Skip to content
Part 40 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Wani sa’in fahimta tana baki wahala Amarya amma wannan maganar ai a buɗe take, ki bari sai lokacin yayi zan fahimtar dake, yanzu me ake ciki a gidan naku, ina tsinanniyar yarinyar take Ablah matsiyaciya macijiya wacce bata ramin kanta sai na wani, kinsan Allah wannan yarinyar fa tsekoce a cikin tafiyar mu, domin kuwa mukayi wasa zata mana illah domin kuwa ɗan karan daka raina sai ya iya tsone maka idanu muna buƙatar fara kawo karshen ta a cikin gidan kafin mu cigaba da aikin mu?”?

Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.

“Nima kaina abinda nake hangowa kenan domin kuwa yanzu yarinyar kamar idanunta sun kuma buɗewa Magana take faɗa min idanu cikin idanu babu shakka ko tsoro, tana gwada min zata iya dakatar dani daga ganin cikar muradina, nafi kowa tsanar yarinyar dabadam kin dakatar dani ba, da na juma da manta kamannunta dan wallahi da tuni na ɓatar da ita ko na illata rayuwarta yadda baza ta sake sha’awar jin an ambaci koda sunan ambassador Ahmad ne bare na iyalansa.”

Ɗan dariya Hajiya Mansura tasa tare da dafa kafaɗar Aunty Amarya tace.

“Duk abinda nake yi ina aikatasa ne da dogon tunani da kuma lissafi shiyasa kikaga bamu taɓa kauce saiti ba bare asirin mu ya tonu, duk abinda zaka saka tunani da lissafi a cikin sa tofa mawuyacin abune ka samu akasi komai dai-dai zai dinga tafiya maka, Amarya nasan me nake na dakatar da ke daga cutar da wannan Yarinyar, amma a wannan lokacin bazata kaucewa tuggun mu ba, nasan a yanzu haka tunaninta da kuma lissafinta akan wani daga cikin jinin Ahmad Giwa yake su take ƙoƙarin kare rayuwarsu zamuyi amfani da wannan damarne a yayin da hankalin ta da tunaninta yake kansa sai mu tona mata rami ta yadda bazata ankara ba sai dai taji ta rubza zamu mu jefa shegiya cikin wannan ramin mu rufe shikenan kinga mun kulle babinta dama itace matsalar mu a yayin da babu ita komai dai-dai zai tafi mana.”

“Me kike nufi, kina nufin mu kasheta kenan.?”

“A’a bashi bane manufata domin kuwa mutuwa rufin asiri ne da kuma samun kwanciyar hankalin wasu, ni kuma bana son Ablah ta samu kwanciyar hankali da ita da Uwarta tozarta su za muyi ta yadda zasu ƙyamaci kansu su dinga gudun shiga cikin mutane da kansu, nutsuwa ta gagaresu su gwammaci gara musu mutuwa da rayuwa, wannan halin nake son su shiga bazata mutu ba har sai ta ga cikar burinmu da idanunta a yayin da zamu saka damuwa da baƙin ciki ya zamo ajalin uwarta.”

Dariya Aunty Amarya tasa tare da furta.

“Shiyasa nake bala’in ƙaunarki ƙawata domin kuwa kinsan kan tuggu, wannan tsarin yamin, amma kinsan wani abu kuwa?”

“A’a ban sani ba sai kin sanar dani tell me?”

“Zargi nake kamar ina hango Soyayyar wannan matsiyaciyar a idanun Al’ameen, ina tsoron Soyayya ta shiga tsakanin su domin kuwa ke kanki kinsan idan hakan ta faru to akwai matsala babba domin yanzu ma take taka rawa da ƙarfinta bare kuma ta samu dama, ai kuma sai dai ta karɓi speaker ta fara rera waƙar da kanta.”

Dariya Hajiya Mansura tasa har tana sunkuyawa tare da ɗagowa ta kalli Aunty Amarya.

