Skip to content
Part 59 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Police aka kira sune suka ɗauketa sukayi asibiti da ita koda aka shiga da ita emargency, sim card ɗinta aka cire, numbern Mama aka kira kusan 19 miss calls bata ɗaga ba da alamu bata kusa da wayar ne ƙara duba wata numbern sukayi sukaga Ƙanwata, kira sukayi Nazifa dake zaune tana sharar ƙwalla ne ta ɗaga kiran koda taji wannan mummunan labarin a gigice ta fito ta nufi asibitin tana kiran Baba a waya, sai dai ina cikin rashin Sa’a ya ɗaga tare da cewa.

“Sorry my daughter zan shiga jirgi ne, zan wuce Lagos yanzu idan na isa zamuyi waya.”
Bai jira yaji mai zatace ba ya katse kiran tare da kashe wayar gabaki ɗaya, ƙara kira tayi a kashe, idanunta ta runtse cike da ciwon rai, ta ƙarisa asibitin bata samu ganinta ba kasancewar anyi emargency da ita zama tayi a gefe ta fashe da kuka.

Tana zaune a falo yazo ya zauna kusa da ita, miƙewa tayi zata bar wajen taji muryar sa.
“Wai meyasa kike guduna ne Ablah, dama Soyayyar ƙarya kika nuna min a baya, masoyin gaskiya baya gujewa masoyinsa saboda ƙaramin kuskure.”

“Hmmm! Duk yadda ka ɗauka haka yake, ka gaskata zuciyarka kawai amma abinda na sani shine bana sonka saboda ban dace da kai ba, ƙwarya tabi ƙwarya haka ya kamata.”
“Na yadda nayi kuskure na faɗi hakanne a lokacin da bana cikin hayyacina, amma kema kin sani kece rayuwata.”

“Bani bace Rayuwarka a saboda na tsaneka dan Allah ka ƙyale ni bana buƙatar ka a rayuwata.”

“Idan na rasaki tamkar na rasa numfashi nane ki tausaya min.”

“Hmmm! A baya ka yaudareni da kalamanka, amma a wannan lokacin daɗin zancenka bazaiyi tasiri a kaina ba, a yanzu ina da wanda nake so, kuma na tsayar da zancen Aure tsakanina dashi bana yaudara, kuma bazan yaudaresa ba Abbas shine bugun numfashi na a yanzu.”

Tayi maganar tana barin wajen, Haidar da ya taho ne ya zauna tare da miƙawa Al’ameen takadda yace.

“Gashi ka sanya hannu yanzu pa zaizo ya karɓa kayan shinkafa da za’a kai gashuwa ne motar ta gama lodi da daddare zata tashi.”

“Bazan iya saka hannun ba Haidar bana cikin yanayin daɗi.”

“Amma kasan bazai yiwu motar ta tashi ba tare da saka hannunka ba, mtsss! Wai dan Allah idan Ablah ta rabu da kai numfashin ka ne zai tsaya, Ablah kai take so har yanzu akwai Soyayyar ka cikin idanunta kai baka hango hakanne bazata iya rayuwa da wani ba idan ba kai ba to meyasa zaka ɗagawa kanka hankali.?”

“Wannan motar da zata tashi bata gabana, dole zan damu da halayyar da Ablah take nuna min, na faɗa maka cewa Abbas baya taɓa aikata alkairi dole zai sauyawa Ablah ɗabi’arta, Kuma gashi hankalinta ya koma kansa, mtsss! Ina cikin Matsala.”

“Da Abbas zai sauya mata hankali da yanzu ta tare a gidan sa, ka fahimce ni ɗan uwana, ina da tabbaci akan soyayyarka da Ablah.”
“A’a Haidar dole ne na fara raba Abbas da Ablah tukunna.”

Yayi Maganar tare da tashi yabar wajen, numfashi Haidar ya saki tare da furta.
“Har abada halinka bazai taɓa sauyawa ba Al’ameen ka cika zuciya da yawa.”

Ya furta Maganar yana tashi shima yabar wajen.

Ita kuwa zama tayi bakin bed ɗin ta tare da runtse idanunta, tabbas tana sonsa har gobe sai dai dole na nisance sa saboda gudun wulaƙanci, wayarta ta ɗaga tare da dannawa Abbas kira.

Abbas dake zaune a falonsa yayi shuru yana tunaninta ne yaji ringin ɗin wayarsa dubawa yayi yaga itace, hannu yasa ya ɗaga kiran.
“Laifin me na maka, da zaka manta dani tsawon kwanaki.”

