Nana ta kalli Ameera cike da mamaki ta ce “Wannan ba wannan ƴar aikin taki ba ce haka? Nana ta yi tambayar ne ganin irin shigar dake jikin Haura kamar wata matar gida, ko ɗan kwali babu a kanta, itama Ɓultuwa ta yi shiga irin ta masu iko da gidan ko masu iko da mai gidan. Itama kanta Ameera abun ya bata mamaki ganin irin kallon da suka tsaya suna mu su. Cike da isa da nuna cewar ita ce Ameera matar Adam ta ce “Ke uban wa ye ya baki izinin saka irin waɗannan kayan a cikin gidana? Ko an faɗa miki nan gidan karuwan da kika saba zuwa ne? Karo na farko da Ɓultuwa ta magantu a kan Ameera kenan, ta ce “Dama gurinki zamu je sai kuma gaki Allah ya kawo ki. Cikin girma da mutunci nake son sanar miki da matsayin mu ya sauya daga ƴan aiki zuwa masu gida, sabo da haka kisan irin kalaman da zaki dinga furta mana, nasan mai gidan ki ya sanar dake batun auran da zai yi, kuma Kin san wa zai aura itace Haura. Kuma ya yi haka ne domin rufin asirin ki na kashe mata uwa da kika yi. Saboda haka idan ba so kike maganar baya ta dawo ba to ki bi wannan auran da addu’a ko kiyi shiru, idan kuma kinƙi…! Ɓultuwa ta ƙara sa maganar da alamar barazana.
Lokaci ɗaya ran Ameera ya gama ɓaci, ashe da gaske ya sanar da su, shin dama wai Adam ba wasa yake yi ba ne? Ita babban damuwarta da a ke cewa ita ce ta kashe wannan matar, wato sabo da haka kowa yake kafa hujja da hakan domin auran ko!? Ita dai Nana tana tsaye tana sauraron wannan tatsuniyar wai Ameera ta kashe mutum, kuma wai Adam ɗin Ameera ne zai ƙara aure.cikin kukan da yafi ƙarfin Ameera ta ce. “Duk abun da ku kai masa Allah yana kallon ku, tsinannu dangin mayo karuwai, kuma in sha Allah baza ku ci galaba a kan mu ba. Tana faɗa ta Kama hannun Nana suka shiga ɗaki.
Suna shiga Ameera ta ƙara fashewa da kuka ta faɗa kan gado tana faɗin “Kinga halin Maza ko Nana? Yanzu kamar Adam wai ni zai wa kishiya tsabar zalunci? Nana da ba wannan maganar ta ke son ji ba ta ce “Wai tsaya me ye waccer matar take faɗa ne? Naji ta na cewa kin kashe wata? Ameera ta ɗago ta ce “Wallahi ƙarya suke min, ni bansan yaya a kayi ba sai gani nayi ta faɗi shine suka kaita asibiti suka dawo suka ce wai nine na kashe ta. Nana ta ce “Kamar yaya kikaga ta faɗi? Haka kawai baki mata komai ba? Ameera da ranta ya ƙara ɓaci ta ce “Kaman yadda kika ji dai, nace ban mata komai ba kawai ta faɗi, ban san komai ba na rantse miki da Allah. Ameera ta ƙara sa tana fashewa da kuka mai mutuƙar karya zuciyar mai sauraro. Duk da cewar Nana ta tausaya mata amma sai ta nuna mata kuskuren ta domin ta fahimci maganar. “Gaskiya Anty Ameera zan faɗa miki wallahi samuwar wannan cikin naki masifa ya zamarwa duk wani na kusa da ke, yanzu dubi fa mijin ki ne zai ƙara aure, kuma nasan duk akan abubuwan da kike masa ne, yanzu gashi sabo da ke Nasiru ya ƙara fasa aurena yau, wanda ban san ma me zan faɗa wa Umma ko Abba ba. Har ga Allah Anty Ameera kin ɓata komai da kanki. Ameera ta miƙe tsaye ta ce “Yanzu kema kin yarda nice na ka she matar ko? Nana ta ce “A irin wannan halin da kika sakawa kanki tsab zaki iya kashe mutum idan kika samu dama. “Ta shi ki bar min gida” Ameera ta faɗa tana haɗe rai.
