Skip to content
Part 14 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Ablah gida ta koma cike da sanyin jiki zama tayi tare da tagumi tana kallon Umma, itama Umma dubanta tayi tare da cewa.

“Lafiya Ablah kikayi tagumi kina kallona, hukuncin dana yanke bai miki daɗi ba ko.”

“A’a Umma ba hukuncin bane bai min daɗi ba, domin kuwa nasan baza kiyi abinda zai cutar dani ba, sai dai Umma ina tunanin ta yadda zan fara rayuwa ba tare dake ba, sannan Umma rayuwar gidan masu kuɗi sai nake ganin kamar zai min wahala, domin kuwa ban saba da tasu rayuwar ba, nafi sabawa da rayuwata ta faɗi tashi.”

“Na sani Ablah dole zaki damu da rashina amma ki sani ita duniya makaranta ne, akwai tarin darasi a cikinta mai hankali shine kawai yake lura da wannan darasin, kije ki koyi rayuwa ba tare da uwa ba Ablah domin kuwa ko bamu rabu yanzu ba dole wata rana zamu rabu, ke macece dole zaki gidan miji, ki barni, kije ki koyi wannan Rayuwar sannan nasan dole zaki samu wani darasin a wannan gida na masu kuɗin sai kinje zaki fahimci zance na, domin kuwa yanzu a ɗaure na baki Maganar zaiyi wuya ki fahimta, sai dai abinda nake so dake Ablah karki taɓa bani kunya a rayuwa, na baki tarbiyya dan Allah ki riƙe tarbiyyar ki, bana son ki kasance mai kwaɗayi akan abunsu, ki dinga kawar da kanki daga shiga harkar da bai shafeki ba, ki kasance mai haƙuri akan komai, karkiyi wasa da ibadarki Ablah, sannan ina ƙara jaddada miki cewa karki yadda ki cuci wani da ki cuci mutum gara shi ya cuceki, sannan karkiga abinda zai cutar da wani kiyi shuru idan har kina da halin dakatarwa to ki dakatar, ki taimaki duk wanda yake bukatar taimako muddun kina da abinda zaki taimaka Allah ya miki albarka, insha Allah rayuwarki zata haska.”

Kanta Ablah ta kaɗa tace.

“Shikenan Umma Allah yasa hakan shi yafi alkairi, kuma insha Allah bazan baki kunya ba, duk abinda kika umarce ni shine abinda zanyi a rayuwata, baki da matsala dani Umma bazan taɓa watsar da tarbiyyar ki ba har abada.”

“Allah ya miki albarka, ki ƙarasa karatun ni bara nayi gyaran ɗakin.”

Da to ta amsa tare da ɗaukar ƙur’aninta ta cigaba da karatu.

Washegari da safe, Umma bataje wajen aiki ba, ta taya Ablah haɗa kayayyakin ta, sanda ta tabbatar sun haɗa dukkan abinda zata buƙata Ita dai Ablah jikinta duk da sanyi haka kawai take jin bata son tafiyar, haka ta wuni sukuku jikin ba daɗi, ko da azhar kamar yadda Inna Jumma ta umurci Faruq haka akayi ƙarfe biyu bayan sun idar da Sallar azhar, daga Companyn ya taho unguwar Durmi a ƙofar gidan nasu yayi parking yaro ya samu ya aika yace yaje yace wai Faruq yazo, babu jumawa kuwa Umma suka fito da Ablah tare da akwatin ta, Abdu sai kuka yake baya son rabuwa da ƴar uwarsa Faruq cikin girmamawa ya gaishe da Umma, tare da karɓar kayan Ablah yasa amota, ɗan murmushi Ya saki tare da cewa Abdu.

“Abokina, kana kukan rabuwa da Aunty ko?”

Kansa Abdu ya ɗaga idanunsa cike da hawaye, sunkuyawa Faruq yayi a gabansa tare da cewa.

“Share hawayen ka daina kuka Aunty tana nan ba nisa zatayi ba, zan dinga zuwa na ɗauke ka, ina kaika wajenta kaji, ka daina kuka ka yiwa Aunty fatan alheri, ko so kake itama Aunty tayi kuka.”

Still kansa Abdu ya girgiza alamun a’a yace.

“Ni dai bana son Aunty na tayi kuka, Aunty tace min zata saya min keke ina zuwa makaranta idan ta samu kuɗi, kuma itace take bani kuɗin break kullum, nima idan nayi kuɗi zan sayawa Aunty mota irin taka nan fara mai kyau, to kuma shine yanzu Aunty zata tafi ta barni.”

