Skip to content
Part 16 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

Hamoud

Ya mula ya ƙara mulawa, ya ja tsaki fiye da cikin carbi yana mamakin yadda aka shanya shi.

Ba dan abin da ya kawo shi ya girmi duk wani abu da ke rayuwarsa ba, da sai ya nuna mata ƙaramar shegiya ce ita.

Duba time ya ƙara yi yaga gab ake da kiran sallah, miƙewa ya yi cikin fushi yana kewaye farfajiyar gidan, a haka idanuwansa suka sauka kan wata tukunyar flower, ya sa ƙafa ya dake ta, sai da ta yi ɗai-ɗai a gurin.

“Sai ka biya ai, tunda ba na gidanku ba ne, idan ba ka iya jiran wa ya saka zama?”

Ya ji sautinta, da ƙamshinta da ya rasa dalilinsa na zama cikin ruhinsa a tun ranar da ya ganta gurin walimar, tana ta ihun ya yaudareta.

Ya juyo yana kallonta, tana tsaye ta rungume hannayenta a kirji. Tabbas tana da kyau daidai nata, bai ma san dame Fakriyya ta fita anan ba.

Ƙarasowa ya yi gabanta shi ma ya tsaya.
A cikin idanuwansa take hango ɓacin ran da yake ƙoƙarin ɓoyewa.

“Oh, kin gama barcin ke nan? To ya yi kyau, dama zuwa na yi na tambayeki inda kika Sanni har muka yi soyayya?

“Ni…?”

Ta furta tana yatsine fuska.

“Kai ba na tunanin na taɓa ganinka ma, kamar dai kamin kama da wani da na taɓa gani ranar walimar kawata, me kake so gurina?”

Wani murmushi ya kuɓce ta gefen bakinsa, gyara tsayuwarsa ya yi yana jinjina rainin hankali irin nata.
“Oh, ashe bake ba ce, Ni ma yanzu na kula da hakan. Waccar ɗin da nake nema akwai alamun taɓin hankali cikin kwakwalwarta.”

Ya furta, yana tsareta da manyan idanuwansa domin yaga yanayinta.

Ƙanƙance idanuwanta ta yi, ta ƙara takunta zuwa gabansa, ta tsaya a tsayinsa da ya ƙere nata, tana watsa masa harara.

“Oh, ashe kwatancen asabitin da take kake nema, za ka iya duba duk wani Psychiatry dake fadin ƙasar nan ko za ka da ce da ganinta a can, nan kam ba mu da mahaukata, ban dai sani ba ko mahaukaci ne ke da ikon gane ɗan uwansa mahaukaci. Shi ya sa kake tunanin akwai masu faɗa.

Ta furta tana juyawa akan takunta dake cike da rangwaɗa, tana ƙokarin bar masa wurin.

Fisgota ya yi gaba ɗaya, takalminta ya kwasheta ta faɗa jikinsa. Ɗago da ita ya yi yana damƙe kafaɗunta, da idanuwansa da suka rikiɗe zuwa ja yake watsa mata kalmomin.

“Ke kinsan kinyi kaɗan ɗin ki dubi tsabar idona ki ce mini mahaukaci, amma ba zan kula ki ba, saboda girman abin da ya sa ni zuwa gareki bai cancanci na tsaya ɓata lokacina ga halittar da bata aje komai ba sai saɓon Allah. Ki tsaya ki saurareni!”

“Ashe ba daɗi.”

Ta furta tana kwace jikinta daga nasa.

“To ai sai ka zauna, na ji abin da ka zo neman, ban faye jure tsayuwa da baƙaƙen mutane irinku ba, kana ɓata min zuciya na ji kamar zanyi amai, Please dama za ka rufe idanuwanka da baƙin gilas, da na samu nutsuwar saurararka.”

Ta furta, tana takawa zuwa wurin kujerun, ta zauna tana jijjiga kafafuwa.

Shi ma biyo ta ya yi ba tare da ya kula da maganganunta ba, abu ɗaya ya sani, duk bala’inta ba za ta kai ko rabin sa a kyawu ba.

A haka ya zauna yana sauke numfashin ɓacin ran da ta haddasa masa.

“Aurenki na zo nema, ina neman amincewarki ayi shi a satin nan.”

“Ko? Wane irin aure ke nan?”

Ta furta da halin ko in kula, duk da cewa kalaman sun doketa, bata yi tunanin da haka ya zo ba.

