Skip to content
Part 18 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

FAKRIYYA

“Na gama magana da gayen, ya ce zai yi ko da kuwa abin yafi haka hatsari. Sai dai ya saka mana kuɗi masu yawan gaske. A cewarsa ko da abin ya lalace sun wadace shi ya samu damar barin ƙasarsu kafin a farga.”

“Nawa ya ce?”

“Miliyan biyar.”

“What!!! Amma ba shi da hankali ko? Daga Ghanan kawai da zai zo ya yi wannan aikin shi ne sai an ba shi wannan uban kuɗin, gida zai gina halan?”

Fakriyya ta furta tana miƙewa daga kwanciyar da ta yi.
“Sanin shi kaɗai ne ke da damar yin aikin yasa shi ambatar wannan adadin. Idan har buri zai cika menene million biyar? A bashi kawai tunda dai muke da riba a gaba.”

“Ba Ni da ita ne Linda, ke kinsani kamfaninmu baya  tafiya sosai yanzu. Abin da ke gareni a ƙasa bai fi 2.5m ba, ina za a samu cikon in dai ba motata ta gurin Hamoudi za a siyar ba?”

“Da yake kin taho da ita ko? Ina ce can kika bar komai naki dan tsabar shashanci? Shi kuma bai aiko ba alamun ya cinye…”

Hmm! Karki damu, akwai 2M wurina sai a haɗa a bashi ya rage sauran biyar ɗin, ko kuma a sai da tawa motar a cik…”

“A’a, sam! Akan cikar burina ba zan bada ƙafar da za a illatani gaba ba. Ko da jikina zai iya samo min abin da zan ci, rayuwar talauci ai babu daɗi, mu rabu da komai ke nan dominta? Idan abu ya ɓaci ribar ta zama ta ta?”
“Ba zai ma ɓaci ba, amma tunda kince haka abar batun motar, a bashi 4.5m ɗin kawai.”

Gyaɗa kai ta yi tana komawa kwanciyarta.


HAMOUDI

Sororo ya yi yana duban wayar da wani irin takaici. Wai shi ake kashewa waya a fuska saboda tsabar samun wuri.

A zuciye ya ɗaga wayar zai tura mata zafafan kalaman da za su hanata barci amma ya tarar ta mutu, mamaki ya kama shi sanin cewa shi bai kashe wayar ba, haka a cike take da Caaji. kunna ta ya gwada yi taki kunnuwar, ya miƙe da sauri ya jona ta a wuta nan ma taƙi kawo haske ballantana a gane ta ɗau wutar. Da wata irin fusata ya maka wayar a bango ta yi ɗai-ɗai a ƙasa.

Dawowa ya yi saman gadonsa ya zauna yana huci. Haushi kan haushi. An kashe masa waya a fuska abin da yafi tsana a dukkan shika-shikan wulaƙanci, gashi bai rama ba wayar ta sume.

Jan bargonsa ya yi har kansa yana ƙudundunewa ciki. Ga haushinta da yake ji, ga kalamanta da suka daskarar da yawun bakinsa na dawo masa, ga kuma tunaninta da ke mamaye duk wani saƙo da lungu na halittarsa, haka suka haɗu suka sanya masa ciwon kan da ya kwana bai runtsa ba.

Kwana biyu ya kwashe yana azabtuwa da tunaninta da shi kansa bai san dalilin da yasa yake jinta a ransa irin jin da bai taɓa yiwa wani ba A ran na uku ya shirya zuwa gidan duk da ransa a dagule yake. Fatansa ya isa ya sauke mata kwandon masifarsa ko zai ji daɗi. A rayuwarsa idan kana son ganin lagwansa, to ka masa abu ya kasa ramawa. Yanzu zai fita hayyacinsa ya rasa inda zai tsoma ransa. Yana cikin dalilin da ba zai iya kyale Fakriyya ba ko da kuwa ita ce ajalinsa.

