Skip to content
Part 10 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Mtss! Ina ga hakan zamuyi insha Allah gobe zamu fasa, dan wallahi ba ƙananan kuɗi nake buƙata ba, a hanunsa, jiya wannan ɗan iskan Alhaji Atiku Naira ya kirani wai mu haɗu a hotel.”

Murmushi Amnat ta saki tare da cewa.

“Za kuma ki samu domin kuwa ko duka dukiyar sa kikace ya kawo miki zai kawo babu musu, ai kinsan aikin malam, kinje hotel ɗin ne.?”

Kanta Nafeesa ta ɗaga alamun eh.

“Naje ina ga ban dawo gida ba ma sai 10:30pm kinsan dawowata har Baba ya dawo, da sanɗa kamar munafuka haka na shige room ɗin mu, dama Allah ya rufa min asiri bai ganni ba, dana shiga Uku da mita.”

Dariya Amnat ta saka tace.

“Kai ƙawata kice kin tsallake rijiya ta baya, da ya kamaki wallahi da kin shiga Uku, dan babu abinda zai hana bai jibgeki ba, dan wannan tsohon naku ba dai bala’i.”

Bakinta Nafeesa ta taɓe tare da cewa.

“Babu kuma abinda yake iya tsinana mana sai, sai iko da gadara, ke nifa yanzu Allah ko kallon fuskar wannan tsohon bana sonyi, balle na tuno cewa ubana ne.”

Dariya Amnat ta saka tare da miƙewa tace.

“Time na ƙurewa, nasan yanzu haka yana can mu yake jira, ƙawata nafa faɗa miki karkiyi Maganar sayan gidan nan yanzu.”

Miƙewa tayi ta ɗauki jakarta ta saka hijabinta har ƙasa suka fita, bata ma yiwa Mama Sallama ba, a ƙofar gidan nasu suka gansa tsaye jikin motar sa, tunda suka fito yake sakin murmushi cike da ƙaunar Nafeesa.

“Assalamu alaikum Duniyata Barka da isowa.”

Tayi Maganar tana kashe murya tare da murmushi mai shiga rai, shima murmushin yayi tare da amsawa da.

“Amin wa’alaiku mussalam Farin ciki na, ya naga sai walwali kike kinyi kyau fa sosai farin ciki na.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.

“Duk walwali na ban kaika ba Duniyata, domin kuwa a ko wani lokaci kyawu kake ƙara min fiye da kullum, idanuna ko yaushe a cikin begen ganinka yake, zuciyata kuwa bata da aiki ko yaushe zai tunaninka, hanci na bashi da muradin daya wuce jiyo ƙanshinka, idan har na wuni guda ba tare da naji muryarka ba, sai naji kunnuwa tamkar sun kurmance, Soyayya ni’ima ce musamman idan ka haɗu da masoyi na gari mai addini ilimi tarbiyya sanin darajar manya mai riƙon Amana to Tabbas ubangiji ya gama maka ni’imar duniya, shiyasa nake jina yanzu bani da wata damuwa saboda na sameka, kasan meye kuwa.?”

Sosai sonta yaƙe ƙara shiga zuciyarsa domin kuwa macece ita wacce ta gama fahimtar yadda ake kula da masoyi wanda shine burin ko wani namiji ya samu mai kula dashi, ji yake bazai taɓa iya rayuwa ba tare da Nafeesa ba, tamkar numfashin sa haka yake jinta a zuciyarsa, kansa ya kaɗa alamun a’a yana lumshe idanunsa.

Murmushi tayi tare da jan numfashi kafin ta cigaba da cewa.

“Kana da kyawawan ɗabi’u sannan ka fito daga gidan mutunci, ga ka kuma da tausayi, wannan dalilin yasa nakejin bazan taɓa iya rayuwa babu kai ba, ina sonka Duniyata kuma zan cigaba da sonka har ƙarshen rayuwata I love You.”

Wani lumshe idanunsa yayi cike da jin daɗin maganganunta, dariya yayi tare da cewa.

“Bansan wacce irin Soyayya nake miki ba, Nafeesa Soyayyar ta wuce ma’auni a zuciyata, na dai san bazan iya rayuwa babu keba, koda zan rayu to Tabbas zanyi rayuwa ne cikin wahala, bazan iya rabuwa dake ba komai tsanani ko mai wahala bazan gujeki, kimin alƙawari bazaki gujeni a ko wanni irin yanayi domin kuwa ji nake tamkar na shekara goma tare dake mantawa nake da bamufi kwanaki tare ba, shekaru nake ɗauka munyi.”

