Skip to content
Part 2 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Tun daga nesa Haidar yake binta da kallo cike da mamakin waye kuma zaune gaban motar sa cike da mamaki ya ƙaraso bakin motar ya tsaya tare da zuba hannayensa cikin aljihu yana kallon ta, sosai yake ƙare mata kallo, “waye ita?” Ya furta cikin ransa numfashi ya sauƙe tare da tsugunnawa a gabanta zuciyarsa na jin tausayin ta domin kuwa da dukkan alamu bata da lafiya, a hankali ya furta.

” Baiwar Allah lafiya meya sameki?”

Tana jinsa ta kuma narkewa tana ƙara mutsutstsuku ba tare da tayi Magana ba, iska Haidar ya fesar daga bakinsa domin kuwa shi sauri yake ya ƙarisa ma’aikatarsu ana jiransa.

“Baiwar Allah lafiya ki ɗan matsa gefe zan ja mota ta.”

Sai yanzu Nafeesa ta ɗago idanunta da suka kaɗa suka koma ja, na makirci.

“Cikina ka kaini gida zan mutu dan Allah ka taimake ni.”

Shuru Haidar yayi, cike da tunanin anya kuwa zai ɗauke ta rayuwa ta lalace mugaye sunyi yawa a wannan duniya, amma daga ganin yanayin shigarta cikin hijabi harda niƙaf sai yake ga kamar mutumiyar kirki ce, da wannan shawarar ta Zuciyarsa ya ce.

“Sorry sister, ni bansan gidan kuba, kuma sauri nake sai dai na tara miki adaidaita sahu ya kaiki.”

Wani ras zuciyar Nafeesa ta buga, ina bazata yadda ta rasa wannan damar ba, ƙara damƙe cikin tayi tare da ɗan ƙara tana cije leɓenta tace.

“Ashsh wayyo na shiga Uku cikina zan mutu, ka kaini gida dan Allah.”

Tayi Maganar cikin marairaicewar murya, sosai ta bawa Haidar tausayi yace.

“Okay tashi muje.”

A hankali ta miƙe Haidar na mata sannu tare da zagawa ya buɗe mata gidan gaba ta shiga sannan shima ya zago ya shiga, yaja motar, sunyi nisa da tafiya babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu, sai Nafeesa dake shagwaɓe ta jingina jikin motar sosai take lumshe idanunta jin sanyin ac da ƙamshim turarensa ya gauraye motar ya na kaɗata, sunyi nisa da tafiya Haidar yace.

“Wacce unguwa zan kaiki?”

Idanunta ta buɗe a hankali tare da ɗaga niƙaf ɗin fuskarta cikin daddaɗar muryarta domin kuwa Nafeesa macece mai daɗin murya da kuma kyawun sura duk inda ake neman kyakkyawar mace mai sura Nafeesa ta kai, tace.

“Unguwar Maitama, na gode sosai Tabbas kai Mutum ne mai tausayi dabadan kai ba da bansan ya zanyi ba a tsakiyar titi na gode, zan iya kiranka da YAYANA.

Haidar kansa na bisa titi ba tare daya kalleta ba yace.

“Meyasa kika fito baki da lafiya.”

“Lafiya ta ƙalau na fito, lokaci ɗaya ciwon cikin ya riƙeni amma yanzu ma naji da sauƙi.”

Kansa Haidar ya ɗaga bai kuma ce mata komai ba, ita kuwa sai satar kallonsa take har suka iso unguwar mai tama a bakin layin yayi parking tare da juyawa ya kalleta, ras zuciyarsa ta buga, haka kawai kansa ya kawar a Zuciyarsa ya furta “ashe kyakkyawace shiyasa ta ɓoye fuskarta cikin niƙaf, to amma meyasa zuciyata ta buga dana kalleta” numfashi ya sauƙe tare da cewa.

“Kiyi hkr ki sauƙa a nan sauri nake ana jirana a office.”

Murmushi Nafeesa tayi tace.

“Hakama nine da godiya na gode, sosai yanda ka taimakeni kaima Allah ya taimake ka, amma dan Allah idan babu damuwa ko zaka iya bani numbern wayarka saboda kai mutumin kirki ne, ma dinga gaisawa ni sunana Nafeesa kaifa?”

Numfashi Haidar ya sauƙe tare da cewa.

“Sunana Haidar.”

Yayi maganar a taƙaice yana ciro katinsa ya miƙa mata.

Fita Nafeesa tayi tana murmushi tace.

“Na gode Yaya Haidar.”

Motar sa Haidar yaja yabar wajen ba tare daya amsa ba, dariya Nafeesa tasa tare da furta.

“Bazaka taɓa kufcewa Kaidina ba, dole ne sai na moreka duk inda kuɗi yake bana taɓa barin wajen HAIDAR bazaka taɓa tsallakewa tarko na ba” katin ta kalla tana murmushi”

HAIDAR MUHAMMAD GIWA It means familyn AMBASSADOR AHMAD GIWA ne lallai jinin arziki ne” dariya tasa tare da nufar gidan su da Sallama ta shiga Mama ne kawai zaune a falon kusa da Mama ta zauna tana cewa.