Da zuwansa da fitowarta duk bai fi minti uku ba. Kallonta yake ganin yadda take tahowa a sanyaye, yana kula da yadda ta rame kamar ta yi ciwo. Sai kuma ya ji wani iri, duk wata tsiya da ya taho da ita na nutsewa a ruhinsa.

Harta iso ta zauna bai bar binta da idanuwan tambaya ba, a sannu kuma idanuwan suka sauka kan zoben yatsanta da ya saka su ƙanƙancewa yana mata duban ina ke ina Diamond Ring?

Ko da ta zauna bata ce da shi ƙanzil ba, sai ma juya kanta da ta yi wani ɓarin.

“To fa! Me ke damunki?”

Shiru ta yi kamar bata ji shi ba.

“Magana fa nake?”

“Da me ka zo?”

Ta furta tana juyowa idanuwanta akan fuskarsa.

“Ki fara amsar tambayata mana.”

“Abin da ke damuna bai shalleka ba.”

“Ni da zan zama mjinki, Ni ya kamata ace duk wata damuwarki na fara sani, me ya sa kika rame?”

“Ka bari sai ka zama tukun.”

‘Oh Allah, ba ta da lafiyarma bakinta ba zai saitu ba.’
Ya furta a ransa yana dafe kai.

“Ki faɗa mini, please.

Shiru ta yi tana nazartar fuskarsa, gani take kamar da gaske ya damu da damuwarta ne shi ya sa harda magiya.”

“Ko na faɗa makan ba za ka iya min magani ba…” Ta numfasa muryarta na sake rauni. 

“Wanda na danƙawa dukkan zuciyata ya tafi ya barni saboda ban kasance a jinsinsa ba, kuma kai ne sila, me ya sa ba ka da lokacin kira na sai cikin dare da nasa ne shi kaɗai?”

“Reza!!!”

Ya furta da tsawa yana dukan tebirin gabansu da ya sata ɗagowa tana dubansa da idanuwanta da suka fara cikowa.

Bai farga da abin da ya yi ba sai da ya ga kallon da take masa, a hankali kuma ya koma ya zauna yana huci kamar wanda aka zagi uwar da ta haifi tasa uwar.

“I’m sorry, ban san me ya sa ba na so kina ambatar wani gabana ba. Aurenki zan yi, ki gane mana, ko ya ya ne babu daɗi, ko da kuwa ba na sonki, ko da kuwa auren na lokaci ne…”

“Kai ka ce in faɗa maka damuwata fa.”

“Ba irin wannan ba, kina faɗa mini wani ke tare dake da daddare, kina so na fara zarginki ne?”

“Ban san meke tsakaninmu da zan  kasa gaya maka hakan ba.”

“Baiko, tunda har kin amsa za ki aure Ni ina ganin baiko ya tabbata, ke nan zan iya samun darajar da ba za ki dubi tsabar ido na kina gaya mini wani ne damuwarki ba.”

“Ba fa wani ba ne, ka gane mana, shi ne ke taimakawa fitar duk wani numfashina da kake gani kana ƙara linkin ciwon dake zuciyata.”

Numfashi ya furzar mai zafi yana sauke idanuwansa da suka kaɗa a nata.

Ya kula kawai so take ta ƙure duk wani haƙurinsa.
“Quraisha!”

Ya furta yana riƙo hannayenta cikin nasa.
Ɗagowa ta yi tana masa kallon HAMOUD ne ko HAISAM?

“Kina ji ko? Ina sonki, son da ban taɓa yiwa wani mahaluƙi ba…”

“Kai ne? Are you okay? “

Ta furta da taraddadi tana kallon cikin idanuwansa.

“Na sani za ki yi mamaki, amma ki sani ba zan taɓa miki ƙarya domin kawai na ji daɗi ba. Da gaske a cikin satin nan da fara zance dake kin mamaye dukkan ruhina.”

“Fakriyya fa?” Ta samu bakinta na furta wa da wani kalar mamaki. 

“Kin cike duk wani gurbi da soyayyarta ta taɓa wanzuwa cikinsa.”

