Skip to content
Part 32 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Mtsss! Wai kai meyasa yanzu ba’a maganar arziki da kaine, magana fa nake maka akan rayuwata, wani solution zamu ɗauka amma kake gwada min cewa babu wani hari da za’a kawo min barazana ce domin a ceto Ablah, to naji barazana ce idan kuma na mutu sai ka faɗawa waɗanda zasu tambayaka meya kasheni barazana ce.”

“Hmmm! Al’ameen meye na ɗaukar zafi da yawa dama ai dole zamu samo solution magana ce nayi akan Ablah bawai akan rayuwarka ba, abinda zai faru yanzu jami’an tsaro zamu saka subi bayanka idan ka fita amma da farin kaya zasu bika insha Allah in har da gaske ne ina tabbatar maka cewa sai mun kama koma wanene, idan har hakan ya tabbata to zan yadda ba Ablah ba ce tayi kisan.”

Zama Al’ameen yayi tare da dafe kansa har yanzu tunanin Ablah ne ya azuciyarsa wani hali take ciki domin kuwa yasan kwanan zaune zatayi ga sauro, tsuka yaja tare da duban Haidar yace.

“Hakanma yayi, Haidar ina da matsala damuwa tana damuna, dama haka so yake da zafi Haidar.”

Murmushi Haidar ya saki tare da faɗawa saman bed ɗin Al’ameen ya lumshe idanunsa tare da cewa.

“Ƙwarai kuwa so yana da zafi yana kuma da daɗe idan zuciyoyinku suka haɗu aka amince da juna sai dai fa shi so baya taɓa barin ƙwaƙwalwa ya huta saboda kullum cikin tunani kake akan abar ƙaunarka, shiyasa bana son kana kallon laifina akan Nafeesa domin kuwa zuciyata ta gama haukacewa akanta, amma Abokina tell me waye ke chaja maka ƙwaƙwalwa.”?

Hararar Haidar Al’ameen yayi tare da cewa.

“Wai tambayata ma kake waye ce, hmmm! Ina jin aina sanar maka da wacece, ABLAH ne itace ta tafi da ruhina.”

“Ablah Ni fa bawai bana sonka da ita bane amma dai ina guje maka son baƙar kunama wacce zata tashi ta barka da zafin harbi.”

“Me kake nufi da wannan maganar taka, ban fahimce ka ba Ablah ne baƙar kunama, wai Haidar ko kana rama abinda nake maka akan Nafeesa ne, nifa bari kaji wallahi duk abinda zai fito daga bakina kafi kowa sanin gaskiya ta ne domin kuwa bana wasa ko zolaya, gaskiya nake faɗa maka akan Nafeesa domin kuwa ɗabi’un ta nake hangowa cikin idanunta shiyasa nake faɗa maka gaskiya, sannan da kake kiran Ablah baƙar kunama na tabbata zuwa gobe sai kayi nadamar faɗa mata wannan kalmar.”

Yayi Maganar yana kau da kansa gefe. Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Bazance bazanyi nadama ba, saboda ban san me gobe zata haifar ba, kai ba boka ba ba kuma allan musuru ba, taya zaka fahimci ɗabiar mutum ta idanunsa, hmmm! Koma meye lokaci shine zai gwada mana haka.”

“Allah ya nuna mana lokacin.” Al’ameen yayi maganar yana kwanciya tare da jawo blanket ya lulluɓu ranar a bedroom ɗin Al’ameen Haidar ya kwana.

Washe gari da safe bayan sunyi breakfast Haidar da kansa yayi magana da Dpo yake sanar dashi abinda ke faruwa tare da neman a basa jami’ai masu farin kaya.

“Mu zamu shige Aunty.”

Al’ameen ya yiwa Aunty Amarya dake zaune cikin falon sallama, murmushi tayi tare da cewa.

“To Al’ameen a dawo lafiya, Allah ya tsare gabanka da bayanka, ya rabaka da sharrin maƙiya, ka dawo mana da Apple idan ka tashi dawowa bamu da shi ya ƙare.”

“Okay to shikenan Aunty insha Allah zan dawo dashi, amm idan Daddy ya fito kice masa ya kamata yaje police station yaji halin da ake ciki saboda ina da meeting yau ba lallai bane na samu zuwa ba.”

“Shikenan zan sanar dashi, Allah ya tsare.”