Murmushi mai cike da salon yaudara Nafeesa ta saki kafin tace.

“Ka daina kiran cewa zan gujeka, babu macen da zata sameka a matsayin miji kuma taji ta gujeka abune da bazai yiwu ba, har abada ina tare da kai.”

Tayi Maganar tare da ƙin amsa masa cewa tayi alƙawari, Amnat ne tayi gyaran murya cike da zolaya tace.

“Au sannunku romio, wato ma kun manta dani shanye ko.”

Dariya Haidar yasa tare da cewa.

“Ni ɗinne idan tana gabana bana kallon komai sai ita, ta haske min kene ya kk.”

Yayi Maganar yana dariya, sun ɗan juma suna zance har aka fara kiraye kirayen sallar magaruba, numfashi Haidar ya saki tare da cewa Nafeesa.

“Kince akwai Magana gashi anfara kiran sallah ya kamata na koma gida, ina jinki menene.?”

Kanta Nafeesa ta sunkuyar alamun kunya tare da cewa.

“Dama akwai ƴar sister ɗin Mama mijinta an koresu a gidan haya to suna cikin matsala yanzu haka tana gida sun rasa inda zasu zauna, shine Mama tace a maka Magana ko zaka taimaka musu.”

Ɗan murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Ikey ba damuwa dama akwai wacce itama muke da burin a taimaka musu so insha Allah zansa da ita a ciki babu damuwa zan miki Magana idan komai ya kammala.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da masa godiya, Sallama sukayi yaja motar sa ya tafi, Nafeesa tafa sukayi da Amnat suna dariya, sannan suka shige cikin gida.

Bayan sallar magaruba, kusan isha’i Aunty Amarya ta gama haɗa komai girki mai rai da lafiya tayi musu yau zuciyarta wasai take jinta domin kuwa gani take burinta zai cika zasu dawo dai-dai da Ummi a cikin gidan, ita kuwa Ummi babu komai a cikin zuciyarta Tamkar ƙanwa haka ta ɗauketa, Ummi zoɓo ta haɗa musu sosai take farin ciki da zuwan yaran nata shekara biyu rabon da su dawo gida hutu sai yau ga Ambassador ya hanata zuwa tagansu, Al’ameen da kansa ya kira Haidar cewa yazo su tafi ɗauko Khalifa da ashfat airport, ƙarfe bakwai da rabi, Al’ameen ya fito, numbern Haidar ya kira baya tafiya, da kamar zai shige sai kuma ya shiga part ɗin nasu babu kowa a falon sai ƴar aikinsu Azumi, cikin girmamawa Azumi ta gaishe da Al’ameen, a daƙile ya amsa mata tare da tambayarta “Haidar fa” Azumi sanin cewa Haidar baya nan ya sata sanar daahi ya fita, bai kuma cewa KOMAI ba yayi fitarsa, bai kuma nemi sabon drevern da suka samu ba, yaja motarsa ya tafi duk shige da ficen Al’ameen Aunty Amarya idanunta yana kansa, sanda ta tabbatar da cewa shine da kansa ya tafi ɗaukosu ya sata kiran Hajiya Mansura ta sanar da ita, wayar ta kashe tare da komawa cikin su Ummi da Inna Jumma, dama ita Maimu tana part ɗin Aunty tare da Madina da Rufaida.

Hankalinsa kwance yake dreving ɗin, yayi nisa da tafiya harma ya kusa shiga airport ɗin yaji wayarsa na ringin dubansa ya kai ga wayar, Bros Haidar, amsa kiran yayi tare da cewa.

“Ina jinka”

Daga can Haidar yace.

“Sorry Company na koma yanzu Abdul ya kirani game da ɓatan kuɗaɗen nan, amma insha Allah yanzu zanzo airport ɗin sai mu haɗu.”

“Okay sai ka iso”

Abinda ya faɗa kenan ya katse kiran, ya cigaba da dreving ɗinsa, harya shiga airport ɗin, parking yayi tare da fitowa, can gefe ya hango kujeru Uku babu kowa a wajen da alamu dai wajen bazaiyi hayaniya ba, hakanne ya basa sha’awar zuwa ya zauna yana jiran isowar jirgin su Khalifa, tunda ta zauna ya maida hankalin sa ga wayarsa a yayin da Isah Alolo ke haƙonsa, sai da suka tabbatar cewa hankalinsa baya ga motar sannan suka samu suka sunce tayar motar cikin hanzari suka bar wajen, cike da saɓani suna fita Haidar kuma na shigowa, shima hango motar Al’ameen ya sashi yin parking gefenta, tare da kiransa ya faɗa masa inda zai samesa, sun ɗan juma kusan 8:15pm jirgin nasu ya sauƙa, miƙewa sukayi dukkan su tare da nufar jirgin suka tsaya, yayin da fasinja suke ta ƙoƙarin fitowa, a hankali yake jawo jakarsa fuskarsa cike da murmushi bayansa wata budurwa ce, wacce take mungun kama da Marigayiya khairat, hango su yasa Al’ameen sakin murmushi shima, ashfat da gudu ta faɗa jikin Al’ameen tana dariya Shima murmushi yayi tare da buga bayanta yana cewa.