Ya furta, yana danne takaicin da ya taso masa na kiran sunanta a yanayi irin wannan.

“Ban san yadda ake fara son wani a daina cikin ƙanƙanin lokaci ba komai kuwa girman lefinsa. Ka na son nuna mini Fakriyya ba son gaskiya ka mata ba shi ya sa har son zai yi tsuntsuwa zuwa kaina?”

“Ba zan taɓa fifita soyayyar iyayena akan na mace ba Quraisha, kowa da muhallinsa a rayuwata. Ke nan idan Fakriyya ta ma iyayena  lefi irin wannan dole in barta, girmansu yafi girman duk wani abin halitta a gare ni.”
Shiru ta yi tana ganin gaskiyar zancensa dake bayyana ɓaro-ɓaro saman fuskarsa.

“Barinta za ka yi, ke nan ba sonta ka daina ba…”

“Akwai wani a ruhina Ni ma, bari in faɗa maka tsakaninmu, na sani za ka mini haƙuri har na fidda shi kafin na bawa soyayyarka wurin zama.”

Shiru ya yi yana dubanta alamun ita yake saurara.
“Haisam…!”

Ta furta, tana ɗora masa MAFARIN LAMARIN har zuwa shekaran jiya da ya barta domin shi.

Tun kansa na ɗaurewa har ya zo ya warware. Bai taɓa yarda ma akwai wata halitta wai Aljanu dake rayuwa da mutane ba sai yau. A da idan ya samu labari irin wannan dariya kawai yake yi ya ɗauka tatsuniyoyi ne irin na hausawanmu. Lallai Haisam ya masa abu mai girman da ba zai iya manta shi ba. Gwara da ya tafi, da ace yana nan bai san yadda zai iya yaƙin soyayya da Aljani ba. Ke nan mutuwar da wayarsa ta yi ranar shi ne sila. Ko da ya bar masa Quraisha, baya tunanin zai iya ganinsu tare bai ji damuwa ba. Yana jin yafi shi zafin kishi nesa ba kusa ba, da shi ne, ba zai iya barinta ba, ba Aljani ba, ko da yana daga cikin hallitun da ke shanye jinin bil’adama dan magance yunwa bai barinta, ta riga ta zauna masa wurin da ba zai iya gogeta ba.

Lamarin ya zo masa da gigitar da har bai san sa’adda ya isa gabanta ya ɗago ta zuwa cikin jikinsa yana bubbuga bayanta alamun rarrashi.

“Ki yi haƙuri da duk abin da na miki, da na sani nake yi ina jin kamar na yanke hannuwan da suka taɓa marinki kan gaskiyarki. Ki mini addu’a Allah ya sassauta min wannan zafin zuciyar.”

Wani abu ke kewaya jinin jikinta da bata taɓa jin irinsa a jikin wani namiji hatta Haisam da take masa son da za ta ji hakan, yanayi ne mai girman da ya haddasa mata mutuwar jiki har bata san sa’adda ta kewaya nata hannuwan a bayansa tana ƙara shigewa ƙirjinsa.

“Hakan ya miki ke nan, uhmm kwana nawa ya rage?”
Ya furta a saitin kunnuwanta.

Da sauri ta janye jikinta wata kunya da bata san tana da ita ba na lulluɓeta.

Zumɓura baki ta yi tana harararsa.

“Allah tsare ni, me zan ji anan in ba turarenka da ke tada min zuciya ba. Gani na yi ana kallonmu, ban ce kuma ka juya ba.”

Murmushin gefen baki ne ya kuɓce masa, wai shi za a yiwa wayo.

“Shi ke nan bari na wuce. Gobe nake sa ran a fara hidindimu, ki sanar saboda masu kawo kayan za su zo.”
“Kar suyi yawan da na ambata rannan, muje mana ka ga mahaifiyata.”

Jerawa suka yi zuwa gidan. Tana ganin yadda aka saki labulan windown da take hange.

kina tare da wahala da kike iya jure gani.’

