Skip to content
Part 17 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Amini kuma ɗan Uwa irinka abune da yake matuƙar wahala a wannan zamanin, duk da haka dole ne na gode maka, Allah ya saka da alkairi.”

“Nasha faɗa muku cewa bana buƙatar godiya daga gareku, duk abinda na muku a rayuwata ban faɗi ba, bani da wanda ya fiki kaf wannan duniyar idan aka cire Daddy da Ummi, bani da wani gata sai ku, ni dai fatana a rayuwa mu kasance cikin farin ciki har ƙarshen rayuwar mu, bana ƙaunar abinda zai raba kanmu.”

“Al’ameen ba’a halicci abinda zai shiga tsakanin mu ba, koda kuwa shaiɗanne haka zai ganmu ya ƙyale Rayuwar zata kasance cikin farin ciki kanmu bazai taɓa rabuwa ba.”
Yayi Maganar yana duban agogon hanunsa.
“Kaga bara naje Nafeesa na jira na a Amina kitchen.”

Murmushi Al’ameen ya saki tare da cewa.
“Oh da alamu dai wannan Nafeesan ta ɗauke maka zuciya dole nima na haƙura naso zaɓinka, zan iya ganin pictures ɗin ta.”

“Me zai hana kuwa, dama nasan ai dole zakaso abinda nake so, bara kaga pictures ɗinta KYAKKYAWA ce mai hankali da kuma nutsuwa.”

“Hummmm! To yabi zaɓinka, ai sai ka bari idan na gani na faɗa, wataƙil mummuna ce, amma dai bari na gani na yanke hukunci.”
Murmushi Haidar yayi yana buɗe pictures ɗin Nafeesa ya mikawa Al’ameen wayar tare da cewa.
“Gashi yanke hukunci.”
Karɓa Al’ameen yayi yana murmushi tare da zubawa pictures ɗin Nafeesa idanu, na wajen 30second tare da miƙawa Haidar wayar yana taɓe baki tare da cewa.

“Eh to ba laifi tana da kyau, amma dai bata kai ɗan uwana kyau ba.”

Dariya Haidar yayi tare da dukan kafaɗar Al’ameen yace.

“Wannan son kai ne ka nuna, bara naje time na ƙurewa.”

“Okay kace ina gaisheta kafin na kawo mata ziyara saƙo na baka.”

Yayi Maganar yana buɗe motarsa ya shige, shima Haidar tasa ya shiga yana murmushi duk sukaja, Haidar darect Amina kitchen ya nufa tana zaune ta saka lemo a gaba tana kurɓa jikinta sanye da hijabi, hangota ya saka Haidar sakin murmushi, jawo kujerar ya fuskance ta.

“Assalamu alaikum farin ciki na, da fatan duniyarki ya sameki lafiya.”

Ɗago idanunta tayi tana sakin murmushi tace.

“Ameen wa’alaiku mussalam Duniyata, kayi matuƙar kyau, kayiwa kayan kyau.”

“Wow wato nine ma na yiwa kayan kyau.”

“Eh mana Duniyata, ai yanda kyawunka ke haskawa dole su haske kayan, Duniyata kasan me kuwa?”

“Ban sani ba farin ciki na, bani haske.”

“Ina matuƙar ƙaunar ka, ji nake bazan iya numfashi ba babu kai, kai mutum ne na mussaman a rayuwata.”

Murmushi Haidar yayi tare da lumshe idanunsa yace.

“So So So wannan kalmar tana mungun mini daɗin ji, mussaman idan na tuna da cewa itace ta haɗani dake ina matuƙar alfahari da zuciya domin kuwa da’ace ba zuciya da ba’a halicci SO ba, ina sonki fiye da komai a rayuwata zan iya yaƙi da koma waye akan soyayyarki.”

Dariya Nafeesa tayi har fararen haƙwaranta suka bayyana.

“Duniyata da alamu yau kana cikin farin ciki meya faru nima na tayaka wannan farin cikin.?”

“Kina fuskantar abinda ke cikin zuciyata, Tabbas ina cikin farin ciki Abu biyu suka sani farin ciki yau, na farko wannan kyakkyawar fuskartaki, na biyu kuma yau ɗin nan ɗan uwana kuma *AMININA AL’AMEEN AHMAD GIWA* ya sani farin ciki ta hanyar saka mana hanun jari a Ahmad sd rice Wanda zamu samu riba a shekara sama da 5.2b amma mu biyu zamu raba ribar nida Faruq, shima kuma ya saka nasa na kansa wanda shi kaɗai zai mallaki nasa ribar, yau Al’ameen ya sani cikin farin ciki sosai aminine na ƙwarai mai son ganin cigaban mu.”