Numfashi ya saki, tare da ɗan cije leɓensa yace.

“Laifi kuma Ablah, ni kuwa wani laifi zaki min, kawai bana jin dadi ne kwana biyun nan.”
“Baka iya ƙarya ba, shiyasa ma idan kayi ake ganeka, cemin zakayi ka gujeni ne saboda na maka tayin ka aureni, a yayin da kai kuma kake ganin cewa ban dace da rayuwarka ba, kai ɗan masu hali ne, ni kuma ƴar marassa hali, kayi hkr bisa wannan kuskuren da nayi, na haɗa kaina da naka na manta cewa kafi ƙarfina.”

Runtse idanunsa Abbas yayi yana jin wani irin ƙuna da raɗaɗin soyayyarta, ce mata yayi.

“Hmmm! Ablah kenan, banfi ƙarfinki ba, sai dai ma kece kikafi ƙarfina, ki fahimceni Ablah da ace babu Al’ameen a cikin Rayuwarki zanyi maraba da ke, domin kuwa ke macece wacce ko wani Family zaiyi maraba da shigarki cikin su, Al’ameen ya fini dacewa daya mallakeki kuma kema shi zuciyarki ke so, meyasa bazaki fahimcesa ba, Ablah yana da kyau duk laifin da mutum ya mana idan ya tuba kuma yayi nadama mu tsaya mu fahimcesa muji menene uzurinsa wani dalili yasa ya mana laifi, a soyayya dole akwai saɓawa, yana dakya Idan mun saɓa kuma mu gyara,dan Allah ki saurari Al’ameen koda na minti biyar ne nasan zaki fahimcesa ni ƙanwa na ɗaukeki Ablah.”

Idanunta ta runtse cike da takaicin abinda Al’ameen ya faɗa akan Umma tace.

“Bazan taɓa tsayawa na sauraresa ba, bare na fahimcesa na faɗa maka cewa na ciresa daga cikin rayuwata, kai nake so, idan har baka son na shiga wani hali to ka amince da aurena.”

Tayi Maganar tare da katse kiran, numfashi Abbas ya saki yana dafe kansa, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ya janye jikinsa daga gareta a wannan kwanakin, saboda tarayyar sa da ita zaisa ya iya amincewa da bukatar ta, yayin da hakan zai zame masa kuskure, text ya gani ya shigo cikin wayarsa dubawa yayi tare da karantawa.

“JAMILA TA WATSAWA NAFEESA ACID A FUSKARTA, FUSKARTA TAYI DAMAGE KUMA JAMILA TA GUDU YAYIN DA ITA KUMA NAFEESA KE GADON ASIBITIN ST KUMA ANA BUƘATAR KUƊI KIMANIN DUBU ƊARI ZA’A MATA AIKI MAHAIFINTA YACE BASHI DASHI, MAHAIFIYARTA KUMA DA ƳAR UWARTA BASU DA WANNAN KUƊIN WANNAN MASIFAR TA FARU NE SABODA KAI, KAINE KA HAƊA WUTAR DA TA KAMA DAN HAKA YA KAMATA KAZO KA CECI RAYUWARTA KA BIYA KUƊI A MATA AIKI TUNDA KANA DASHI.

Numfashi Abbas ya sauƙe tare da dafe kansa, wayar Faruq ya kira suna zaune tare da Haidar ɗaga wayar yayi daga can Abbas yace.

“Faruq akwai matsala fa.”

“Matsala kuma Abbas, wacce irin matsala?”
“Bari na maka forwarding ɗin message ɗin da aka turo min, idan ka karanta sai ka kirani.”
“Okay to shikenan.”

Katse wayar yayi bai juma da katse kiran ba, sai ga text ɗin ya shigo zaro idanunsa Faruq yayi tare da cewa.

“Haidar karanta ka gani.”

Amsa yayi ya karanta tare da duban Faruq yayi shuru na wasu mintuna kafin yace.
“Allah mai yadda yaso, lallai kaji tsoron haƙƙin wani, Faruq wannan dama ce mai kyau da muke da ita na rama cin amanar da Nafeesa ta mana.”

“Ban fahimta ba, wacce Irin dama kenan.”

“Faruq ni zan biya kuɗi a yiwa Nafeesa visa zuwa Indiya ina son a sauya mata fuska, fuska mafi muni ma’ana mummunar fuska wacce kowa zai ƙyamace idan ya kalleta ta kuma ji tsanar kanta idan ta dubi madubi so nake naga rayuwar Nafeesa ta tozarta.”