“Aure dai, wanda ake taruwa a masallaci ko ƙofar gida a ɗaura.”

Ya furta, da yanayin rainin hankalin da ta tambaya.
“Okay, sai yanzu na gane. Ashe dai mutum zai iya aurar wadda ta yi sata a cikin gidansu? Sorry fa, abin ne da mamaki.”

“Babu mamaki, idan shi auran bai kai zuci ba, za a yine kawai domin cimma wani buri na rayuwa.”

“Oh, Auren wucin gadi ke nan, tunda babu soyayya, babu niyyar zama tare.”

“Haka nake nufi, zan kuma baki duk wani abu da kike buƙata, fatana ki yadda muyi auren, na yi alƙawarin rabuwa dake a duk lokacin da kika buƙata.”

Ya furta yana murmushi.

“Fakriyya fa?”

“Tana gidansu, a tun lokacin da kika ba ni wannan hotan…”

Ya furta yana danne abin da ke taso masa.
“Oh sai ka ce auren huce haushi za ka yi da ni.”

“…Akwai abubuwa masu tarin yawa da nake son tambayarki, kinki ba Ni damar hakan.”

“Bana buƙata ne, kai ina kai ina tsayawa doguwar hira da karuwa? Game kuma da auren, zanyi tunani.”
“Tunani kuma?”

“Eh, ko ban isa yi ba ne?”
“No, kawai kin ɗauren kaine, kamar ba ke kike ikirarin kina so na ba?”

“Hakanan kan naka zai ci gaba da ɗauruwa, kamar dai ka manta harufan da ka zano mini ka umarce ne da na barsu su zauna a kwakwalwata, to na bar sun, na aje su wurin da ba za su taɓa gogewa ba komai nisan zamani. Har a cikin jijiyoyin jikina ina jin yadda sunan ke tafiya da jinin da ke zagaye dasu.”

“Haisam!”

Ya furta yana jin sunan na haddasa masa wani yanayi a kirjinsa.

“Amma kinsan idan har za ki zama matata dole sunan ko wane mutum ya fita daga bakinki ko.”

“Idan ka ga na aure kan ke nan wannan dokar za ta hau kai na ko? Ba ma wannan ba, ba na tunanin akwai abin da zai hanani ambaton Haisam. Yanzu haka da na ce maka zanyi tunani, ina nufin sai na yi shawara da shi, idan ya yarda, tukunna na aure kan.”

“REZA!!!”

Ya furta cike da gargaɗi yana miƙewa.

“QURAISHA sunana, ina jiye maka tsoron ranar da za ka furtawa mahaifiyarka sunan REZA a matsayin na matar da za ka aura. Ba za ta taɓa yarda ba ne. Dan haka ka riƙe sunan, ka barshi ya zauna a cikin hamshaƙiyar kwakwalwarka.”

Ta furta, tana miƙewa ita ma.

Huci ya yi yana kallonta, yarinya ƙarama tana ƙoƙarin haddasa masa ciwon kan da ya fi na jiya zafi.

“Zan wuce naga har an fito sallah, gobe zan dawo na ji abin da kika yanke.”

Shiru ta yi tana ji a jikinta kamar ana kallonta, ɗaga kanta sama ta yi saitin windown da yake da tazara sosai a tsakaninsu, tabbas ana iya hango su, ita ce dai bata iya hango wanda ke tsaye jikin tagar.

‘Fakriyya’ Ta furta a ƙasan ranta.

Wani murmushi ta yi ta matsa jikinsa.

Ji ya yi kawai ta riƙe masa hannu.

“Ana kallonmu, amma karka waiga, idan kana so wasan ya yi kyau dole ka haɗa makaman ta da hankalin maƙiyi. Ina da buri kan Fakriyya, kai ma kana da, ina tunanin haɗin zai iya yiwuwa.

Muje na ɗan taka maka.”

Ta furta tana jansa, kamar wanda aka cire ma laka haka yake sauke duk wani takunsa akan nata.

Hannunsu cikin na juna haka suke takawa, sun dace, ƙarshen dacewa. Ta gefen ido ta hangota laɓe ta ɗan buɗe gate ɗin tana kallonsu.

“Ka yi duk abin da ya zo maka, gata nan laɓe tana kallonmu.”

