Skip to content
Part 18 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Bedroom ɗinsa zai shige sai ya juyo kamar shashsheƙar kuka, shuru yayi tare da tsayuwa ya kasa kunnen sa, Tabbas shashsheƙar kuka ne yake fitowa daga bedroom ɗin su Madina ƙanwarsa, numfashi ya saki tare da girgiza kansa ko ba’a faɗa masa ba, yasan Rufaida ce, door ɗin ya tura ya buɗe a hankali tare da shigewa ciki, tana kwance ruf da ciki sai famar kuka take tana dafe da ƙirjinta, idanunsa ya runtse cike da fara jin haushin Rufaida.

“Rufaida! Rufaida!”

Taji muryar sa ya doki dodon kunnenta, duk a zatonta gizo kunnenta ke mata kamar yadda ya saba, Haidar ganin bata da niyyar ɗago kanta ya sashi saka hanu ya dafa kafaɗar ta, a ɗan firgice ta ɗago kanta, ganinsa tayi zaune gefen bed ɗin, kanta ta sunkuyar tare da share hawayen ta.

“Gaskiya a yanzu kam na fara tunanin baki da hankali, yanzu ke Rufaida ki zauna kina ta sawa zuciyarki ƙunci kuma kinƙi kije ki sanar masa shine rayuwarki, idan kikayi wasa wallahi ciwon zuciya zai kamaki ki kashe kanki a banza shikam ba ruwansa domin kuwa bai san kinayi ba tunda tsoro yasa kinƙi sanar dashi, idan kika mutu ai kin huta, sai kije kiyi soyayyar a lahira.”

Yayi maganar cikin ɓacin rai ganin ransa ya ɓaci yasa Rufaida ƙara sautin kukanta, ta yaya zata iya sanar masa cewa shine take so, ta sani duk wannan kulawar da yake bata yanzu yana jin cewa shine take so zai gudunta sai dai a wannan taƙin dole zata sanar dashi damuwarta idanunta ta kulle gam cike da tsoro ta furta.

“Kaine! Ya Haidar kaine!”

“Nine kuma, Ni ne me ban gane ba Rufaida, au na fahimceki kina nufin nine zanje na sanar dashi kina sonsa, to shikenan karki damu insha Allah kuwa zanje har inda yake na samesa, mu tattauna, ki bani adress ɗin sa da kuma numbern wayarsa zanyi ƙoƙarin na fahimtar dashi yadda kika damu dashi wataƙila ya tausayawa halin da kike ciki.”

Rufaida hawayenta ta goge tana cigaba da shashsheƙar kuka, ya gagara fahimtar ta bare ya gano alƙibilarta shi zato yake wani can a waje take so duk kulawa da ƙoƙarin da take domin ya fahimta ya gagara fahimta, kanta ta girgiza tare da furta.

“Baka fahimce ni ba ya Haidar, ina nufin kaine wanda zuciyata take so, ina tsoron sanar da kai Saboda bansan ta yaya zaka ɗauki lamarin ba Ya Haidar nasan kana da wacce kake so shine kukana domin kuwa ka bada zuciyarka duka zuwa gareta, nayi ƙoƙarin cire Soyayyar ka a zuciyata na kasa, ka taimakawa rayuwata dan Allah ka bani gurbi komai ƙanƙantarsa a zuciyarka na yadda ni zanje a ta Biyu koda kuwa zaman boranci zanyi muddun zanyi rayuwa da kai ni hakamma ya min.”

Tunda ta fara Maganar ya zuba mata idanu yana kallonta cike da mungun firgici gumi ne ya keto masa tamkar almara yake jin maganganunta, Nafeesa ce kawai zaɓin rayuwarsa baya tunanin zai iya mata kishiya, gurbinta ne kawai a cikin zuciyarsa, baya tunanin zai iya bawa wata matsuguni a zuciyarsa, ta yaya zai iya duban ƴar Uwar sa yace mata baya sonta, ya sani Tabbas tana cikin matsanancin Soyayyar sa, shine shaida akan haka, gashi baya jin zai iya bata wani matsuguni a cikin zuciyarsa, numfashi ya saki tare da miƙewa tsaye, kansa ya kawar gefe tare da nufar barin cikin ROOM ɗin, Rufaida da kallo tabi bayan sa tare da ƙara sakin kuka mai cin zuciya Tabbas ta sani dama bazai sota ba, bazai tausaya mata ba, ganin harya isa bakin ƙofa ya sata cewa.