Nana ta ɗago ta kalleta ta yi murmushi ta ce “Yau ina gidan nan domin anan zan kwana, kuma gaskiya ce sai na faɗa miki ko me zaki yi. “Da yake gidan na ubanki ne ai dole ki zauna, na ce ki tashi ki fita ko na fitar da ke. Ameera ta faɗa cike da nuna tabbacin abun da ta faɗi ɗin. Nana kuwa kallon cikin jikin ta ta yi ganin yadda yayi wani ƙatoto wai amma a haka zata fitar da ni. Kawai sai na Nana ta gyara zama a bakin gadon ta na faɗin “Anty Ameera yanzu zauna muyi magana ta fahimta dan Allah?
Kawai sai Ameera ta fashe da kuka tana ɗora kanta a cinyar Nana. Ita kanta wallahi bata san me ke damunta ba,
Duk inda Adam ya je da batun auran Haura babu wanda yake bashi goyan baya, shi kuwa yana jin idan bai aureta ba to tabbas mutu zai yi. Ganin haka yasa ya koma gurin Najib akan shi ne zai zama wakilin Haura. Aikuwa sosai da Najib yay masa kaca-kaca wanda har sai da ta kai su da faɗan fatar baki. Sosai Adam ke cikin damuwa da rashin samun madafa, ga kuma itama Haura ɗin ta dame shi da batun auran. Ita kuma Ameera daga ya shiga gidan sai masifa akan sai ya kori su Haura mayu ne kuma karuwai ne. Sosai kansa yayi zafi, yana cikin wannan tunanin ya samo mafita.
Gurin wani malami ya je ya zaiyane masa komai dake faruwa akan cewar yarinyar da zai aura ɗin bata da kowa hakan yasa danginsa suka ƙi amincewa da ita, shi kuma yana so ya taimake ta ne. Haka dai Adam ya gama shawo kan malamin shi kuma ya ce zai zama mata wakila. Take Adam ya sanar da shi ranar da za’a ɗaura auran, malamin ya sanar da shi cewa ai ranar ma a kwai ɗaurin aure har biyu da za’ayi, kaga naka zai zama na uku kenan.
Wannan tabbacin wakilan da ya samu ne yasa hankalin sa ɗan kwantawa hakan ya sa ya sanar da su Haura cewar sati mai zuwa za’a ɗaura auran. Sosai Haura da Ɓultuwa ke murna da farin ciki. Ita kuwa Ameera awannan lokacin ta fara ciwo sam-sam. Sosai ta ke shan wahala da cikin ta a wannan lokacin, hakan yasa bata ko fita sosai.
Ɓangaren Nasiru kuwa kaman yadda ya faɗa a ranar da abun ya faru ya turo mota domin kwashe kayan sa. Sai dai wannan karan Abba ya ce “Wallhi babu shegen da ya isa ya mai she su ƙananan mutane. Muddin ya fasa auran ta to sai ya tsaya har Allah ya kawo mata wani in yaso idan anyi auran sai yazo ya amshi kayan sa. Jin haka yasa ran Nasiru ɓaci. Sosai fa wannan karan rikici ya ɓarke wanda har iyayen Nasiru ɗin sai da suka shigo zancen. Dama biki ya rage kwana shida, hakan ya sa a ka dinga rikici har sai da a ka cinye kwana biyar ana abu ɗaya, wanda su masoyan har yanzu babu wanda ya baiwa ɗan uwansa hauƙuri ko wanda ya naimi ɗan uwansa, wanda shi Nasiru yana jira ne tazo ta bashi hakuri, itama kuma Nana jira take sai ya kirata ya bata haƙuri. Sosai wannan karan kowa ya ɗauki zafi domin Abba ya ka sa ya tsare, ita kanta Umma abun ya ɓata mata rai ganin yadda iyayensa ke shigewa gaba-gaba akan rashin mutuncin da yaran su ke shirin aikatawa. Haka dai har a ka wuce kwana shida da ya rage amma Abba bai ba da kaya ba. Hakan yasa maganar ta kai ga yan sanda. Suma suga kasa raba wannan rikicin hakan yasa suka turasu kotu. Sosai ran Abba yayi mugun ɓaci hakan yasa ya tare Nana cikin faɗa ya ke tambayar ta yadda abun ya faru. Take ta sanar masa da komai akan wai hanata zuwa gidan Ameera ya yi shine ita kuma taƙi. Sosai ran Abba ya ɓaci har ya na zubar da ƙwalla. Sosai yake tunanin halin da Ameera ta ke ci, komai a ce Ameera, Ameera dai yarinyar da kaf anguwar nan ake kwatance da ita wajan hakuri da natsuwa amma yanzu ta koma hk. Haka Abba ya tanadi lauya suka fara gabatar da Shari’a da dangin Nasiru.
