Skip to content
Part 54 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Ihsan! Ihsan! Ihsan! Wai ina Yarinyar nan ta shige ne, tun ɗazu ina kira shuru?”

Aunty Amarya tayi maganar tana fitowa falo, Ladiyo ta samu tana goge daining ce mata tayi.

“Ladiyo ina kika gane min ihsan ne?”

“Ehh ɗazu naga sun fita da Afnan.”

“Sun fita da Afnan kuma ita Afnan ɗin fita tayi bata sanar dani ba, Maimu ma ta sanar dani zata fita bare kuma Afnan, hmmm! Afnan ta raina ni.”

Tayi Maganar tana zama tare da jan tsuka, Daddy ne ya sauƙo yana cewa.

“Amarya wai ina yaran nan suka shiga ne naji shuru banji ko motsin ihsan bane?”

Yayi Maganar yana zama gefen Aunty Amarya, cewa tayi.

“Mitar da nake ta yi kenan yanzu Ladiyo ke sanar dani Afnan sun fita tare da Ihsan Maimu kuma tace min zataje gidan Zainab.”

Daddy baika ga magana ba Inna Jumma ta fito ranta a matukar ɓace, bata kula Daddy ba domin kuwa haushinsa takeji akan amincewa da sukayi da Auren Ladiyo ta kira tare da cewa.

“Ladiyo idan kin gama aikin da kikeyi kizo zan aikeki Durmi.”

Da to Ladiyo ta amsa tare da komawa kan aikinta juyawa Inna Jumma tayi zata koma bedroom ɗin ta taji muryar Daddy.

“Inna sannu da fitowa.”

Inda yake Inna Jumma ba ta kalla ba tabar wajen, shuru Daddy yayi cike da sanyin jiki sai dai shi harga Allah alƙawari yayi bazai yiwa ɗansa Auren dole ba,wacce yake so zai basa.

Shi kuwa Al’ameen tunda ya shiga cikin bedroom ɗinsa jikinsa yayi mungun sanyi ji yake kamar bashi ba tamkar an sauya masa halittar sa, idanunsa ya runtse yana cije bakinsa, meyasa ya yiwa Ablah gorin asali, ashe dama haka papa ya zalunceta, mtsss! 

Yaja tsuka tare furta.

“Wai me yake damun rayuwata ne, ji nake kamar bani ba, mena aikata haka meyasa na mata gori, mtsss?”

Tsukar ya kuma ja tare da ƙara furta cewa.

“To ma ina ruwana da ita, meyasa zan damu akanta har naji ba daɗi Saboda na mata gori mtsss.”

Yayi maganar yana jawo bargo ya rufe jikinsa.

*****

“Ya Haidar ga tea ɗin.?”

Rufaida tayi maganar tana ijiye tea ɗin a gefensa tare da zama cikin sanyin jiki tace.

“Yaya Haidar ita fa rayuwa haƙuri ake akan komai ba ko wacce damuwa ake sakawa a rai ba, domin kuwa wata damuwar tana illata mutum, Yaya Haidar Meyasa kake yawan tunani duk abinda baka samu ba, ka ɗauka Allah ne ya ƙaddara ba rabonka bane, domin kuwa ba ko wani abu muke so ya zamo alkairi a garemu ba, na sani kana jin zafina kuma kana jin haushi na amma hakan bazai sa na baka hkr akan abinda Nafeesa da yaya Al’ameen suka maka ba.”

Duban Rufaida yayi tare da cewa.

“Basu nake tunani ba, saboda na kawar dasu daga rayuwata, ina tsanar maci amana shiyasa na tsanesu, damuwata akan Papa ne da rashin kyautawar da ya yiwa mahaifiyar Ablah da ita kanta Ablah, bai kyauta musu ba, hakan yasa nake jin kunya da kuma tsoron haƙƙin su akan Papa Muddun basu yafe masa ba, ga Momma ta ɗauki zafi da Papa, wannan shine damuwata ba waɗannan banzayen ba, amma meyasa kike ƙoƙarin lallai sai kin shiga rayuwata ne, ki sani zaki iya shiga ɗakin aurena bisa tursasawar iyayena amma ki sani bazaku taɓa shiga zuciyata ba, kullum ina faɗa miki cewa bana sonki, kuma bazan soki ba meyasa bazaki daina damuwa dani ba?”