“Kaine kamin alƙawarin ƙwacomin soyayyata ta ko wacce hali, kamin alƙawari cewa zaka tayani yaƙi akan soyayyata, meyasa zaka tafi ba tare da kace komai ba, ka tuna da wannan alƙawarin, ka yankewa soyayyata hukunci da gaggawa domin nasan inda alƙibilata ta nufa mai daɗi ko marar daɗi, amma dai nasan kai mutum ne mai cika alƙawari.”

Tsak Haidar ya dakata yana sauraron kalamanta, yana jin maganganunta tamkar narkakken ruwan dalma take tsiyaya masa a kunnuwansa, Tabbas yayi dana sanin shigowa bedroom ɗin ta a yanzu da yasan wannan maganar zata sanar dashi da bai yadda ya shiga ba, Tabbas ya mata alƙawarin yaƙi a soyayyarta amma bai mata alƙawarin bata zuciyarsa ba, bazai yadda ya ci amanar Nafeesa ba, domin kuwa zuciyarsa nata ne ita kaɗai, cikin sanyin jiki ya juyo tare da zubawa Rufaida idanu cikin sanyin murya mai cike da rauni yace.

“A yanzu bani da nutsuwa da hankalin da zan yanke hukunci tsakanina dake domin kuwa kin firgita ƙwaƙwalwata ban taɓa zaton wannan kalmar daga bakinki ba, Allah ya sani zuciyata bata da wani sauran fili da zaki zauna a cikin sa, haka kuma bani son kallonki cikin mungun yanayi damuwarki takan ɗaga min hankalina a matsayin ki na ƴar uwata, na sani na miki alƙawarin yaƙi akan soyayyarki, HMMM! Sai dai ban miki alƙawarin baki zuciyata ba, Nafeesa itace kawai muradina bana jin zan iya son wata mace bayan ita, ina mata tsananin Soyayyar da bana yiwa kaina, bazan iya yiwa Soyayyar Nafeesa kishiya ba, ita ɗin rayuwata ce, bazan iya mata kishiya ba, na ƙara maimaita miki, ki gafarceni Rufaida bazan iya baki zuciyata ba.”

“Kaine ka faɗa min ban faɗi ba a soyayyata, kace min koda na faɗi nayi ƙoƙarin na tashi wannan itace alamun Nasara, na faɗi na kasa tashi wannan shi ake kira da rashin Nasara, kaine ka faɗa min wannan ka bani ƙwarin gwiwwa kasa na cigaba da renon Soyayyar ka a tunanina wanda ya faɗa min haka idan har ya fahimci shine muradina zai tausaya min, sai dai kash gashi yanzu kaine kake ƙoƙarin kaini ƙasa kana so Lallai nayi faɗuwar da bazan iya tashi ba, dan Allah karka azabtar da zuciyata ta hanyar Soyayyar ka, kai ɗan uwana ne ka tausaya min dan Allah.”

“Na sani ko me zan faɗa miki bazaki fahimta ba, Saboda kina makance ne, shiyasa naƙi baki amsa daga farko, bansan yadda zan miki ba ki fahimta.”

Yayi Maganar yana saka kai ya fice daga bedroom ɗin nasu, nasa ROOM ɗin ya shiga cike da damuwa gami da tashin hankali, a kujerar dake tsakiyar ROOM ɗin ya faɗa tare da dafe kansa maganganunta suna yawo a cikin kunnuwansa, idanunsa ya runtse, a fili ya furta.

“Dama duk wannan wahalar da Rufaida take sha nine take so, meyasa ta kasa faɗa min tun kafin na haɗu da Nafeesa, da a wannan lokacin zan rarrashi zuciyata na koya mata Soyayyar ki, sai dai kash mun makara komai ya ƙwace domin kuwa Nafeesa itace ƙaddarar rayuwata bana jin zan iya rayuwa da wata idan ba Nafeesa Duniyata ce farin ciki na, ta yaya zan fara korar ƴar Uwata daga cikin rayuwata, gashi kuma bazan iya baki soyayyata ba, mtsss! Bansan ya akayi haka ta faru ba, sai dai koma mai zai faru bazan taɓa cin amanar Nafeesa ba.”