“Sannu da hutawa Mama.”

“Harkin dawo nayi zaton ai sai dare zaki dawo.”

Mama tayi Maganar murmushi Nafeesa tayi tace.

“Eh yau ban juma ba, Amada hotel kawai naje nida Alhaji Atiku, kinga yau 100,000 ya min transfer ta account ɗina na kusa nayi gida da mota mama.”

Murmushi Mama tayi tana karɓar wayar ta kalli alart ɗin tace.

“Wow har dubu ɗari ya baki, gaskiya wannan alhajin akwai kyauta amma dai zaki bani koda dubu talatin ne saboda ina da matsalar kuɗi ga bikin Umaima a gaban mu, kuma dai kinsan dubu goma zan bada gudunmawa ga anko da zanyi.”

Dariya Nafeesa tayi tana kwantar da kanta jikin Mama tace.

“Kwantar da hankalinki Mama dubu hamsin zan baki domin kuwa ina da tabbacin daga yau na daina samun kyautar dubu ɗari daga ɗari biyu sai sama, amm Mama ina Nazifa?”

Dariya Mama tayi tace.

“Allah dai ya miki Albarka Nafi shiyasa nake godewa Allah daya bani ke mai taimakona ba irin Nazifa ba laka susare, komai sai na mata, ki cigaba da neman kuɗin ki Allah ya dafa miki nima na samu, tana nan cikin Kitchen.”

Dariya Nafeesa tayi tace.

“Ameen Mama shiyasa nake sonki saboda kinsan ƴan cinki, Abba ya dawo ne.”

“Bai dawo ba sai gobe Bauchi yaje ai.”

Miƙewa tsaye Nafeesa tayi tace.

“Mama na gaji bari naje nayi wanka na samu nayi bacci.”

“To shikenan aje a huta”

Shigewa Nafeesa tayi tana murmushi daidai fitowar Nazifa dake cikin Kitchen tana jiyo dukkan hirar Nafeesa da Mama zama Nazifa tayi gefen Mama ranta na haɗe ta dubi Mama tare da cewa.

“A gaskiya Mama abinda Aunty Nafeesa takeyi sam baya kan tsarin musulunci ko sunnar annabi, haba Mama taya kina raye da idanunki kina ganin Aunty Nafeesa tana abinda taga dama rayuwarta tana neman lalacewa, meyasa bazaki faɗa mata gaskiya ba ki dakatar da ita a matsayinki na Uwa, Mama haƙƙine a kanki ki kula da tarbiyyar mu, ranar gobe sai Allah ya tambayeki akan tarbiyyar yaranki, Mama Nafeesa tana yawon banza kuma kin sani amma kika biye mata saboda kawai tana ɗaukar ɗawainiyar ki, wallahi mama ina mun…”

Marin da Mama ta ɗauke Nazifa dashi shiya hanata ƙarisa maganar, wani irin haske ta gani mai ɗauke da azaba, Mama cikin ɓacin rai ta nuna Nazifa da hanu tare da cewa.

“Ni zaki gayawa tarbiyyar ku dan ubanki, Nazifa wato har ke kinyi girman da zaki min wa’azi, daga ganin ƴar uwar ki tana walwala tana samun kuɗi shine har hassada ta shiga ranki kin fara mata baƙin ciki harda mungun ƙazafi wai tana yawon banza oh ni Hajara wai yanzu a masu maka hassada harda ɗan uwanka, to bari kiji dan ubanki sai dai hassadar ki ta kasheki amma wallahi Nafeesa yanzu ta fara samun alkairi.”

Cike da mamaki Nazifa take bin Mama da kallo baki buɗe wai itace zata yiwa Aunty Nafeesa Hassada.

“Mama nine zanyiwa aunty Nafeesa hasssada, zanfi kowa farin ciki ace Aunty Nafeesa ta zamo miloniya, amma ta samu kuɗin ta hanyar halak, Mama wallahi ina mungun jin takaicin rayuwar da Aunty Nafeesa takeyi, amma tunda a matsayinki na Uwa kinga hakan shine daidai shikenan.”

Nazifa tayi Maganar tana hawaye tare da miƙewa zata bar wajen muryar Mama taji.

“Akan daidai Nafeesa take, kece dai kike hanyar rashin daidai da kike yiwa ƴar uwar ki uwa ɗaya uba ɗaya baƙin ciki, kuma wallahi daga yau kika kuma zuwa zaki min maganar banza sai na ɗaga miki nono.”

Kanta Nazifa ta kaɗa tare da shigewa Kitchen idanunta na zubar da hawaye tsuka Mama taja tana famar mita.

