Skip to content
Part 56 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Kinyi shuru Jamila ko bazaki iya aikin bane?”

“Buƙatar ne naji yamin nauyi amma hakan bashi yake nufin bazan iya ba, saboda koda naci amanar ta ba abun damuwa bane tunda itama amanar taci kuma dama haɗuwar bariki babu Amana, amm! Abbas zan faɗa maka komai amma sai kamin alƙawari guda ɗaya.”

“Ina jinki faɗi alƙawarin da kike so na miki.”

Numfashi ta saki tare da tashi ta fita taje ta rufe ƙofar gidan saboda tsaro sannan ta dawo ta zauna tare da cewa.

“Alƙawarin da nake son kamin shine cewa bazaka faɗawa Nafeesa ko wani cewa ni ce na bankaɗa sirrinta ba, idan kamin wannan alƙawarin ni kuma zan bankaɗa maka komai.”

“Jamila zan iya rufe miki sirrin sai dai dole mutum biyu zasuji wanda nake wannan aikin saboda su Faruq da Ablah, sannan na Tabbata suma zasu faɗawa wani dan haka ban miki alƙawarin ɓoye wannan maganar ba, ciniki nazo muyi na sayi jaridar da kuɗina dan haka babu batun kin shimfida min sharaɗi idan zaki iya aikin ina sauraronki idan kuma bazaki iya ba sai na tashi na tafi da kuɗina.”

“Bazan bari wannan kuɗin su koma ba dole zan sayar da jaridar duk abinda zai faru ma sai ya faru domin kuwa nasan Nafeesa koda taka kuɗi take bazata bani irin wadannan kuɗaɗen ba, nasan waye Nafeesa idan ka shirya bara na sanar da kai.”?

Wayarsa Abbas ya ɗauka tare da danna recording yace,

“ina jinki.”

“Abbas Nafeesa taƙi Haidar ne tun ranar da ya Kawo mata Al’ameen suka gaisa, ya kuma sanar da ita cewa Al’ameen shine asalin ɗan Ahmad Giwa ba shiba, ya kuma sanar da ita cewa Companyn da suke aiki mallakin Al’ameen ne, a taƙaice dai ya nuna mata cewa Al’ameen ya fisa kuɗi nasa ba kusa ba, daga wannan ranar son Duniyar daya sata shiga rayuwar Haidar ya ɗarsu akan Al’ameen, ta fara gudun Haidar tana kusantar Al’ameen, a yayin da Al’ameen ke kauce mata, harga Allah Al’ameen yaƙi Nafeesa kuma ya nuna mata ƙiyayya ta zahiri, ganin haka yasa mahaifiyar Nafeesa taje wajen boka saboda ayi aikin da Al’ameen zaiso Nafeesa, a takaice dai asiri ta masa ba soyayyar Allah bane ta asiri ne, sannan maganganun da ta faɗawa Haidar na cewa shi mutumin banza ne bashi da kirki ta dai ɓatasa a idanun Haidar harda haɗa hoton ƙarya wanda aka haɗa Haidar da mace suna kwance a matsayin wai Al’ameen ne ya turo mata wallahi duk ƙarya ne sharrin Nafeesa ne itace ta haɗa wannan shine abinda na sani.”

Murmushi Abbas domin kuwa yayi wannan tunanin cewa saboda abin duniya Nafeesa ta naniƙewa Al’ameen domin kuwa Al’ameen mai kuɗin gaske ne business man ne ba ƙarami ba bayan Companyn su na three Star yana da ƙananan Company’s sun kai Takwas banda shaguna da yake dasu a cikin kasuwanni ga hannayen jari da yake zubawa, Jamila ce tace.

“Abbas ya banga ka firgita alamun mamaki ba sai ma dariya da kayi.?”

“Kuka kike so nayi Jamila wannan ai ba abun mamaki bane abune da yake faruwa life, asiri da son dukiya, wannan duk halayar mata ne bance duka mata ba, amma mafi yawansu haka kuke, na fahimci maganganun ki Jamila meye kike ganin solution wanda zan iya taimakon Al’ameen dashi na kuɓutar dashi daga wannan MASIFAR da ya faɗa?”

“To solution ɗaya ne kawai ni a tunanina kawai muje wajen bokan ya warware abinda ya ƙulla shikenan hankalin Al’ameen ya dawo jikinsa, abune mai sauƙi.”