“Welcome my sweet sister”

Kasancewar duk cikin ƴan uwansa Al’ameen yafi jituwa da ashfat sosai yakan iya zama da ita yayi hira, shi kuwa Khalifa Haidar ya rungume cike da farin ciki suke yiwa juna sannu, Haidar ne cikin zolaya yace.

“Oh wato dai ashfat kin manta dani Al’ameen kawai kika gani, daɗin abun ma dai nima ga nawa ɗan uwan ya zo gareni.”

Murmushi ashfat tayi tace.

“Kai yaya Haidar, wayace na manta da kai, babu ta yadda zan manta da ya Haidar ɗina, ina yaya Faruq.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Au baki san yana can American tare da Daddy ba.”

“American kuma”?

Khalifa yayi Maganar cike da mamaki, Al’ameen ne yaja hanun ashfat tare da cewa.

“Kunga nan fa ba wajen hira bane, ku bari mu ƙarisa gida kuyi zancen, kai Khalifa shiga motar Haidar ke kuma ashfat muje.”

Yayi Maganar yana buɗe motar itama ashfat zagawa tayi ta shiga, bai tsaya jiran shigansu Haidar ba yaja motar yayi gaba, kafin suma Haidar suka bi bayansa.

Tunda suka ɗau titin ashafat ke famar bawa Al’ameen labari wani ya bata amsa wani kuma yayi dariya kasancewar ta mutum mai shegen surutu.

“Ya Al’ameen Allah kuwa da Bro khalifa yace na shirya jibi zamu dawo gida Nigeria sai naji zuciyata ta cinke, kawai naji bana son tafiyar, amma fa a raina ina son ganinku Nigeria ne kawai bana son d…………”

Bata ƙarisa ba birkin motar ta ƙwace daga hanunsa take motar ta fara juyi a tsakiyar titi, taya ɗaya ta fice, karo motar ta dinga ci da motocin dake gabanta, accident ya dinga haɗuwa, ashfat kanta ne ya dinga gwaruwa da ƙarfen motar yayin da Al’ameen yake ƙoƙarin dakatar da motar a gigice amma ya kasa aiwatar da hakan, Haidar dake bayansa ne yayi parking suka fito a gigice suna salati, wani mai mashin Al’ameen ya daka da ƙarfi take mutumin yayi gefe shida mashin ɗinsa, ƙara dukan wata mota tayi da ƙarfin gaske furfin motar ne ya buɗe da ƙarfi, tamkar wacce aka wulllo ashfat haka ta faɗo daga cikin motar ta bigi ƙarfen mashin, fitt ƙafarta guda ɗaya ta fita tamkar an saka wuƙa an dashe, wani irin mungun ƙara ta saki mai shiga har cikin ƙwaƙwalwa jin ƙararta yasa Al’ameen runtse idanunsa, daga wannan ƙarar koda motsi ashfat bata kuma yiba, bayan motar Al’ameen ta daki wannan motar ne sai ta tsaya, cikin ikon ubangiji da buwayarsa Al’ameen ko ƙwarzane baijiba a jikinsa a matuƙar gigice ya fito daga cikin motar ya nufo ashfat da gudu yayin tuni har Haidar da khalifa sun isa, Haidar runtse idanunsa yayi cikin wani irin tashin hankali mai wuyar fassarawa, ya ɗago kanta yana jijjigata alamun ta tashi shi kuwa Khalifa kuka yasa tamkar ƙaramin yaro, Al’ameen yana isowa yaga jini har gudu yake dubansa ya kai ga inda jinin ke zuba, ƙafar ashfat ne da ta fita saurin kawar da kansa yayi tare da rufe idanunsa yana ambaton innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! Wani irin nauyi yaji zuciyarsa ta masa, wannan wata irin munguwar ƙaddara ce, ya furta cikin zuciyarsa yana jin kansa na sara masa da ƙarfi, Khalifa ne ya tashi da sauri tare da faɗawa jikin Al’ameen ya kuma sakin kuka, cikin kukan yake cewa.