Murmushi Rufaida tayi zatayi nagana wayar Haidar tayi ringin Afnan abinda ya gani rubuce.

“Afnan kuma?”

Ya furta tare da saka hannu ya ɗaga wayar babu sallama yaji ance.

“Mai wannan wayar sunyi accident a titin Shehu Lamiɗo mun sami wannan numbern ne cikin wayarta shine muka kira kuyi gaggawar zuwa domin kuwa akwai matsala gagaruma.”

A matuƙar razane Haidar ya miƙe tsaye tare da furta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Gani nan zuwa yanzu.”

Yayi Maganar yana katse kiran.

“Yaya Haidar meke faruwa ka tsinka min zuciyata.”?

“Babu komai.”

Yayi Maganar a taƙaice saboda baya son ya sanar da ita ta ɗagawa mutane hankali, gara yaje ya fara dubawa ya gani ya accident ɗin yake, ko Daddy bai sanar ba ya tafi wajen

Koda Haidar ya ƙarisa sosai hankalinsa ya tashi, har jiri yaji kamar zai kayar dashi kansa ya dafe sai hawaye shar a idanunsa, gawa biyu lokaci ɗaya ya Daddy da AUNTY Amarya zasuji, da ƙyar ya ciro wayarsa ya kira Faruq shima Faruq Al’ameen ya sanar suka taho tare, Al’ameen durƙushewa yayi a ƙasa tare da furta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wannan wacce irin masifa ce take bibiyar rayuwar mu, suma an kashesu, Why! Why?”

Miƙewa yayi a fusace ya furta.

“Faruq na rantse da sarkin dake busa min numfashi a wannan karon jinin ahalina bazai tafi a banza ba, na rantse da Allah sai na binciko wanda ya ke yi mana ɗauki ɗaiɗai wannan shine ƙarshe koma waye ne yayi na ƙarshe kuma shima karshensa yazo.”

FARUQ idanunsa ya runtse cikin zuciyarsa yana furta, ta yaya mota zata taka rai ta kashe haka kuma ta gudu, wannan accident ɗin shiryasa akayi.

Yayi maganar zucin yana sunkuyawa kan gawar.

“Haidar meka fahimta kan wannan mutuwar da Afnan sukayi?”

“Faruq duk wanda ya kalli wannan motar zai tabbatar da anshirya kashesu ne akayi amfani da accident, AMMA koma waye yayi wannan kisan za fito zamu kamasa.”

Ya yi naganar yana ciro wayarsa tare da sanar da Daddy abinda ke faruwa Daddy sosai hankalinsa ya tashi yayin da hukuma ta ɗebi gawar tayi hospital da su, Daddy tashin hankali da ruɗanin waye yake kashe masa ahalinsa ya dirar masa zuciya, koda yaga Afnan daƙyar ya iya ganeta saboda irin sauyawar da kammaninta yayi, yayin da gidajen tv ya ɗauka cewa ƴar gidan Ahmad Giwa tayi accident a mota ƙirar venz ana tunanin cewa sun mutu, Aunty Amarya dake zaune ita kaɗai cikin falon ne ta saki murmushi tare da furta.

“Alhamdulillah! Hajiya Mansura aikinki yayi kyau Maimu tabi bayan uwarta, a wannan karon ba’a kuskure ba, lallai wannan shine alamun nasara, Tabbas nice magajiyar dukiyar Alhaji Ahmed Sani Giwa hmmm.”

Dariya tasa harda riƙe ciki tare da miƙewa ta kashe tv Hajiya Mansura ta kira tare da mata albishir tace ta kunna tv tasha labari, frinch ta buɗe tare da ɗauko yaghourt ta tsiyaya a cup hankali kwance take shan kayanta tana nan Zaune Maimu ta shigo da Sallama Aunty Amarya a matuƙar razane ta miƙe tsaye tana nunata da yatsa tace.

“Maimu kece! Ba yanzu na gani a tv cewa motar da kika shiga tayi haɗari da ke kuma ana tunanin kin mutu, shine kuma yanzu na ganki, waye a cikin motar to?”