Ihu take yi tana riƙe cikin ta da yake murɗawa kamar zai fashe, sai faman kiran sunan Nana take yi, ita kuma Nana da ke tsaye a kanta sai sannu take mata. Sosai Ameera ta fita a haiyacin ta, hakan yasa Nana ɗaukar waya ta kira Umma ta sanar mata da kamar fa haihuwa ce. Hakan yasa Umma faɗin ta kira mai gidan ta ta sanar da shi sai a kaita asibiti. Wani irin ihu da Ameera ta sake yasa Nana saurin ka shi wayar tana mata sannu.
Haura da Ɓultuwa kuwa suna gurin gyaran jiki da Adam ya kai su domin kuwa yau za’a ɗaura auran, hakan yasa Ɓultuwa tanai mi da ya basu kuɗi zasuyi gyara irin kitso da lalle da dai sauransu, shi kuma Adam ya ce zai kai su har gurin da a ke yin kitson, haka kuwa ya ɗauke su ya kai su sannan ya basu kuɗi yace su rika a hannunsa, sannan ya biya mai wankin kan.
Adam da yake gaban malam wanda za’a ɗaura auran dake gaban nasu kafin a zo kan nasa yaga wayarsa na ƙara, bai so ya ɗauka ba amma ganin Nana ƙanwar Ameera ya sa ya ɗaga ya na tambayar ta dalilin kiran. Nana ta sanar masa da cewar Ameera ce zata aihu. Ai tun kafin ta ƙara sa yaji irin ihun da ta ke yi. A hankali ya ce “Ina zuwa yanzu amma kafin nazo ki ɗauke ta ki kaita asibiti kafin na iso. Nana ta ce “Wallahi ba zan iya ba, kawai kazo yanzu. Adam ya dawo gurin Malam ya sanar da shi cewar har yaje ya dawo ko? Malam ya ce “Eh har ka dawo domin kaga ba’a ma fara wannan ba, sai dai karka daɗe ka dawo da wuri.
Ko da ya iso gidan Ameera ta gama fita a haiyacin ta, ta haɗa zufa kamar mai wanka. Lokacin da ya ganta sai da gabansa ya fadi, domin bai taɓa ganin yadda ake naƙuda ba. Sosai tsoron Allah ya ƙara kama shi yana jin ƙaunar mahaifiyarsa a ransa, nan take ya mata addu’a cikin ransa. Bai ankara ba yaji hawaye na zubowa daga idanunsa. Sosai yake kallon Ameera wancce take ta shure-shure kamar zata mutu, idanun ta sun tsaya, sai kiran sunan mutane ta ke yi harda sunan sa. Nana ce itama da sai yau ta taɓa ganin naƙuda ta fara kuka dan itama tsoro abun ya bata. Sun tsaya sai kallonta suke yi suna kuka sun kasa bata wani taimako duk jikin su ya mutu!. Adam ne yayi ta Maza ya zo kanta ya kamota da niyyar ɗagota amma ta sake kurma wani ihu ta na kiran sunan Allah. Lokaci ɗaya Adam ya ajiye ta kukan sa na kufcewa ya faɗin “Sannu honey Sannu, in sha Allah ba za ki ƙara aihuwa ba daga wannan I’m so sorry my Honey I love you so much please don’t left me! Sosai yake kuka ya rungumota jikinsa yana mata sannu. Lokaci ɗaya ya kamota ya ɗaga ta ya nufi Mota da ita, izuwa lokacin Ameera neman sumewa take yi. Nana ta biyo shi da gudu ta na kuka, haka suka bar gidan cikin namijin gudu har suka isa asbinti. Labour room (ɗakin aihuwa) aka shiga da ita cikin sauri, da gaske Adam yazo zai shiga amma a ka tsayar da shi a kan ba’a shiga. Haka suka tsaya shida Nana a gurin suna safa da marwa. Nana ce ta tuna da kayan haihuwa hakan yasa ta tambaye shi. Shi ma sai yanzu ya tuna ya ce taje ɗakin Ameera ɗin ta kwaso komai. Ya ce “Kin iya tuƙa mota? Nana ta ce “A’a ban iya ba. Adam ya zaro kuɗi ya bata ya faɗa mata inda kayan su ke.
Wasa-wasa aihuwa har ƙarfe biyar babu alamar fitowar jariri. Sosai hankalin kowa ya tashi musamman Adam, ita kanta Nana duk ta fita a haiyacin ta, Umma sai kira take tana tambayar an haihu? Misalin shida na yamma Allah yayi ikon sa, Ameera ta haifo jariranta guda biyu mace da namiji, sai dai ita uwar jini ya ɓalle mata. Sosai lokacin da Adam da Nana suka ji batun aihuwar suka yi murna, amma jin halin da uwar take yasa murna ta koma ciki.