“Bata son zuwa, nine na tilasta mata lallai mu taho ashe ƙaddara take gujewa, ni kuma nake jawo mata, duk wannan laifi nane dana sata zuwa dole nine na jawo mata tayi asarar ƙafarta, na cucet….”

Saurin toshe masa baki Al’ameen yayi da idanunsa yayi jajur yatsarsa yasa a bakinsa tare da cewa.

“Shish!! “

Gidan wata mata aka shiga da sauri aka karɓo fallen zani ƙafar dake bulbular jinin Haidar ya kama ya ɗaure idanunsa sai gudun hawayen tausayi yake, shi kuwa Al’ameen ƴan sanda ya kira tare da kiran Papa ya sanar dashi ba’a juma ba kuwa sai ga police ɗin tare da ambulance, Al’ameen Haidar khalifa duk ambulance ɗin suka shiga suka nufi asibiti, darect emargency aka shige da ita cikin gaggawa, tunda aka shiga da ita Al’ameen ya zauna tare da dafe kansa dake famar sara masa idanunsa sunyi jajur maganganunta da take masa a cikin mota sune suke yawo a zuciyarsa, (Ya Al’ameen Allah kuwa da Bros khalifa yace na shirya jibi zamu dawo gida Nigeria, sai naji zuciyata ta tsinke, kawai naji bana son tafiyar amma fa a raina ina son ganinku Nigeria ne dai kawai bana son…….) Runtse idanunsa yayi, a hankali yake jin jiri yana ɗibarsa tunda yake a tsawon rayuwarsa bai taɓa jin tashin hankali irin wannan ba, shin wannan wacce irin masifa ce, Haidar ya gagara zama waje ɗaya sai famar kaiwa yake da komowa, ya rasa nutsuwar zama, sosai hankalinsa yake tashe, sun kai kusa 40minute sai kuwa gasu Ummi da Inna Jumma har Aunty Amarya, Momma ma ita da Aunty sunzo, Maimu Sosai take kuka tamkar za’a zare mata rai yayin da kuka yake zuwa da sauƙi a zuciya shi wanda zuciyarsa ta cunkushe da baƙin ciki kukan ma gagararsa take haka take a wajen Ummi da Al’ameen tashin hankali da baƙin ciki ya kanasu kuka sai ajiyar zuciya kawai da Ummi ke sauƙewa, babu wanda bai tausayawa Ummi halin da take ciki ba, Aunty Amarya cike da makirci ta riƙo Al’ameen tana kuka tace.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! Lallai yau munga baƙar ƙaddara, yanzu ina ashfat take, ta mutu ko, sun kaita mutuware ne, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Allah sarki ashfat ashe ajaline ya kawo ki Nigeria, ba’a gujewa mutuwa da kinsani da bakizo ba.”

Tayi Maganar tana kwantar da kanta a kafaɗar Al’ameen shima Al’ameen hanunsa yasa ya riƙe Aunty Amarya ya gagara koda furta kalma guda ɗaya hakan tasa ya kasa bawa Aunty Amarya amsa wanda ita kuma burinta kawai taji ance ashfat ta mutu, Khalifa jikin Ummi ya faɗa yana sakin ajiyar zuciya, cike da tsanar Nigeria, kusan awannin likitocin Biyar sai ƙarfe ɗaya da rabi na dare suka fito ko wannensu yana sharce gumi, doctor Gurama ne ya dubi Papa dake tsaye ya harɗe hanunsa yayi shuru yace.

“Tana buƙatar jini domin kuwa ta zubar da jini da yawa leda Uku muke buƙata, sannan muna tunanin ta tafi dogon suma bamu sani ba ko zata farfaɗo idan ma zata farfaɗo to zai ɗauketa kwana biyu, sai dai ku godewa Allah kanta bai samu matsala ba, amma tayi missing ɗin ƙafarta guda ɗaya i am sorry!”

Doctor yayi Maganar yana zubawa Papa idanu dama sukan su Al’ameen sun san ta rasa ƙafarta, Ummi sai yanzu taji kuka yazo mata kuka ta saki mai cin rai tana durƙushewa a wajen shikenan ƴarta ta zamo nakasasshiya, Inna Jumma ne tayi saurin riƙe Ummi ta gagara rarrashinta domin kuwa gara a barta tayi kukan ko baƙin cikin zai ragu a zuciyarta yaushe ma ta rasa ƴarta, yanzu kuma ga wani tashin hankalin, Haidar ne ya miƙe tsaye tare da cewa DOCTOR suje a gwada jininsa idan yayi dai-dai da nata sai a ɗauka, haka kuwa akayi yabi bayan likitan suka wuce lap, Aunty Amarya kuwa sosai taji baƙin ciki da ba’a tabbatar mata da cewa ashfat ta mutu ba sai taci alwashin bazata bari ta farfaɗo da numfashin ta, ba ko bata mutu ba sai ta ƙarisa ta bazata yarda ta bari ashfat ta farfaɗo ba, murmushi ta saka tare da tashi ta koma gefe, a hankali ta furta.