“AL’AMEEN AHMAD GIWA kuma ban fahimta ba, dama ba cikin ku ɗaya dashi bane, taya zai saka maka hanun jari gani nayi tare kuke business kuma dukiyar nan ta mahaifinku ne?”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Oh wai ke ɗauka kike ciki ɗaya muke dashi, a’a shine ɗan AMBASSADOR AHMAD GIWA na Cikin sa, mahaifina ƙanin Ahmad Giwa ne, Tabbas shine ya saka mana hanun jari nida Faruq Saboda ya fimu arziki, ko Companyn da muke aiki yanzu nasa ne wanda mahaifinsa ya mallaka masa, sai dai shi yana ɓoye hakan yana nuna cewa Companyn duka namu ne, sam baya taɓa nuna cewa shi wanine dai-dai yake rayuwarsa data kowa, yama ce na gaisheki, duk da baki san fuskarsa ba, shima sai yau yasan taki fuskar.”
Tunda ya fara Maganar Nafeesa ta saki baki tana kallon sa, ashe dama zaɓen tumun dare tayi, ta gama zaton Haidar shine ɗan AMBASSADOR AHMAD GIWA, ashe abun ba haka yake ba wani ne can ɗan Ahmad Giwa, shima wannan albarkaci yake ciki, to shi Al’ameen ɗin ya yake, numfashi ta saki tare da sakin murmushin yaƙe cikin kissa da ɓoye mamakinta tace.

“Wow gwanin burgewa, congratulations l, na tayaku Murna, amma Duniyata zanso ganin wannan Al’ameen ɗin.”

Wayarsa Haidar ya zaro tare da miƙo mata hoton sa, karɓa tayi ta zubawa hoton idanu, sosai take kallon pictures ɗin ita kaɗai tasan me take ayyanawa a cikin zuciyarta, miƙa masa wayar tayi tare da cewa.

“Ka fisa kyau Duniyata, ka kira min shi a wayarka mu gaisa mana.”

Murmushi Haidar yayi yace.

“Shima haka yace na fiki kyau, shikenan kin rama, bara na kira miki shi.”

Yayi Maganar yana dannawa Al’ameen kira, yana danna kiran Nafeesa tayi saurin karɓar wayar ta katse kiran tana cewa.

“sorry Duniyata na manta ashe Amnat ta kirani wai na tura mata kati, zatayi Amfani dashi da gaggawa na manta sai yanzu na tuna, Please dan Allah taimakeni ka karɓa min katin a wancan shagon kafin mu gaisa, karmu tsaya Magana na kuma mancewa.”
“Hakane farin ciki na, babu damuwa bara na karɓo miki katin nazo.”

Yayi Maganar yana tashi ya fita, numfashi mai nauyi Nafeesa ta saki tana dafe kanta cikin gaggawa ta ɗauki numbern Al’ameen a wayar Haidar tare da tura pictures dinsa..

“Sam ba kai bane zaɓina Haidar bakai ya dace na ɗaukewa hankali ba, shine domin kuwa shine mai kuɗin da nake nema, tayaya zan saki rafi na hau dukan tafki, hmmm! Sam rayuwa da kai Haidar bazai yiwu ba, a yanzu rawata ta sauya kuma dole kiɗan ma sauya, Idan har kiɗar ta sauya itama rawar sauyawa take, Finally Haidar munzo taƙin ƙarshe tsakanina da kai Soyayyar ta ƙare, dole ka rabu dani koda kuwa mutuwa zakayi domin kuwa kuɗi sunfi min komai a rayuwata, sai yanzu naga wanda ya cancanta nayi rayuwa dashi.”

Tayi Maganar a fili tana sakin murmushi tare da ƙurawa pictures ɗin Al’ameen kallo.

“Kyakkyawa ne na kerewa sa’a, ga kuɗi ga kyau, gaskiya haɗuwar zata bada citta, amma dai kuɗin sai sunfi kyawun mahimmanci da gani zakayi wasa da kuɗi.”

