Skip to content
Part 25 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Da misalin sha ɗaya da rabi na rana wayar Inna Jumma tayi ringin hanu tasa ta ɗaga tare da karawa a kunnenta tana Sallama daga can Hafsa ta amsa da.

“Wa’alaiku mussalam, sannu Inna, sunana Hafsa daga gidan su ABLAH nake Umma ne ta bani wannan numbern tace idan nazo na kira saboda security sun hanani shigowa.”

Murmushi Inna Jumma ta saki tare da cewa.

“Ayya to bara na turo Ablah sai ku shigo da ita.”

Da to ta amsa ta katse kiran, Inna Jumma Ablah ta kwaɗawa kira jin shuru ya sa ta tashi ta leƙa bedroom ɗin Ablah tana zaune tsakiyar gado tayi shuru da alamu tana cikin tunani ne, ƙarasawa Inna Jumma tayi tare da dafa ta.

Ɗago idanunta tayi ta dubi Inna Jumma tare da sakin numfashi tace.

“Inna Jumma yaushe kika shigo ban ganki ba.”?

“Yanzu na shigo tunanin me kike haka har bakya jin shigowar mutum kusa dake.?”

“A’a Inna kawai tunanin school ne.”

Tayiwa Inna Jumma ƙarya domin kuwa gaskiyar zuciyarta tunanin lamarin da zata ɓullowa Aunty Amarya takeyi domin kuwa a wannan karon taci alwashin lallai sai ta ƙalubalanci Aunty Amarya duk da bata da powar a cikin gidan amma dole tayi fito na fito da ita, Inna Jumma ce tace.

“Kije can first get akwai baƙuwa tazo wajenki ki shigo da ita security sun hanata shiga wai sunanta Hafsa.”

Cike da murna Ablah ta sauƙo daga bed ɗin tana dariya tace.

“Inna Jumma da gaske Hafsa ce tazo gidan nan?”

“Au zan miki ƙarya ne ja’ira”

Dariya Ablah tasa tare da miƙewa tana fita da gudu tace.

“Ni dai bance ba Inna Jumma.”

Kanta Inna Jumma ta girgiza tana murmushi domin kuwa Allah ya ɗaura mata ƙaunar Yarinyar ji take tamkar jininta ne.

Ablah First get ɗin ta nufa tare da tsayuwa tana duban security tace.

“Baba Audu sannu da aiki, amm nace akwai baƙuwa a waje Inna Jumma tace na shigo da ita.”

Murmushi Audu yayi tare da cewa.

“Aiki alhamdulillah! Ablah kije ki shigo da ita.”

Fita Ablah tayi tana dariya a tsaye taga Hafsa dariya tasa tare da rungumeta itama hafsan dariyar take cike da farin cikin ganin aminiyar tata suka shige cikin gidan.

Darect bedroom ɗin Ablah suka shiga a bakin gado Hafsa ta zauna tana ƙarewa room ɗin kallo, sosai ya burgeta.

“Ablah wannan ɗin ɗakin waye ne?”

Murmushi Ablah tasa tare da cewa.

“Shine bedroom ɗin da suka bani na zauna ma’ana dai nawa ne.”

Masha Allah, gaskiya ɗakin yayi kyau sosai tamkar na matar Aure to ya bayan rabuwa ƙawata?”

“Ai ke dai Hafsa wallahi baki da kirki, sai kace ba AMINIYATA ba, tunfa dana zo gidan ban kuma kallonki ba, ko a waya baki kirani ba, saboda ba kawai rashin mutunci.”

“To ƴar rainin wayo faɗi na wani naki yana ragaya, ke ai kin nemeni ko,gara ma ni kullum wajen Ummi nake wuni.”

Dariya Ablah tasa tace.

“Sarkin kare kai, to ai ni ɗin ma naje gidan ku ranar da naje wajen Umma, Mama tace bakya nan.”

“Ta sanar dani, yanzu dai ya hkr Umma ke sanar dani matar gidan ta rasu, shine nazo na muku ta’aziyya.”

“Hmmm ƙawata ke dai bari ta rasu ko an kasheta Umma bata sanar dake abinda yake faruwa a cikin gidan nan ba?”

Numfasawa Hafsa tayi tare da gyara zamanta tace.

“Ta fara sanar dani ɗazu amma dai bamu gama maganar ba, mai adaidaitan da zai kawoni yazo, amma wai da gaske ne Amaryar gidan itace take kisan nan, abunne da mamaki.?”