“Ba zamuje wajen boka ba, mu hallaka kamar yadda ta hallaka tunda kince asiri ne karki damu zamuyi roƙon Allah malamai zasu shiga lamarin, ki bani account number ɗinki zakiji alart.”

Numfashi Jamila ta saki tare da basa account numbern sukayi sallama ya ce idan akwai wani abu zai kirata, sannan ya tafi.

Ko da ya fita ƙofar gidan su Ablah ya yaje ya kirata ta fito tazo ta samesa a cikin mota.

“Abbas ina wuni?”

“Lafiya! Ya naga kin faɗa ko dai fargabar masoyin naki ne, umm! Mrs Love ki kwantar da hankalin ki fa Al’ameen zai dawo gareki.”

Kanta Ablah ta kawar gefe, tare da haɗa rai tamau, murmushi Abbas yayi yace.

“To fa haɗa ran kuma na menene.?”

“Abbas meyasa kake ɓoye min abinda ke damunka, meyasa bazaka sanar dani gaskiyar ka ba, banji daɗin hakan ba.?”

Idanunsa Abbas ya zaro tare da cewa.

“Whattttttt! Kamar yaya me nake ɓoye miki kuma, Ablah kin sani babu abinda zan ɓoye miki.”

“Ka ɓoye min Abbas! Ka ɓoye min kana sona, zato kake bazan soka ba saboda Al’ameen shiyasa zaka ɓoye cuta a cikin zuciyarka, Abbas ka sani kamin hallaci mai yawa a rayuwata, tsiya bai taɓa haɗani da kai ba sai alkairi, tun farkon haɗuwar mu kake wahala da ɗawainiya akaina, to meyasa zan ƙika, shifa wannan Al’ameen da kake faɗa haɗuwata ta farko fashi wulaƙanta ni ya fara yi, nasha wahala dashi sosai kafin ya soni kuma itama soyayyar ashe ta yaudara ce saboda ya cutar da rayuwata, Abbas meyasa bazan aureka ba, na shiryawa aurenka Abbas ina sonka.”

Tayi maganar cikin kuka, tunda ta fara Maganar Abbas yake kallonta cike da so da ƙauna sai dai yasan wannan maganar da take iya bakinta ne kawai amma zuciyarta na ga Al’ameen.

“A’a Ablah Al’ameen ba yaudarar ki yayi ba, ki saurareni kiji gaskiyar…”

“Dakata Abbas babu abinda zan saurara akan Al’ameen dan Allah ka daina min maganarsa kwatakwata a rayuwata, na share babinsa, dama ka faɗa min ahalin AHMAD GIWA ba mutanen kirki bane ban fahimci hakan ba sai yanzu.”

“Ablah ni fa a wannan lokacin na faɗa miki cewa ba mutanen kirki bane saboda tsakanin daddyna da Daddyn Al’ameen sun samu matsala, amma bayan mutanen kirki ne al’umma na yabonsu suna kyautata musu, Al’ameen bashi da laifi a juya mik…”

“Na ce ka daina kawo min Maganar Al’ameen, iya maganata na yita idan har da gaske kake kana sona na baka damar turo iyayenka sai dai kuma idan ba sona kake ba shikenan.”

Ta yi maganar tana buɗe motar ta fita.

Kansa ya dafe tare da runtse idanunsa, shuru yayi ya juma a wajen yana nazarin kalamanta kafin yaja motar sa ya shige gidan su, falon Momy ya shige darect ya sameta tana zaune a falon ita da Aknam suna hira ya Zauna gefen Momy tare da kwantar da kansa a jikinta yayi shuru cike da damuwa Momy kallon ɗan nata tayi da ya shigo cikin sanyin jiki kuma da alamu yana cikin damuwa.

“My son meke damunka, da alamu baka jin daɗin wannan ranar.?”

Ƙara kwantar dake kansa jikinta yayi cikin sanyin jiki yace.

“Momy na kasa nasara a soyayyata ina ƙoƙari wajen ganin na cireta a raina amma abun yaci tura kullum Soyayyarta maimakon ya ragu sai ma ƙaruwa da yake, zuciyarta bani take so ba Momy, zuciyarta na ga wani, ƙoƙarin mallaka mata muradinta nake amma yau sai take nuna min cewa ni zata aura ba shi ba, Saboda wulaƙanta ta da wanda take so yayi, kuma na fahimci har yanzu zuciyarta na garesa ta yaya zan yadda na auri gangar jikinta zuciyarta na ga wani Momy ya zanyi?”

