Skip to content
Part 2 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Lagos, 1981

Quraisha Ashana, shi ne sunanta, ita ce karuwar da a zamaninta aka dinga rufe gidan karuwai saboda masifa da bala’inta. Ta zo bariki tun tana yar shekara Sha Shida lokacin iyayenta sun rasu, ‘yan uwanta kuma za su aura mata wani Wada da ake raɗe-raɗin yana da cutar kuturta.

Sun ɗaura, ta kuma zauna da shi har tsawon shekara ɗaya. A daren da ta cika shekarar ta haifi ɗanta Namiji, da gama mata wanka ko ɗuminta yaron bai ji ba ta direshi gefen yar tsohuwar da ke kula da su tana barci, ita kuma ta haɗa ya na ta-ya na ta za ta gudu. Sai dai cinkaro da ta yi da mijinta daga zaure ya sa ta tsayawa suna kallon-kallon, kan ya buɗe bakinsa jin ba’asi ta caka masa basilla a kirjinsa, inda nan take ya zube gurin. Ita kuma Zakara ya ba ta sa’a ta cale ita da Aminiyarta Zenabu da ta ɗora ma ta wannan shawarar ta kashe mijinta, sai su gudu gidan Auntynta da ke zaune legos.

Sun isa, sun kuma samu tarba mai kyau, in da ta ciyarsu na tsawon kwana bakwai. A ranar na takwas ta ce kowa sai ya je ya nema, kamar yadda ita ma take nema danta kula da marayun yaranta. Zenabu ta ba su shawarar su dinga sai da maganin gargajiya, haka suke gammo su tafi, ganin ba wata riba ya sa suka watsar suka koma yiwa mai tuwo-tuwo wanke-wanke a kasuwa, nan ma hantara ta yi yawa suka watsar sukai dawowarsu gida suka zaune.

Auntyn da ta tambayesu dalili suka gaya ma ta, Zenabu ta ƙara da cewar su dai ta sa su ana ta harkar suna taya ta. Murmushi ta yi tana kallonsu, su ba su san me take yi ba, kawai gani suke tana shiga tana fita, sana’arta ba ta tayi ba ce, ba kuma ta hutu ba ce, sai dai kowa jikinsa ya nema masa. Da ta faɗa musu ba ɓata lokaci suka yarda.

Su fa kuɗi suka zo nema ba hutu ba, a ƙauyensu da suka baro a shekara sau ɗaya suke ganin shinkafa da Masara, sai fa gero da dawa. Kai ko raken nan mai ɗan zaƙi babu, balle su Acca da Alkama masu ƙara lafiya.

A ranar ta kai su babban gidan da take harkar, a take kuma aka ba su ɗakuna a gidan da cewar dole sai an musu karatu kan harkar, da sharaɗin duk abin da suka samu raba dai-dai ake yi da uwargijiyarsu da ake kira Anty Kankana, kuma ba za ka bar gidan ba sai ka yi shekara goma, sannan za a baka ‘yancin kai. Ba ɓata lokaci suka yarda da duka sharaɗin, inda Quraisha ta koma Ashana, Zenabu kuma ta koma Bitas, rayuwa ta fara kyawu.

A shekara biyar da Ashana ta yi cikin gidan nan ya yi tumbatsar da babu wani gidan karuwai da zai doke shi. Sai da ta kai ta kawo har Anty Kankana na shayinta saboda ita ce macen farko da ta karya duka dokokin gidanta, saboda Zenabu ta samu wanda take so za su yi aure, sun hana.

Haka Saboda ita ɗan takarar gwamnan garin na wancan lokacin ya bige gidan da suke ya sa a gina musu wani na zamani mai daƙuna Hamsin, domin kawai Ashana ta yarda ta aure shi. Ita kuma da ta ji labarin bokansa ne ya ce idan har ya aure ta sai ya yi shekara Ashirin yana gwamna a garin ba tare da an sake wata siyasar ba, sai taƙi, a cewarta ba sonta yake ba, ita wanda zai dinga kwanciya tana taka bayansa da tsinin takalmi take so, ba ma za ta yi auren ba sai ta shekara Arba’in domin ka da ta haihu.

A shekara ta goma da zuwansu legos Aunty kankana ta kai takarda, nan take aka ɗora Ashana a matsayin shugabar gidan. Nan ta bawa kowa dama ya ci karensa babu babbaka, ita kawai a biya ta kuɗin hayar ɗakunanta, haka ta saka dokar daina karɓar yara ‘yan ƙasa da shekara ashirin.

A wannan shekarar ta ta ƙaddarar ta fara tambali da rayuwarta ta hanyar sa ma ta soyayyar wani talakan mutumi tiƙis da ko me goge ma sa takalmi ya fi shi cin abinci sau uku a yini.