“Kaji wani shirme, yanzu ke har wani tunani kike Al’ameen zaiso wannan abar ɗiyar matsiyata talakawa kuma ƙasƙantattu, ko cikin mafarki jakan bazai taɓa faruwa ba, domin kuwa ta ko ina Al’ameen yafi ƙarfinta, ko kin manta da izzarsa da kuma girman kansa, shine zai so ƴar aikin gidan su, impossible, kinga ke koda ma yana sonta mu zamu dakatar da faruwar hakan domin kuwa kina nan kuma ubansa a hanunki yake muna da makullin kulle Soyayyar koda ta faru, kin fahimta?”

Dariya Aunty Amarya tasa tace.

“Ƙwarai kuwa na fahimta, yanzu zata fara gane kurenta, dama na sani faɗa da zaki bazai yiwu a wajen damusa ba.”

Tayi Maganar tana miƙewa tare da ɗaukar jakarta, Hajiya Mansura ce tace.

“Wai tafiya zakiyi ne yanzu fa kika zo.?”

“Ehh tafiya zanyi asibiti na tambaya banje ba nayo nan, asibitin zan shige yanzu.”

“Asibiti kuma waye bashi da lafiya.”

“Sadiya ƴar gidan Hajiya Goggo.”

“Okay Allah ya bata lafiya muje na rakaki bakin mota.”

Tayi Maganar tare da miƙewa har bakin mota ta rakata kafin ta koma cikin gida.

Bayan Kwana Biyu

Jingine yake jikin motar yana jiran fitowarta daga school ɗin, hakan yayi dai-dai da shigowar Al’ameen shima cikin school ɗin, motar Haidar ya hango a parking space dake cikin jami’ar Gwagwalada, cike da mamakin meya kawo Haidar wajen, fitowa yayi bai gama mamaki ba sai da ya hango Haidar jingine jikin motar, nufar sa yayi har inda yake tare da tsayuwa ya furta.

“Haidar.”

Ɗago idanunsa Haidar yayi ya kalli Al’ameen tare da cewa.

“Meya kawo ka nan?”

“Ablah na shigo ɗauka Inna Jumma ta aiki Isah driver shiyasa nazo ɗaukarta, kai me kazo yi?”

“Nazo na haɗu da Nafeesa ne, yanzu nake da niyyar shiga department ɗin nasu ma na duba ko sun fito daga lectures Amma tunda ka shigo muje ka rakani kafin time ɗin su Ablah ya cika naga da sauran time.”

Numfashi Al’ameen ya fesar tare da kallon Haidar cike da tausayin sa, idanunsa ya runtse tare da cewa.

“A’a Haidar bazani ba, kaje kawai ina son zan haɗu da Ferfesa Daniel office ɗinsa zanje.”

“Amma Al’ameen meyasa k…”

Hanu Al’ameen ya ɗaga masa tare da cewa.

“Meyasa na tsani alaƙar ka da Nafeesa ko, shine tambayar da zaka min na sani, Haidar ban tsani alaƙar ka da Nafeesa ba hasali ma ina maka fatan ka sameta ta dawo gareka.

Yayi maganar yana shigewa yabar Haidar tsaye numfashi Haidar ya saki tare da girgiza kansa ya shige department ɗin su Nafeesa Mass communication, hango ta kuwa yayi tsaye ita da Jamila suna tsaye tana nuna mata Littafi a yayin da yake hango dariya saman fuskarta, murmushi Haidar yayi a rayuwarsa yana matuƙar ƙaunar ganinta cikin farin ciki inda take ya ƙarisa tare da tsayuwa yana zuba mata idanu yace.

“Amincin Allah ya tabbata a gareku.”

Kusan tare suka ɗago kansu da Jamila ganin Haidar yasa Nafeesa jan dogon tsaki tare da maida kanta inda ta ɗago Jamila ce ta saki murmushi tare da cewa.

“Haidar kaine a school ɗin namu?”

Ɗan murmushi yayi yana kallon Nafeesa da ta maida kanta tamkar bata san Allah yayi ruwan tsaronsa a wajen ba.