“Hafsa itace da gaske take wannan kisan, ni kaina sanda na fuskanci haka na gane abun yayi matuƙar gigitani harfa zaɓi ta bani tana iƙirarin nima zata kawo karshena.”

“Umma ta sanar dani komai har barazanar da ta miki, amma ni abinda yake ɗaure min kai menene dalilinta na wannan kisan?”

Numfashi Ablah tayi tare da cewa.

“Ni kaina abinda nake son na sani kenan meyasa take kisan na kasa fahimta har tambayarta nayi amma ta ƙi sanar dani, na rasa meye mafita domin kuwa a yanda na fahimce ta, ran kowa take so a cikin gidan nan har shi kansa mai gidan yana cikin target ɗinta, zama cikin wannan gidan akwai mungun haɗari Hafsa naso na gudu gida domin kuwa bazan iya rayuwa cikin su ba, amma Umma ta dakatar dani saboda kawai Inna Jumma da Al’ameen sun taimaki rayuwar mu ta kasa gane cewa ina cikin haɗari domin kuwa matar nan tunda ta gane cewa nasan komai a kanta ta ɗaura min karan tsana, ina tsoron karta cutar da rayuwata a karon banza.”

“hmmm! Ƙawata nima ina bayan Umma domin kuwa bai kamata ki guje musu ba, Saboda masifa ta samesu, Ablah ki sani sufa suka taimaki rayuwar ki dana mahaifiyarki suka cire mata tsoro da fargar yadda zata kula da rayuwarku, suka hanata aikin ƙarfi Saboda tausayinta, a ƙarshe ma dai suka cikawa umma burinta na karatunki domin kuwa Umma bata da wani buri a duniya daya wuce taganki kina karatun likita, yanzu abinci a gidan ku baya ƙarewa ake kai wani Allah Sarki Umma mai fafatukar yadda zata ciyar daku yanzu itama har kyautar abinci take, to meyasa bazata so ki taimaki waɗannan mutanen da suka mata hallaci ba a rayuwa, kin sani Umma bata taɓa manta alkairi komai ƙanƙantarsa, dan haka dolene a gareki ki kare rayukansu daga salwanta.”

Numfashi Ablah ta saki tunda Hafsa ta fara Maganar ta zuba mata idanu harta kawo ƙarshe.

“Na sani sun mana inuwar da bazamu taɓa iya saka musu ba, amma kun kasa fahimta ta ne Hafsa na faɗa miki cewa matar nan tana da matuƙar haɗari munguwace bata tsoron Allah, mage ce mai kwanciyar ɗaukar rai, amma idan harma zan taimaka musu ta ina zan fara kina gani fa Hafsa a Ranar da zata kashe Ummi ta sanar dani ta kuma ce idan na isa na dakatar da ita, na gagara dakatar da ita har sai da ta cimma mummunan manufarta, abun haushi da takaici nine na ɗauki gubar na bata da hanuna ban sani ba, to ta yaya kuke tunanin ni zan iya dakatar da wannan munguwar da ta fini wayo?”

“Ablah dama dole a zaki fuskanci hadari domin kuwa babu wanda zaiyi ƙoƙarin ceton ran wani ba tare daya fuskanci ƙalubale ba, ciki ma harda sadaukar da Rayuwarki domin kuwa a domin ceton Rayuwar wani dole sai ka bada taka cikin uku ko kayi Nasara Kuma ka tsira da rayuwarka ko kayi Nasara ka rasa rayuwarka ko kuma kayi rashin Nasara, babu yadda za’ace ki ƙalubalanci azzaluma kamar amarya ace baki ci karo da matsaloli ba, to ya zamo wajibi gareki ki cire tsoronta a zuciyarki ki nuna mata cewa bakya shakkarta sannan zaki iya tona mata asiri ta hanyar da batayi tsammani ba muddun kika bayyana mata haka kuma taga rashin tsoro a idanunki to fa Tabbas zata fara shakkarki ta fara bin hanyar zaluncinta cikin tsoro da fargaba kinga kenan kin saka mata tsoro a cikin zuciyarta dole ne ta fara kaffa-kaffa dake, yanzu ma rauninki da tsoronki take hangowa a tare dake yasa take miki barazana, matsoraci baya taɓa cin Nasara ABLAH domin kuwa tsoro na karya zuciya da zarar kuma zuciyarki ta karaya to fa komai yana iya ɓaci a domin ceton Rayuwar su dole ne ki saka a ranki komai yana iya faruwa dake domin kuwa kin dinga fuskantar ƙalubale kenan.”