Murmushi ya yi ya zare hannunsa daga nata, ya saƙalo ƙugunta ta baya, a haka suka ci gaba da takawa suna faɗawa junansu baƙaƙen maganganu, har suka isa motar.

Dawowa ta yi, ta zo daidai motar Gayen da yama Hamoud kwatance, ta ji abu ya fashe kamar kwalba, da sauri ta ƙarasa gare shi ta tare shi, ganin zai faɗi saman wani dutse.

“Keee da Allah malama cika Ni, ke baki san na tsani duk wata mace ba, dilla kauce.”

“Na sani, ina gidanku na kaika, nan unguwar dare ya yi yanka mutane ake.”

“Gidaaaa, ina nema gidanmu? Idannn aka yankaaaaani me damuwarki? Kauce dillah, Ni fa idona idon wata mace sai na fille mata kai…”

“Oh God!”

Ta furta tana ƙara riƙe shi ganin za su zube, haka kawai ta ji ba za ta iya barinsa a wannan halin ba, matashi ne sosai da bai gaza shekaru Talatin Da Hudu ba(34), bai yi ma kalar lalatattu ba a yanayinsa.

“To muje ka kwanta gidanmu, gobe sai ka tafi, ina key ɗin motar taka a rufe.”

Ta furta tana saƙalo hannunsa a kafaɗarta.
“Mota? Hahaha, ke amma makauniya ce ko, wannan ce motar…?”

Ya furta yana dukan motar da ƙafa.

“Wannan ai dutse ne da na aje kwalaben lemuna irin wannan.”

“Na sani ai, kawo abin da za a rufe ma dutsen.”
Da ƙyar ta gano key ɗin ta rufe motar.

Ƙara riƙo shi ta yi suka fara tafiya a hankali.

“Me sunan ka ne?”

“Niiiiii? ko Mu…Hammad, kaiii na tuna, ɗan Alhaji ake ce mini, wai Ni din nan da nake ɗan Alhaji, wai uwata ta mara kan sai na auri ƙanwata, ƙanwata fa da muke uwa ɗaya uba ɗaya…Alhaji ma ya zo yana ɗaga min murya wai na masa sataaa, wai dama Ni ba ɗansa ba ne, na gado halin uwata da ta kashe ubana ta guduuuuu. Ke kinji kyautawa a zancen nan?”
“A’a basu kyauta ba.”

“To Ni bantaɓa sata ba, yamaaa za ai na ɗaukarwa mahaifina abunsa, kawai wani ne ya min sharri, kuma ina zaton uwata ce ta mini, ke kema fa da kike riƙe da Ni ba wai barinki zanyi ba, muna isa inda za ki kaini, zan fille miki kai.”

“Na sani ai, kwalba nawa kasha ne?”

“Za ki sha ne kema? Duka-duka fa kwalba uku na sha,”

“Muje to nama asir ɗin lemon ka sha.”

Da haka ya yi shiru suka ƙarasa cikin gidan.

FAKRIYYA

Kuka take mai cin rai, yayin da wani ƙulli ya tokare mata a wuyanta, ɗaci take ji cikin zuciyarta, gefe guda kuma numfashinta ke ƙoƙarin sarƙewa.

Da ta san zata yi irin wannan mugun ganin, da babu dalilin da zai sa ta buɗe windown, harma ta biyo su nan bakin gate tana kallonsu.

So take ta san yadda Hamoudi ya zo gidansu Reza har ya shafe waɗannan lokutan tare da ita. So take ta san yadda Hamoudi zai iya jan Reza cikin jikinshi duk irin tsantsanin da ta san yana da shi.

Tunanin take ita kanta tana jin tsoron amsar tambayarta, tana hango girman abin da zai faru gareta idan ya zamana hasashen dake tsungulin wani sashi na zuciyarta gaskiya ne.

Ta sani, babu wani guri da ya saura a zuciyar Hamoudi da bata gama cike shi ba, sai dai tana tsoro, tsoron dake jefa zuciyarta hali na karaya. Ta san Reza fiye da duk wata halittar dake tare da ita, tana da wata baiwa mai girman da take iya mamaye zuciyar duk wani da zai kusance ta. Da wannan kawai  za ta iya finta gurin Hamoudi, za ta iya samun soyayyarsa ta gaskiya wacce ba a surka da taimakon wani abin halittar ba. Ba kamar ta ta da silar samun soyayyar, KWALLI NE.