Ta furta a ƙasan ranta, murmushi na bayyana saman laɓɓanta.

Ya daɗe yana mata addu’ar samun sauƙi, yana godewa rahamar Ubangiji da ya barsa ransa da lafiyarsa.

“Tana kuwa samun gashin ƙashi yadda ya kamata?”
Ya furta yana miƙewa daga gabanta.

“Tana samu lokaci zuwa lokaci.”

“Ya kamata a dage, akwai alamun za ta iya warkewa tunda harta fara juya kanta tana kuma motsa yatsunta.”
“Hakane, da na samu nutsuwa ɓangaren lafiyar tata kawai zan juyo, In ya kamata a fita da ita waje ina ga hakan zai fi.”

“Yawwa Ni ma tunanina ke nan, bari bayan an kammala komai sai mu kaita.

“Muje na ɗan taka maka.”

Addu’a ya ƙara yiwa Mama Quraisha da ke ta binsu da ido, fuskarta na nuna zallar farin ciki.

Sai da ta raka shi  gun motarsa ya tafi, tukunna ta dawo cikin gidan. Tana jin komai dake ranta na washewa.

*****

Hidindimu ake ba kama hannun yaro. Kayane zube saman gadon tana ta ɗagawa. Gown ɗin da zata sa a Dinner take jinjinawa jin kudin da Sumoli ta ce an zuba mata. Sosai take mamakin yadda ya dage yana zuba mata kuɗi, duk ta san a gurinsa ba komai ba ne tunda yana da aikinsa mai ƙarfi da yake yi a kamfanin mahaifinsa, amma kuma sunyi yawa.

Ajiye rigar ta yi ta ɗago tana yatsine fuska, idanuwanta akan Soupy.

“Unguwar da babu masallaci bata yi ba.”

Kallota ta yi da mamakin yau kuma meya kawo masallaci cikin tunaninta.

“Eh mana, kinga da anan za a ɗaura auren, limamin masallacin ya yi mini walicci.”

“Oh, na ga ai ana gina wani yanzu a can baya. Amma ai na ɗauka malamin nan da kuka taɓa zuwa ya gaya miki yadda za ki yi Istibra’i shi za ki nema ya miki waliccin.”

Ta furta, tana son tuno wani abun.

“Yawwa kin ga da mun san inda Zenabu take sai mu nemeta ta kaiki ki ga dangin mahaifiyarki. Ni kaina ko sunan garinsu ban sani ba.”

“Ko kin sani babu abin da zai kaini gare su, mutanen da suka yi silar faruwar komai a rayuwarmu kike cewa naje musu? Fita please Soupy, kinsa ma duk farin cikina ya koma.”

“To na ji, Allah ya kyauta.”

Ya furta tana barin ɗakin.

A daidai nan taji shigowar saƙo wayarta, ta ɗauka ta buɗe.

Akwai sirri mai girma da nake son gaya miki, ki faɗa mini inda za mu haɗu. Karkiyi wasa da maganar, ya danganci auren da kike shirin yi a gobe.
Dr, Igwe.

Dr Igwe kuma da hausa? Ta furta tana ƙara kallon sunan, tana duba Number ɗin da ba irin ta ƙasarta ba ce. Wane irin sirri ne wannan? Ina ma ya san aurenta?. Sai kuma taja tsaki tuna ko wani ne da ta taɓa mu’amala yake son mata wasa hankali.

Ban da lokacinka.

Ta tura masa tana kashe wayar baki ɗaya.

*****

Daga wanka ya fito yana goge kansa da ruwa, sauri yake tayi yaje ya samu kawunsa Ishaq Shareef da yake ta ƙoƙarin ɓata masa lamarin. Mamaki yake wai kamar shi ace ya yi ƙarami da aure sau biyu cikin wata guda. Ya kuma faɗa masa ya fa saketa saboda mazinaciya ce, nan ma ya ƙeƙashe ƙasa ya bari ya huce daga waccar kafin ya auri wata. Kai bai taɓa ganin jarababban Kawu irin nasa ba, ya sani da Abbansa na nan da komai ya zo masa da sauƙi.