 “Hmmm! Hafsa na fahimceki kin Kuma bani ƙarfin gwiwwa domin kuwa ina tabbatar miki da cewa zan ɗaura ɗamarar ɗamban yaƙi da Amarya sai dai kuma ina buƙatar taimakon ki koda da wasu shawarwarin ne, domin kuwa samun mai bani ƙarfin gwiwwa akan wannan lamarin yana da matuƙar mahimmanci, sai kuma gashi babu waya a hanuna wanda zan dinga waya dake domin kuwa idan nace zan dinga amsar wayar Inna Jumma muna waya bazai yiwu ba domin kuwa muna buƙatar sirri, mtsss bansan inda zan samu waya ba, amma ban sani ba ko zaki iya taimaka min domin bana ƙaunar na saka rayuwarki cikin haɗari.”

Numfashi Hafsa ta saki tare da sakin murmushi tana kama hanun Ablah tace.

“Ƙawata zan taimaka miki, ta ko wacce hanya kama daga shawara har zuwa wasu abubuwan, na yarda na saka rayuwata cikin haɗari koda kuwa mutuwa zanyi muddun zamu ceto rayukan waɗannan bayin Allah, waya kuma zan baki tawa sim card biyu ne a ciki duka mtn ne, zan ɗauki wanda nafi amfani dashi na bar miki wanda ba’a sanni dashi sosai ba, ni zan saka layina a wayar Mama sai mu dinga waya ta nan, insha Allah komai zai tafi dai-dai.”

Wani irin daɗi Ablah taji a ranta tare da ƙara jin ƙaunar Hafsa a zuciyarta, domin kuwa aminiyace ta Amana wacce take iya sadaukar mata da komai nata na rayuwa duk son da take masa kuwa.

“Bansan da wani irin baki zan miki godiya ba Hafsa domin kuwa kina iya bani komai a rayuwarki, Hafsa naji daɗin bani wannan wayar da kikayi domin kuwa ina buƙatar ganawa da ke da kuma Umma cikin sirri na gode sosai ƙawata.”

“Ba komai Ablah ni dai burina ki kwantar da hankalin ki, ki kuma sawa zuciyarki jarunta.”

“Hakane ai nama sawa raina jarunta, kinga sai zuba muke kamar kurna ban baki ko ruwa bane balle abinci bara na tashi naje na kawo miki abinci.”

Murmushi Hafsa tayi tare da cewa.

“Ke yi zamanki ni a ƙoshe nake domin kuwa yanzu dana biya wajen Umma na samu ta gama shinkafa da wake da salad na zauna naci nasha ruwa na ƙoshi dan haka na gode, tafiya ma zanyi yanzu, sai ki rakani na musu ta’aziyya na shige saboda mama tana jirana zan mata aiki, ungo riƙe wayar na cire sim card ɗina.

Tayi Maganar tana ɗaurawa Ablah wayar akan cinyarta, miƙewa sukayi suka nufi bedroom ɗin Inna Jumma tana zaune tare da Faruq suna hira, gefe guda suka zauna Ablah ce tace.

“Yaya Faruq sannu da shigowa ya aiki.”?

Murmushi Faruq yayi tare da amsawa da.

“Aiki alhamdulillah Ablah, ina kika shige na shigo ban hango ƙeyarki ba?”

Ɗan dariya Ablah tayi tace.

“Ina bedroom ɗina nai bakuwa ce daga gidan mu.”

Duban Hafsa Faruq yayi tare da ce mata.

“Okay ƴar gidan kune kenan, baiwar Allah sannu, ya Abokina Abdu.”?

“Abdu na barosa ya tafi islamiyya, ina wuni Inna.”

Tayi Maganar tana gaishe da Inna Jumma, Inna Jumma fuskarta a sake ta amsawa Hafsa gaisuwarta ta’aziyya ta mata sun ɗan juma kaɗan kafin Hafsa da Ablah suka bar room ɗin Inna Jumma, atamfa biyu da dubu biyar ta bawa Hafsa godiya sosai Hafsa ta mata kafin suka haura bedroom ɗin Aunty Amarya tana zaune hakince ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya suka yi Sallama jin muryar Ablah yasa Aunty Amarya sakin murmushi tana hangowa Ablah tashin hankali da zata shiga da zarar an hango shatin hanunta jikin cup ɗin domin babu mai iya fidda da ita sai Allah, amsa sallamar tayi suka shigo da kallo tabi Hafsa tana nazarinta ita kuma wannan mai kama da kafi shanun kuma daga ina, nuni ta musu da kujerar dake tsakar ɗakin nata alamun su zauna itama hafsa da kallon take bin Aunty Amarya cike da tsantsar ƙyamar ta ji take tamkar ta shaƙo shegiya ta kasheta kowa ma ya huta, muryar Ablah taji tana cewa.