Yayi Maganar yana cije bakinsa, miƙewa yayi tsaye ya hau zagaye bedroom ɗin, yana nazarin kalaman Rufaida, ya juma yana kaiwa da komowa a cikin bedroom ɗin amma ya rasa mafita, numfashi ya sauƙe tare da faɗawa saman bed ɗinsa ya runtse idanunsa. 

Ita kuwa Rufaida tunda ya fita take risgar ta rasa yadda Zatayi da zuciyarta ta kasa control ɗin kanta a garesa, sosai tasha kuka har sai da idanunta suka kumbura.

Ablah cike da nutsuwa take aikin girkinta, yau haka kawai taji a ranta ta girka musu tuwon burabusko miyar ganye, komai a nutse take yi, take kuwa ta kammala girki, farar shinkafa ta dafawa Al’ameen tare da miyar stow, kasancewar Ladiyo ta sanar da ita cewa Al’ameen baya son tuwo bayan ta gama ne ta fito daga cikin kitchen ɗin.

Tunda Ablah ta fara girkin Aunty Amarya ke kaiwa da kawowa ta tunanin ta wacce hanya zata zubawa Al’ameen gubar nan a cikin abincin sa, ga Ablah bata nisa ga girkinta, numfashi ta sauƙe tana tsaye saman step ɗin ta hango Ablah ta fito daga kitchen kira ta ƙwala mata, amsawa Ablah tare da haurowa, dubanta Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Me kike dafawa ne yau a cikin gidan nan?”

“Tuwo ne nayi na gero miyar ganye.”

 Zaro idanunta Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“What! Tuwo kuma wai ke meyasa baki da hankali ne Ablah an faɗa miki cikin gidan nan an damu da tuwo ne mtsss! Ke shashace wallahi, to maza kije ki nemawa Al’ameen abinda zaici domin kuwa dai shi baya cin tuwo, sannan yaci shinkafa ɗazu bazai cita ba yanzu sai kisan yadda zakiyi dashi.?”

Tayi Maganar tana juyawa ta shige bedroom ɗin ta shuru Ablah tayi tana nazarin to me zata dafawa Al’ameen, ita wallahi lamarin gidan nan ya fara isarta komai kayi ba dai-dai ba ne, tsuka taja tare da sauƙa ƙasa, ta ƙara nufar kitchen, ko da ta shiga cikin ɗin rasa me zata dafawa Al’ameen tayi domin kuwa tsoron masifarsa takeji gashi shi duk abinda tayi a wajen sa ba daidai bane, kai gara kawai na koma wajen Aunty Amarya na tambayeta me za’a dafawa Al’ameen tunda ita tasan duk abinda yake ci, fita tayi ta nufi bedroom ɗin Aunty Amarya hanu tasa zata buɗe room ɗin sai taji wata kalmar da ta gigitata daga cikin ROOM ɗin Aunty Amarya, nutsuwa tayi tare da toshe bakinta tana zaro idanunta.

“Yanzu haka Hajiya Mansura neman hanyar da zan saka masa gubar nake, Yarinyar da take girkin ne mayya ce wallahi shiyasa na tsaneta taƙi kaucewa bare na samu na zuba gubar, amma karki damu dole zansa masa wannan gubar a yau ɗin nan dan wallahi Al’ameen dole sai ya mutu Yau.”

Wani irin gigita Ablah tayi idanunta ta zaro cikin mungun tashin hankali da mamakin Aunty Amarya, matar da take yiwa kallon Uwa a garesu wanda bata taɓa tunanin zata cutar dasu innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Lallai ne Mutum mungun icce, to amma meyasa zata kashesa, meya mata, yanzu idan ta saka wannan gubar waye za’a zarga, dole nice tunda nine nayi girkin.

Tayi Maganar zucin ƙirjinta na bugawa cike da matsanacin tsoro, jin alamar motsin Aunty Amarya zata fito yasa Ablah saurin barin wajen cikin sanɗa saboda kar Aunty Amarya ta ji sautin tafiyarta, a gigice ta sauƙo daga step ɗin, wani irin karo taci dashi baya tayi zata faɗi yayi saurin saka hanu ya riƙota, yana ƙare mata kallo ganin tamkar tana cikin tsoro ya sashi sakinta yana cewa.