Murmushi Faruq ya saki hanunsa ya riƙe tare da miƙewa mota ya buɗe ya ɗauko kuɗi, dubu arba’in ya danƙawa Abdu a hanunsa tare da cewa.

“To ga kuɗin keken naka, ka bawa Umma ta saya maka ko, sannan Aunty ma zatana zuwa.”

Cike da farin ciki, Abdu ya rungume ƙafar Faruq, Umma murmushi tayi domin kuwa Faruq ya birgeta Sosai tana son mutum mai ƙaunar yara, motar sa ya shiga yana ɗagawa Abdu hanu, Ablah Umma ta rungume idanunta na cikowa da hawaye tace.
“Umma zan tafi ki cigaba da min addu’a, ki kuma yafe min idan akwai laifin dana miki.”
Hawayen da Umma ke ɓoyewa ne suka gangaro, Faruq cike da ƙaunar familyn yake hangosu ta cikin motar basu dashi amma suna da wadatar zuci da ƙaunar junansu, Umma cewa tayi.

“Na yafe miki Ablah babu abinda kika min, Allah ya rabaki da sharrin Mutum da aljan Allah ya zamo gatanki a duk inda kika tsinci kanki.”

Sake Umma tayi ta kama hanun Abdu.

“Zan tafi Abdu, zan dinga zuwa ina dubaka, karkayi wasa da karatunka kaji, ka kula.”
Kansa ya ɗaga, Ablah ta juya ta shiga motar, tana ɗagawa su Umma hanu, idanunta na hawaye har ta daina ganinsu, sunyi nisa da tafiya ita da Faruq babu wanda ya yiwa wani Magana.

Sunyi nisa da tafiya Faruq yace.

“Ablah baki son tafiya ko?”

Ɗago daradaran idanunta tayi tare da kallon Faruq, hawayen ta ta goge tare da girgiza masa kai alamun a’a.

“To meyasa kike kuka, tunda naga ai ba nisa kukayi ba, ina nan ina AMBASSADOR AHMAD GIWA ESTATE”

Still dai shuru tayi bata tanka masa ba, murmushi Faruq yayi tare da cigaba da dreving ɗinsa har suka iso first get ɗin Estate ɗin idanunta ta ɗaga jin Faruq na danna hon hon, ta kalli get, AMBASSADOR AHMAD GIWA FAMILY ESTATE, taga an rubuta da manyan baƙi wani irin tsinkewa taji zuciyarta tayi, idanunta ta runtse tare da ambaton LA’ILAHAILLAH ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN, har aka buɗe get ɗin suka shiga bata bar furta wannan kalmar ba domin kuwa har yanzu zuciyarta bata daina tsinkewa ba, ji take tamkar zata haɗu da mungun Abu a cikin gidan, jin yanda ƙirjinta ke bugawa sai taji tamkar tace Faruq ya mai data gida, da kallo take bin Estate ɗin, gidane na kerewa sa’a gidan masu kuɗin ma irin wanda suka kai suka kawo manyan masu kuɗi, haka ta yiwa gidan kallo, komai a tsare yake ga wasu shimfiɗaɗɗun fulawowi, numfashi ta saki, get ɗin da zai sadaka da part ɗin su Al’ameen Faruq ya nufa nanma sanda ya danna hon sannan aka buɗe musu gadin get ɗin farko security ke gadi amma taga wannan kuma ba security bane, sai dai duk tsaruwar da taga can ya mata, sai kuma taga inda suka shigo yanzu yafi kyau nesa ba kusa ba, a parking space yayi parking tare da buɗe motar ya fito ya zaga itama ya buɗe mata, fitowa tayi a nutse tana bin part ɗin da kallo, mai bawa flowers ruwa Faruq ya kira tare da basa kayan Ablah yace ya kai wajen Inna Jumma, sannan ya cewa Ablah muje, gaba yayi ta bisa a baya cikin babban falon suka shiga babu kowa kasancewar su Maimu da Afnan suna school, ihsan kuma ta dawo tana bedroom ɗin Ummi Aunty Amarya da Ummi kuma duk suna bedroom ɗinsu, duk da kayan more rayuwa da ƙawatuwa da falon yayi baisa Ablah ta masa kallon ƙauyanci ba, bedroom ɗin Inna Jumma suka shiga har yanzu tana kan darduma tana lazimi, Faruq sanin cewa muddun Inna Jumma tana laziminta ba magana takeyi ba, ya sashi juyawa tare da cewa Ablah shiya koma office.

A hankali ta furta.

“A dawo lafiya Allah ya tsare.”

Murmushi Faruq yayi ya amsa da ameen yana ficewa, Inna Jumma ta kai wajen miti talatin tana lazimi, kafin ta idar tare da murmushi tana kallon Ablah.