Dariya tasa har tana ɗan dukan teburin gabanta, sai kuma tayi shuru tare da nutsuwa hango Haidar tahowa, bayan ya iso ne ya jawo kujarar daya tashi tare da zama yana sakar mata murmushi, itama murmushin ta maida masa tare da cewa.
“Har ka sayo katin kenan duniyata?”

“Eh na basa numbern ta nace ya tura mata 10k ina ga hakan ya miki ko farin ciki na.?”
Murmushi Nafeesa tasa tana kallon sa cikin slow voice.

“Ƙwarai kuwa Duniyata hakan yayi, bara na ari bakinta na ci mata albasa, ta gode Allah ya ƙara buɗi.”

“Kinfi ƙarfin godiya a wajena abinda ya zamo dole a gareni shina miki, ki sani farin ciki na, zan iya komai kuma komai wahala indai akanki ne, banƙi na mutu ba, kece farin ciki na, ina ƙaunar ki sosai Nafeesa, rayuwa zata min daɗi idan kin kasance mata a gareni, haka Rayuwa zata min tsanani idan na rasaki, sai dai na sani zuciyoyinmu a haɗe suke babu ƙaddarar da ta isa ta raba tsakanin mu.”

Tunda ya fara Maganar ta zuba masa idanu tana masa kallon mahaukaci , domin kuwa ita ko yanzu da yake wannan maganar jinsa kawai take domin kuwa cikin mintina 17 da suka wuce ta wurgar da soyayyar, amma shi kuwa gashi sai ɗorawa kansa dakon wahala yake, duk cikin zuciyarta take wannan maganar, ɗan murmushi ta saki tare da cewa.

“Duniyata ƙaddara tana sauyawa a duk sanda ubangi ya aikota, ya kamata mu sawa zuciyarmu haƙurin rashi domin kuwa bamu san me ƙaddara ta shiryawa Rayuwar mu ba, saboda wannan dalilin yasa nake roƙon ubangiji kullum a duk sallah ta biyar, idan har ya jarabceni da rashin abinda nake so, to ya bani hkrn jure rashin sa, sannan ya mantar dani wannan Soyayyar,kaima haka nake son ka kasance.”

A matukar razane ya ɗago idanunsa yana kallon ta, tare da furta.

“Whatt! Nafeesat kinsan me kike faɗa kuwa yanzu ke har kina tunanin cewa akwai ƙaddarar da ta isa rabamu, bana tunanin akwai ta Nafeesa, bazana taɓa iya haƙurin rasaki ba domin kuwa rasaki tamkar rasa numfashi nane, muddun ba mutuwa bace zata rabamu to babu wata ƙaddarar da ta isa shiga tsakanin mu, ki saka wannan a zuciyarki kisa cewa nine mahaɗin rayuwarki.”
Murmushi mai sauti Nafeesa ta saki tare da miƙewa tsaye tana ɗaukar bag ɗinta tace.
“Bana musu da maganarka Duniyata, ka kwantar da hankalinka kai nawa ne na har abada, kaga yanzu time ya ƙure Mama zatayi faɗa idan na zarce time ɗin da ta bani, ina jiranka gobe ka taho min Al’ameen mu gaisa, muje ka sauƙeni a gida.”

Shima murmushin ya saki yace.

Ko kefa amma da har kinsa hantar cikina ta fara kaɗawa, muje.”

Dariya Nafeesa tayi tare suka jera har cikin mota, a ƙofar gidan su ya sauƙeta, shi kuma ya shige, cikin falon nasu ba kowa hakanne ya bata damar shigewa bedroom ɗinsu, Amnat ta samu kwance a bed ɗinsu tana ta sharara bacci, bag ɗin ta Nafeesa ta ijiye tare da cire hijabin daya bi ya dameta, ta zauna tare da ɗakawa Amnat duka, a ɗan firgice Amnat ta buɗe idanunta ganin Nafeesa ya sata sakin tsuka.

“Mtsss! Aikin banza, wallahi baki da mutunci har kin razana ni, ya naga kin dawo da wuri.?”
“Hmmm ba dole na dawo da wuri ba, naga baƙon abu, kinga 10k recharge card?”

“Ehh na gani, wani baƙon abu kika gani?”

“Hmmm! Amnat Allah ya ciyar dake matsiyacinne ya turo miki.”

“Matsiyaci kuma Haidar ɗinne matsiyaci,

kardai yaƙi amincewa da buɗe miki kantin?”