“Lafiya kika sauƙo a tsorace.?”

Kanta Ablah ta girgiza har yanzu a tsorace take tace.

“Lafiya babu komai.”

Tayi Maganar tana shigewa cikin sauri kitchen ɗin ta nufa cike da tsoro lallai bazata bar kitchen ɗin nan ba har sai kowa ya fito daining, tayi Maganar tana sakin numfashi.

Shi kuwa Al’ameen da kallo ya bita tare da taɓe bakinsa, ya shige.

Aunty Amarya kuwa fitowa tayi daga bedroom ɗinta, zata sauƙa sai taga Afnan ta fito itama daga nasu ROOM ɗin murmushi Aunty Amarya ta saki na samun dama.

“Yauwa Afnan ƙasa zaki sauƙa ne.”?

Amsa Afnan ta bata da cewa.

“Ehh Aunty ƙasa zan sauƙa.”

“Yauwa dan Allah gashi kije ki bawa Ablah kuɗin nan ta fita waje ta karɓo min Virony a kantin dake gefen Estate ɗin nan, na duba bedroom ɗina babu kuma ina buƙatar sa yanzu ki tabbatar ta fita akan idanunki saboda ina buƙatar sa ne.”

Amsa Afnan tayi tare da sauƙa ƙasa murmushi mai sauti Aunty Amarya ta saki ta naɗe hanunta tare da tsayuwa jikin step ɗin tana jiran fitar Ablah.

Ita kuwa Afnan kitchen ta nufa kanta tsaye, Ablah ta gani ta sauƙe doya akan gas, sunanta ta kira.

“Ablah!”

Juyowa Ablah tayi ta amsa da.

“Na’am Aunty Afnan kece da kanki me kike so da kin kirani ai dana kawo miki.”

Murmushi Afnan ta saki duk da Afnan bata son zama cikin mutane sai dai sam bata da baƙin hali ko raina Mutum cewa Ablah tayi.

“A’a babu abinda nake nema, Aunty ne tace na baki kuɗin nan kije kantin Audu ki amso mata virony yanzun nan zatayi amfani dashi, kuma naga kina aiki, ki kawo na kwashe miki doyar sai kiyi maza kije ki amso mata.”

Wani irin tsinkewa zuciyar Ablah tayi take taji zuciyarta ta ɗarsu da zargin Afnan, tana tunanin cewa sun haɗa baki da Aunty Amarya ne saboda ta bar wajen su sakawa Al’ameen guba, numfashi ta sauƙe bata son zuwa sai dai babu yadda ta iya aiki take musu dole ne taje amsa tayi tare da amsawa da to, ta fice zuciyarta na tsinkewa, tana tsoron mummunan abinda zai faru yau a gidan, a harabar gidan ta hangosa tsaye shida mai gadi suna magana da kallon tausayi ta bisa, tana tausayawa halin da zai shiga yau shi kuwa sam baima lura da shigewarta ba.

Aunty Amarya tana ganin shigewar Ablah ta zuba idanu taga fitowar Afnan, ta kusa 15minute kafin ta fito ta shige ROOM ɗin Inna Jumma, ai kuwa ganin haka yasa Aunty Amarya fitowa da sauri ta shiga cikin kitchen ɗin murmushi ta saki tare da jawo ƙaramar kular da aka sawa Al’ameen miyar stow ɗin ta zuba gubar, cikin sauri gami da tsoron shigowar wani har zata fito sai tayi tunanin me zai hana ta zuba a sauran na tukunyar ma, ai kuwa take tayi na’am da shawarar zuciyarta da sauri ta koma ta zuba a wannan ɗin ma, kafin ta fita ba tare da kowa ya ganta ba.

Ablah Kamar yadda ta fita cikin tsoro haka ta dawo da wannan tsoron, Afnan ta iske a falo ta bata virony ɗin amsa Afnan tayi tare da bawa ihsan da ta sauƙo daga sama tace ta kaiwa Aunty Ablah kitchen ɗin ta shige da sauri, dube dube ta fara ko zataga alamun wani abu sai bisa mamakinta yanda tabar komai haka ta dawo ta samu tamkar ba’a taɓa komai ba, sai doya da Afnan ta kwashe ta saka a kula numfashi mai nauyi Ablah ta saki tare da furta.

