Skip to content
Part 1 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Dafin So

Kano, 2015

Ƙarar fashewar tangaraye da gilasai kawai kake ji da ka doso kofar gidan. Da sassarfa ‘yar kututturar matar ta ƙarasa cikin falon, sai dai, da sa ƙafarta wani abu mai kama da tsinin wuƙa ya caketa, wanda ya sa ta sakin ƙara da komawa baya.

Falon ta shiga ƙarewa kallo, tun daga TV ta bango, har kwalabe na aje flowers ba a bar su da ransu ba. An lalata komai kamar yadda rayuwar mamallakiyar gidan ke a lalace. Da ƙyar ta samu damar kauda wanda idonta ya gane mata, wani kuma ya soketa, a haka ta ƙarasa cikin ɗakin da ƙarar tafi yawa. Sai dai, da kutsawarta ta samu na ta rabon a goshi da wata babbar kwalbar turare da aka jefo.

Ba ta kula ba, haka nan ta ƙarasa tana mai cukwikwiyeta cike da son rarrashi, “Haba mana Asabe, wane irin rashin hankali ne wannan da za ki ɓata rayuwarki kan abin da bai fi ki take da ƙafarki ba. Na ce miki ki yi haƙuri, Ni zan ɗau duk irin matakin da kike so kan lamarin.

“Ki ga dai zambar da Fakriyya ta yi min kike cewa na yi haƙuri? Ni ce yake so, ni ce ya yi ma alƙawarin aure, haka ni ke wanzuwa a dukkan mafarkinsa, me ya sa Hamoudi ya yi haka? Wane irin abinci ne ban ci da Fakriyya ba? Shin ban cancanci ta duba girman hakan ba? Akwai ƙaunar da tafi ka ci abinci kwano guda da mutum? Menene ta fi ni, ki gaya min me Fakriyya za ta nuna min da Hamoudi zai zambace ni?” Ta faɗa tana mai jijjiga matar cikin tashin hankali marar lissafi.

“Bari ki ga abin da Fakriyya ta fi ki.”

Ta furta tana jawo hannunta zuwa gaban tangamemen Mudubin ɗakin da ya rage da rai. Kalli fuskarki da kyau ki ga abin da kike da shi wanda Fakriyya za ta iya cin kowacce irin nasara a kanki Reza!”

Zuru ta yiwa Madubin tana ƙarewa halittar fuskarta kallo. Babu wani abu mai kyau a fuskarta idan ka ɗauke idanuwan da ƙaramin bakin. Idan ana hudar kunne guda bakwai, to ita bayan bakwai na kunne, gefen bakinta daga saman haɓa barima ce, haka saman girarta akwai barima, ga ta hanci guda. Kallo guda za ka ma ta ka gane tantiriyar yar bariki ce ta bada labari.”

“To wannan kamalar da babu a fuskarki ita Fakriyya za ta gwada miki duk da idan lalata ce ba za ki gwada ma ta ba. ASABE ba kya jin magana ko misƙala zarratin, idan da kina ji da ba mu zo nan gurin ba. Sau nawa na ce ki cire tarkacen fuskarki alama ce ta mashaya jini kika ki? Sau nawa na ce miki babu wani namiji a duniya mai son zaman lafiya da zai aure ki a wannan halin.” Cikin karaya da dukkan rayuwar take dubanta.

“Shi ya ce yana so, shi ya hanani cirewa, zan rantse miki da Allah Hamoudi shi ya ce kar na cire, ya fi so na haka…”

“Ƙarya yake miki baya sonki Asabe! Ki shiga hankalinki Hamoudi bai taɓa sonki ba. Haka bai taɓa burin kasancewa dake ba! Ki gane wannan shirin makirci ne da aka dade ana kitsa shi. Shi Jakin ina ne da zai auri macen da ta yiwa ubansa sata ko da ta Sule Biyar ce?”

Tarwatsewar madubin da suke gabansa ne ya sakata yin tsit! Tana duban Asabe da jikinta ke tsuma, gashin kanta ya yi cirko-cirko a sama tamkar Bushiyar da ta hangi silalowar Maciji bakin raminta. Yankin madubin mai tsini ta riƙe a hannunta cikin rashin hayyaci.

“Ki ka ƙara cewa Hamoudi baya so na, sai na kashe ki SOUFY, na kashe kaina! Wallahi yana so na shi ya faɗa min. Wannan menene idan ba so ba?” Ta faɗa tana jawo wasu tulin cards dake gefe duk na wasiƙun soyayya.

“Taho ki ga nan” ta ja ta zuwa ma’ajiyar kayanta. Nan ta shiga fiddo da wasu dogayen riguna, “na ce wannan uban menene idan ba so ba? Waya ba Ni su idan ba Shi ba?” Tamkar mahaukaciya haka ta shiga yin ɗai-dai da duk wani abu da Hamoudi ya taɓa ba ta.

“Ɓacin ran da kike tarawa kanki shi ne damuwata ni. Mafita ɗaya ce yanzu ki shirya su Disco su je su sato miki shi, Ni da kaina zan baki addar da za ki daddatsa shegs….”

Ƙum! Ji kake iron ya haɗu da haƙoran Soufy. Nan da nan jini ya fara wanke bakin, baya ta soma yi tana duban Reza cike da wani irin mamaki, ba ta taɓa tunanin duk zarewarta za ta iya bugunta ba, ita da ta ci kashi da fitsarinta. Ita da ta ma ta riƙon da ko uwarta ba za ta iya shi ba.

A hankali take tahowa gareta har sai da ta haɗata da bango ta hanyar tokareta da dukkan hannuwanta. Cikin sanyi ta fara magana.

“Ba ki san duk wani fitar numfashin Hamoudi ina jinsa a nawa Ruhin ba? Ya daɗe da sace min dukkan wani numfashin da nake shaƙa a duniya. Dan shi ki ke ci gaba da ganina cikin wannan rayuwa da har kike iya duban tsabar idona kina cewa a kashe shi. Kin taɓa tambayata me nake yi da cinnakan da nake ɗauka ina sawa cikin rigata ko? To yau za ki ji amsar, ina sa cinnaka a rigata ne saboda ya ciji Hamoudi, Ni kuma ba zan iya nutsuwa ba sai na sa shi Ni ma ya cije Ni, domin in ji irin raɗaɗin da ya ji. Wannan ƙunar da kike gani a cinyata kike neman sanadin samuwarta, to, bari ki ji ta yau. Ruwan zafi ne ya ƙona Hamoudi, shi ya sa Ni ma na ɗora garwashi a cinyata dan na ji irin raɗaɗin da ya ji. Ina son Hamoudi, irin son da ba nawa wani a duniyar nan, ba nawa ubana, haka ba nawa uban da ya haifi ubana! Ina son Hamoudi son da ko gawarsa babu wani limami ko malami da ya isa ya rabani da ita, na gwammace na zauna da ita idan za ta ruɓe mu ruɓe tare!”

A hankali kuma ta sulale ƙasa tana mai fasa wata irin ƙara, da sauri kuma ta sake miƙewa tana Jijjiga Soupy da ta daɗe da sandarewa.

“Idan har dan munyi fashi a gidansu ne zai rama ta hanyar sace dukkan numfashina, shin wa ce ce jagorar tafiyar?”

“Fakriyya.”

Soupy ta faɗi yayin da wani danshi-danshi ke saukowa tsakanin ƙafafuwanta.

Asabe Reza 2 >>

1 thought on “Asabe Reza 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×