A daren wata lahadi ne suka fita dan fasa gidan wani babban Attajiri saboda ya taɓa ‘yar lelenta Soupy. Soupy ita kaɗai ce yarinyar da Ashana ta yarda ta shigo gidansu a shekararta ta Sha Bakwai, ba don kome ba sai dan labarinta da ta ji na kwarewarta a satar tabarmar masallaci da kaji da tumakin garinsu ne ya sa mutanen garin suka ma ta atile har wajen garin.

In da bata ya da zango ko’ina ba sai gidan Ashana, bayan interview ne ta samu babban matsayi na zama yar lelen Ashana. Baiwar sata gareta irin wacce ko gaisawa za ku yi yanzu za ka ji ba sarkar wuyanka. Tamkar dai wacce ke da siddabarun rufa ido.

Wannan kuma ita ce fitarta ta farko, anan tama Alhajin da aka haɗata da shi satar Agogo, shi kuma ya zaneta da dorina mai baki biyu. Sharaɗin ɗaukan karuwa gidan Ashana kuwa babu duka, duk kuwa cin kashin da karuwar za ta maka.

Wannan dalili ya sa ranta ya ɓaci an taɓa yar lelenta, shi ya sa ta fito dan suyi operation a gidan Alhaji. Duk kuwa fitar da za ka ga anyi da Ashana, ba ƙaramar fita ba ce.

A wani ƙofar shago mai ɗan duhuwa motarsu ta tsaya. Nan ta ce su ƙarasa gidan ita za ta jirasu saboda kanta da taji yana sara ma ta. Take suka amsa inda suka sassaka manyan hijabansu da niƙab suka fi ce, bayan ta gargaɗesu da karsu taɓa kowa banda Alhajin.

Ɗora kanta tayi saman sitiyarin motar jin kan na ma ta wani nauyi. Ta shafe minti ashirin a haka kafin kuma taji wani ƙamshin turare irin ɗan saudi na dukan hancinta kasancewar yana da ƙarfi. Dagowa ta yi a hankali jin kamshin na ƙara karuwa, sai dai ga mamakinta babu kowa. Ƙofar da ke gabanta kuwa ba ta tunanin akwai mahaluƙin da zai rayu cikinta saboda yanayin kwararraɓewar shagon. Sai dai jin sautin buɗe ƙofar ya sata ware ido don son ganin mai buɗewa.

Ƙirjinta ne ya buga, ya ƙara bugawa sau ɗari da tamanin ganin mutumin da ya fito. A cikin hasken farin watan ta gama hango tsantsar kyawu da nutsuwarsa na Fulani, a kuma lokacin Allah ya da sa na sa ikon kanta, kallonsa take shi ma kallonta yake yana mamakin abin da mace ke yi a wannan talatainin daren.
Kauda kansa ya yi yana mai bi ta gabanta dan zuwa masallacin da yake limanci.

Ba ta san tana binsa a baya ba sai da hannun Soupy ya jawo ta zuwa baya, ganin kawai tafiya take ba tare da sanin in da za ta ba. Da ƙara Soupy ke janta da su tafi an kira ‘yan sanda, sai dai ina har aka kama su a ɗura su cikin motar yan sandan ba ta dawo hankalinta ba. Ba abin da take ambato sai; “wallahi ina sonsa, idan ban same shi ba mutuwa zanyi.” Kafin akai police station ta cika carbi uku da waɗannan kalmomin.

*****

Tafin hannu tasa tana dukan goshinta kamar mai son tuna abu, da sauri kuma ta fara dube-dube, can gefen gado ta hangota ta yi ɗai-ɗain da ba za ta ƙara amfanuwa ba.

“Damn it!” Ta faɗa tana duban Soupy. “Latsomin Sumoli maza a wayarki ta zo nan inda nake, jirani na watsa wanka.”

Bin ta ta yi kawai da ido tana mamakin canjawarta lokaci guda tamkar wata mai Rauhanai.

Mintina arba’in ta kwashe tana wankan sai gata ta fito, tundaga tafin ƙafarta za ka gane ta canja, ta cire zobunan da ke ƙafar haka sarkar, ta cire duk wani tarkace na fuskarta.

Ba Soupy da ke tsaye tamkar an dasa ta ba, hatta Sumoli da shigowarta ke nan sai da ta ƙame tsaye tana ma ta kallon mamaki.

Ba annurin da take yi ba ne ya ba su mamakin, a’a, shin ina sirrikan da ta ce suna jikin duk wani ƙarfe da ta huda jikinta ta maƙala? Shin ina asarar da take ikirarin za ta yi duk lokacin da ta ciren?