“Ehh Ni ne Jamila” kallon Nafeesa ya kuma tare da cigaba da cewa,

“Bansan wani irin laifi na miki ba Nafeesa kike wahalar da zuciyata kike gwada min ƙiyayya, ko wani irin laifi na miki ya kamata ki tausaya min ki , ki duba mawuyacin halin da nake ciki, ki bani dama na gyara kuskure na, ina sonki Nafeesa bazan iya jure rashinki ba, Nafeesa zuciyata na ƙuna idan kina nuna min ƙiyayya Nafeesa Haidar ɗinki ne fa farin cikin ki kuma duniyarki karki manta da wannan kece kika faɗa min kina kirana da waɗannan sunan amma yau har kin manta kin cireni a duniyarki why Nafeesa meyasa bazaki tausayawa zuciyar da take muradinki ba?”

Murmushi Nafeesa ta saki domin kuwa maganganun sa ma dariya suka basa ɗago idanunta tayi tare da duban taron mutanen dake wajen gefe guda kuma wasu ƴan mata Uku ne sun zuba musu idanu bata damu da kallon da suke musu ba ta cewa Haidar.

“Kake wahalar da zuciyarka dai Haidar, da fa kana da zuciya Haidar daka ƙyaleni amma sai dai kash baka dashi tamkar maloho haka kake, wai ana Soyayya dolene, Tabbas a baya na kiraka da Duniyata amma a yanzu na sauya, bana buƙatar ka a rayuwata dan Allah kaima ka fita daga rayuwata, Shi fa *SO TAMKAR TSUNTSU NE YAKAN TASHI DAGA WANNAN BISHIYAR YA KOMA WACCAR BISHIYAR* to soyayyata ta tashi daga kanka ta koma kan wanda ya fika dacewa, kaga Haidar ni baka min laifin komai ba sonka ne bana yi, gara ka koyi jure rashina domin kuwa na barka bari na har abada bazan taɓa dawowa gareka ba, idan kuma harka matsa akan soyayyata to Tabbas zuciyarka zata fashe ka mutu a banza bani da asara sai dai iyayenka da ƴan uwanka suyi kukan rashinka ni hawaye ko kaɗan bazai zuba a idanuna ba, idan har baka yayewa kanka sona ba na faɗa maka fashewa zuciyarka zatayi domin kuw…

Saurin toshe mata baki Jamila tayi cike da kissa da munafurci tana girgiza mata kai tace.

“Haba Nafeesa wannan wani irin maganganu marassa daɗin ji kike furta masa, hakan bai dace ba, komi tsiya fa shi masoyinki ne masoyi kuma yafi maƙiyi, dan Allah kibar waɗannan maganganun bazai iya jurewa ba, basu dace ki faɗa masa ba Please Nafeesa?”

Bige hanun Jamila Nafeesa tayi tana huci cikin ɓacin rai ta nemi waje ta zauna tana hararar Haidar, shi kuwa Haidar tunda ta fara waɗannan maganganun ƙirjinsa ke ƙuna kansa ke sara masa, har wani jiri yake ji kamar yana ɗaukarsa ya rasa wani irin so yake mata daya kasa rabuwa da ita duk da waɗannan munanan kalaman da ta faɗa masa hakan baisa yaji sonta ya ragu a zuciyarsa ba dai-dai da ƙwayar zarra sai ma ƙara sonta da yake cikin nauyin baki mai haɗe da zallar baƙin ciki yace.

“Bazan taɓa daina sonki ba Nafeesa koda kuwa zan mutu ne, numfashi nane ke dole sai da ke rayuwata zata daidaita, idan ke bakya buƙatar rayuwa dani ni ina buƙatar rayuwa da ke, na yadda ni Maloho ne akan soyayyarki, domin kuwa bani da bambanci da wawa,Ki sanar dani wani azzalumin ne yazo ya shiga tsakanina da farin ciki na, wani mungun ne yake ƙoƙarin rabani da ke, bazan taɓa yafe masa ba ko waye shi, shine mutumin da nafi tsana fiye da kowa a duniya domin kuwa yayi ɗamarar kashe min rayuwa, ko waye shi naci alwashin ganin bayansa, bazan taɓa yadda na rasaki ba, saboda nine Wanda yake miki Soyayyar da babu wanda zai miki irinta a gida nane zaki samu farin ciki mai ɗaurewa zan kula dake tamkar yadda uwa take kulawa da ɗanta, ni ya kamata ki bawa damar aurenki ba wani matsiyaci ba marar y…”