“Shalelena har kun iso, sannu da zuwa, ina miki barka da shigowa cikin mu.”

Murmushi Ablah tayi tare da zamewa har ƙasa ta gaishe da Inna Jumma, ta amsa cike da sakin fuskar jin Ablah take tamkar jininta numfashi ta saki tace.

“Jirani Ablah bara na watsa ruwa na fito ko.”

To Ablah tace Inna Jumma ta shige tollet koda ta fito sosai ta dinga jan Ablah da hira har ta ɗan saki jiki kaɗan, ƙarfe Uku dai-dai falon ya fara cika da mutanen gidan, kasancewar duk wanda suka tafi school sun dawo, khalipa shima yana kwance a doguwar kujera, Ashfat ma tana gefen sa, sai Maimu dake zaune ita da ihsan tana mata assignment, dama ita Afnan Uwar baƙin hali bata cika zama cikin mutane ba, tana can bedroom ɗinsu, Aunty Amarya da Ummi suma suna zaune suna taɗi, kasancewar yau Ladiyo ce take girki, Inna Jumma ce ta fito tare da ABLAH, Ashfat kallon sani ta yiwa Ablah domin kuwa bazata manta da ranar da Al’ameen ya wurgota a asibiti ba, Aunty Amarya ma da kallon mamaki tabi Ablah, Maimu idanunta ta ɗago ta kalli Ablah tare da Inna Jumma, tana bin Ablah da kallon rashin sani, khalipa ne ya kasa hkr yace.
“Ke tsohuwar nan a ina kuma ki ka sato Wannan kyakkyawar halittar.”

Yayi Maganar yana nuna Ablah da yatsa.

“A gidan ubanka”

Inna Jumma ta basa amsa tana jawo hanun Ablah, Maimu dariya tasa tare da ijiye pencil ɗin dake hanunta tana duban Ablah tace.

“Ke dai tsohuwar nan ba’a rabaki da rikici koma daga ina kika satota idan tayi tsami zamuji.”

Harara Inna Jumma ta jefawa Maimu tare da cewa.

“Bani da lokacinki, ina wannan shegiyar kura Uwar baƙin halin.”

Sanin da wanda Inna Jumma take yasa Khalifa sheƙewa da dariya ya mata nuni da sama, taɓe bakinta Inna Jumma tayi tana zama cikin ɗaya daga cikin kujerun falon, Ablah cike da girmamawa ta ƙarisa wajen su Ummi da Aunty Amarya, sunkuyawa tayi har ƙasa a hankali ta furta.

“Sannunku da hutawa, ina wuni.”

Numfashi Aunty Amarya ta saki tana kallon Hajiya Mansura tace.

“Ƙawata kwana biyu na jiki shuru babu wani labari, ni fa na fara gajiya da tura mota Wallahi.”

“Haba Amarya gajiya fa kike kira, hmmm! Ai bari kiji ba’a taɓa gajiyawa ga naiman cikar buri, kinga yanzu ne ma fa zamu saka ɗanban neman Nasara, yanzu ma aka fara wasa farin girki, karki manta ɗaya kawai muka samu muka rage nan gaba akwai sauran huɗu da muke neman rayuwarsu.”

“Hajiya Mansura, yanzu fa kina ji take sanar dake Monday zasu koma Egypt, sai yaushe kenan zamu ta jiransu, ni fa burina idan na gama dasu shima Uban nasu na dawo kansa, amma abubuwa a wannan karon sun gagara.”

“Babu abubuwan da suka gagara, su tafi mana so what, kinga ba dole sai akansu zamuyi aiki ba, karki manta a yanzu kina tare da Uku, Al’ameen Maimu da kuma Uwar tasu, domin kuwa idan ta gagara sai mu turata lahira a madadin ƴaƴanta biyu, dan haka daina damuwa, wannan karon bada Isa Alolo zamuyi aiki ba, da guba zamuyi aiki.”

“Da guba! Taya zamuyi amfani da guba a wannan gidan sannan waye za’a fara sawa gubar?”

“Tambaya mai kyau, *AL’AMEEN* shi zamu fara sakawa domin kuwa gani nake kamar shine matsalar mu, idan mun aikasa sauran aikin zaizo mana da sauƙi dan haka ki ijiye girki a cikin gidan nan ki barwa ƴan aiki domin gujewa zargi, kisan yadda zakiyi kice kin daina girki dole ki ƙirƙiri wata matsalar da zata sakaki ijiye girki.”

<< Aminaina Ko Ita? 13Aminaina Ko Ita? 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×