“Come on, let’s go!… Ta faɗa tana duban Sumoli da ke ta zare ido. Ganin ta gaza magana ya sa ta ci gaba.

“Let’s go and show Fakriyya that I am still the very best….”

“Maa….”

“Wait! This is an order, Sumoli.”

Ta faɗa a kausashe tana ci gaba da ɓalle botiran baƙar Abayar da ta saka. Ta yane kanta da gyalen abayar bayan ta karyoshi yadda zai rufe fuskarta kamar Niƙab, sai ta yi wani irin kyau mai sanyin kallo, ta fito a Asabenta Sak! Ba Reza ba.

Ganin ta yi gaba ya sa Soupy saurin shan gabanta, “Haba mana Reza ki bi a hankali, yau fa ta tare? Me za ki je yi gidan Amarya a wannan daren in ba wani sabon ɓacin ran kike son ƙarawa kanki ba.

“Amarya? Hahaha.” Ta fasa wata irin dariya.

Sai kuma ta yi shiru idanuwanta na cikowa da ruwan hawaye.

“Wannan Amaryar ba za ta amsa sunanta ba muddin ina numfashi Soupy. Sai na hanata duk wani jin daɗi na rayuwar nan, sai na nuna ma ta Ni ce dai Asabe da akai naƙudarta tsakiyar gidan karuwai ba wai haye na yi ba! Bariki jini na ne da aka ciyarni da shi aka shayar Ni!”

Sai kuma ta ƙarasa daidai saitin da Sumoli ke tsaye.

“Ki tabbata na tararki a motar kafin in gama saka takalmi.”

Ta fice tana mai maida kwallar da ke shirin zubo mata.

A hankali motar ta tsaya nesa da tangamemen gidan da ke fuskantar su. Daga cikin motar take ƙarewa gidan kallo wani abu na sake zauna mata a kirji, zuciyarta na ƙara curewa, tunawa take yi da ranar da ya fara kawota gidan ya kira shi da matsayin mafarkinsu.

‘My everything wai gaske kike ba za mu fita ba? Ya faɗa yana mai kewaye hannunsa saman barimar girarta’

A hankali ta ture hannun da sigar wasa tana harararshi.

‘Uhmm! Ni dai ba na so, kai kanka ka sani ba na son duk wani abu da zai nisanta kasancewa tare da kai. Sai dai dole mu bi umarnin Allah, mu kiyaye zama mai tsaho tare har na kammala Istibra’i na zama mallakinka. That’s why ka ga ba na son fitar nan, ni kaina ina tsoron kaina Hamoudi, I don’t trust myself!’

Shiru ya yi yana kafe ta da idanuwansa masu dafi, har sai da ta hure masa da bakinta.

“Wannan kallon fa? Bansan irin kakanninka ba…”

Cafka ya kai mata ta yi saurin kaucewa tana dariya, shi kuma ya danƙi filon da ke gefen kujerar da suke zaune.

“Ba kallo ba ne, mamaki kawai na ke.”

“Na canja ko? Saboda kai ne Hamoudi, Zanyi fiye da haka dominka, ba da wasa nake jinka araina ba.”

“To in tafi ke nan tunda ba za ki bi Ni ki ga surprised din da na kwashe shekara ina yinsa dominki ba.”

Da sauri ta dawo gabansa kamar za ta rungume shi sai kuma ta yi baya tana murmushi.

“Ai baka ce min abu zan gani ba, mu tafi, Please Hamu Bulaki.” Sanin zai iya riƙota ya sa ta yin waje da sauri tana kyalkyala dariya.”

Ba ta taɓa zato ba, ba ta taɓa tunanin akwai abin da za a mata da zai sata zubar hawaye irin haka ba, gidane gashi nan, an saka duk wani abu da aka san tana so, harta launin labulayen gidan zabinta ne.
Ita Asabe da ba ta tunanin akwai mahaluƙin da zai iya furta mata kalmar so kawai ba ma ta aure ba tsabar lalacewarta. Amma yau ga wani da ta taɓa munanawa ya yi ma ta abin da bata zata ba.

Sai kawai ta saki kuka a hankali tana cukwikwiye siririn gyalenta.

Takardun gidan ya ɗora ma ta saman cinyoyinta, wannan ya sata dagowa tana kallonsa a ladabce.

“Ba zan iya ba, ba zan taɓa yafewa kaina ba idan na yi haka, ina da sauran kunyar da ba zan manta abin ya faru ba da zan iya sa hannu na karɓi wannan kyautar, soyayyarka kaɗai gareni ta wadaceni Hamoud, ban sani ba, ban san me ya sa ba har yanzu na kasa samun sukuni a ƙasan zuciyata, ka yi hakuri ba zan iya karɓa ba…”

“Shiiii…”

Ya furta yana mai ta da ta tsaye.