“Alƙawari na ɗauka sai na tayar da bom ɗin da sai ya tashi da kowa a cikin gidan, idan har kashe ƴaƴanki ya gagara Gaji wallahi sai na haɗa munguwar fitinar da wutar ta zatayi wahalar kashewa a wannan familyn.”

Murmushi ta kuma saki dai-dai Haidar ya dawo daga wajen ɗaukar jini, duban Aunty Amarya yayi wacce tunda ta hangosa ta fara sakin kukan munafurci, girgiza kansa yayi cike da tausaya ahalin nasu kama hanunta yayi a hankali yace.

“Ki daina kukan haka Aunty Amarya, kanki zaiyi ciwo tun ɗazu kike kuka, dan Allah mu ɗauki ƙaddara a yanda ta zo mana, bazamu iya sauyata ba.”

Kukan ta kuma saki tare da cewa.

“Dole ne nayi kuka Haidar, ka duba halin da Ashfat ta shiga, dole ne kuka, yarinya da ƙafafuwan ta, amma ace ta zamo miskiniya ai abun da tausayi.”

Shuru Haidar tare da cije bakinsa shima yana jin zafin fitar ƙafar Ashfat, haka suka kasance kowa a tsaye babu wanda ya iya runtsawa.

Gudu yake sosai yayin da matar ke famar binsa da gudu hanunta riƙe da wuƙa, shi kuwa sai famar gudun neman ceto yake, sosai yake gudu duk ya jiƙe da gumi idanunsa sunyi jajur, tuntuɓe yaci tare da faɗuwa ƙasa, ja gindi ya fara yana baya baya yayin da take nufosa da wuƙar, hangota da yayi ne ya sashi ƙwala mata kira.

“Ablah! Ablah!”

Sautin kiran da taji ne ya sata juyowa da sauri idanunta zaro ganin ta sunkuya kansa ta ɗaga wuƙar zata soka masa a ƙirjinsa, shi kuwa sai miƙo mata hanu yake, wani irin ƙara ta sa tare da cewa.

“Al’ameen!! Al’ameen!! A’a karkiyi haka.”

Tayi Maganar cikin ƙaraji mai sautin gaske sai da wajen ya amsa, ai kuwa jin muryar mutum a wajen ya saka matar sakin wuƙar ta juya da gudu, da gudu Ta ƙarisa tana kallon bayan matar, taso ganin fuskarta sai dai ina ta bata baya, a gabansa ta sunkuya tare da zuba masa idanu tace.

“Meya sameka Al’ameen meka mata zata kasheka, waye ce ita ɗin.?”

Ta jera masa tambayar tana haki, shuru yayi ba tare daya amsa mata ba, sai ma faɗawa da yayi jikinta tare da ƙanƙameta a hankali cikin tashin hankali yace.

“Karki bari ta cutar da rayuwata, dan Allah ki zamo min katanga tsakanina da ita, karki bari burinta ya cika.”

Firgit git ta farka daga baccin da take, duk ta haɗa gumi zuciyarta sai bugawa take, sosai wannan mafarkin ya bata tsoro.

” to meke faruwa dashi, mutumin da bata sansa ba sai sau ɗaya, daya bigeta ya Kaita asibiti kuma yaci mutuncin ta, shine har zatayi mafarki yana neman taimakon ta, anya wannan ba shirmen mafarki bane, kai shirme ne babu ta yadda wannan mungun abun zai faru da wannan mai jiji da kan daga kallon sa yana da gata.”

Tayi Maganar tana dafe kanta, miƙewa tayi ta duba agogo ƙarfe 2 na dare, tsakar gidan su ta fito ta ɗauki buta tayi alwala, ta dawo ɗakin nasu ta hau Sallar nafila tare da addu’ar Allah yasa wannan mafarkin nata ya tafi a shirme domin kuwa ba mafarki bane mai kyau ta juma akan sallayar kafin ta tashi ta koma tayi addu’a tare da maida kanta gefen Umma dake bacci ta kwanta, sai dai baccin ya gagareta, tunani da fargabar mafarkin da tayi shine yake a zuciyarta….

<< Aminaina Ko Ita? 9Aminaina Ko Ita? 11 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita? 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×