Cike da mamaki Maimu ke duban matar da ta shigo ta samu tana shan yaghourt hankali kwance harda murmushi kuma wai taga cewa motar da ta shiga tayi haɗari, to kuma taji wannan take zaune hankali kwance anya kuwa lafiyar Aunty Amarya.

“Tambayar ki fa nake Maimu kin min shuru?”

Tayi maganar dai-dai Inna Jumma na fitowa daga bedroom ɗinta.

“Accident kuma Aunty wacce mota kike magana akai ne.?”

“Wacce motar zanyi Magana a kai idan ba wacce kika fita da ita ba venz.”

“Venz! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Motar tayi accident, wayyo Allah na shiga uku.”

Aunty Amarya cikin tsawa tace.

“Kin shiga Uku kamar yaya, tambayarki nake meya shigar dake Uku.?”

“Aunty ai Afnan da Ihsan ne suka fita da motar ba ita na hau ba, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! AUNTY Yanzu ina Afnan ɗin take suna ina?”

Tayi maganar cikin kuka da mungun tashin hankali, Aunty Amarya wani irin bugawa zuciyarta tayi jikinta ya hau rawa ko wacce gaɓa ta jikinta ta tsaya cak sai idanu da take bin Maimu dashi, da ƙyar ta furta.

“Me kike nufi Maimu kina nufin ƴaƴana sune suka shiga wannan motar Afnan da Ihsan?”

“Ehh Aunty sune ki faɗa min ina suke?”

Wani irin mungun ƙara Aunty Amarya tayi tare da yankar jiki ta faɗi ƙasa.

Da sauri Maimu tayi kanta tana AUNTY Aunty, Inna Jumma ruwa ta ɗauko da sauri ta watsa mata sai dai ko gezau Aunty Amarya batayi ba, ita kanta Inna Jumma hankalinta ya tashi ta rasa Abokiyar faɗanta Afnan hawaye ne ya zubo daga idanunta sai Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un take furta a bakinta a haka Daddy ya shigo cikin sanyin jiki ya samesu, asibiti akayi da Aunty Amarya, inda suka tabbatar da dogon suma tayi zai iya yiwuwa tayi kwana biyu bata farfaɗo ba, Daddy tamkar zai faɗi haka yakeji zuciyarsa sai zafin yake, yayin da ƙirjinsa ya masa nauyi sai kuma bugawa da zuciyar keyi, saurin dafe ƙirjin nasa yayi sai ya hau tari sosai yake tarin, hannunsa ya saka ya rufe bakin yana ɗago hanun sai jini, shi kansa yasan hakan zata faru domin kuwa tun mutuwar Aksat da Ummi da kuma harin da aka dinga kawowa ahalinsa yake cikin munguwar damuwa, sai kuma ga gawa biyu a gabansa, Abi saurin riƙo Daddy yayi cike da tashin hankali yana basa baki Al’ameen zuciyarsa ne ta taso masa ji yake tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu tsabar baƙin ciki da takaici, bango ya daka da ƙarfi idanunsa na cikowa da hawaye, wani irin huci yake tamkar baƙin kumurci, a wannan lokacin ji yake da zai samu wanda ya musu wannan aikin ya rantse da Allah sai ya kashesa, Papa ne ya dafa kafaɗarsa tare da cewa.

“Cool down! Komai a rayuwa ƙaddara ce, kwana su ne ya ƙare kuma bazasu wuce lokacin su ba, ka kwantar da hankalin ka.”

Yayi maganar cikin rarrashi, Daddy shima kwantar dashi akayi a gado a yayin da Papa da Abi ne kawai suka samu halartar jana’izar su Afnan, Allah sarki Aunty Amarya ko gawarsu Allah bai bata ikon gani ba, cikin mintuna ƙalilan gari ya ɗauka da labarin mutuwar.