“Yau ni naga bala’i yarinya ubanki ya ƙuntata min ya tauye min haƙƙina sannan na haifi ƴarda zata taimakawa rayuwata ta tallafe ni shikenan sai kuma ki ɗauko hassada kisa a ciki ke baki min ba sannan kice itama bazata min ba, wallahi ƙarya kike wannan kuma baki isa ba, sai na iya tsine miki Albarka akan Nafeesa.”

Tana mitar tare da shigewa Bedroom ɗinta.

Washe Gari Da Safe

Yau tun tara na safe Faruq ya gama shirye-shiryen sa, tunda Daddy ya sanar dashi cewa 10 am jirgin su zai tashi sam baya son yayi late ɗin time, a kintse Faruq ya fito main falon nasu da ke ƙawace da adon white and pink sosai falon yayi kyau harya so ya zarce falon su Al’ameen kyau, AUNTY ce hakimce a falo fuskarta ɗaure tamau sai famar zazzagawa Atine ƴar aikinsu masifa take kasancewar ta mace mai faɗa, numfashi Faruq ya sauƙe yana tsaye bakin step ɗin falon ya riƙe kunkumi, kansa ya Girgiza tare da furta.
“Oh AUNTY faɗa.”

Yayi maganar yana takowa inda take zaune, gefe ya zauna tare da duban Atine dake duƙe kanta a ƙasa sai bawa Aunty haƙuri take, a hankali ya furta.

“Sorry Aunty ayi hakuri Atine tuba take bazata kuma ba.”

Yayi Maganar yana kallon ƙwayar idanun Mahaifiyar tasa, Aunty hararar sa tayi cikin faɗa tace.

“Naƙi nayi haƙurin uban ƴan kanzagi wato ka ari bakinta ka ci mata albasa!!! Kai ga ɗan ɗaurewa ƙarya gindi.”

Murmushi Faruq yayi har sai da haƙwaransa suka bayyana kasancewar sa mutum wanda bai cika fushi ba, ga wasa da kuma barkwanci, yace.

“Haba dai Auntyna aiko ban ciwa Atine albasa ba, kina kallonta zaki fuskanci nadama a cikin su, kinga Aunty kawai ki yafe mata karki ɗauko wancan tsoho mai balum wanda sam baya…”

Bakinsa Aunty ta bige tana murmushi tace.

“Kaci gidan ku wato shi Baban nawa ne tsoho mai balum, malam kam zakaje ka samesa zaiyi maganinka.”

Dariya yayi tare da cewa Atine.

“Tashi kije abunki Atine ki kiyaye gaba, babu daɗi ɗan Adam ya fiye kuskure cikin rayuwarsa zai tashi daga kuskure idan yayi yawa ya dawo ganganci, ki kiyaye naga alamar kina yawan samun matsala da Aunty.”

Tashi Atine tayi cike da ƙaunar Faruq domin kuwa mutum ne shi mai yawan afuwa da yafiya a duk sanda mahaifiyarsu take musu masifa muddun yana wajen sai ya san yadda yayi ya dakatar da ita.

“Insha Allah zan kiyaye Faruq na gode Allah ya kaiku lafiya.”

Da ameen ya amsa yana cewa Aunty.

“Wai ina Rufaida da Ahmad ne, jiya na nemesu bamu haɗu ba?”

“Ahmad yau tun 9 ya tafi school ya leƙa Bedroom ɗinka baka tashi ba, yace min zakuyi waya Rufaida kuma tana Kitchen tana haɗa breakfast, kunyi waya da Papan ku ne?”

“Munyi waya jiya da daddare, yama ce jibi zai shigo AMERICAN ɗin zamu haɗu.”

“Okay daga India kenan can America zai shige Allah ya kaimu, Faruq baka buƙatar na maka faɗa amma dai ka zamo mutum mai hakuri a duk inda ka kasance karka yadda koda mutum ɗaya a cikin rayuwarka ya kiraka azzalumi, ka kasance mutumin da kullum ake masa kyakkyawan shaida, Su Al’ameen zasuyi kewarka.”

Murmushi Faruq yayi tare da cewa.

“Insha Allah Aunty bazan taɓa zaluntar al’ummar Annabi ba, Aunty ni kaina bana jin daɗin rabuwar da zanyi dasu harna tsawon shekara guda, sai dai babu yanda na iya dole na hakuri naje amma zan kasance cikin kewarsu har Allah ya dawo dani mussaman Haidar sai nafi kewarsa.

“To ya aka iya haka rayuwa take dole a rabu ko mutuwa ko wata sanadiyyar Allah dai yasa mu dace.”

Aunty tayi maganar tana danna remote ta kunna tv tashar aljazira, Rufaida ce ta fito daga Kitchen Faruq ta nufo tana dariya tace.
“Ya Faruq kar dai ace harka fito.”

Murmushi yayi yana duban ƙanwar tasa cike da ƙauna yace.

“Eh na fito zanje part ɗin Ummi muyi breakfast sai nazo nayiwa Aunty Sallama.”