A haka yaji shigowar saƙo cikin wayarsa, ya ɗauka  da sauri a tunaninsa Reza ce. Sai dai ganin Number wajen Naija ya kauda zatonsa ya bude.

Akwai sirri mai girma da nake son gaya maka, ka faɗa mini inda za mu haɗu.

Karkayi wasa da maganar, ya danganci aurenka da kake shirinyi gobe.

Dr, Igwe.

Shiru ya yi yana jinjina sunan kamar ya taɓa jinsa, sai dai ya gaza tuna inda yaji. Aje wayar ya yi kamar ya share sai kuma ya dauka tuna ance SIRRI. Gwada kiran Number ya yi amma taƙi shiga. Tsaki yaja ya fara rubuta masa saƙo.

Duk sa’adda ka shirya ka neme ni ina sauraronka, koma menene na san ba zai hanani zuwa ɗaurin aure na ba.

Ya tura yana jefa wayar kan gado. Ya daɗe yana jira ko wani saƙon zai shigo, ganin shiru ya sashi juyawa yana ficewa daga gidan zuwa gidan kawunsa ayi wacce za a yi.


*****

Mutanen da suka cika a babban masallacin na jumma’ar ba su kai ko rabin na Fakriyya ba. Kowa ya haɗu daga barin amaryar har nasa.

Yana tsakiyar abokansa suna masa shaƙiyanci ya ji an dafa kafaɗarsa ta baya. Juyowa ya yi yana kallon mutumin mai zubin yarbawa da bai taɓa gani ba.

Hakan bai hana shi kin miƙa masa hannu su gaisa da murmushi saman fuskarsa.

Dr, Igwe, ni ne wanda na turo maka saƙo jiya.

Mamaki ya faɗaɗa a fuskarsa ganin yana Hausa tarwai, sai kuma ya juye da masa kallon baka iya zuwa ba.

“Okay lafiya kuwa?”

Hoto ya miƙo masa ya karɓa ya duba, ɗagowa ya yi yana masa duban rashin fahimta. Duk da kalar hotan na da ne, Duk da bai santa tana ƙarama ba, amma wannan ta jikin hoton babu wani abu daya rabata da Mama Quraisha mahaifiyar Reza.

“I’m sorry to say, na san ba zaka ji daɗi dana sameka a wannan lokacin ba, sai dai taimakonka zanyi, haka na daɗe ina nemanka dan na faɗa maka sirrin da bana iya samun barci tsawon shekaru talatin da huɗu (34) dominsa. A binciken da na sa aka mini game da inda zan samu ɗan gidan Nawazuddeen Sheerif ne na samu labarin kana shirin auren ɗiyar wannan matar ta jikin hoton. Na daɗe cikin tsoro da girmama yadda ubangiji ke kama bayinsa ta hanyar da suka kauce masa. Ka yi haƙuri, wannan ta hotan ba kowa ba ce face MAHAIFIYARKA da kake shirin auren ɗiyarta, kuma  ƘANWARKA.”

Kawai gani akai ngo ya turmushe wani mutum yana bugu da duk wani ƙarfi da ya mallaka.

Abokansa suka farayin kansa suna ƙoƙarin daga shi daga jikin mutumin amma ya watsarsu, Kawu da sauran manyan mutanen dake gurin ciki harda ‘yan jarida suka nufo wurin a sukwane, da ƙarfi yake masa faɗan ya ɗaga shi, amma ina kamar ma baya cikin hayyacinsa, wasu majiya ƙarfi ne suka iso suka raba shi da ƙyar daga jikin DR Igwa dake ta kiran Yesu.

Miƙewa ya yi  yana share jinin dake fitowa ta hancinsa, a haka ya yi murmushin ƙarfin hali yana kallon mutanen dake gurin har ya sauke idanuwansa cikin na ‘yan jaridar ya musu wata irin alama. Ya waigo ga kallonsa ga kawu dake ta huci yana masa tambayar me ke faruwa ne?