Ɓangaren su Haura kuwa an daɗe da gama musu komai amma har yanzu Adam bai zoba, gashi basu da waya. Haka dai su kai ta jiran sa amma shiru, har ran Ɓultuwa ya fara ɓaci da irin wannan abun. Wasa-wasa har shida na yamma suna gurin, gashi basu san sunan unguwar da su ke ɗin ba. Suna gurin har bakwai babu alamun Adam. Kawai sai suka tare mai keke napen ya kai su gurin da suke bara. Koda suka zo gurin sai suka fara tunanin abin yi, shiru Haura ta yi tana tuno sunan anguwar su Adam ɗin ranar da zata kai musu abinci asibiti. Da ƙyar ta iya tunawa hakan yasa suka tare mai keke napen again suka faɗa masa inda zai kai su. Suna isa suka sallamshi suka tako har zuwa ƙofar gidan. Sai dai ƙofar a rufe take. Haka suka samu gefe suka zauna suna jiran dawowarsa, basu kawo komai ba domin dama Adam ɗin yana rufe gidan yanzu tunda babu mai gadi.
Cikin yardar Allah aka tsayar da jinin sai dai ana buƙatar jinin da za’a saka mata domin ta zubar da jini sosai. Haka Adam ya kamata a ka kwashi jini leda biyu bayan gwajin da a kayi masa babu wata matsala a jinin nasa. Bayan an gama kwasar jinin nasa ne Adam ya ce da Nana taje gida gobe sai ta dawo. Taso tayi musu amma ganin yadda ya haɗe rai yasa ta kama hanya. Har zata ta fi ya ce “Dama kin tabbatar kin rufe min gidan ko? Nana ta amsa da “Eh na rufe.
Har asuba jinin bai gama shiga ba, a wannan lokacin Adam ne ya kifa kansa a bakin gadon bacci ya ɗauke shi kasancewar jiya bai samu rsintsawa ba. A cikin barccin yake mafarkin wani yazo zai raba shi da Ameera, hakan yasa yayi saurin buɗe ido ya sauke a kanta wancce take kwance tayi fari sosai, lokaci ɗaya yaji wani irin sonta na fusgarsa, ga wani irin natsuwa da yake jin ya samu yanzu.
Nana da Umma ne suka shigo ɗakin ɗauke da kayan abinci da ruwan zafi na yiwa baby’s wanka, domin Nana ta sanar musu da cewar ta haifi tagwaye mace da namiji. Bayan sun shigo ɗakin ne Adam ya gaida Umma sannan ya tashi daga gurin da yake. Ummu ta ce “Kaje gida ka watsa ruwa sai ka ɗan huta kafin ka dawo ko? Adam ya amsa da “Ok Umma. Ya fita ba domin zai iya mata musu ba, yana fita ya tuno ashe fa bai sanarwa da kowa bafa. Nan take ya kira Najib bai ɗaga ba, ya kira Khadija kira ɗaya ta ɗaga haɗi da yin sallama. Adam ya amsa lokacin da yake shiga cikin motarsa. Khadija ta gaida shi tana jiran taji ya mata batun auran sa da zai yi jiya domin jinsa cikin farin ciki. Adam ya ce “Sister albishirin ki? Najib dake kusa da ita ya ja tsaki ya kawar da kai! Cikin ƙarfin hali ta ce “Goro Yaya na” ya ce “I’m a daddy now! Ya faɗa yana dariya. NAJIB da Khadija cike da rashin fahimta suka haɗa baki gurin ce wa “Me kake nufi? Sai a lokacin Najib ya kula da ya yayi magana. Shima Adam ɗin da makin jin muryar Najib ya ce “Ameera ta haihu ta haifi ƴan biyu yanzu haka muna asibiti. Yana faɗa ya kashe wayar yana dariya. Daidai lokacin ya karyo kwanan anguwar su. Tsayawa yayi a daidai get ɗin gidan sa، kana ganin sa kasan yana cikin farin ciki. Fitowa ya yi ya buɗe get ɗin sannan ya zo zai shiga motar domin shigar da ita ciki sai yaji an kira sunan sa cikin fushi da ɓacin rai. Ɓultuwa ce ta ce “Adam yanzu dan Allah ka kyauta mamu da ka barmu muka kwana a waje? Tun jiya daga kaimu gurin wankin kai sai ka manta da mu, Allah dai yasa an ɗaura auran?