“Mtss! Wama yake Maganar kanti yanzu ni ko maganar ban masa ba, domin kuwa da matsiyaci mai shiga rigar arzikin wani nake tare ban sani ba, ina ɓata lokaci na a banza.”

“Ban fahimceki ba Nafeesa, kina min magana a duƙunƙune, ki ware min mana yanda zanfi mahimta?”

“Amnat kinga arzikin da kike tunanin Haidar yana dashi, hmmm! Abun haushi abun Allah wadarai, duk ba nasa ba, har Companyn da suke aiki.”

“Idan na fahimceki Haidar ɗan ƙaryar arziki ne, to amma idan ba nasa bane na waye ne, ɗan AMBASSADOR AHMAD GIWA ne fa taya zaki ƙaryata arzikinsa luck Nafeesa, idan ma wanine ya faɗa miki to ƙarya yake miki, kawai yaga kina samun arziki ne, zai miki ƙarya domin ya rabaki da samunki amma ta yaya za’ace ɗan Ahmad Giwa yayi ƙaryar arziki, ai sune arziki a ƙasar nan sanin kanki ne wannan domin kuwa meye Haidar ya rageki dashi komai kika nema yana miki shi, da kuwa a rigar arzikin wani yake to wallahi da bazai miki bajintar da yake miki ba.”

“Amnat ki tsaya ki saurareni kiji yadda mukayi da Haidar ɗin kansa domin kuwa shine ya faɗa min wannan maganar da bakinsa.”

Ta ƙarshe Maganar tana sanar da Amnat tattaunawar da sukayi da Haidar.

“Ki faɗa min idan wannan ba shiga rigar arzikin wani bane?”

“Hmmm! Na fahimci inda Maganar ta dosa, naji Haidar yana aiki a Companyn Al’ameen, to So what meya rageki dashi me kika nema bai miki ba, duk abinda kike nema a rayuwa Haidar yana baki, sannan meye banbancin sa da ɗan gidan Ahmad Giwa, babu domin kuwa shima ɗa yake garesa tunda duk tsiya jini ɗaya dai yana yawa a jikinsu abinda yayi Ahmad Giwa shi yayi mahaifin Haidar wando ɗaya suka fito suka kuma sha nono ɗaya, dan haka ki daina neman sauya tunani akan Haidar.”

“Amnat kenan da alamu kin manta ƙudirina, dama nayi alƙawarin Rayuwa da Haidar ne, idan baki manta ba, na faɗa miki cewa ko yau na samu wanda yafi Haidar kuɗi zan wurgar shi na ɗauki wanda ya fisa, kowa yana buƙatar cigaba nima kuma dole na nema, rayuwa fa tana tafiya zuwa mataki ne, daga matakin farko har zuwa na gaba, yau wannan Ranar itace matakina ta ƙarshe da Haidar, zan kuma taka matakin gaba.”
Amnat da kallo tabi Nafeesa cike da fara tsoron lamuran ta, domin kuwa duk hatsabibancin ta Nafeesa ta fita.

“Idan har na fahimceki dai-dai kina nufin zaki rabu da Haidar ki koma kan Al’ameen?”

“Ƙwarai kuwa Amnat wannan shine ƙudirina.”

“Anya kuwa kina da hankali Nafeesa?”

Murmushi Nafeesa tayi cike da gatsali ta cewa Amnat.

“Mahaukaciya ce ni?”

“Ai kuwa alamun haukar tana neman tabbata a gareki ba sai kin min gatse ba, yanzu Nafeesa tayaya zaki iya rabuwa da Haidar ki koma kan amininsa shaƙiƙi kuma ɗan uwansa kice yanzu shi kike so ba Haidar ba, ta yaya zaki fara, abun ai da a kwai nauyi, idan kika yiwa Haidar haka baki masa adalci ba, Tabbas kin zalunci rayuwarsa, karki manta ɗan uwansa ne Al’ameen, idan kikayi haka nafeesa zaki hura wutar da kasheta zaiyi wahala.”

“Hmmm yaushe kika fara wa’azi ni ina ruwana da wata wuta da zata huru, Amnat akan cikar burina banƙi kowa ya mutu ba, muddun zan samu biyan buƙata ta, dan haka ki daina tuna min da kusancin dake tsakanin su, dole ne Al’ameen ya kasance nawa na har abada domin kuwa a wannan karon Auren Al’ameen nake son nayii saboda shine mutumin da zan tabbata cikin dukiya muddun na auresa.”