“Hmmm! Alhamdulillah! Daga gani bata shigo ba, Allah ya taimakeni”

Tayi Maganar tana duban window ganin su Afnan da Maimu Ashfat ma an fito da ita yasa Ablah fito da abincin ta jeresu a daining kafin ta tafi bedroom ɗinta.

8:30pm kuwa kowa ya hallara a daining ɗin har Daddy da Inna Jumma, kaf wajen babu wanda baiyi farin ciki da tuwon gero da Ablah tayi ba, mussaman Ummi da Daddy da Inna Jumma sunfi kowa murna, ihsan ma cewa tayi shi zataci, Al’ameen shine kaɗai yake yiwa tuwon kallon ƙyama, Afnan ne tayi seving ɗinsu, yayin da Aunty Amarya zuciyarta ke cike fal da farin cikin Al’ameen zai mutu, abincin ta ta kai bakinta cike da farin ciki, Al’ameen kallon doyar dake gabansa yayi tare da jefawa Afnan mungun kallo yace.

“Na zuba abincin da kaina ne?”

Bakinta Afnan ta tura tare da miƙewa ta jawo kular ta saka masa doyar tare da miya, ta tura masa gabansa, Daddy murmushi ya saki tare da cewa.

“Oh ikon Allah, wato dai Zakina kai da mamana bazaku daina ƴar tsama ba kenan ko bana fa son Wannan abinda kuke yi.”

Shuru Al’ameen yayi yaƙi amsawa Daddy Afnan ce ta tura bakinta tare da cewa.

“To dai bashi bane yabi ya tsaneni, duk gidan babu wanda yaƙe ƙuntatawa sai ni kuma duk kuna kallo babu mai bi mini kaduna.”

Idanunsa Al’ameen ya ɗaga ya zubawa Afnan yana harararta, kanta ta kawar gefe, murmushi Daddy ya kuma yace.

“Kinga mamana ki yi haquri kinji yayanki ne dole zai hukunta ki, ke dai ki kiyaye.”

Inna Jumma ne tayi carap tace.

“Karma ta kiyaye dan ubanta, ta dinga jibguwa kenan kamar jaka, ni na rasa wacce ƙaddara ce tasa ka sakawa wannan Yarinyar sunana.”

Dariya Al’ameen yasa yana duban Inna Jumma tare da cewa.

“Waya sani ko halinki ta biyo idan ta ɗauro ma abinda takeyi shi kikayi kina kamarta.”

Gabaki ɗayan su dariya suka saka, Inna Jumma cike da haushi ta kaiwa Al’ameen duka kaucewa yayi yana dariya tare da saka hanu ya jawo plat ɗin abincin nasa, spon ya ɗauka tare da saka hanu ya ɗibi doyar zai kai bakinsa yaji muryar Ummi na ce masa.

“Am gobe fa zakayi sammako ka kai su Ashfat da Auntyn Faruq airport zasubi jirgin 7:00am”

Ajiye spon ɗin yayi tare da amsawa da.

“Okay Allah ya kaimu.”

Ablah tunda ta shiga cikin bedroom ɗinta hankalinta ya kasa kwanciya gabaki bata da nutsuwa, ji take tamkar idan Al’ameen yaci abincin nan akwai mummunan abu da zai faru kasa haƙuri tayi ta fito da sauri.

Shi kuwa doyar ya ɗago zai kai bakinsa, Ablah ta ƙwala masa kira.

“Al’ameen! Al’ameen!”

Tayi Maganar da ƙarfi, juyowa dukkan su sukayi suna kallon ta, da gudu ta ƙaraso daining ɗin tare da saka hanu ta ture abincin gaban Al’ameen, sauran miyar dake cikin kular shima ta ɗaga ta zubar dashi, gabaki ɗayan su da mungun mamaki suke kallon ta, Al’ameen wani irin ɓaci yaji ransa yayi, gani yake Ablah ta masa cin mutunci, a matuƙar harzuke ya miƙe tare da ɗauketa da mari zai kuma ƙara mata Daddy ya daka masa tsawa.

“Karka kuskura ka sake marinta idan ba haka ba ranka ya ɓaci meye abin duka anan, sai ka fara tambayarta tukunna meyasa tayi maka, bana son wannan zafin zuciyar taka.”