“Na shirya ƙarbar duk wani hukunci da zaka mini saboda na san zafin da lamarin ke da shi, sai dai hakan ba zai hanani na faɗa maka gaskiyar ƙanwarka kake shirin aure ba.”

“Meee?”

Kusan duk mutanen da zancen ya isa cikin kunnuwansu suka ambaci kalmar a tare. Wasu har sun fara yo kansa limamin wurin ya hana.
“Kwarai kuwa, ga tarin dalilaina.”

Ya furta yana takawa da ɗingishi zuwa wurin motarsa, ya ɗauko wasu files, ya zari guda ya miƙawa Kawu Ishaq.

“Ni ne likitan mahaifiyarsa, ta yiwu ai kana da labarin sun sha zuwa Ghana saboda ganin likita. To Ni ne suke gani.

Wannan file ɗin shi zai tabbatar maka da cewar Mahaifiyarsa ba za ta taɓa haihuwa ba.”

“Ga wannan hotan kuma shi ne na mahaifiyarsa  Ashana da budurwa ta ce a wancan lokacin. Dalilin cikinsa yasa muka ɓata, ƙarshe muka shirya da ta ce mini wanda ya mata cikin ya mutu, ke nan yaron ba shi da uba. Ni na yaudareta harta haihu a hannuna na ce mata yaron ya mutu. Na ɗauka na bawa su Nawazuddeen da suka tabbatar mini zasu siye shi koma nawa ne domin kawai su samu farin cikinsu.”

“Ya isa!!!” Kawu ya furta da tsawa jikinsa na rawa.”

“Abu ne na family gida ya kamata ka same mu ba cikin tarin jama’a ba. Wuce muje gidan, ka kuka da kanka idan har ya kasance kalamanka ƙarya ne na rantse da Allah sai ka ƙarashe rayuwarka a Prison!”

Ya ƙarasa yana warto hannunsa.

Ya bada umarnin a saka Hamoud a mota da ya daɗe da daskarewa a tun kalmar data shiga kunnuwansa na SIYANSA AKA YI.

*****
Kina ina ne, Fareeda! Fito na ce!

Jin muryar Kawu Ishaq na kwala mata kira ya sata ruɗewa tana jawo babban gyalenta. Mamaki take abin da ya kawo shi, shi da rabon da ya zo gidansu tun ranar da ya zo ya sauke musu kwandon bala’in sun hana Hamoudi fita waje karatu, ƙarshe ya sa su dole su barshi.

A haka ta taho tana saukowa daga matattakalar benen, idanuwanta suka sauka kansa har bata san lokacin da ta buɗe baki ba.

DR Igwe? Kai ne kuwa?”

“Oh kin sanshi ke nan baƙar makira?”

Kawu ya furta yana zama jin ƙafafuwansa sun gaza ɗaukar nauyinsa.

Dakatawa ta yi da saukowar tana kallon Kawu, ta sani duk familynsu shi ne babba kuma jarababben da babu na biyunsa, amma duk masifarsa bai taɓa zaginta ba.
“Me ya faru Kawu, likitana ne da muka taɓa gaya muku ta sanadinsa muka samu cikin Hamoud ya zauna.”
“Ehhhh, haka fa, ga ribar nan na gani.”

Kawu ya furta yana jijjiga ƙafafuwa.

“Kai kuma ka mata bayani mana ka tsaya min kerere kana buso min warin Arna.”

Da sauri ta ƙarasa saukowa idanuwanta suka sauka kan Hamoud da Direba ke ta shafa masa ruwa.

“Mee…Me ya same shi?”

Ta furta tana takawa gare shi, kafin kuma ta ji kalaman da suka sata ƙamewa.

