gane nauyin kuɗin sa. Ta sha kwalliya kamar ka sace ta ka gudu, ga cikinnan yayi turtsitsi a gaba. A hankali take sauƙowa tana ƙoƙarin yafa ɗan ƙaramin mayafin da ke hannunta fuskar nan tata a murtuƙe babu ko a lamar fara’a.

Tun daga nesa ya zuba mata ido ko rsintsawa baya yi, sosai ya yi suman tsaye yana kallon matar tasa kamar an sauya ta, har ta ƙara so gurin yana tunanin lokacin baya da ta taɓa irin wannan wanka kafin su yi Aure wanda ranar tsabar kyau har faɗa suka nai mi suyi domin shi Adam bai san lokacin da ya rungumota ba ita kuma bata tsammaci haka daga gare shi ba domin basa haka a rayuwar soyayyar ta su.

Ita haushi ma ya bata da irin wannan kallon hakan yasa ta ce “Wai dan Allah me ye wannan ɗin, kaman wacce bata saba yin wanka ba, yanzu fisabililahi idan wani ya gani ai sai ya zata bana maka kwalliya ne sai wata-wata. Adam da ya dawo daga tunanin sa ya ce “Honey kenan ai ke kullum wankanki idan kin yi Allah ƙara rikitani kike yi, kalleki fa kamar wata amarya. Ya faɗa yana ƙara sawa kusa da ita ya shiga shafo cikin nata kamar ya fito da yaron dake ciki. Ganin abun nasa ba na ƙare bane yasa ta ce “Wai zamu tafi ne ko dai sai ka gama wannan abun na ka? Adam ya ce “No mubari wannan yarinyar ta fito domin tare zamu tafi, idan na ajiyeki sai mu ƙarasa da ita mu sayo kayan. Take gaban Ameera ya bada wani darararammm! Jin kamar zata faɗi ne yasa ta naimi guri ta zauna tana kallon sa. “Kenan da gaske Adam yake yi a kan wannan yarinyar! To me yake nufi da haka! Haka dai bata ce masa komai ba har Haura ta fito cikin shigar ta na doguwar riga babu mayafi sai kanta da ta yane, sosai rigar ta amshi jikinta sai sunne kai take yi kamar tai wa sarki laifi. Da kyau Ameera ta kafe yarinyar da kallo ta na so taga ko a kwai wani abu na daban a jikin yarinyar da bata san da shi a gurin mata ba ne. Haka suka shiga motar gaba ɗayan su ba tare da Ameera ta ce komai ba. Har suka isa gidan shi kaɗai yake zan censa domin Ameera kamar ma bata cikin motar. Fitowa ta yi ta na miƙawa Haura jakar hannunta alamar ta ƙarɓa su tafi.

Adam ya ce “Tare da ita fa zamu tafi ko kin manta ne? Ai kuwa dama abun da take jira kenan, dama tana so ta ji ko yana da kunya ko baida ita, jin ya nuna mata tsan-tsar rashin kunya ne yasa cikin harziƙowa ta ce “Tunda ita ɗin ƙanwar uwarka ce ai dole ku tafi tare, yarinyar da ba maharramarkaba itace zaka ce min wai tare zaku tafi, dama naso naga ƙarshen rashin ta idon ka ne, kuma ka nuna min, dama na lura gaba ɗaya ka manne ma wannan yarinyar to wallhi ka sani sai ta bar gidan nan ko kaso ko baka so ba. Adam da ransa ya gama ɓaci jin har tana zaginsa ya ce “Ni kike zagi akan nace zan je da ita na sayo mata kaya? Ya tambaya cikin ɓacin rai! “Ameera ta ce “Ni dai ban zageka ba sai dai ko kaine kaji zagin amma babu inda wannan yarinyar zata bika har ga Allah! Ta na faɗa ta dakawa Haura tsawa dake zaune a cikin motar tana sauraron su. Haka kuwa ta fito daga cikin motar riƙe da jakar tana komawa gefe ta tsaya. Tana fita Adam ya tada motarsa ya fuzgeta a guje ya bar unguwar ba tare da ya ƙara ce mata komai ba. Afili Ameera ta ce “Idan ka ga dama karka tsaya har wata uku kana gudu.