Inna Jumma ce tace.

“Idan bai ci mata mutunci ba zaiji daɗi ne, ai hankalinsa bazai kwanta ba idan bai wulaƙanta ta ba, kai ga ubanta bari ka daketa koko Saboda tana bauta a gidan ku.”

Al’ameen runtse idanunsa yayi zuciyarsa na masa ƙuna yace.

“Daddy kana gani fa abin…”

Hanu Daddy ya ɗaga masa tare da cewa.

“Ya isa bana son jin muryar ka anan.”

Bakinsa ya cije tare da juyawa a zuciye yabar falon yana hararar Ablah tare da ƙwafa.

Ita kuwa Aunty Amarya wani irin baƙin ciki ne ya daki zuciyarta, take taji wani mungun raɗaɗi da ƙunci ta gama sawa a ranta cewa Al’ameen zai sheƙa yau lallai wannan Yarinyar tayi mungun cutarta to meye nufinta na zubar da abincin Al’ameen, muryar Ummi ya daki dodon kunnenta.

“Ablah meyasa kika zubar da abincin sa?”

Ablah da kanta ke sunkuye idanunta na zubar da Hawaye ne tayi shuru domin kuwa ta rasa me zata ce, Ummi ƙara maimaita mata tambayar tayi, cikin inda inda Ablah tace.

“Amm….amm….dama kamar kyankyaso na hango cikin miyar shine yasa nazo da sauri na zubar karya ci wani abu ya faru.”

Tayi Maganar cikin tsoro Aunty Amarya cikin tsana da haushin Ablah tace.

“Ƙarya kike baƙar munafuka a ina za’a samu kyankyaso cikin gidan nan ko an faɗa miki irin gidan kune wannan gidan gidan ƙasa da shaddar masai mtsss kiji Yarinyar nan da rainin way…”

“Ya isa haka amarya bana son cin mutunci, abinda ya faru ya riga ya faru kowa yabar Maganar, ke Ablah jeki abinki kinji karki sake irin haka.”

Cewar Inna Jumma, cikin sanyin jiki Ablah ta juya ta tafi.

Cike da mungun ɓacin rai har tana jin idanunta suna rufewa Aunty Amarya ta juya tabar wajen, Daddy ne ya dubi Maimu tare da cewa.

Ki tashi ki goge wajen, shima yayi maganar yana barin wajen, Ummi numfashi ta saki itama ta tafi haka duk suka watse ba tare da kowa yaji daɗi ba, Maimu wajen ta gyara.

AUNTY Amarya tunda ta shiga room ɗin ta take kaiwa da komowa cikin baƙin ciki zargi take anya kuwa Ablah bata san wani abu game da shirinta ba, idan ba haka ba meyasa zata zubar da abincin ta hanasa ya ci, kai ina dole naje na binciki Yarinyar nan da alamu akwai wata a ƙasa, tayi Maganar tana fitowa, bedroom ɗin Ablah ta shiga tare da dannawa bedroom ɗin key, tana zaune tayi shuru jikinta duk yayi mungun sanyi ji tayi Aunty Amarya na magana a kanta.

“Ki faɗa min gaskiya meyasa kika zubar da abincin Al’ameen kaɗai domin kuwa akwai abinda kika sani?”

Ɗago idanunta Ablah tayi tare da cewa.

“Na faɗa muku gani nayi kamar kyankyaso cikin miyar shiyasa na zubar.”

“Ƙarya kikeyi domin kuwa na hango inuwar mutum sanda nake waya zubar da abincin da kikayi shine ya tabbatar min da kece hmmm! Wato kin min laɓe, yayi kyau to ki sani ke ɗin nan baki isa ki hanani abinda naga dama ba, karfa ki manta matsayinki a cikin gidan nan *ƳARKI MARAR ƳANCI* shine kawai matsayin da kike dashi, ni kuwa uwace wacce kowa keso a cikin gidan.”

Numfashi Ablah ta saki tare da ɗago kanta ta kalli Aunty Amarya tace.

“Meyasa kike so ki kashe sa, nayi mamakin hakan matuƙa kefa uwace kamar yadda kike faɗa min yanzu wacce kowa ya yadda da ita acikin gidan, meyasa kikayi Amfani da yardar da suka miki kike cutar dasu?”