Da ameen Al’ameen ya amsa yana fita, yau shi da Haidar basu hau mota tare ba,kowa tasa ya hau suka harba titi, Al’ameen tunda ya shiga motar driving kawai yake amma hankalinsa ba’a kwance yake ba, numfashi ya saki yana ambaton Allah cikin zuciyarsa, bayansa kuma police ne ke biye dashi cikin farin kaya wanda bazaka taɓa cewa police bane sunyi nisa da tafiya, Al’ameen yaji an harbi tayar motar sa, wani irin kufcewa sitiyarin motar tayi a hanunsa, saurin kai hanunsa yayi ya riƙe sitiyarin tare da taka birki da sauri kafin tayar ta fice cak motar ta tsaya a tsakiyar titi, harbi aka kuma yiwa motar wannan karon Al’ameen aka nufa, yayi saurin yin ƙasa yana sunkuyar da kansa, Haidar dake tasa motar ne ya zaro idanunsa, tare da parking ya fito da sauri police ɗin suma fitowa sukayi yayin da jama’a ke guduwa, kowa yana ta kansa mutum uku ne suke Harbin sun rufe fuskokinsu police ɗin bindigarsu suka ciro wasu suka sha gabansu kewayasu sukayi tare da harbin mutum ɗaya a ƙafa.

“Ku dakata ko mu harbeku.”

Police suka furta suna nufarsu tsaya sukayi cak tare da ɗaga hanunsu sama, da gudu Haidar yazo gaban motar Al’ameen yana kiran sunansa sai yanzu Al’ameen ya ɗago kansa tare da buɗe motar ya fito yana ambaton innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, dubansa ya kai ga mutanen dake neman rayuwarsa, police ɗin ne suka cire musu wannan abinda suka rufe fuskokinsu dashi, ko kaɗan bai taɓa ganin su ba, numfashi ya sauƙe tare da duban Haidar yace.

“Ka gani ai da ban samu labari ba da yanzu wataƙila nima nabi bayan Ummi yanzu ka yadda da Ablah ko?”

Kansa Haidar ya kaɗa tare da cewa.

“Ƙwarai kuwa na yadda ba ita bace tayi kisan.”

Duban police ɗin da suka saka wa waɗannan mutanen ankwa tare da wurgasu cikin mota yace, ku tabbatar sun gane kurensu.” Yayi Maganar yana jan hanun Al’ameen suka nufi motar sa, shiga sukayi Haidar zai ja motar yaji muryar Al’ameen.

“Bazan iya zuwa Company yau ba, muje police station ɗin ina son sanin halin da Ablah take ciki.”

Kansa Haidar ya girgiza tare da cewa.

“Okay muje police station ɗin, ina ga ai Faruq ya juma a Company babu matsala.”

Yayi maganar yana jan motar, police ɗin sun rigasu isa, kafin su suka isa, tun daga cikin police station ɗin zaka jiwo ihun waɗannan Mutanen da ake jibgarsu, Al’ameen direct office ɗin Dpo ya nufa yayi Sa’a kuwa yana nan zama sukayi tare da musabaha Dpo ne yace.

“Zakin Ahmad Giwa, gaskiya kayi jarabtu, kasan rayuwar mutane irinku dama dole akwai maƙiya a cikin ta, amma ni abinda ya bani mamaki su waye suka sanar da kai ya kamata a binciko su domin kuwa duk yadda akayi sun san komai, zamuyi amfani da numbern da suka buɗe e-mail address ɗin dashi, muyi tracker ɗin numbern domin gano su, insha Allah zamu haɗa da ita wannan Yarinyar da muke zargi muyi bincike sosai a kansu sai dai bisa alama yana cewa ita Yarinyar tana da gaskiya domin duk wani binciken da muka mata bamu samu komai game da ita ba, da alamu ta taka sawun ɓarawo ne, sai dai zamuci gaba da bincike a kanta.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Ranka shi daɗe Ablah bata da laifi domin kuwa bazata iya kisan kai ba, sai dai bazan hanaku bincike a kanta ba, saboda aikin ku kuke sai dai ina son ku saketa ku cigaba da bibiyar ta domin tabbatar da gaskiya, zan tafi da ita yanzu.”

Yayi Maganar yana duban Haidar domin kuwa ya faɗi haka ne kawai domin Haidar ya kawar da kansa akan Ablah amma har zuciyarsa ya ɗauki alwashin a yau zai zame Ablah daga cikin case ɗin a rufe file ɗin ta daga police station.

