Hamoud
Ya mula ya ƙara mulawa, ya ja tsaki fiye da cikin carbi yana mamakin yadda aka shanya shi.
Ba dan abin da ya kawo shi ya girmi duk wani abu da ke rayuwarsa ba, da sai ya nuna mata ƙaramar shegiya ce ita.
Duba time ya ƙara yi yaga gab ake da kiran sallah, miƙewa ya yi cikin fushi yana kewaye farfajiyar gidan, a haka idanuwansa suka sauka kan wata tukunyar flower, ya sa ƙafa ya dake ta, sai da ta yi ɗai-ɗai a gurin.
"Sai ka biya ai, tunda ba na gidanku ba ne. . .