Murmushi Aunty Amarya tayi tare da zama gefen Ablah tace.

“Tambaya me kyau, Tabbas ni uwace amma ba ga Al’ameen da ƴan uwansa ba, ga ƴaƴan dana haifa a ciki na, baki san cewa baka sanin yadda zaka kifar da mutum , har sai ka shiga jikinsa ka gama sanin yaya wannan mutumin yake sannan ya gama basa yardar sa, da zarar ya yadda dakai to fa kafin ya ankara ka kifar dashi, wannan shine salon yaƙi na, banyi zaton akwai wanda zaiji asirina nan kusa ba, sai dai kash tsautsayi yasa kinji sannan har hakan yasa kin dakatar min da aikina na yau hakan ba ƙaramin ciwo yamin ba, sai dai kina da zaɓi tsakanin ki dani na farko tunda kinji sirri na, na baki dama ki dawo gareni mu haɗe ki tayani aiki, zaki samu kuɗin da har ki mutu keda uwarki bazaku yi talauci ba, na biyu kuma idan kinƙi zaki shiga cikin uƙuba ta, zaki gwammaci mutuwa da rayuwa domin ni kaina nasan bani da imani, Tabbas zan ɗanɗana miki azabar da tafi mutuwa ciwo zaɓi yana gareki.”

Tunda ta fara Maganar Ablah ke kallonta cike da mamaki tunda take a duniya bata taɓa ganin Mace Irin Aunty Amarya ba, murmushi Ablah tayi cikin izzar da bata san tana dashi ba tace.

“Bana buƙatar abun duniya shiyasa kuɗi basa gabana, hmmm! Rayuwar talauci wannan ai mun saba rayuwa cikin sa, domin kuwa cikin sa muka taso kuma rayuwar tafi min daɗi a haka, bana taɓa aikin zalunci bazan tayaki ɓarna ba, domin kuwa Asali ma ni zan tona miki asiri zan sanar da kowa mugun nufin ki domin su ankara dake su kare rayukansu, bana tsoron uƙubar ki domin kuwa baki isa kimin Abinda ubangiji na bai min ba.”

Dariya Aunty Amarya ta saka tare da cewa.

“Au naji tsoro ko zaki tona min asiri, yaro bai san wuta ba sai ya taka, ki tashi yanzu kije ki faɗa muga ko zasu yadda, ni ce fa wacce suka fi yadda da ita fiye da kowa a cikin gidan nan duk abinda zaki faɗa bazasu taɓa yadda ba, a ƙarshe ma kece reshe zai juyewa da mujiya, kije kiyi tunani akan zaɓi na, ki zaɓi zama lafiya ko zaman baƙin cikin rayuwa.”

  Tayi Maganar tana ficewa daga ROOM ɗin, da kallo Ablah ta bita dashi tana hango tsantsar rashin imani ƙarara a idanunta Tabbas gaskiya ta faɗa koda ta sanar dasu Al’ameen bazasu yadda da ita ba, sannan zata iya aikata duk wani abinda ta faɗi domin kuwa babu Allah a ranta, rasa mafita Ablah tayi sai dai ko me zai faru bazata taɓa yadda ta goyawa Amarya baya ba sai ta mata duk abinda taga dama.

Tana shiga bedroom ɗin ta ta kira Hajiya Mansura ta sanar da ita abinda ke faruwa har yadda sukayi da Ablah itama Hajiya Mansura cike da tashin hankali tace.

“Ba’a raina maƙiyi amarya domin kuwa zai iya maka illar da bazaka ganu ba, karki raina shirin wannan Yarinyar, nama rasa wani hukunci zan yanke ta gigitani da yawa.”

Amarya tana hucin ɓacin rai tace.

“Ni na yanke mata hukunci mafi muni a rayuwar Mace muddun bata amsa ƙudirina ba, na rantse da Allah sai na saka an aikata mata.”

Hajiya Mansura cewa tayi.

“Wani irin hukunci kika yanke mata?”

“Hajiya Mansura muddun bata amince da buƙatata ba, to zansa a mata FYAƊE kuma na rashin imani wallahi alƙawari na ɗauka…”

<< Aminaina Ko Ita? 17Aminaina Ko Ita? 19 >>

2 thoughts on “Aminaina Ko Ita? 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×