Bedroom ɗinsa zai shige sai ya juyo kamar shashsheƙar kuka, shuru yayi tare da tsayuwa ya kasa kunnen sa, Tabbas shashsheƙar kuka ne yake fitowa daga bedroom ɗin su Madina ƙanwarsa, numfashi ya saki tare da girgiza kansa ko ba'a faɗa masa ba, yasan Rufaida ce, door ɗin ya tura ya buɗe a hankali tare da shigewa ciki, tana kwance ruf da ciki sai famar kuka take tana dafe da ƙirjinta, idanunsa ya runtse cike da fara jin haushin Rufaida.
"Rufaida! Rufaida!"
Taji muryar sa ya doki dodon kunnenta, duk a zatonta gizo kunnenta ke. . .
I want to join
Interesting story