Kunnen Haura ta kamo ta murɗe tana faɗin “Shigiya dan gin arna wata ƙikama karuwa ce ke, ko kuma wani abun ki kai wa mijina har yake neman damuwa da ke. Haka suka nufi gidan kunnen na hannunta Haura kuwa ta kasa ko yin ihu sai rintsaye ido da ta yi.

Sai da suka zo shiga gidan kafin ta sakar mata kunne tana shiga gidan nasu da sallama. Sosai ta yi murna jin an saki Abban nasu, sai dai abun da ya ɓata mata rai shine jin cewar wai auran Nana da Nasiru yana nan wai sun shirya. Afili ta ce “Kai wannan yaro ina ga wallahi maye ne ko dai yana da dangi mayu! Haba duk irin abubuwan da suka faru amma ya dawo, anya Umma wannan yaron alkairi ne a gurin Nana kuwa? Umma ta yi saurin faɗin. “In sha Allah Nasiru alkairi ne kuma shi ba maye bane, sannan ki dinga iya bakinki a kan abun da zai fito daga ciki, sharrin maita bata da sauƙi. Ameera ta saki guntun tsaki ta na faɗin “Wannan auran dai kawai ganganci za’ayi, ya za’ayi yaro kullum dukan ta tun kafin ayi aure amma hakan ace wai shi zata aura, anya Umma kun duba wannan lamarin da idon basira kuwa? Umma ta kafe Ameera da ido ta ce “Wai ke manene matsalar ki da wannan yaron ne? Ameera ta yi caraf ta ce Dukan ta da ya ke yi, kinga duka ko a addinin Musulunci haramunne namiji ya daki matarsa. Kinga Umma in sha Allah zan kawo miki wani littafi mai suna Addininmu mu wanda S-REZA ya rubuta nasan in sha Allah zaki ƙaru sosai littafin yana faɗin abubuwa da dama a kan addininmu, nima ban daɗe da fara karatun sa ba. Umma ta ce “Allah ya tsareni da karatun shirme da ƙarya, tun da banyi ba sai yanzu, idan sanin addini ni to ga Alkur’ani mai girma ko sauran littatafai irin su Mahuwul Islam da ƙawa’idi Ahadari. Ameera ta ce “To ai daga cikin su ake ɗaukowa a rubuta. Umma zata ƙara magana sai ga Nana ta shigo tana sallama.

Tana haɗa ido da Ameera ta zo da gudu tana faɗin anty Meera albishirin ki? Dama ke naso na fara sanarwa da wannan albishir ɗin. Ameera ta ce “Kinga ni ɗagani karki ƙarasa baiwar Allah. Nana ta kalli Umma ta ce Umma ɗan bamu guri, Umma ta ce “Ko baki faɗa ba ta shi zanyi ai! Bayan Umma ta fita Nana ta kalli Haura kafin ta yi magana har ta miƙe zata fita. Ameera ta ce “Munafuka ai da kin tsaya kinji gulma. Nana ta ce “Wai wacce wannan ɗin ne? Ameera ta ce “Wannan bai shafe ki ba.

“To ai naga bata kama da mijin naki ne bare nace ƙanwarsa ce ko ƴar uwarsa. Amma ta ce “Wai Nana a ina kika koyo munafunci da gulma da

Gutsiri tsoma ne? Ganin zata fara masifarne yasa Nana faɗin. “Anty Meera kin san me?

Ta ce “Sai kin faɗa “

Nana ta gyara zama ta na faɗin “wallahi wai harda makulli mota zai haɗo min a sabon lefen da zai kawo, wai yana so ya bawa mara ɗa kunya. Ameera ta ce “To ai idan yana so ya burge ko kuma yayi abin da wasu basu yi a wannan layin ba to jirgi zai baki, domin mota tsohon yayi ce, ko baki faɗa masa cewar Adam ya haɗe lefena da sabuwar mota ba ne, kuma shi bai taɓa shiga har cikin gidan iyayena ya ci musu mutunci ba, ko kuma yasa a kulle ubana a police station ba, to shi wannan in bada rashin kunya har ya iya ƙara haɗa ido da mu dan gyatumarsa. Nana da izuwa yanzu ta gana ƙuluwa ta ce “Ta ce to anty ko dai ɓakin ciki keke min ne da wannan abun arziƙin?

<< Ameera Da Adam 8Ameera Da Adam 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×