“Ya Faruq dan Allah duk sanda ka tashi dawowa daga America ka sayo min redmet ɗin Jeans da shirt, kasan nasu latest ne dan Allah yaya Faruq karka manta.”

Murmushi Faruq yayi tare da miƙewa tsaye yace,

“Karki damu sweet sister insha Allah bazan manta ba, koda kuwa na manta da saƙon Ahmad, ni bara naje wajen Inna Jumma.’

“AL’AMEEN wai kai meyasa a rayuwarka ka fiye taurin kaine sau nawa nake faɗa maka ka saurarawa yarinyar nan tayi rayuwar ƴanci, ka takura mata ka hanata sukuni a gidan ubanta sai kace ba ƴar uwar ka ba, ko uwa bata haɗa ku ba, uba dai ya haɗa ku, ran mahaifiyarta bazaiyi daɗi ba akan abinda kake yiwa ƴarta, Afnan dai ƴar uwar ka ne ya kamata ka dinga tunawa da hakan.”

Duk faɗan da Mahaifiyarsa Ummi take tamkar zata dokeshi Al’ameen kansa na ƙasa ya nutsu cike da biyayya yana sauraronta sai da tayi shiru sannan ya fara magana cikin nutsuwa.

“Ummina nifa ba tsanar Afnan nayi ba, kinfi kowa sanin rashin jituwa ta, da ita akan wannan yaron Salisu, ba yaron kirki bane, nayi nayi ta rabu dashi Ummi taƙi, har ta tsaya a gabana wai Afnan tana faɗa min cewa, ita Salisu take so ko zan kasheta bazata rabu dashi ba, ita na takurawa rayuwarta, shiyasa Ummi na yanke alaƙa tsakanina da ita kowa yaje yayi abinda ya damesa.”

Numfashi Ummi taja tare da sassauto da muryar ta tace.

“Wannan hukuncin daka yanke a kanta sam ba dai-dai bane, a matsayin ka na babba bai kamata kayi fushi haka ba, ka mata yayi ka yanke mata hukunci a tsakaninka na babban wanta, yanzu da wani zai shigo cikin gidan nan yaga yanda kake kyarar Afnan wallahi cewa za’ayi saboda ba uwarku ɗaya bane kana taya uwarka kishi, ni kuma da ason raina ne wallahi Al’ameen babu mai banbance tsakanin ku, dan Allah ka tsayar da wannan ƙiyayyar haka muddun baka ƙaunar ganin fushi na.”

“shikenan Ummi na bari kiyi hkr insha Allah bazan sake ba, Allah ya huci Zuciyarki ummina.”

Murmushi Ummi ta saki tare da shafa kan Al’ameen tace.

“Alhamdulillah!!! Ya wuce tunda ka amsa laifinka Allah ya maka Albarka, nikam yau banga HAIDAR ba tun safe.”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Ummi kinsan halin HAIDAR da son aiki tamkar agogo yanzu haka nasan yana office, yanzu zanje na samesa bari ma naje wajen wannan sarkin mitar na gaisheta.”

Ɗan murmushi Ummi tayi tana zungurin kansa tace.

“Kaji ɗan rainin wayo, wato Inna Jumma ne sarkin mitar, zakaje ka sameta ai tana dai-dai dakai.”

Al’ameen yana murmushi ya miƙe yana ƙoƙarin fita yace.

“Ko kuma ni ina dai-dai da ita ba.”

Ya ƙarisa Maganar yana ficewa dariya Ummi tayi tare da cewa.

“Ai kuwa zaka haɗu da Inna Jumma.”

Amarya ce zaune cikin falon ita da Maimu sai famar hira suke suna dariya Al’ameen cike da girmamawa ya zo ya zauna gefen hanun kujerar da Amarya kishiyar UMMIN sa ke zaune fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

“Amarya yau banji gidan nan yana tashin ƙamshi ba, ko dai ba’ayi breakfast ɗin dani bane?”

Murmushi Amarya tayi tare da masa nuni da daining table da yatsanta, kallonsa Al’ameen ya kai wajen HAIDAR ne zaune sai kwasar breakfast yake hankali kwance, amarya na dariya tace.

“Ga can wanda ya fika so yana cinye rabonka, tunda kai sarkin let ne.”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Amarya, sai naji daɗi da yau naga Haidar yana zaune yana cin abinci cikin nutsuwa, rabona da naga Haidar yana breakfast akan lokaci harna manta lokacin, kullum cikin aiki yake baya breakfast har sai rana ta ɗaga nan ba nutse ba, yafi bada lokacinsa ga business ɗinmu, sai nake ji tamkar nine nake cin wannan abincin koda zan wuni yau banci komai ba bazanji damuwa domin Haidar ya ƙoshi, hmmm!!! Amarya HAIDAR mutum ne mai tsananin bawa lokaci mahimmancin sa.”

Ya ƙarisa Maganar fuskarsa ɗauke da murmushi, Maimu ma da kallo tabi Haidar tana sakin murmushi tace.