“Aunty Amarya ga Hafsa tazo muku ta’aziyya, ƴar Uwar muce.”

Hafsa cike da mamaki ta ɗago idanunta tana kallon Ablah da ta zugawa Aunty Amarya ƙarya wai (ƴar Uwar muce.) 

“Ina wuni Aunty ya haƙuri ashe abinda ya faru kenan Allah ya jiƙanta da rahama yasa ta huta.

Bakinta Aunty Amarya ta taɓe muryarta a daƙile ta amsa da.

“Ameen, kuna iya tafiya idan iya abinda ya kawo ku kenan, sannan ke Ablah daga yau karna kuma ganin ƙafarki a cikin bedroom ɗina har sai mun cure guri ɗaya.”

  Idanunta Ablah ta ɗaga ta kalleta tare da sakin murmushi ta miƙe ta cewa Hafsa da ta ƙurawa Aunty Amarya kallo tace.

    “Mu tafi Hafsa.”

Miƙewa Hafsa tayi suka fita mata a bedroom.

Hanyar waje suka nufa, Hafsa tace.

   “Kina jin matar nan korar mu take, abun dariya wai karki kuma shigo mata room har sai kun cure waje guda, wai ita a haukarta zaki yadda ki zo gareta ne.”

   “Hmmm! Haka take gani mana tunda tamin barazana dole zanji tsoro na yadda da mungun nufinta, shiyasa fa na mata ƙarya akan alaƙar dake tsakanina dake domin kuwa dana faɗa mata cewa ke ƙawata ce to zata fara bibiyar ki, domin kuwa zata tsargu tace kona sanar dake wani abu a kanta, kinsan cikakkiyar mahaukaciya ce.”

Dariya Hafsa tasa dai-dai sunzo First get ta tsaya tare da cewa.

“Gaskiya kam cikakkiyar mahaukaciya ma kuwa domin kuwa idan ba mahaukaci ba wanda baisan imani da Addinin sa ba, babu wanda zaiyi kisan kai haka, kinga ki koma ni bara naje mai adaidaita na yana jirana sai munyi waya.”

Murmushi Ablah tayi tare da cewa ta gaishe da Umma da Mama kafin ta juya zuwa cikin gidan ita kuma Hafsa ta fice, Ablah cike da ƙwarin gwiwwar karawa da Aunty Amarya ta dawo cikin gidan bedroom ɗin ta ta shige ta kwanta domin kuwa bacci ne cike a idanunta bata juma da kwanciyar ba kuwa bacci ya kwasheta.

5:20 pm

Can kuwa part ɗin su Haidar misalin ƙarfe biyar da minti ashirin Haidar ya fito da saurin cikin shirinsa domin kuwa zasu koma police station domin jin sakamakon finger text ɗin da aka musu, babu zato Rufaida ta tare gabansa tana riƙe ƙarfen step ɗin, da kallo Haidar ya bita tare da furta.

“Rufaida lafiya kika tsare min hanya?”

“Yaya Haidar ka fini sanin dalilin da yasa na tareka, na gaji da ƙunsar baƙin cikin Soyayyar ka a cikin zuciyata wanda bansan matsayinta a zuciyarka ba, amsar soyayyata nake buƙata.”

Numfashi ya saki tare da dafe kansa cikin yamutsa fuska yace.

“Bakya ganin shirin fita ne a jikina yanzu zaki tsareni da waɗannan tambayoyin, kinga kauce ki bani hanya na shige Rufaida.”

“Bazan kauce ba yaya Haidar har sai ka sanar dani Matsayin soyayyata a zuciyarka sannan na kauce maka daga hanya.”

Idanunsa ya runtse cike da ƙunar rai, shifa harga Allah baya sonta kuma baya son sanar da ita kalmar baya sonta Saboda kalma ce marar daɗin ji yafi so ta fahimta da kanta ta janye amma ta kasa ganewa dubanta yayi tare da cewa.

“Ya kamata ace zuwa yanzu kin fahimci abinda yake zuciyata Rufaida amma kin kasa, kiyi hkr da abinda zakiji daga bakina Rufaida bansa furta miki ba sai dai ya zamo wajibi a gareni na sanar dake Saboda kin kasa ganewa, kiyi haƙuri Rufaida babu Soyayyarki a zuciyata, soyayyata tana can wani waje daban da ace zan iya baki gurbi a zuciyata da nayi ƙoƙarin hakan sai dai ina zuciyata bazata bari ba saboda mace ɗaya take so,kiyi hkr zan tayaki da addu’a Allah ya baki wanda ya fini komai.”

