Ablah gida ta koma cike da sanyin jiki zama tayi tare da tagumi tana kallon Umma, itama Umma dubanta tayi tare da cewa.
"Lafiya Ablah kikayi tagumi kina kallona, hukuncin dana yanke bai miki daɗi ba ko."
"A'a Umma ba hukuncin bane bai min daɗi ba, domin kuwa nasan baza kiyi abinda zai cutar dani ba, sai dai Umma ina tunanin ta yadda zan fara rayuwa ba tare dake ba, sannan Umma rayuwar gidan masu kuɗi sai nake ganin kamar zai min wahala, domin kuwa ban saba da tasu rayuwar ba, nafi sabawa da rayuwata ta. . .