“Yaya Al’ameen *AMINTARKU* tana matuƙar burgeni kuna ƙaunar junanku, kun yarda da junanku komai naku tare kuke yi ba ku taɓa faɗa ko cacar baki ba, tausayin junanku da ƙauna shine kawai a zuciyarku babu ƙyashi ko hassada a tsakanin ku, da ace dukkan wasu abokai haka suke da tabbas izuwa yanzu babu ƙyashi ko Hassada a duniya, Ya Al’ameen, ya kamata kaima kaje ka samu kayi breakfast, dan Daddy ya kusa fitowa, jirgin 10 zasu bi.”

“Ai kin sani bazan iya breakfast Wannan lokacin ba just 9:40am fa, sai after 11 barshi shi dai yayi, amm Amarya were is your Minal?”

“Minal bata tashi daga bacci ba, kasanta da bacci tamkar kai.”

Tayi Maganar tana murmushi, shima murmushi Al’ameen yayi tare da nufar daining wajen Haidar, kujera ya jawo ya zauna tare da cewa.

“Wai malam da yunwa ka kwana ne kake cin abinci sassafe.?”

Murmushi Haidar yayi tare da ɗago kansa yace.

“Sai mutum ya kwana da yunwa sannan zaici abinci da safe, hmmm!!! Kasan ni bani da wani time na cin abinci duk sanda na samu lokaci muddun ina jin yunwa zanci, bama wannan ba Al’ameen jiya kace min zaka shigo Company, ban kuma ganka ba, daga kai har faruq, wai meyasa kuke nuna ko oho ne akan wannan Company, kuna bani matsala wallahi.”

Ɗan dariya Al’ameen yayi yana saka hanunsa ya ɗauki cup ɗin dake cike da ruwa a gaban Haidar ya kurɓa tare da cewa.

“Wasu sabgogin ne suka ɗebeni, shine fa naja faruq muka je, sannan ai duk abinda zamuyi kaima ka wadatar kayi sa.”

“To yanzu dai ya Maganar waken nan a ina kake tunanin zamu samu, Egypt sun matsa suna buƙatar wake sannan su Tailan ɗin sun kira suna buƙatar wake amma sunyi mana sara da ƙwaƙƙwafa akan a kawo musu ingantacce.”

Shuru Al’ameen yayi kafin yace.

“Bazamu kaiwa Tailan wake ba.”

Ajiye spone ɗin dake hanunsa Haidar yayi cike da mamaki yace.

“Whattt!!! Bazamu kaiwa Tailan wake ba, akan me to?”

“Saboda sun raina mana hankali sun barmu da asara wanda a harkar kasuwanci, asara ya kamata mu raba dasu, bamu taɓa kai musu wake mai magani ba sai wancan karon maimakon su karɓa su nemi mu rage musu farashin tunda ai zai ciwo ba guba bane, amma suka saka muka juyo Nigeria dashi kafin mu dawo a airport ruwan sama yazo ya taɓa wannan waken ya lalatasa, gaba ɗaya ya ɓaci mukayi asara to akan me zamu kaiwa mutanen da basu da kara kayan mu.”

Tsuka Haidar yaja tare da ɗago kansa ya kalli Al’ameen.

“Ba haka ake kasuwanci da fushi ko zuciya ba Al’ameen, dole ne mai kasuwanci yana buƙatar haƙuri, amma kai sam baka da haƙuri, kasa zuciya a gaba kai sai kace da zarar an samu matsala da mutum baza’a nemi sulhu ayi gyara ba, sai dai kawai a rabu, karfa ka manta Tailan ba ƙananan ciniki suke mana ba, babu ta yadda za’ayi ace mu rabu dasu bazai yiwu ba.”

“Why bazamu rabu dasu ba Haidar?”

Haidar ba tare da ya kalli Al’ameen ba yace.

“Ka kyaleni naci abinci na dan Allah.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da zaro wayarsa, suna nan zaune Faruq ya shigo yana ƙwalawa Inna jumma kira, Al’ameen kansa ya ɗaga yana kallon Faruq tare da girgiza kansa ya furta.

“Faruq drama, Haidar zanyi kewar faruq da ina da iko bazan bari Daddy ya tafi dashi.”

“HMMM!!!! Ni kaina banso wannan tafiyar tasa ba, sai dai babu yanda muka iya fafa da Daddy sun yanke hukunci”

Muryar Inna Jumma sukaji tana fitowa daga room ɗin ta.

“Wani ja’irin ke kwaɗamin kira, tamkar yana bina bashi.”

Idanunta ne ya sauƙa akan Faruq dake tsaye ya harɗe hanunsa a ƙirji yana kallon ta.

“Oh ai dama na sani babu me min wannan iya shegen idan ba kai ba faruƙu, to me kuma ka zuba min ido tamkar zaka cinye ni, to aniya bi aniya kurwata kur tafi ƙarfin ka.”
Dariya Faruq yasa tare da nufo Inna Jumma ya saka hanu ya dafa kafaɗar Inna Jumma tare da kashe mata ido ɗaya yace.