Juyawa ta yi ta koma cikin gidan tana dafe kirjinta da take jin tamkar zai rabe dan zugi, a falon ta tadda Linda, ta wuce ta kawai zuwa cikin ɗakinta.

Da kallo ta bi ta, kafin kuma ta miƙe tana rufa mata baya.

“Sai da na ce karki fita Ree, me ya sa ne haka? Kin sani na yi girman da a kowane
lokaci jinina zai iya hawa ni ma ki rasa ni, ba na son damuwarki Ree, ba na son ganin hawayen nan da kike kwana kina yini da su kan abin da bai fi ƙarfinmu ba. Idan damuwar za ki cigaba da yi kizo muje inda za a zare miki soyayyarsa, ki manta kin taɓa sanin ko da mai sunansa ne.”

Ta furta, tana jawota, ta ɗora kanta saman cinyoyinta.
Zame wa ta yi a hankali ta tashi zaune tana girgiza kanta cikin hawayen da ta kasa  tsaida zubarsu.

“Ba so nake in bar sonsa ba, ba so nake in daina jinsa a ruhin da ya gama aminta yana ci gaba da rayuwa ne dominsa. So nake kawai na same shi koma ta ya ya ne, so nake na hana zuciyarsa yarda da duk wata ɗiya mace idan ba Ni ba. Da Reza fa na ganshi Linda?A kan idanuwana ya jata cikin jikinsa. Kin sani, ko a can baya bana taɓa kusantar duk wani da ya yi mu’amala da Reza, balle yanzu da take ikirarin tana son MIJINA, so fa da aure irin wanda nake masa? ya ya kike so na tari wannan lamarin? Ya ya kike so zuciyata ta amshi abin da ko da wasa bai zo hankalina ba?”

Numfashi ta ja ta furzar da zazzafar iska, kallonta take tana hango yadda lamarin nasu zai kasance. Matsawa ta yi tana lalubar kunnenta, a cikinsu ta furta mata abin da ya sa ta ɗagowa da sauri tana dubanta da tsantsar mamaki.

“Kwarai kuwa, ba dai Reza ce ba ki so ta aure shi ba? To abin da na gaya miki shi ne mafitar, dole a fara raba shi da ita, kafin ma ayi tunanin zamanku taren. Idan bai yiwu ba, sai a taɓa sauran biyun. Na tabbata ma zai yi duk wani abu da kike so, dole ya yarda ya zauna da ke ki juya shi tamkar bawa da ubangidansa…”

“Amma ina za a samu takaddun? Ya za mu yi da ɗumbin jama’ar da suke da shaida kanshi? Ya za mu yi idan iyayensa suka tsaya tsayin daka kan batun? Wannan abu ne mai girman da ba zai yiwu ba. Zuciyoyin mutane sama da bakwai kike so mu ɓata akan mutum guda? Idan ba so kike mu ƙara lalata komai ba, to a bar wannan batun.”

Miƙewa ta yi da murmushi, ta rungume hannuwanta a ƙirji tana juya mata baya.

“Lalle soyayya ta gama toshe tunaninki Ree, ya za ai na furta miki waɗannan kalmomin ban gama samun duk wani abu da nake so ba. Wai ma tambayata kike ina za mu samu takaddun? Kamar dai kin manta wacece ke? Kamar dai kin manta duk wani abu da za mu iya yi. Kamar dai kina son nuna min tausayinsa ya fi soyayyarsa tasiri a zuciyarki? Ina faɗa miki, hatta mahaifiyarsa sai ta yi ruɗewar da za ta gaza gane

, balle ma ta fahimci lamarin.”

“Aww! Na gane. Hmm, taɓdijam! Amma fa Linda kin shammace Ni, sai na ji ma kamar an lalata komai an gama, a ina Guy ɗin da kike magana yake?”
Ta furta tana riƙe bakinta da murmushin da tun jiya da safe rabonta da yin irinsa.
“Ghana.”
Linda ta furta tana ficewa daga ɗakin. Ta barta da zuciyarta da ke mamakin inda ta samo dukkan waɗannan a abubuwan.
‘Tirƙashi! Lalle dole mahaifiyarta ta bawa Linda amanarta. Mata CE da ta san ta kan kowane kalar makirci da mummunan ƙulli.’


******

REZA

Sitting room ta wuce da shi, ta kwantar shi a saman ɗaya daga cikin kujerun. 

Ɓangarensu ta koma tana kiran Soupy.