Faruq kansa ya girgiza domin kuwa shi harga Allah Nafeesa ta basa tausayi.

“Haidar wannan ba mafita bace mai ɓullewa, idan ka barta da wannan tabo na damage ɗin fuskar ma ya isheta baƙin ciki saboda babu wata fuska da za’a samata wacce zatafi damage ɗin da tayi muni, shawara ɗaya nake da ita itace mu biya kuɗin jinyar ta saboda ta rayu taga baƙin ciki domin kuwa na Tabbata ta dinga kuka kenan har ƙarshen rayuwarta duk sanda ta dubi mirror taga yadda kamannunta suka sauya wannan shine tabon da zai sata cikin baƙin ciki.”

“Ka kawo shawara mai kyau amma babu mai biya mata kuɗin jinya daga kai har Abbas,ku barta ta wahala kamar yadda ta wahalar damu.”

“Shikenan ba damuwa bara na kira Abbas ɗin sai mu haɗu da yamma mu tattauna bara naje Company.”

Cewar Faruq shima Haidar tashi yayi tare da cewa.

“Okay sai ka dawo Bara nima naje cikin gida.”

Koda Haidar ya shiga falon Momma ya samu zaune zai haura ta kira sunansa dawowa yayi ya zauna gefenta tare da cewa.

“Gani”

“Aliyu ya muke ciki da maganarka da Rufaida har yanzu kana kan bakar ka ne na bazaka aureta ba.”

Numfashi Haidar ya saki cikin sanyin jiki yace.

“Momma na amince da zaɓin ku, a domin na fahimci rayuwa, na yadda Rufaida itace alkairi a gareni, ta juma tana fama da ciwon sona ni ne shaidar haka, zuwa yanzu ya kamata na nuna mata kulawa ki gafarce ni Momma na ƙoƙarin biremiki da nayi akan wata shasha.”

Murmushi Momma tayi cike da farin ciki ta jawosa jikinta ta saki dariya tace.

“Alhamdulillah! Kai naji daɗi sosai Aliyu, tun da nake ban taɓa jin farin ciki irin na yau ba, ga kuma kyakkyawan albishir, ƙanwarka Madina itama iyayen Mussadiq zasu turo tambaya gaskiya yau ina cikin farin ciki yarana zasu girma.”

Dariya Haidar yayi tare da cewa.

“Masha Allah! Hakanma yamin domin kuwa Mussadiq ɗan gidan mutunci ne, bara na haura sama.”

Yayi Maganar tare da tashi ya haura Momma murmushi tayi cike da ƙaunar yaran nata.
A bedroom ɗinsa ya samu Rufaida tana gyara masa, ganinsa ya sata ɗan tsorata gudun masifarsa, ijiye glass flowers ɗin da ta ɗaga tayi tare da ɗaukar mopper ɗin zata fita taji muryar sa.

“Rufaida ina zakije baki ƙarisa abinda ya kawoki ba.”

Cak ta tsaya cike da mamakin Haidar yana mata Magana cikin taushin murya ba tare da faɗa ba.

“Zanje falo ne idan ka fito sai nazo na ƙarisa.”
Murmushi yayi tare da cewa.

“Dawo ki zauna muyi magana.”

Babu musu ta dawo ta zauna gefe dubanta yayi tare da kiran sunanta cikin cool voice yace.

“Rufaida ina sonki.”

Cike da mamaki ta ɗago idanunta da sauri ta kallesa, kansa ya ɗaga mata alamun ehhh yana sonta, sunkuyar da kanta tayi tana jin kamar mafarki amma har cikin zuciyarta sanyi takeji tamkar ta tashi ta taka rawa, murmushi tayi Haidar ya cigaba da cewa.

“A baya nine abokin shawaranki kina faɗa min dukkan damuwarki na kawo miki solution, sai saɓani da rashin fahimta ya shiga tsakanin mu lokacin da kike min son maso wani, Rufaida a yanzu na gane kuskurena kuma na gane cewa kece mai sona tsakani da Allah da bazaki cutar dani ba KOMAI tsanani, ina roƙonki afuwa ki yafe min ƙuntata miki da nayi, sannan ki cigaba da ɗaukata a matsayin wanda zaki faɗawa dukkan damuwarki, ina sonki zan aureki Rufaida na shiryawa hakan ina fatan zan samu kulawa daga gareki.”

Dariya mai haɗe da hawaye Rufaida tayi ta ɗago ta kallesa tare da cewa.