“Meye kuma faruƙu sunan ko daɗin faɗa babu, kinga Hajiya Inna Jumma, ya kamata ki fara koyon kirana da Faruq domin yafi daɗin faɗi a baki, kai tsohuwar nan, ni kuwa me zaisa na tsotsi wannan ƙashin naki mai ɗacin tsiya, kinga rabu da wannan zancen ma, kina sane da yau zan tafi American da Daddy kuwa.?”

Ranƙwashin sa Inna Jumma tayi tare da cewa.

“Na sani faruƙu da tun farko Amadu ya sanar dani cewa dakai ya shirya wannan tafiyar bazan bari ba, Saboda zamuyi kewarka faruƙu ƴan uwanka ma bazasu ji daɗi ba, sun amince ne kawai badan ransu yana so ba sai dan babu yadda suka iya ne, muje wajen ƴan uwan naka.”

Tayi Maganar tana jan hanun faruq suka nufi daining, Al’ameen murmushi yayi tare da jawo kujera yace.

“Ran Hajiya Jumma ya daɗe uwar gidan Alh Adamu Giwa kuma amarya.”

Ya zolayeta cike da tsokana fuskarsa ɗauke da murmushi,zama Inna Jumma tayi tana ranƙwashin Haidar tace.

“Aminu duba kaga yanda wannan Alin ke kwasar abinci tamkar mayunwaci sai kai loma kake babu sassautawa, anya kuwa jiya kaci abinci?”

Murmushi Al’ameen yayi tare da kallon Haidar dake cin abincinsa koya kalli Inna Jumma cewa Al’ameen yayi.

“In banda ke tsohuwar nan gaki ga Haidar ɗin sai kin tambayeni gashi ya baki amsa.”

“Kaima ka kulata Al’ameen, kaf gidan nan akwai wanda ma ya kaiki ci ne wama ya sani ko ke na gado a cin abincin.”

Kafin Inna Jumma ta bashi amsa Daddy da Ummi suka sauƙo a falo Daddy ya zauna shida Momy su Haidar tashi sukayi har Inna Jumma suka nufo cikin falon suka zauna Daddy har ƙasa ya sunkuya ya gaishe da mahaifiyarsa, Momy ne da Abi suka shigo iyayen Haidar, falon gaba ɗaya kacamewa yayi da surutu, ba’a juma ba Aunty da Rufaida suma suka shigo Rufaida na janye da akwatin Faruq, Inna Jumma ce tayi gyaran murya kowa shuru yayi falon ya nutsu tamkar ba kowa a cikin sa Daddy ta duba sannan ta fara magana.

“Aminu jiya Hajiya maimuna take sanar dani cewa tare da Faruqu zaka tafi, zaije ya tayaka aiki harna tsawon shekara ɗaya wanda Ni baka sanar dani hakan ba, da ka sanar dani Aminu bazan barka ka raba Faruqu da ƴan uwansa ba saboda sun shaƙu, basu kuma taɓa rabuwa da junansu ba, sai yanzu rana tsaka zaka rabasu meyasa kayi haka.?”

Nisawa Daddy yayi tare da gyara zamansa yace.

“Inna nasan ko na faɗa miki ba zaki barni na tafi dashi ba, kuma dole ina buƙatar matashi mai jini a jiki a cikin aikina saboda ni tsufa ya fara cimin ina buƙatar magajin da zai gajeni ta fuskar siyasa, bana son nabar wannan gomnatin ba tare da nabar magaji ba, dalilin ds yasa zan ɗauki Faruq naje na nuna masa yadda muke harkokin mu, Al’ameen da Haidar bazasu iya siyasa ba shiyasa ban ɗauki ɗaya a cikin su, Faruq ya fisu iya mu’amala da jama’a da kuma sakewar fuska wanda wadannan ɗabiun shine ɗabi’un ƴan siyasa, Inna ina ji a jiki na muddun faruq ya iya siyasa zai zamo babban ƙusa a gomnati , dalilin kenan da yasa nake son tafiya dashi, Kuma Inna ai rabuwa tsakanin su wannan dole ne koda tafiya bai rabasu ba akwai mutuwa Inna dole ne ana tare wata rana za’a rabu.”

Duk da Inna Jumma taji daɗin zancen Daddy akan Faruq domin kuwa niyarsa mai kyau ne akan sa sam bashi da mugunta da ace son kai zaiyi Al’ameen zai ɗauka ba faruq ba, amma sai Inna Jumma tace.