“Oh ni, wannan kira ko auren kuka je aka ɗaura ai sai haka, sai yanzu ya tafi ke nan?”

Yatsine fuska ta yi tana dosar kitchen.

“Lemon nake so ki ba Ni zan bawa wani, baki ganshi ba abin tausayi, ya sha giya harta masa yawa. Na dai aje shi sitting room saboda ko gidansu ba zai gane ba.”

“Ohh, bari na matse ki kai masa, ya kukai da Hamoud ne? Na ganki kina wani walkiya kamar wacce aka bawa kyautar diamond.”

“Kai Soupy kin faye san zance, ni fa tun jiya a daidai na nake, ki bari na dawo na faɗa miki komai.”

“Gidanku Reza, ki faɗa mini mana, na ƙagu na ji abin da ya saka shi shafe awa yana jiranki.”

“Wai aurena ya zo nema.”

Dakatawa ta yi da matsar tana kallonta baki sake.

“Rufe bakin mana, ba fa wani aure na azo a gani ba. Domin ya rama abin da Fakriyya ta masa ya yanke shawarar auren.”

“Hmm! Na kasa ganewa, gaba ɗaya kin rikita min lissafi, wai nufinki har yanzun bai tuna ya sanki kunyi soyayya ba?”

‘Ba za ki gane ba kam’ Ta furta a ranta tana zama saman dining ɗin dake gurin.

“Karki damu, zan warware miki komai…”

“Uhmm, a cikin satin nan yake so ayi komai fa.”

“Ikon Allah, haka abin ya girmama? Ya faɗawa iyayensa sun yarda?”

“Wa ya san masa, Ni dai zan yine saboda nawa burin Ni ma.”

Ta furta tana ɗaga kafaɗarta guda.

“To, Allah ya kyauta, kai masa lemon ɗin, Ni sam ba gane kalamanki nake ba.”

Ƙarɓa ta yi tana murmushi ta fice. 

Yadda ta barshi haka nan ta same shi ya ƙara bajewa yana kallon lissafa fitilun Falon.

“Tashi to ka sha.”

Ta furta tana ɗago da kansa, buɗe bakin ya yi yana lumshe ido alamun ta bashi, a hankali ta fara bashin har ya shanye tas! Yana yatsine fuska.

“Ta ki ba daɗi kamar tawa.”

“Na sani ai.”

Ta furta tana zare masa takalman ƙafarsa.

“Ke dillah cikan ƙafa, da haka ƙanwata ta fara ƙarsheee ta ceeeee wai nii take sooo.”

Ya furta yana ture ta da ƙafar, sai kuma ya yi saurin sunkuyawa yana kelaya aman duk giyar da ya sha. Da gamawarsa ya zube gefe, a hankali yake lumshe ido har barcin ya kwashe shi.

Miƙewa ta yi ta tattara gurin, kafin kuma ta gyara masa kwanciyar saman kafet ɗin. Ta fice zuwa nata ɗakin.

8:30am alarm ɗin da ta saka ya buga, tashi ta yi tana tunanin baƙonta, so take ta ganshi cikin nutsuwarsa ta ji ƙarashen zantukan da yake mata jiya.

A hakan ta faɗa wanka. Ta fito ta kimtsa cikin baƙaƙen kayanta.

Kai tsaye sitting room ɗin ta dosa ɗauke da abin kari. 

Da tura ƙofar ta fara watsa idanuwanta a kewayen falon, ganin bata ganshi ba ya sata ƙarasawa da hanzari tana nufar Toilet.

Kwankwasawa ta yi ta ji shiru, ta buɗe, sai dai wayam ba ya ciki. 

Aje kayan ta yi ta fice daga gurin tana mamakin inda ya tafi. Fita ta yi can waje  inda motarsa take, ita ma ba ta wurin.

Tsaki taja me ƙarfi tana nadamar abin da ya hanata rufe shi ta baya, koma ta tafi da mukullin motar.

Taɓe baki ta yi ta dawo falon tana kallon Soupy da ke ba Mamanta abin kari.

“Kin ga sa’adda baƙon nan ya tafi?”

“Ina zan sani Ni da ko kalarsa ban gani ba?”

“Ya tafi, da yake riƙaƙƙene ko godiya ba zai iya yiwa mutane ba? To shi ya jiyo.”

Ta furta tana juyawa zuwa ɗakinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 15Asabe Reza 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×