Miƙewa tsaye Amnat tayi cike da mungun ɓacin rai domin kuwa tana hango babban kuskure ga abinda ƙawarta take ƙoƙarin aikatawa, tabbas tasan itama kusan halinsu ɗaya da Nafeesa sai dai Nafeesa ta fita son Zuciya da rashin imani.

“Wai me zakiyi da kuɗi ne haka Nafeesa da bazaki haƙura da iya wanda Haidar ke baki ba shin meye baya miki, wannan abinda kike shirin yi babban zunubi ne a rayuwarki domin kuwa kina shirin kunna wuta tsakanin masoyan abokai, ina laifin ace wani bare can kika samo ba ɗan uwan Haidar da abin zaizo da sauƙi na roƙeki Nafeesa karki yiwa Haidar haka dan Allah.”

“Wai ke meye haɗinki da Haidar ne, da kika bi kika damu akan wannan lamarin, kinga Amnat wallahi babu abinda zai hana ban mallaki Al’ameen ba, domin kuwa yamin a irin mijin da nake son Aura dan haka ki daina ɓatawa kanki lokaci.”

“Amma kuwa Tabbas idan kikayi haka kin cika azzaluma marar imani wanda shiga aljanna zai miki wahala.”

Ɗago daradaran idanunta Nafeesa tayi tana kallon Amnat cike da mamakin kalamanta cikin ɓacin rai tace.

“Shiga aljanna zata min wahala kikace Amnat, ke kuma ta cikin sauƙi zaki shiga ko, to ni dake ɗin ai babu bambanci duk ƙwaryar sama ce da ta ƙasa, kuma ai abokin ɓarawo ma ɓarawo ne, nasan wallahi ko kece kika samu wannan damar dana samu abinda nayi shi zakiyi dan haka naji shiga aljanna zata min wahala aje a hakan, ke kije ki shiga ta sauƙi.”

“Ni dake da akwai banbanci Tabbas nasan ina son kuɗi amma ba irin naki ba, ni nasan hallaci ban iya cin amana ba, Tabbas ni karuwa ce kamarki, amma duk da haka zan faɗa miki gaskiya Nafeesa.”

“Bana buƙatar gaskiyar ki, ki riƙe abinki, ba shawara nake nema a wajenki ba Amnat ba kuma umarni nace ki bani ba, ko uwata bata isa dakatar dani ba bare kuma kee! Ga hanya Amnat tanan kika shigo to ki fita.”

Ta ƙarisa Maganar tana nunawa Amnat hanyar fita da kallo Amnat ta bita tare da cewa.

“Saboda na faɗa miki abinda ya dace shine yau kike korata a gidan ku, zan tafi amma kiyi tunani akan maganata kafin yankewa kanki mungun hukunci.”

“Yau korarki kawai nayi a gidan mu, gobe idan kika kuma kwatanta min irin abinda kika min yau ALAƘA ZAN YANKE DAKE domin zan iya rabuwa da ke akan wannan lamarin, bake kaɗai ba duk wanda yayi ƙoƙarin tare min hanya to wallahi zan turesa na wuce.”

Kanta Amnat ta girgiza ba tare da ta kuma cewa komai ba tasa kanta ta shige, tsuka Nafeesa taja tana bin Amnat da harara.

*****

Tun ɗazu yake zaune ya gagara tashi a wajen idanunsa ya lumshe yana jin jikinsa duk ya mutu duk da ba wani aiki yayi ba, amma jikinsa duk babu ƙarfi, idanunsa ne suka sauƙa a kanta zata shige kitchen, murmushi ya saki yana bin bayan ta da kallo, Tabbas yanayin tafiyarta yana burgesa, duk da macece mai sanyin hali sai dai da alamu zatayi mugunta, numfashi ya saki yana kawar da zancen zucin nasa cikin slow voice ɗinsa ya kirata.

“Keee! Soloɓiyo”

Cak Ablah ta tsaya jin muryar sa ta doki dodon kunnensa domin kuwa shine kawai yake kiranta da wannan sunan *SOLOƁIYO* kamar bazata juyo ba dai gudun Fitina ya sata juyowa tana kallon sa.

“Kizo nan.”

A hankali cike da nutsuwa ta ƙariso gabansa ta tsaya tare da cewa.

“Sunana ABLAH ba SOLOƁIYO ba.”