Ablah ko da taji sosai ta kiɗime hankalinta ya tashi ita tasan ko za’a kasheta, Aunty Amarya itace zatayi wannan kisan, to amma meyasa zata kashe ƴaƴanta, tayi maganar zucin a ruɗe tare da miƙewa daga zaunen da take da sauri zata sayo kati ta kira Abbas wani irin karo sukaci da Nafeesa, littatafanta suka zube a ƙasa, kallon kallon suke yiwa juna Ablah tsuka taja tare da ɗaga kanta zata shige, Nafeesa tayi baya da ita tana sakin murmushi ta furta.

“Ya akayi tsohuwar yayi mai farmanet sit, au sorry ashe fa kare ya fiki daraja a wajen sa.”

Murmushi Ablah tayi ta raɓe gefenta zata shige ba tare da ta tanka mata ba, Nafeesa ta kuma dawo da ita baya.

“Saurin me kike haka ƴar matsiyata, jaje fa nazo na miki amma da alama naga baki biɗar haka, shin ya kikaji a zuciyarki na faɗa miki faɗa dani babu riba kikaƙi ji wai har kirana kike kina faɗa min Magana, abun mamaki romie da Juliet sun rabu su laila majnun anga ƙarshen Soyayya, sai a koma wajen tsohuwa mai dattin ɗan kwali, a cigaba da fama da wahala, domin kuwa kukun ma da kike a gidan su sweetie na daga yau yazo ƙarshe zansa ya miki korar kare.”

Kanta Ablah ta girgiza duk da taji zafin maganganun Nafeesa sai dai ta shanyesu a cikin ta domin nunawa maƙiyi gazawarka tamkar nasarar sa ce cewa tayi.

“Kaga aikin jahilci oh mu ƴaƴan talakawa mun godewa Allah da ya bamu iyaye na gari masu bamu tarbiyya, ba irinsu Oh Oh ba ƴaƴan ƙaruna masu Shashashun iyayen da basu san darajar kansu ba bare na ƴaƴan su, bama yawo a tiiti bamu san bin maza ba, bamu da abun kunya, alhamdulillah!! Gumin mu muke nema bama yawon banza”

Tayi Maganar tana barin wajen fuskarta cike da murmushi, Nafeesa ita ta fara faɗawa Ablah Magana, sai kuma ta Ablah tafi nata zafi shan gabanta Nafeesa tayi a zuciye ta ɗaga hanunta zata ɗauke Ablah da mari taji an riƙe hanunta ta baya juyowa tayi a fusace sukayi ido biyu da Abbas, idanunta Nafeesa ba buɗe tana kallon Abbas yaushe ya dawo daga ƙasar waje.

“Abbas meya kawoka nan?”

Sakin hannunta yayi tare da furta.

“Uban me ya haɗani dake da zaki san ranar dawowata , marinta zakiyi ne, to mareta ke kuma na kwantar dake a wannan wajen, ɓace min da gani shasha bunsuru jarababbiya.”

Duk tsiyar Nafeesa tana mungun shakka da tsoron Abbas domin kuwa ta san halinsa kamar yunwar cikinta, kanta ta saka tabar wajen, cike da baƙin ciki da ƙunar zuciya.

“Abbas kati zanje na sayo na kiraka yaushe kazo makarantar nan?”

“Ablah yanzu nazo zan mai daki gida ne saboda nasan yanzu baki da mai zuwa ya ɗaukeki sannan zan dinga saka driver yake zuwa yana kawoki.”

“Ba wannan ba Abbas kasan abinda yake faruwa kuwa a Familyn Ahmad Giwa.?”

“Na sani Ablah ban sanar dake bane saboda abun bazai shafi wani ba, a iya kanta da ta shirya ya tsaya kuma nine na shirya abun ya juye kan amarya.”

Ban fahimta ba Abbas mekake faɗa haka?”

“Kiyi haƙuri Ablah naji wayar amarya da Mansura sun shirya kashe Maimu kuma ita bata da haƙƙi Bayan sun katse wayar ni kuma sai na kira Afnan na sanar da ita cewa tazo Gest hause na Lamiɗo ɗan uwanta Faruq yana cikin haɗari amma idan suna da mota venz ta taho a ciki saboda tafi sauri tazo ta ceci rayuwar Faruq da sauri banyi zaton su biyu zasu hau motar Ba, amma Tabbas ni ne na juya mutuwa daga kan Maimu zuwa kan Afnan domin kuwa nasan amarya zata gane kurenta rayuwa zata mata zafi biyu babu nake so tayi kuma nayi alƙawarin cewa bazata ci koda Naira biyar a gadon Ahmad Giwa ba, kisa a ranki cewa ƙarshen amarya ne yazo kuma a yanzu haka na shiryawa nunawa Al’ameen gaskiya bayan gama sakadar bakwai na Su Afnan.”