“Wannan ba hujja bace da zaka rabasa da ƴan uwansa, ina jin dadin yanda nake ganin kan jikokina a haɗe sam bana son abinda zai taɓa rayuwarsu, domin kuwa da wani abu na ɓacin rai ya samesu na gwammaci ni ya sameni, Kafin yanke hukuncin tafiya dashi ya kamata ka tuntuɓesa kaji meye ra’ayinsa shin yana da burin siyasa, domin kuwa yana da ƴancin da zai zaɓawa rayuwarsa abinda ya dace dashi siyasa ana shigarsa ne da zuciya da kuma ra’ayin mutum ba wai ra’ayin wani ba, a yanzu ka yanke hukunci akansa kuma kun gama shirya tafiyarku bazan dakatar daku ba, ina fatan alheri da samun cikakkiyar nasara, amma ina son Idan kunje ka tattauna dashi akan ra’ayinsa kafin ku fara aikin hakan yana da kyau ka bawa mutum damarsa.”

Murmushi Daddy yayi cike da jin daɗi domin kuwa yayi zaton Inna Jumma zata hanasa tafiyar ne da Faruq cike da ladabi yace.

“Insha Allah zan fara magana dashi kafin aiwatar da komai naji daɗi da kika bani wannan damar baki hanani tafiya dashi, insha Allah Inna zakiyi alfahari da siyasar Faruq, ina jin a jikina wata rana zai zamo babba a wannan ƙasar.”

Kafin Inna Jumma tayi Magana Al’ameen cike murmushi ba tare da ƙyashi ko nuna Hassada ba, ya miƙe tsaye tare da dawowa kusa da Inna Jumma ya zauna yana dafa kafaɗar ta kamar dai yadda ya saba Magana cikin iko da taƙama ya kalli Daddy tare da cewa.

“Daddy waya faɗa maka Inna Jumma ce kawai zatayi alfahari da kasancewar ɗan uwanmu cikin siyasa, gaba ɗaya wannan ƙasar sai tayi alfahari dashi, zuciyamu ɗaya idan ɗayan mu yana son abu haka take a zuciyar ɗaya shima zaiso, muna son Wannan siyasar nasan kuma shima Faruq yana so, zai kuma yi Nasara da yaddar Ubangiji sai ya zamo tamkar kai kuma ina da tabbacin cewa al’ummar wannan jihar zata karɓi jinin *AHMAD GIWA* bazasu butulcewa alkairan daka musu ba”

Haidar shima murmushi ya yi ya miƙe ya zauna a ɗayan gefen Inna Jumma suka sanyata a tsakiya tare da cewa.

“Kayi gaskiya Daddy Faruq ya fimu da abubuwa masu yawa MUSSAMAN ta fuskar Al’umma mutum ne mai son jama’a da ganin ya kyautata musu taimako kuma wannan a jininsa yake, tabbas ya fimu wasa da dariya da kuma mu’amala da mutane wannan halin shi ake so a samu daga zakwaƙurin ɗan siyasa, sai dai Daddy ga wata tambayar da nake bukatar amsar su?”

Ya ƙarisa Maganar yana murmushi, Faruq duk da kallo yabi ƴan uwansa domin kuwa yana jin daɗin yadda suke yawan ƙarfafa masa gwiwwa, kullum cikin son cigaban sa suke, duk da bayi da ra’ayin siyasa, sai dai bazai bawa Maganar ƴan uwansa kuma *AMINANSA* kunya ba dole zai karɓi wannan al’amari da zuciyarsu maimaita kalmar Al’ameen yayi a zuciyarsa ” zuciyar mu ɗaya ce idan ɗayan mu yana son abu to haka take a zuciyar ɗaya shima zaiso muna son wannan siyasar nasan kuma shima Faruq zaiso” numfashi ya sauƙe yana jin Soyayyar ƴan uwansa har cikin ransa zai iya komai domin kare rayuwarsu ciki harda bada rayuwarsa, muryar Daddy yaji yana cewa.

“Ina jikinka Haidar yi tambayarka ni kuwa zan amsa maka.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Hausawa suna cewa da rarrafe akan tashi har a fara tafiya, amma kai sai naga kamar so kake Faruq ya Fara da gudu, a Nigeria Faruq ya kamata ya zauna ya koyi siyasar sa amma kai kuma kana shirin kaisa American ko meyasa Daddy.”

Numfashi Daddy ya sauƙe tare da yin murmushi na manya tare da cewa.

“A harkar siyasa ba’a taɓa tashi da rarrafe domin kuwa kace da rarrafe zaka tashi to fa zaka daɗe baka fara koda tsayuwa bane bare kuma tafiya, ita siyasa tana buƙatar Babban ubangida ne wanda zai maka jagora ya tsayar dakai ga al’umma wanda nasararka zata fara ne da ga wannan ubangidan, kamar dai yadda nake son ɗaga Faruq yayi gudu bama tafiya ba, bima’ana ina son na fara gabatar da Faruq ga shugaban kasar American Jolieurs Abom Wanda yake shaƙiƙi ga shugaban kasar Nigeriya Olusegun Asom Faruq zai zauna tare da Jolieurs Abom na wannan shekara ɗayan domin shaƙuwa dashi ta hakan zamu fara gabatar da son shigar dashi siyasa bisa samun babban kujerar ministan Jiha daga nan nida Jolieurs sai mu tunkari Olusegun da wannan buƙatar wanda hakan bazai bamu matsala ba wajen samun cikakkiyar nasara yanzu ka fahimci ni.”