‘Na sani, na san me kike tunani zai faru, sai dai ki sani ina ƙaunarki, na daɗe da tabbatarwa zuciyata anyi ta ne dominki, ba za mu taɓa rayuwa ba tare da juna ba, haka ban san ya zanyi da rayuwar ba lokacin da babu ke, ki ƙarɓa, kyauta ce daga masoyinki, zanyi kome domin kawai ki yi murmushi Asby!’

“Maa!… “

“Maa dare!!”

Taɓa tan da Sumoli ta yi ya sa ta dawo cikin tunaninta cike da mutuwar jiki, ji take ina ma ta dawo da waɗannan kyawawan ranakun da suka shuɗe yanzu. Tana jin kamar ƙarshen ke nan, zuciyoyinsu sun riga sunyi tsinkewar da babu zaren da zai iya ɗaurasu. Amma kuma, abin da ba ka taɓa zaton wanzuwarshi zai iya wanzuwar a kowane lokaci.

Ta fito daga motar cike da kwarin gwiwar hakan. Sai dai acan wani sashi na ƙasan zuciyarta na ma ta luguden hakan ba zai taɓa faruwa ko da a mafarkinta na barcin safe. Hamoudi dai ya tsaneta!

Ita ta san duk wani sirri na gidan a zuwa guda da ta yi! Ta yi mamakin yarda ya zuba Sojoji a matsayin masu gadin gidan. Can ƙasan zuciyarta take murmushi da ta tuna ƙila ya yi ne dan ita, idan har zuciyoyinsu sun taɓa wanzuwa a tare, to kuwa tabbas zai ji a jikinsa za ta iya zuwa gidan a wannan daren.

Ta yiwu bai san ta kula da wata yar siririyar ƙofa da ke bayan Garden din gidan ba, to, idan ma ya sani ita dai buƙatar ta biya tunda ta buɗe ta, babu kuma wani muhaluƙi a gurin idan ka ɗauke kukan Gyare.

Da sanɗa take tafiya tana mai nunawa Sumoli da ta tsaya ta mata gadin kofar haka ta mata flashing idan da matsala.

Ta faffaɗar tagar glass din da ke nesa da cikin garden din ta hangoshi shi sa’ilin da iska ta kaɗa labulen tagar.

Dama ta sani! Tana iya ganin lokacin a cikin idanuwanta….

“My everything wannan shi ne ɗakin kwananmu”. Ya faɗa yana mai ƙarasawa jikin window.

“Kinsan me ya sa na yi bedroom a jikin Garden.”

Kaɗa kai tayi.

“Saboda kawai idan na kwanta ina shaƙar sassanyan ƙamshin furannin…”

Kin san amfanin kallon green da farar safiya?”

“Yana ƙaramin ƙarfin ganin da zan iya tantanceki ko da a inuwa ne.”

Haaaa! Ta buɗe baki kawai tana kallonsa.

A haka ta ƙarasa, yana kwance ya yi rigingine cikin barcinsa me cike da nutsuwa, sai dai ga mamakinta babu kowa kusa da shi.

“To ina Fakriyya?”

“Tana toilet” wata zuciyarta ta sanarta, ji ta yi ranta na ƙara ba ci.

Da dabara ta yaye labulen tagar duka, a hankali ta ɗare ta, ta dire a cikin ɗakin, wata nutsuwa ta ji tana ratsa dukkan wata jijiya da ke jikinta. Tsaye ta yi kawai tana ƙare masa kallo.

Da ƙamshin turarenta ya san ta shigo, sai dai a dukkan tunaninsa mafarki yake da ita, ƙoƙarin yake dan ya farka daga mafarkin da yake jin muninsa har ƙasan ruhinsa abin yaƙi yiwuwa.

Sassanyar hannunta da ya sauka saman sumar ƙansa ya ankararshi me yake yi.

Zahiri ita ce! Tana zaune gefensa cikin baƙaƙen kayanta, ta sauke tarhar kanta tattausan gashinta ya zuba kafadunta.
Ba ta san ya farka ba sai da ta ji an figeta ana mai haɗata da bango da wata irin shaƙa.

“How dare you came to my house at midnight, are you stupid?”

Muryarshi a disashe, can cikin ƙasan maƙoshinsa take jinta, da alama ɓacin ran da ta wanzar masa ya girmama.

Ta ɗago da rinannun idanunta tana kafe su cikin nasa idanun. A zahiri so take ta fahimci yanayin da yake ciki.

A hankali yake sassauta shaƙar da ya ma ta.

“My love for u is indescribable Hamoud.”

Ta faɗa a wahalce tana tari!

<< Asabe Reza 1Asabe Reza 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×