Dafin So
Kano, 2015
Ƙarar fashewar tangaraye da gilasai kawai kake ji da ka doso kofar gidan. Da sassarfa 'yar kututturar matar ta ƙarasa cikin falon, sai dai, da sa ƙafarta wani abu mai kama da tsinin wuƙa ya caketa, wanda ya sa ta sakin ƙara da komawa baya.
Falon ta shiga ƙarewa kallo, tun daga TV ta bango, har kwalabe na aje flowers ba a bar su da ransu ba. An lalata komai kamar yadda rayuwar mamallakiyar gidan ke a lalace. Da ƙyar ta samu damar kauda wanda idonta ya gane mata, wani kuma. . .
Lalle wannna shine reza cakwakwiya