Murmushi Al’ameen ya saki yana kallon ƙaramin bakin nata dake masa magana.

“Jeki kawo min tea, karki saka sugar yayi yawa guda biyu ya isa.”

Hararar sa Ablah tayi tare da juyawa zata bar wajen taji ya riƙo hanunta, a mungun tsorace zuciyarta na bugawa wani irin shocking taji runtse idanunta tayi tana ƙoƙarin ƙwace hanun nata amma ta kasa cike da mugunta yake murza mata hanun wani irin azaba take ji hanun na mata.

“Ka sakeni meye haka zaka wani riƙe min hanu kasan dai haramunne namiji ya riƙewa mace hanu ko?”

“Ban sani ba ni jahili ne, Uban waye kike harara?”

Kanta ta sunkuyar ƙasa tana ƙoƙarin ƙwace hanunta taƙi yin magana.

“Ba kuwa zan sakeki ba har sai kin faɗa min Uban waye kike harara?”

“Ni fa ban harareka ba, gacan abin da nake harara shine ya cimin tuntuɓe ɗazu.”

Dariya ce taso ƙwacewa Al’ameen wai bakin step shi take harara bayan kuma ya ga shi take hararar, sakin hanunta yayi tare da cewa.

“Jeki Soloɓiyo ki kawo min yanzun nan”
Shigewa tayi tana ƙunƙuni tace.

“Allah ya isa mungun banza, haka ka zalunceni da safe yanzu ma haka, kai ga baƙin mungu, Allah ya bimin kadu na.”

Jin kamar tana Magana ƙasaƙasa yasa Al’ameen cewa.

“Me kika ce?”

“Nifa bada kai nake ba.”

Ta basa amsa tana barin wajen cikin sauri, lumshe idanunsa yayi tare da sakin murmushi yana dubanta harta shige kitchen ɗin.

Jin wayarta na ringin yasa Aunty Amarya ijiye naɗin kayan da take ta ɗauki wayar, HAJIYA MANSURA murmushi tayi tare da ɗaga wayar tayi sallama daga can Hajiya Mansura ta amsa tare da cewa.

“Ya akayi sun tafi ne Ashfat ɗin.?”

“Ina kuwa sai gobe ne zasu bi jirgin 11am”

“Okay yayi, ga nan gubar nan fa na turo Abbas da ita yana ƙofar gidan ku, mai gadi ya hanasa shiga, ki fita ki karɓa, sannan ki kula wajen sawa ki tabbatar babu wanda ya ganki sannan ki tabbatar Al’ameen ne kawai zaici wannan gubar kiyi taka tsantsan.”

Numfashi Aunty Amarya ta saki tana murmushi tace.

“Ai kin san bana wasa akan wannan aikin babu wata matsalar da za’a samu tabbas Al’ameen yau ɗin nan ba sai gobe ba zai baƙunci lahira.”

Dariya Hajiya Mansura tasa tare da cewa.
“Hakane ƙawata nasan halinki babu wasa kije yana bakin get yana jiranki.”

Tayi Maganar tana katse kiran, tashi Aunty Amarya tayi da sauri ta fito, a falo taga Al’ameen yana kwance a 3ster shi kaɗai ya ɗaga kansa sama murmushi Aunty Amarya tayi tana kallon sa cikin zuciyarta tace.

“Al’ameen ka huta da kyau yau dai rayuwarka tazo ƙarshe kai ga magajin mai gida, ai kuwa bazaka taɓa gadon ubanka ba, bazan bari hakan ta faru ba muddun numfashi na yana bugawa.”

Murmushi ta saki tare da kiran sunan sa a fili tace.

“Al’ameen kai ɗaya ne yau a falon ina khalipan yake.”

Idanunsa ya ɗago ya kalleta tare da sakar mata murmushi yace.

“Eh ni ɗaya ne, Khalipa tun ɗazu ya fita ai.”
Ya ƙarisa Maganar dai-dai ABLAH na isowa wajen hanunta riƙe da cup ɗin tea, dubanta Aunty Amarya tayi tare da kau da kanta gefe ta cewa Al’ameen.

“Okay”

Tare da ficewa ta nufi wajen Abbas dake jiranta bakin get, Ablah da kallo ta bita kafin ta ijiye masa tea ɗin ba tare da tayi Magana ba tabar wajen shima baice mata komai ba ya saka hanu ya ɗauki tea ɗin…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita? 16Aminaina Ko Ita? 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.