Kansa Dpo ya ɗaga tare da cewa.

“Okay ba damuwa, bara merry ta fito maka da ita, amma fa dole zamu cigaba da bibiyar lamuranta.”

Da to Al’ameen ya amsa tare da miƙewa tsaye Haidar hanu ya bawa Dpo tare da cewa.

“Mun gode da ƙoƙarin ku Dpo, dan Allah waɗannan mutanen karku rage masu koda kaɗan ne, duk wata azaba da kuka tabbatar zaisa su bayyana gaskiya to ku musu.”

Yayi Maganar yana ficewa Al’ameen kuɗi ya tsiro cikin aljihun sa tare da ijiyewa Dpo yace.

“Ku kulle duk wani file akan Ablah ku yaga record ɗinta a cikin police station ɗin nan domin kuwa na tabbatar da cewa bata da hannu cikin wannan case ɗin nayi bincike bayan wanda kukayi yarinyar bata da wuni rigima ko mummunan record, har zuciyata ina jin ba ita bace tayi kisan, Ummi mahaifiyata ce, da Ablah tana da hanu cikin kasheta wallahi sai nafi kowa tsanarta a duniya, sai dai bincike ya nuna bata da laifi, ina fatan idanuna su gane min wanda yake da alhakin ƙarar da ahalina na tana da masa mummunan hukunci mafi muni a duniya, zuciyata tana ƙuna duk sanda Ummi ta faɗo min, idan na juya ko ina a cikin gidan mu ban ganta ba hankalina yana tashi ta yaya zan iya yafewa wanda ya rabamu da farin cikin mu, Uwa ba abun wasa ba ne sai dai wani mahaukacin marar tsoron Allah yayi min wasa da Rayuwarta na Tabbata ko wayene dole komai jumawa sai asirinsa ya tonu jinin Ummi bazai tafi a banza, waɗannan da suka kawowa rayuwata hari suna da hanu da kuma tabbacin kisan Ummina karku raga musu, sannan ina son ku nunawa Haidar cewa Ablah bata da laifi cikin wannan Case ɗin domin kuwa bazan iya saka idanu a zalunci mutumin da bashi da haƙƙi ba.”

Murmushi Dpo yayi tare da cewa.

“An gama zakin Ahmad Giwa, daga yanzu bata da wani Case a cikin wannan station ɗin mun rufe file ɗin ta, har a idanun mahaifinka, shi kansa Dsp Habu Sarki daya amshi file ɗin ta ya tabbatar min da baya zaton da hanunta cikin kisan insha Allah komai yazo ƙarshe tunda mun kama waɗanda sukayi kisan.”

“Shikenan na gode ni na tafi.”

Al’ameen yayi Maganar yana fita dai-dai an fito da Ablah daga cell ɗin idanu suka haɗa Ablah ta sunkuyar da kanta idanunta na ciko da hawaye, shima Al’ameen cikin sanyi jiki da ƙaunarta yake kallonta a hankali ya furta.

“Muje.”

Yayi Maganar yana yin gaba tabi bayan sa, a jikin mota suka samu Haidar yana tsaye, kallon Ablah yayi tare da buɗe motar ya shiga, baya Ablah ta buɗe ta shiga itama shima Al’ameen ya shiga Haidar yaja motar suka bar station ɗin, sun ɗanyi tafiya Haidar ya cewa Ablah.

“Ablah kiyi hkr mun fahimce ki ba dai-dai ba, ki yafe mana.”

   Numfashi Ablah ta saki cikin rawar murya mai alamun kuka tace.

“Ban riƙe kowa a zuciyata ba, saboda banga laifin ku ba dan kun nuna ƙauna ga Ummi, hakan da kikayi shine dai-dai saboda ba’a taɓa gane mungu a fuska sai ya iya yiwuwa na kusan ka wanda kafi kowa yarda dashi wataƙil ma kallon wa ko ƙani ko uwa ko uba kake masa, amma zai zama shine mungun shine yafi kowa son ganin bayan rayuwarka, dan haka banji haushin kowa ba, saboda mutum ba abun yarda bane, sai dai yaya Al’ameen ina son dan Allah ku sauƙeni a gidan mu.”

Juyowa Al’ameen yayi tare da zuba mata idanu cikin cool voice ɗin sa yace.