“Ya isheka haka! Ƙarya kake babu wani farin ciki da zan samu a gidan ka, Karka kuma zagin Rayuwata domin kuwa yafi min kai sau dubu, shi ba matsiyaci bane domin kuwa ya fika komai na rayuwa, saninsa bazai amfaneka da komai ba sai dai ma ya tarwatsa maka zuciya, gara ka daina neman sani akansa saboda shine kwanciyar hankalin ka, idan har kasan waye shi to daga ranar bacci zai yanke daga idanunka karka kuma kirana da sunan rayuwarka domin kuwa ni ba rayuwarka bane idan kuwa har na zamo rayuwarka to babu makawa mutuwa zakayi.”

Ta dakatar da Haidar cikin munguwar tsawa, tana kai maganar ƙarshe ta bar wajen a fusace cikin ɓacin rai, da idanu ya bita yana jin hawaye na ƙoƙarin biyowa idanunsa danne hawayen nasa yayi ganin idon mutane a kusa dashi Jamila ce tace.

“Kayi hkr Haidar bata kyauta ba, baka cancanci walaƙanci daga gareta ba saboda ka nuna mata Soyayyar gaskiya da babu wanda zai mata irinsa, Nafeesa bata da kirki son zuciya ya mata yawa, kullum cikin faɗa da nasiha nake mata akanka ina gwada mata karta rabu da kai domin idan tayi kuskuren rabuwa da kai bazata taɓa samun kamanka ba, dama ka faɗa Soyayyar Nafeesa ne saboda baka san wacece ita ba, da kasan wace…”

Hanu Haidar ya ɗagawa Jamila tare da cewa.

“Bana son jin mummunar kalma akan Nafeesa, koma yaya take ni ina sonta, anya kuwa ke ƙawar arziki ce kina cin dunduniyar kawarki bayan idanunta, wannan ba halin abokin ƙwarai bane.”

Yayi maganar yana juyawa yabar wajen cikin nauyin ƙirji, murmushi Jamila ta saki tare da cewa.

“Wahalallan banza, naso na aibatata ta yadda zaka tsaneta na har abada, dama wa ya faɗa maka ni abokiyar ƙwarai ce, hmmm bariki babu na ƙwarai kowa gwaragurbi ne.”

Tayi Maganar tana jan tsuka tare da nufar inda Nafeesa yayi, Haidar tafiya yake yana haɗa hanya cike da baƙin ciki, ya shige inda Nafeesa take ya fita daga department ɗin ya nufi wajen motarsa, koda ya shiga da mungun gudu yaja motar ransa a ɓace.

Kusa da Nafeesa Jamila ta zauna tana dariya tace.

“Shegiya ƙawata, kin iya rashin mutunci har tausayi ya bani, gaskiya yana sonki sosai anya kuwa bazai haukace ba?”

Bakinta Nafeesa ta taɓe tare da cewa.

“Umhm! Wannan damuwarsa ne idan ya ga dama ma a sashi a mari ƙarshen hauka dole dai sai ya rabu dani komai maitarsa, tashi muje sauri nake Atiku Naira yana jirana.”

Bakinta itama Jamila ta taɓe tare da miƙewa suka fita.

Shi kuwa Al’ameen ya juma sosai a Office Daniel har sai da Ablah ta fito daga lectures kafin suka fito tare da Daniel tana tsaye hanunta riƙe da handout tana jiran Isa driver bata san Al’ameen bane yazo ɗaukarta sai da ta gansa cike da mamakin meya kawosa tace.

“Yaya Al’ameen! Kai kuma a school ɗin nan yanzu.”

Murmushi ya mata tare da cewa.

“Banson tambaya muje.”