Aunty ne tayi murmushi tare jin daɗin yadda kowa a wajen ke buƙatar cigaban ɗanta ba tare da Hassada ba Haidar dariya yayi tare da duban agogon hanunsa ya ce.

“Yes Daddy na fahimta, time is over.”

Ɗan dariya Daddy yayi tare da miƙewa yana miƙawa ɗan uwansa hanu Abi hanu tare da cewa.

“Ka kula da Al’ameen da Haidar kasa ido sosai a kansu, kaine ubansu mai kula da lamuransu a yanzu nida Alh Kabeer ba mazauna ƙasar nan bane kaine kake cikin ƙasar KULLUM haƙƙin kula dasu ya rataya ne a wuyan ka, zamu iya tafiya.”

Gabaki ɗayan su miƙewa sukayi, kowa na rungumar Faruq cike da Soyayya sukayi sallama, Abi Haidar Al’ameen, sai Rufaida Da Sai Maimu sune suka rakasu har airport, sun juma zaune kafin jirgin ya tashi, sosai sukayi alhinin rabuwa da Faruq jikinsu duk a sanyaye, Suna tsaye har jirgin su Faruq ya tashi, kasancewar mota biyu suka fito da ita yasa Abi cewa Al’ameen yazo ya jasa zuwa unguwa, shi kuma Haidar ya maida su Rufaida gida.

Haidar yazo zai buɗe motar sa ya shige idanunsa suka sauƙa a kanta tana tsaye sanye da dogon hijabi, fuskarta cike da murmushi bakinta taji jan janbaki suna tsaye da wata budurwa wacce bazata wuce shekarunta ba, da kallo Haidar ya bita tare da furta.
” Me kuma ya kawota nan, idanunsa ya lumshe tare da kuma cewa kyakkyawa ce, tana da kyan kallo, kowa ta rako?”

Ya furta yana murmushi tare da shigewa cikin motar yaja, yana binta da kallo, yana jin wani abu a zuciyarsa game da ita, Rufaida lura da wajen da Haidar yake kallo ya sata duban wajen, Nafeesa ta sunkuya sai ƙawarta kawai ta hango a zaton ta ƙawar Nafeesa yake kallo, cike da haushi da kuma kishi kasancewar Rufaida ta juma tana son ɗan uwanna ta wanda shi kwatakwata ya gagara gane hakan, kafaɗarsa ta dafa tare da cewa.

“Mister Love, ja muje ko kuma na fita na maka Magana da ita.”

Juyowa Haidar yayi ya kalli Rufaida yana dariya tare da jan motar yace.

“Kai dai Yarinyar baki da kunya ina matsayin yayanki kike kira na da Mister Love ko,

Yarinyar tana da kyau ya kika ganta ta dace da zama cikin FAMILY mu ko.?”

Kawar da kanta gefe Rufaida tayi tana jin wani baƙin ciki na taso mata, a hankali tayi murmushin yaƙe tare da cewa.

“Ni ban ganta ba, na dai hango bayanta amma banga fuskarta ba.”

Girgiza kanta Maimu tayi tana sakin murmushi tace.

“Yaya Haidar ai ita mace ba kyawunta ake dubawa ba ɗabiun ta sune abin duba nasabar ta da addinin ta, idan har tana da waɗannan to ta dace da zama cikin zuri’ar mu.”

Murmushi Haidar yayi yana harbawa titi yace.

“Bansan komai a kanta ba amma dai naji zuciyata na sonta, zan gwada auna matsayin addinin ta da kuma tarbiyyar ta.”

Runtse idanunta Rufaida tayi ranta na mata ƙuna harta ƙagu su sauƙa domin kuwa zuciyarta bazata jure jin wannan zancen nasu ba.

Ita kuwa Nafeesa dariya tasa bayan sun shiga cikin motar Amnat, hijabin ta cire take ɗamammun kayan dake jikinta suka bayyana rigar jikinta ta kamata tamkar ƙirjinta zai tsage rabin nonon ta duk a waje, siket ɗin jikinta ma a ɗame yake tamkar bom ɗinta zai tsage, kallon Amnat tayi tare da cewa.

“Da alamu dai bai manta dani ba a yanayin yadda yake bina da kallo, naso ace yazo ya samemu amma tsabar MISKILANCI ya share yayi tafiyar sa, ina da buri na samun manyan kuɗaɗe fa a wajen wannan gaye ɗin, amma da alamu bana gabansa, sai dai fa dole ne sai na juyo da hankalin sa gareni dole na shiga zuciyarsa domin kuwa ina buƙatar cikar burina.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita? 1Aminaina Ko Ita? 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×