Numfashi Momy ta sauƙe cike da tausayin sa ta ɗago kansa tare da share masa hawayen daya zubo masa cikin tausayawa tace.

“My son kowa da ƙaddararsa sannan rayuwa da wanda baya sonka akwai matsala, idan da zaka ɗauki shawarata karka kuskura ka Auri wanda baya sonka, ka haƙura da ita Abbas ka nemi wata, kai da kanka ka fahimci ba kai take so ba, to zata iya kware maka daga baya, gara ka hkr.”

Momy tayi maganar cikin sigar rarrashi domin kuwa ita Aknam take so ya aura ba wata bare can ba. (Mema zaiyi da ƴar matsiyata kowacce ƙwarya da Abokiyar Burminta ga ƴarmu rainon ac rarrafen falo, karatun turai, insha Allah itace matarka)

Tayi Maganar zucin tana jawosa jikinta, cikin sanyin jiki yace,

“Momy dama nima bazan yadda na rabata da farin cikin ta ba, insha Allah zanyi ƙoƙari naga sun daidaita da Al’ameen Momy Ablah macece mai tarbiyya da kowa zaiso ya haɗa iri da ita, ina sonta sosai Momy zan hkr da ita ne saboda haka ƙaddarata tazo ta.”

“Hakane insha Allah zaka samu wacce ta fita komai a rayuwa.”

“Hmmm! Ba komai ake rasawa a samu ba Momy mussaman ingantaccen Abu idan ka rasashi bazaka samu wanda ya kaisa ba, sai dai ƙasa dashi zanje na kwanta kaina ke ciwo.”

Aknam ce tace.

“Ya Abbas ina wuni?”

“Lafiya Aknam ya jikin Ammi?”

“Da sauƙi.”

 Shigewa yayi ba tare da kuma cewa komai ba.

*****

Washegarin sadakar ukun Su Afnan tare akayi sadakar da Abbas bayan anyi addu’a ne Faruq ya dubi Abbas tare da cewa.

“Ya kukayi jiya da Jamila?”

Abbas duk abinda Jamila ta sanar dashi haka ya mayarwa Faruq bai ɓoye masa komai, sosai Faruq yasha mamaki, musamman da ya kunna masa recording ɗin da yayi.

“To yanzu Faruq menene solution.”

“Bamu da solution ɗin da ya wuce muje mu sanar da Inna Jumma abunda yake faruwa na Tabbata zata kawo mana mafita dama na sani wannan haukar da Al’ameen yake ba haka banza ba, na gode sosai Abbas ka taimake ni, ƴan uwana zasu samu daidaito ta hanyar taimakonka.”

“Ka daina min godiya Faruq abinda nayi shine dai-dai muje ciki saboda ina sauri zan koma.”

“Okay muje.”

Sukayi Maganar tare da tashi suka shiga cikin falon da Aunty Amarya suka fara cin karo cikin falon ta yi tagumi cike da damuwa a cikin kwana uku tayi baƙi ta rame tamkar ba ita ba, kansa Abbas ya girgiza cikin zuciyarsa ya furta. (Lallai rayuwa tana tara bawa takan basa sakamakon sa a lokacin da bai taɓa zato baz Tabbas idan rayuwa bata taraka da alkairi ba, idan ta tashi juya maka juyin bazaiyi kyau ba, hmmm! Taso kuɗi tana jin zata iya kauda kowa akansu, ta manta da cewa suma waɗanda take kashewa suna da wadanda zasuji zafi da raɗaɗin rasasu, ta kashesu batayi tunanin sunfi kuɗin da take nema daraja ba, sai ubangiji ya tsayar mata da alƙiyamarta tun a duniya ya gwada mata mahimmanci ɗan Adam fiye da kuɗin da take nema, lallai muji tsoron Allah mu guji kamun ubangiji.)

FARUQ ne ya taɓasa tare da cewa.

“Abbas tunanin me kake mu ƙarisa bedroom ɗin Inna Jumman mana.”

Kansa ya ɗaga suka shige tana zaune suka shigo da Sallama ta amsa tana dubansu gefe suka nema suka zauna.