“Yaya Haidar ban taɓa kullatan ka ba a raina kullum cikin jira da tsammanin zaka soni nake, ko yaushe ina cikin tunaninka da begenka, na godewa Allah daya nuna min ranar da ka furta min kalmar so ina sonka fiye da komai a rayuwata yaya Haidar.”

Dariya Haidar yayi tare da cewa.

“Daga yanzu damuwarki ta kare saboda yayanki kuma mijinki zai kore duk wata damuwarki umm kin samin idanu kina kallona ko irin kunyar nan babu ko dai kallon Soyayya ce.”

Dariya Rufaida tasa tare da tashi da gudu tabar bedroom ɗin murmushi Haidar yayi tare da kwanciya yana runtse idanunsa, tabbas yana ɗan jin Soyayyarta zai dage wajen ganin ya bata kulawa domin kuwa ko ba komai ta mace a Soyayyarsa.

*****

Hajiya Mansura duk ta haɗe kadara da Aunty Amarya ta bata ijiyar sa ta saida, ba ƙananan kuɗaɗe ta haɗa ba, kuɗine na kerewa sa’a sanda ta gama saidawa ta je ta yanki visa zuwa ƙasar china, a cikin kwana biyu ta tsallake tabar ƙasar domin kuwa tabbas tasan idan ba haka tayi ba zata rashi ne a zero, abinda ita Amarya bata sani ba kenan barin Hajiya Mansura Nigeria, ita duk a haukarta zataje ta amshi kuɗaɗen ta.

Daddy yana zaune gefen Aunty Amarya Haidar ya shigo da kuɗaɗe a cikin jaka, gefe ya samu ya zauna tare da cewa Daddy.
“Daddy ga kuɗin, naso na sanya a banki, to dare yayi amma insha Allah gobe da sassafe sai na kaisa.”

“Okay ba damuwa ni anjuma jirgin mu zai sauƙa a kaduna muna da meeting so ka shiga da kuɗin cikin bedroom ɗina ka ijiye a cikin drower ko bana nan goben sai kaje ka kai bankin, ka tabbatar ya cika 10b ɗin.”
“Ehh Daddy ya cika Bara na je na ijiye.”
Yayi Maganar yana miƙewa ya shige bedroom ɗin Daddy ya ijiye kuɗin.
Al’ameen ne dake tsaye jikin step ɗin yana sauraronsu ne ya sakarwa Haidar murmushi tare da binsa room ɗin Daddyn.

Da misalin takwas na dare Daddy jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa kaduna.

Aunty Amarya kasa nutsuwa tayi ganin wannan kuɗin tunani tayi kawai gara ta sace kuɗin, kiran Abbakar Jibo tayi tace ya tsaya a first get ɗinsu, ɗaya na dare zata kirasa ta basa saƙo, harta kashe wayar tayi tunanin gara ta sanar dashi, ƙara kiransa tayi tare da cewa.

“Jibo kuɗi ne zan baka ka fita min dashi, zuwa sansanin ka, da safe zanzo na amsa na yadda da kai yasa zan baka wannan amanar, sannan kana da tukwici Naira dubu ɗari, karka ci amanata jibo.”

“Hajiya ai kema kinsan babu cin amana tsakanin mu karki damu.”

“Shikenan Jibo ka jirani.”

Tayi Maganar tare da katse kiran.

Da misalin ƙarfe ɗaya ta fito kasancewar ta tabbatar da cewa kowa yayi bacci ya sata fitowa ta nufi bedroom ɗin Daddy shuru kowa yayi bacci sai ƙarar ac kawai dake tashi, kuɗin ta ɗauko a jakar ta fito siɗi siɗi Ablah da ta fito ɗiban ruwa taga fitarta da sauri Ablah tabi bayan ta ganin ta fita can waje yasa Ablah cigaba da bin bayanta, har first get maƙalewa tayi a jikin bango tana kallon ikon Allah, mai gadi taga ta tasa, sun ɗan juma suna magana da mai gadi wanda batasan me suke cewa ba kafin ya buɗe mata ƙofa daga inda Ablah ke tsaye take hango Aunty Amarya, hasken mota aka dallara da sauri Ablah ta siɗaɗe ta fita, ta ƙara maƙalewa jikin motar, video Ablah ta danna tana ɗaukar su, motar mutumin ya shiga ya rufe Aunty Amarya ta juyo ciki da sauri Ablah ta shigo itama duk ba wanda ya lura da ita cikin su, har sunzo cikin falo, Taji muryar Ablah.

“Aikinki yana kyau Aunty Amarya.”
A gigice ta juyo tana kallon Ablah cike da mungun tsoro.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 61Aminaina Ko Ita 63 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×