Lagos, 1981
Quraisha Ashana, shi ne sunanta, ita ce karuwar da a zamaninta aka dinga rufe gidan karuwai saboda masifa da bala'inta. Ta zo bariki tun tana yar shekara Sha Shida lokacin iyayenta sun rasu, 'yan uwanta kuma za su aura mata wani Wada da ake raɗe-raɗin yana da cutar kuturta.
Sun ɗaura, ta kuma zauna da shi har tsawon shekara ɗaya. A daren da ta cika shekarar ta haifi ɗanta Namiji, da gama mata wanka ko ɗuminta yaron bai ji ba ta direshi gefen yar tsohuwar da ke kula da su tana barci. . .