“Umaru bakuje can makabartan bane anyi addu’a da ku?”

“Bamuje ba Inna Jumma, saboda muna da Magana mai mahimmanci da ke.”

Abbas ne yace.

“Sannu Inna Jumma ina wuni?”

“Lafiya yaro ban ganeka ba kuma.”

FARUQ yace.

 “Umm bazaki sanshi ba Saboda ba’a ƙasar nan yayi rayuwa ba, ba wannan ba Inna Jumma Magana ne akan Al’ameen da wannan Yarinyar Nafeesa.”

“Magana akan wannan gambayen Yarinyar fitsararriyar, to me kuma ya sake faruwa?”

Faruq zaiyi Magana Abbas ya dakatar dashi tare da zaro wayarsa ya kunnawa Inna Jumma recording ɗin Jamila, sanda ta gama saurara ta hau tafa hannu da salati tana salallami tace.

“Ai dama nasan za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya, dama ai ba abun hankali Aminu ke aikatawa ba, an juyar masa da hankali, hmmm! Allah sarki Ali ashe shima cutarsa tayi ga kuma gabar da ta haɗasu lallai wannan yarinyar akwai makira, yau naga tsinanniyar uwa mai kai ɗanta ga hallaka, hmmm! Amm meye ma sunanka?”

Ta nuna Abbas da yatsa.

“Abbas sunana Inna.”

“Sannunka Abashe Allah ya naka albarka, lallai kai ɗan arziki ne, abinda zai faru gobe da safe zamuje gidan su Ablah wajen mahaifiyarta da iyayenku, idan mun dawo Abashe kazo da misalin huɗu na la’asar zamuje wajen Malam Yusuf mai tsangaya insha Allah zai karya mana wannan sihirin, “Zuwa dare kuma na sanar da iyayensa abinda yake faruwa.?”

“Shikenan Allah ya kaimu Inna ni zan koma gida.”

“To na gode.”

Sukayi Sallama da Inna Jumma, Faruq ya raka Abbas har bakin motarsa yaja yabar gidan.

******

Suna zaune da Hafsa da daddare Umma kuma na can gefe tana wuridi Ablah ta kunna data, ta shiga WHATSAPP, saƙon Abbas ne taga sun shigo mata,airpies ta sanya a kunnenta tare da buɗe voice ɗin daya turo mata har wajen biyar, a hankali ta fara saurara dukkan shaidar da take nema akan Aunty Amarya ya turo mata, sanda ta gama saurara sai ta buɗe voice ɗinsa na ƙarshe inda yake cewa.

“Ki gafarce ni Ablah tabbas idan nace bana sonki nayi ƙarya, ina sonki fiye da komai a rayuwata Ablah sai dai bazan iya aurenki ba saboda Al’ameen shine farin cikin ki bani ba kuma nasan shine kike so, ki daina ganin laifin Al’ameen akan rabuwar da kukayi dashi, bashi da laifi shima baisan ya aikata ba, ina da shaidar da zata tabbatar miki da baya da laifi amma har sai kin bani umarnin turo miki shaidar, ki ɗauke ni a mazaunin yayanki Ablah mu kawar da Soyayya gefe dan Allah.”

Shuru Ablah tayi tare da ijiye wayar ta zabga tagumi idanunta ta runtse cikin ƙunar rai ta furta.

“Tabbas kayi gaskiya Abbas Al’ameen shine farin ciki na har yanzu ina sonsa sai dai yafi ƙarfina ta ko ina, ya gujeni a lokacin da na fi kowa buƙatar sa, Soyayyar da zakayi baza’a soka ba wannan shirme ce da ɓatawa kai lokaci, bansan meyesa ba rayuwa ta juya min baya, amma abu ɗaya na sani, rabuwa da Al’ameen ko da kuwa zan mutu, na barsa har abada, ya aibata min Umma na da zargi mafi muni a rayuwa zargin fasiƙanci ya zarga min mungun tabo har yana tunanin shegiya ce ni marar uba, to me zanyi da kai Al’ameen, Allah ya isa tsakanina dakai ka cutar da rayuwata ka karya min zuciyata ta hanyar yaudararriyar soyayya meyasa kasan ban dace da rayuwar ka ba, kamin ƙwalelen zuciyarka, meyasa kamin wasa da Soyayya, hakan fa tamkar wasa da rayuwata kake, tabbas nayi wasa da rayuwata a gaɓar mutuwa, saboda kai anya kuwa zan tonawa amarya asiri, nima yaushe ka rufamin asiri da kai zan zan rufa maka, wannan shaidar gogeta zanyi Amarya taje ta cigaba da yimuku duk abinda taga dama, Al’ameen meyasa kaƙi fita ne daga zuciyata, ina sonka ina sonka, kana jina ko Al’ameen ina sonka na kasa jurewa rashin ka.”

