Da ƙyar ya iya haɗa sunan, ya furta su, suka zarce cikin kunnuwanta da wani irin kuwwa.
"Quraishiyya."
Sai da ta runtse idanuwanta, ta buɗe su akan fuskar mutumin da tun shigowarsa take masa kallon sani.
Quraishiyya, suna ne da mutum ɗaya tal! Ke kiranta da shi a duk faɗin ƙauyensu. Ta ya ya ma za ta manta sautin muryar da ta fito da wannan sunan. Wannan matashin da kullum ta dawo daga kogi yake binta a baya yana rera mata waƙa da sunanta. Wannan dai da tun da ta auri ƙaninsa, ba ta ƙara jin. . .