“Ki yi haƙuri, ban riƙe amanarku ba, na faɗa masa sirrin da muka ɓoye ne, sirrin da ba ke ce ainihin mahaifiyarsa b…”

Walkiwar da ya gani a gefen idonsa ya sashi yin shiru harcensa na datsewa har sai da jini ya fita tsabar ya maru.

Tana tsaye gabansa cikin tashin hankali tana ƙoƙarin saita kalmomin bakinta.

“Ni…Ni kake haramtawa ɗa na DR? Ni da yake halaliyata, wane irin jahilci ne haka? Akwai abin da ya haɗa mu da kai ne da zaka mana wannan ƙazafin?”
“I’m sorry Madam, ki bar ni in faɗi gaskiya, ga shaidata nan ta yarjejeniyar da muka yi lokacin da zan baku Babyn, na sani kema kina da irinta. Zan iya rantsewa da girman Bible kan dukkan zancena gaskiya ne.”

Ya furta yana miƙa mata file ɗin hannunta.

“No, no, karka mini haka, karka raba ni da ɗa na, ba sai kamin haka ba za ka samu abin da kake so, ka faɗi gaskiya zan baka ko nawa ne, na sani kuɗi ne kawai zai saka yin haka.”

Ta furta cikin gigicewa tana jijjiga kwalar rigarsa.
“Innalillahi wa inna illahhir raji’un! Yanzu Fareeda zancen nan gaskiya ne? Ga komai nan ya tabbata kina cewa za ki  biya shi? Ya rufa miki asiri ke nan ko? Wane irin rashin tawakkali ne ya hau kanku da kuka karbo dan shege kuka cusa cikin zuri’armu, haba! Shi ya sa kwata-kwata baya kama da ni.”

“Ba shege ba ne! Wallahil azim Kawu ƙarya yake, Hamoudi ɗana ne, bari kaga File ɗinsa na asibitin.”

Ta furta  da wata irin gigita, tana sheƙawa a guje zuwa ɓangarenta. Duk wasu takardunta masu muhimmanci ta dinga watsarwa har sai da ta gano file ɗin Asibitin. Ta dawo da sauri tana miƙa wa Kawu.

Da buɗewarsa kuwa wata ‘yar takadda ta faɗo, ya ɗauko ya karanta. Hular kansa ya fara turewa kafin kuma ya miƙe yana mata wani irin kallo.

“Wannan ba tunanin Nawazuddeen ba ne, na tabbata ke kika ruɗe shi har ya yi wannan aika-aikar. Ga sa hannunsa nan a jikin takaddar dake nuna kun karbi yaro za ku raina. Me kuma ya saura da za mu ƙi yarda da zancen likitan bayan ga shaida nan da kika bayar da hannunki.”

Riƙe kanta ta yi tana durƙushewa a gurin, idanuwanta suka sauka kan Hamoud da yake mata wani irin duba na rashin hayyaci. Ɗan ta, haliliyarta take hango tsanarta cikin idanuwansa.

Da rarrafe ta ƙarasa tana riƙo ƙafafuwan Dr Igwa
“Ka faɗa musu ɗa na ne, wallahi ɗa na ne, karka raba mu, shi kaɗai gare ni, kai ka sani, da ya ya muka samu cikinsa ya zauna. Karka ɓata tsakaninmu DR.”

Ta furta numfashinta na sama da ƙasa. Wasu kalmomi da suka fito daga TVn dake kunne a falon suka daki kunnuwanta, ta ɗago da sauri tana kallon me labaran, kirjinta ta dafe sa’ilin da numfashinta ya katse, ta ida tuntsirewa  idanuwanta a rufe ruf!

Kawu ya miƙe da salati yana kallon TVn, ya kai kallonsa ga Fareeda dake zube, ya sauke idanuwansa kan Hamoud da shi ma ya zube.

Ai sai ya dafe kirjinsa dake ƙoƙarin tarwatsewa  yana zama daɓas a ƙasa. A kan idonsa likitan ya juya ya fice ya gaza tsaida shi. Hatta hannuwansa ya kasa motsa su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 17Asabe Reza 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×