Tayi Maganar a fili tana fashewa da kuka mai tsuma rai, Hafsa dake tsaye bakin ƙofarsu ne ta girgiza kanta tare da ƙarisowa ta zauna gefen ta.

“Al’ameen fa baya wajen nan kike neman haukacewa akansa kina Magana tamkar wadda yake kusa dake, shifa ya manta dake a rayuwarsa meyasa zaki dinga neman cutar da rayuwarki akan wanda bai damu dake ba, da ni ce ke Ablah da na juma da watsa sha’anin sa, karki manta da cewa ya zalunceki ya ci amanar ki, to meyasa zuciyarki kare ya cinyeta kin kasa mantawa dashi, haba haba! Tell me mana ki rabu dashi, Ki share hawayenki Ablah ki rungumi ƙaddararki ko wani bawa yana taka sawunsa ne bisa ƙaddara kuma dole idan santsin ƙaddararka ta kwasheka Dole sai ta kaina inda ƙaddararka take, babu makawa wannan rubutaccen alamari ne da zai faru a rayuwarki, dan haka ki manta dashi, saboda bai dace da rayuwarki ba, duk mutumin da zai aibata miki mahaifiyarki da aibatawa mafi muni a rayuwa to fa wannan mutumin ba abun a kasance tare dashi bane, ko kin manta ne da zargin mazinaciya daya yiwa Umma duk lalacewar masa tafi ƙarfin kashin shanu, Umma uwace daa ta jajurce akan ƴaƴanta, dan haka dole ki rabu dashi babu amfanin rayuwa da mutumin da bazai ga mutuncin iyayenka ba ki rabu dashi Ablah dan Allah ki nemi wanda zaiga mutumcin mahaifiyarki saboda tasha wahala daku a rayuwa akwai buƙatar ku saka mata, kuma hakan bazai yiwu ba har sai kin samu miji ba gari wanda zaisan mutuncin ta dan Allah kiyi Aure inda za’a daraja iyayenki.”

Hawaye ne ke gudu curcur a idanun Ablah dafa kafaɗar Hafsa tayi tare da cewa.

“Na sani Hafsa bazan manta da baƙar azabar da Umma tasha akanmu ba, kamata yayi na tsani Al’ameen sanda ya aibata min ita amma abun takaicin sai naji kullum ƙara sonsa nake, amma ki sani koda soyayyarsa zata kashe ni na barsa a rayuwata.”

Tayi maganar tana goge hawayenta, sun juma suna fira da Hafsa.

*****

Washegari bayan sallar azahar umma tana girki Ablah kuma tana wanke wanke, Inna Jumma da Aunty Amarya suka shigo, harda Momma da Sallama kanta Umma ta ɗaga tare da amsa sallamar tana musu lale da zuwa tabarma ta shimfida musu bayan sun gaisa ne Inna Jumma tace wa Ablah taje waje tace su Daddy su shigo, babu musu Ablah taje ta shigo dasu harda Al’ameen dasu Haidar, tabarma suma umma ta shimfida musu bayan an gama gaisawa ne Inna Jumma tayi gyaran murya tace.

“Hari kingan mu kai tsaye ko.?”

Murmushi Umma tayi.

Inna Jumma cewa tayi.

“Munzo mu baki hkr ne mu nemi afuwarki bisa cutar dake da Kabiru yayi, kuma ya amshi laifinsa, dan Allah kiyi haƙuri ki yafe masa, kuma insha Allah da kaina zanje Niger ƙauyenku na samu mahaifiyarki na gana da ita kafin ke kije.”

Umma kanta na ƙasa cike da ciwon abinda Papa ya mata a rayuwa tace.

“Ba komai Umma na yafe masa Allah ya yafemu gabaki ɗaya.”