“Na sauƙe ki a gidan ku, oh Saboda kina tsoron gidan mu kenan ko kuma kina jin haushin mu tunda mun miki laifi, Ablah babu ɗan Adam ɗin da baya kuskure a rayuwarsa Tabbas mun miki laifi, kiyi haƙuri, idan har kika koma gidan ku to Tabbas Inna Jumma bazata ji daɗi ba, saboda tana ƙaunarki kuma tana baki duk wata kariya dan Allah karki bata kunya, ki sani shi mai gaskiya baya taɓa faɗuwa ƙasa.”

Kan Ablah na ƙasa ba tare data kalli Al’ameen ba ta amsa da.

“Ba wannan dalilin yasa zan koma gida ba, ina son zuwa naga Umma nane idan yaso gobe zan dawo.”

Haidar ne yace.

“Ba haka bane Ablah ke dai kina fushi damu shiyasa zaki ce gara ki koma gidan ku, amma dai ki sani bazamu maidaki gidan ku ba, Ambassador Ahmad Giwa Estate dai nan zaki koma, munyi kuma muna neman afuwa saboda wannan abokin nawa bazai iya jure rashin ki cikin gidan mu ba fa, saboda kin ɗauke masa… “

Saurin tare numfashin Haidar Al’ameen yayi da cewa.

“Amm! Ablah gobe zaki fara zuwa school dan haka dole gidan mu zaki koma, sannan na yiwa Inna Jumma ƙaryar jiya kinje school ne, daga nan kika biya gidan ku kika kwana.”

Kanta kawai Ablah ta ɗaga tare da yin shuru, Al’ameen harara ya zabgawa Haidar yace.

“Kai kuma faɗi ba’a tambayeka ba, a bakin get zaka sauƙe Ablah mu shige Company.”

Dariya Haidar yayi, yana kallon Al’ameen wai mutum yana so amma yana ɓoyewa yaƙi sanar da wanda yake yi dominta, shi baya hango Soyayyar Al’ameen ma a idanun Ablah, karfa abokinsa yayi dakon banza, shi kaɗai Haidar ke maganar zucinsa, har suka iso bakin get ɗin Estate ɗin nasu babu wanda ya kuma magana parking Haidar yayi, Al’ameen ya dubi Ablah yace.

“Ki sauƙa ki shiga mu zamu wuce Office.”

Da to Ablah ta amsa tana fitowa, suna tsaye har sai da sukaga shigarta cikin gidan sannan suka wuce, Ablah tunda ta shiga Estate ɗin ƙirjinta ke dukan Uku Uku domin kuwa bata san wacce masifar kuma zata tarar ba, bata san da wani idanu mutanen gidan zasu kalleta ba, part ɗin su Al’ameen ɗin ta shiga, cikin sanyin jiki, Aunty Amarya dake tsaye ita da Musa mai bayin flower ne ta hango Ablah tafe, murmushi tasa domin kuwa ganin Ablah shiya tabbatar mata plan ɗin Hajiya Mansura yayi aiki, duban Musa tayi tare da cewa.

“Musa dan Allah kayi sauri kaje ka sayo min ina jiranka.”

Musa da to ya amsa tare da juyawa da sauri harɗe hanunta Aunty Amarya tayi tare da zubawa Ablah idanu tana murmushi, ita kuwa Ablah bata ga Aunty Amarya ba saboda kanta yana ƙasa sanda tazo daf da ita taji muryar Aunty Amarya na cewa.

“Sannu da dawowa karen farauta, da fatan zaman gidan su ɗan sanda ya miki daɗi domin kuwa naga idanunki har sun ciko.”

Cak Ablah ta tsaya tare da ɗago idanunta ta kalli Aunty Amarya, wani irin mungun tsanarta takeji a zuciyarta tamkar ta kasheta haka take ji, murmushi Ablah ta saki tare da matsowa kusa da Aunty Amarya tace,

“Yauwa sannu, abun farauta, domin kuwa idan har Ablah karen farauta ce to fa Tabbas kece wacce zata farauto, me kika ɗauka da kin ɗauka idan Ablah ta tafi bazata dawo ba, za’a hukuntata da laifin kububuwa wani da sara wani kuma da amsar hukunci da haka kika zata ba, to ai Ablah murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya, zaneni na dutse gogeni bazai taɓa yiwuwa ba, sannan kuma ciwon idonki dole dai na tsole miki idanu koda kuwa bakya so Ablah ta dawo sai mu ɗaura daga inda muka tsaya.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 31Aminaina Ko Ita 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×