Tunda ya fara Maganar idanunta suke zubar da hawaye harya gama cikin wani matsanacin ɓacin rai Rufaida tace.

“Wai dame wannan Nafeesan ta fini ne kam da kake karkata gareta , dame na gaza wanda ban cancanci ka soni ba! Yaya Haidar wallahi banyi haƙuri da soyayyarka ba, domin kuwa bazan iya numfashi ba tare da kai ba, rasaka tamkar rasa rayuwata ne domin kuwa numfashi nane zai ɗauke, dole ka soni ka cire wannan matsiyaciyar a zuciyarka domin kuwa nice dolenka ba itaba.”

“Hmmm! Ni kaina sai yau fahimci haka Tabbas Rufaida tana sona Al’ameen da badan Soyayyar Nafeesa ta rinjayi zuciyata ba, wallahi da zanso Rufaida domin kuwa bata da makusar da za’a ƙita sai dai zuciyata bazata so Rufaida ba saboda Nafeesa ce kawai a cikin ta, karka zageta saboda soyayya domin kuwa ta kai munzalin da zata tsaya da namiji Bana ganin laifin ta domin kuwa nasan zafin Soyayya abinda ya ɓata min rai da ita yau ɗaga min murya da tayi ne, ka mata magana yadda ya kamata Please karka zageta ya kamata a mata uzuri.”

Yayi Maganar dai-dai sun shigo station ɗin, tare da yin parking motar Daddy da security ɗinsa Al’ameen ya hango buɗe motar yayi ya fito ba tare daya bawa Haidar amsa ba, shima Haidar fitowa yayi suka shiga cikin statin ɗin har Office ɗin Dpo aka musu iso yayin da suka taradda Daddy zaune shida Papa, suma zaman sukayi tare da bawa Dpo hanu sukayi musabaha, Dpo gyaran murya yayi tare da fara musu jawabi.

“To alhamdulillah dama ku muke jira ku iso tunda kun iso bara na sanar daku yadda result ɗin ya kasance, da farko dai mun samu shatin yatsun ita marigayi a jikin cup ɗin wanda ita bamu da zargi a kanta tunda saka mata akayi kuma dole zata ɗaga cup ɗin tasha, sai kuma yatsa na biyu da muka samu, shine shatin yatsun Al’ameen wanda shima bama zargin sa tunda ya ɗaga cup ɗin a gabanmu kafin mu ankara sannan kuma dishi dishi ne shatin hanun nasa a jiki, sai shatin yatsu na Uku da muka samu wanda shine ya fito ɓaro ɓaro a jikin cup ɗin kuma tar shine na wata mai suna ABLAH wacce kuma itace muke zargi da kisan Hajiya, Saboda yatsun hannunta yafi na kowa fitowa har sau biyu yatsun hanun nata suka bayyana, wanda a nazari da lissafin mu, tasa gubar daga farko, sannan kuma ta ƙara ɗaukar cup ɗin ta bata domin tasha, tunda har sau biyu yatsun hannunta ya bayyana, itace abin zargin mu, kuma zamuje har gidanka muyi Arresting ɗinta zamu rufeta domin bincikenta har mu gano gaskiya akanta, sai dai fa Alhaji zarginta muke bamu tabbatar da itace ta aikata laifin ba.”

Tunda Dpo ya fara Maganar Al’ameen yayi wani irin razana yana kallon sa, gumi ne ya keto masa a goshinsa, cike da ruɗani gami da tashin hankali yake mamaki anya kuwa Ablah zata iya aikata kisan kai, shima Haidar sosai yasha mamaki sai dai dama ita rayuwa haka take ba’a gane mungu a fuska, amma muddun ya tabbata cewa Ablah itace tayi wannan kisan to Tabbas tayi asara kuma dole ta mutu kamar yadda ta kashe Ummi, wallahi baza’a sarara mata ba, Tabbas ma Itace tayi kisan idan ba haka ba waye zaiyi wannan aikin a cikin gidan, shekara nawa duk ba’ayi kisa ba sai zuwanta Tabbas babu shakka ko kokonto itace to meye dalilinta na aikata wannan mummunan aikin waye ya sakata domin kuwa dole turota akayi lallai wannan Yarinyar sai ta shiga uƙuba da baƙar azaba domin kuwa bazata ci banza ba…”

<< Aminaina Ko Ita 24Aminaina Ko Ita 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×