Murmushi kowa dake wajen yayi sosai sukaji daɗin karanci da mutuntasu da Umma tayi, Papa ne yace.

“Na gode sosai Hari na gode ina Abdul yake ban gansa ba.?”

“Abdul yana makarantar kwana dake Dutsen Jar.”

Daddy ne yace.

“Hari kin mana karamci mun gode sosai, ina kuma neman alfarmar cewa, ki sake hkr akan hkr ki koma ɗakin mijinki.”

“A’a bazai yiwu ba kuyi haƙuri dan Allah, ina son nayi rayuwata ni kaɗai yanzu bana buƙatar namiji a rayuwata, sannan ina son neman tafiyar mahaifiyata bazan sake aiwatar da wani abu ba sai da shawararta.”

“Amma y….”

Inna Jumma ce ta dakatar dashi da cewa.

“Ya isa haka Amadu mubar Wannan Maganar sai daga baya, Ablah ki shirya gobe zanzo na ɗaukeki ki koma gida.”

“Inna ni bazan koma ba, nafi son zam…”

“Allah ya kaimu goben azo a ɗauketa.”

Umma ta katse maganar Ablah shuru Ablah tayi cikin jin haushin hukuncin da Umma ta yanke.

Sunji daɗin abinda umma ta musu cike da farin ciki suka koma gida.

“Haba umma bance meyasa kika yafe musu ba, amma meyasa zaki yanke hukuncin zan koma gidan su?”

“Saboda sune gatanki.”

“Amma umma y…”

“Ya isa haka na yanke hukunci idan kuma ban isa dake ba sai mu gani.”

Shuru Ablah tayi bata sake cewa komai ba tabar wajen.

Kamar yadda Sukayi alƙawarin zuwa wajen malamin malam Yusuf mai sangaya, haka sukayi tare sukaje harda Abbas da Faruq da Inna Jumma babu wanda suka sanar da abinda yake faruwa a cewar Inna Jumma sai sun karya sihirin tukunna kafin kowa ya sani, ko da sukaje sunyiwa malam bayani sosai, hakan yasa yace gobe ta aiko su Faruq su karɓi saƙo zai kwana yana aiki sannan za’ayi yanka, Faruq da kansa ya basa kuɗi suka dawo gida da addu’ar Allah ya basu Nasara.

*****

“Kinyi mamakin zuwana gidanki ko Mansura, to karkiyi mamaki domin kuwa duk wanda yaci ladar kuturu sai ya musa aski, ki faɗa min meyasa kika kashe min ƴaƴana da gangan?”

Hajiya Mansura cike da hasala tace.

“Wacce irin banzar Magana kike ne amarya kin fara kaini bango, karki bari na hasala, na kashe miki ƴaƴa ko kin kashe ƴaƴanki?”

“Oh kar na bari ki hasala ko? To ki hasala naga me zakiyi, wallahi mansura zan tona miki asiri duk duniya ta sani kece kike kashe ƴaƴan Ahmad Giwa domin kuwa kece kike kisan bani ba, kuma kin kashe ƴaƴana kin kashe masifa domin sai na saki cikin bala’in da bazaki iya fita ba.”

“Ni zaki saka a cikin bala’i, to idan ban shiga cikin bala’i ba ke zaki shiga, kuma ki jira ki gani yadda zan tona miki asiri, ki fice min daga gida kafin na miki ɗan banzan duka.”

Hajiya Mansura tayi Maganar tana riƙe kunkuminta, dariya Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Ko baki koreni ba zan fita a wannan kurkukun gidan ni da ke mu zuba muga wazai shiga masifa zaki gani .”

Tayi Maganar tana ficewa daga gidan, Hajiya Mansura kunkuminta ta riƙe cike da tashin hankali sai kuma ta saki murmushi ta furta.

“Kin min butulci Amarya kuma zaki gane kuranki Tabbas kin manta wacece Mansura ni ce nake ɗaura ki a layi amma nuna min kike ni zaki saka cikin bala’i.”

Dariya ta saka tare da cigaba da cewa.

“Kin manta da duka dukiyarki tana hanuna takaddun filayenki dana gidajenki, duk suna wajena, dan haka ki jira Heart attack da zai sameki domin kuwa zan sayar dasu na tsere da kuɗin bazan yadda nayi biyu babu ba, sai dai kiyi amma banda Mansura…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 58Aminaina Ko Ita 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×