Tunda ya fara Maganar Ablah ke kallonsa cikin damuwa da tashin hankali tace.

“Abbas kasan me kake faɗa kuwa, Abbas kana da hannu cikin wannan kisan meyasa bazakayi kokarin dakatar da Maimu daga fita daga gidan ba, Afnan da Ihsan basu da laifi basu cancanci amsar hukumcin mahaifiyar su ba, ko ubangiji baya hukunta wani da laifin wani meyasa zaka salwantar da rayuwarsu saboda kaga ihun mahaifiyarsu baka kyauta ba Abbas, kaje kata istigfari Allah ya yafe maka, da gaske kake min cewa zaka bayyanawa Al’ameen gaskiya.?”

“Ƙwarai kuwa da gaske nake Saboda naga zuciyar amarya bata da kyau, idan mukayi shuru zata cigaba da ɓarna gara kawai mu Kawo karshen ta.”

“Idan kamin haka Abbas ka gama min komai a duniya kuma bazan manta da kai ba har ƙarshen rayuwata.”

“Karki damu muje na ijiye ki zanje na samu Faruq ne akwai magana mai mahimmanci da zamuyi dashi.”

“Okay AMMA ina suna karɓar gaisuwa ne.?”

“Ehhh can zan samesa.”

Kanta ta girgiza sannan sukaje suka hau motar ya sauƙeta a ƙofar gida kafin ya shige wajen Faruq, yana zaune shida Haidar ta’aziya ya musu har Al’ameen sannan ya yiwa Faruq magana a kunne miƙewa Faruq yayi suka shiga cikin mota.

“Abbas ya akayi ka samo mana mafita ne?”

“FARUQ nayi tunanin mafita ɗaya ce kawai amma tukunna Amarya ta farfaɗo ne?”

“Bata farfaɗo ba, dama doctor sun sanar cewa zata iya kai kwana biyu ko uku cikin suman.”

“Okay! Amm mafitar mu, ɗaya ce itace Jamila ƙawar Nafeesa, idan muka samu Jamila muka sake mata kuɗi masu yawan gaske, duk abinda aka kulla zata sanar damu kuma zata mana aiki muddun zamu watsa mata tsaba, Faruq zanyi wannan aikin ne saboda Ablah kuma nine zan kashe kuɗin ina son Ablah shiyasa zanso farin cikin ta, na fahimci Al’ameen shine farin cikin ta ba niba, har yanzu ƙoƙarin karesa da ahalinsa take yau da taji labarin mutuwar Afnan hankalinta yayi mungun tashi, bata da magana sai ta Al’ameen shiyasa zan sadaukar da farin ciki na saboda ita, zan fara bawa jamila kafin alƙalami Naira miliyan biyu, kuma zata amince Domin kuwa tasan cesa Nafeesa bazata iya bata irin waɗannan kuɗaɗen ba, mayyar kuɗi ce Jamila zata iya juyawa uwarta ma baya akan kuɗi.”

Murmushi Faruq yayi tare da furta.

“Shawara mai kyau hakamma yayi, kace min zamuyi Magana akan waɗanda suke mana ɗauki ɗaiɗai a Family, wayene Abbas kace karna sanar da kowa har sai ka sanar dani.”?

“Bani bane wanda zan fasa tayar wacce alhakin ke kanta itace zata fasa tayar ka jira ka gani komai yazo ƙarshe.”

Faruq cike da mamaki yace.

“Ban fahimta meyasa ka sani kai bazaka sanar ba har sai mun jira wata, ita watan WACECE.?”. 

“Bansan komai ba itace ta sani nima jiranta nake tazo muji menene, karka damu zaka santa.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 56Aminaina Ko Ita 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×