Kanta ta girgiza tare da kama hanya suka nufi parking space, babu wanda ya yiwa wani Magana sai can Al’ameen yace mata.

“Ya na ganki ke ɗaya a tsaye bakiyi ƙawa bace?”

Murmushi Ablah tayi tare da cewa.

“Ta yaya zaka tambayeni bayan kaine ka hanani yinta.”

Ɗan dariya Al’ameen yayi dai-dai sunzo bakin motar dafa motar yayi tare da cewa

“Okay na manta fa ashe nine na hana, to na bada dama kiyi guda ɗaya kawai amma ki tabbatar da tarbiyyar ta sannan karki kuskura kiyi abota da wanda bai damu da karatu ba, yana da kyau idan zakayi abota ka tantance dawa ya kamata kayi.”

Yayi maganar yana kallon ta fuskarsa ɗauke da murmushi, Nafeesa da suke tahowa da Jamila ne idanunta suka sauƙa akan Al’ameen dake tsaye da Ablah yana sakin murmushi, idanunta ta zaro tare da cewa.

“Jamila duba kiga Al’ameen da wata, zuciyata harta tsinke karfa ace budurwarsa ne?”

Dubanta Jamila ta kai wajen da Al’ameen yake ƙoƙarin buɗewa Ablah mota gidan gaba, cikin sauri Jamila tace.

“Ai kuwa tafiya zasuyi, kinga sauri kije ki shiga gaban motar.”

Nafeesa ba tare da ta amsawa Jamila ba ta ɗaga ƙafarta cikin sauri ta nufe su, yana buɗe motar ta shiga cikin sauri ta zauna, cike da mamaki ganin mutum kamar aljani ta zauna Al’ameen yake kallonta, itama Ablah da mamakin take kallonta “wannan kuma waye) Ablah ta furta cikin zuciyarta,

Al’ameen ganin Nafeesa ya sashi haɗa fuska cikin ɓacin rai murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.

“Hubby na ya kake kallona kamar wata baƙuwa, shiga kaja motar mu wuce?”

“Baki da hankali ne, ko mahaukaciya ce ke zaki shigo min cikin mota mtss gidan uban waye zamu shige da ke, fita min a mota mahaukaciya.”

Maimakon ran Nafeesa ya ɓaci sai ma dariya tasa tare da kanne masa idanu ta kuma yin fari da idanun tace.

“Ni fa bana jin haushi idan ka zageni asali ma daɗi nake ji saboda duk abinda zai fito daga bakinka tamkar zuma haka nake jinsa.”

Huci Al’ameen yakeyi ji yake tamkar ya jawota ya ɗauketa da mari cikin fushi yace.

“Ba sai mutum yana da hankali ba idan an zagesa zaiji haushi mahaukaci ai bai san zagi ba, cewa nayi ki fice min a mota ko.?”

Still dai murmushi ta kuma sakewa tare da cewa.

“Hubbyna naji koma meye ka faɗa min, ita kuma da ta zuba mana idanu tamkar mujiya wacece ita.?”

“Ƙanwar uwarki ce, fice daga mota ko kurma ce ke.”

Zaro idanunta Ablah tayi tana kallon ikon Allah, (to ita kuma wannan wacce irin marar zuciyane ana zaginki da iyayenki kina murmushi, Oh na fahimta sonsa take shi kuma baya sonta, hmmm! Lallai mata suna zubar da kimarsu ) tayi maganar zucin tana kallon Nafeesa, zatayi magana Ablah ta rigata da cewa.

“Yaya Al’ameen dan Allah ka daina biye mata kana zagi ba girmanka bane baiwar Allah tunda yace ki fita masa a mota ki fita mana ana zaginki kina murmushi tamkar ba…”

“Ke dallah rufe min baki almajira, ni zaki faɗawa na fita daga motar Mijina, kin buɗe bakinki mai wari zakiyi kinibibi, ki iya bakinki idan ba haba zan sauya miki kammani, ke wacece da zaki faɗa min magana?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 39Aminaina Ko Ita 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×