Skip to content
Part 22 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Da ƙyar ya iya haɗa sunan, ya furta su, suka zarce cikin kunnuwanta da wani irin kuwwa.

“Quraishiyya.”

Sai da ta runtse idanuwanta, ta buɗe su akan fuskar mutumin da tun shigowarsa take masa kallon sani.

Quraishiyya, suna ne da mutum ɗaya tal! Ke kiranta da shi a duk faɗin ƙauyensu. Ta ya ya ma za ta manta sautin muryar da ta fito da wannan sunan. Wannan matashin da kullum ta dawo daga kogi yake binta a baya yana rera mata waƙa da sunanta. Wannan dai da tun da ta auri ƙaninsa, ba ta ƙara jin ɗoriyarsa ba, shi ne yanzu a gabanta.

“Ni ne dai Quraisha, ni ne dai Mudansiru, kai, tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai…”

Ya furta, yana takunsa da sassarfa, yana ƙarasawa gabanta.

“Hawayen ta ji har sun fara sauka, hawayen da suka aure ta a tun ranar da ta fara son Haroun. Sai dai, wannan ɗacin su ya bambanta da duk wata kwalla da ta taɓa yi, suna fitowa ne da tarin baƙin cikin da ta ƙunsa a rayuwarta, tana jin girman lefin da ta aikata gare su na danne ta, ɗanta. Ɗanta take son tambaya, babu baki, ko da yaren kurame ne ba ta da ikon yi. Da ƙarfi, da girman ƙudurir Ubangiji ta ja wata kalma  ‘Haaaaas’ cikin shessheƙa, wacce ta sa Soupy, Reza, Hamoud, zurowa a guje zuwa gabanta. Sama da shekara ashirin ke nan, sai yau suka ji sautinta ya fita da shessheƙa. Tirƙashi! 

“Bari kuka, ga yaron wurin ki nan, shi ne wannan da nake faɗa da shi.”

“Ya furta yana yafito Hammad da tunɗazu ya dakata da buɗe ƙofar, ya tsaya yana kallonsu.”

“Taho ka ji, ga mahaifiyarka nan, durƙusa ka ji ɗumin uwa, ka kuma yafe mata, ni ma ka yafe min da na ce maka ta kashe ubanka, ba ita ba ce, mutuwa ya yi sanadin tarin Tibi. Ita lefinta ɗaya, da ta gudu ta barka.”

Reza ta fara miƙewa ta riƙo hannuwansa, a haka ta jawo shi gaban Mama Ashana, ta haɗa hannuwansu guri guda tana hawaye.

“Gashi, shi ne dai mutumin da na kawo rannan, ya kwana cikin gidan nan, ashe ɗan uwa na ne.”

“Maama.”

Ya furta bakinsa na rawa yana ɗora kansa saman cinyarta.

Ita ma hawayen take, tana son yi masa magana, mamaki take akan mamaki. Wannan zuƙeƙen yaron wai shi ne ɗan ta. Ba ta taɓa zaton ba Wada za ta haifa ba, duba da jinsin da mahaifinsa yake, harda wannan tunanin ya sata tsallakewa ta bar shi. Sai dai, da ta san za ta yi rayuwa kalar wannan. Da ko kusa ba ta fara ƙin wata halittar Ubangiji ba. Buɗe bakin ta yi tana son cewa ya yafe mata,  amma  ta kasa, sautin ‘Haaaaas’ kawai bakinta ke iya furtawa.

Kallo Soupy ta yi da ke durƙushe gabanta, a idanuwanta ta gane me take sonyi, dan haka ta matsa da sauri ta ɗauki hannunta ta ɗora saman sumar Hammad.

Shi ma hannunsa ya ɗora saman nata, yana jin wani daɗi da ke ratsa ɓargonsa.

Ganin haka yasa Alhaji juyawa ga ‘yan sandan dake tsaye. Ƙus-ƙus suka ɗanyi kana suka juya suna masu ficewa.

Hamoud ya kallo Reza, akai sa’a ita ma shi take kallo, da ido yake nuna mata yana son magana da ita.

Dan haka ta miƙe zuwa can gefe. Shi ma ya biyo ta.

“I’m Sorry, uhmm…”

Zumɓura baki ta yi, har yanzu tana jin haushinsa.

“Hmm! Ga Yayana nan ka gani, me kuma za ka ce? Ko kuma bayan mu biyun taka haifeka?”

“Ki yi haƙuri, na gane, ki min addu’a kinji, ban san yadda zanyi na hukunta zuciyata ba.”

Shiru ta yi tana juya Zoben hannunta.

Ya sauke idonsa kan zoben, yana jin wani abu daya tokare masa maƙoshi ya wuce da ƙyar.

“Kamar ka sha giya?”

Zare idanuwansa ya yi sosai, kafin ya fara jan istigfari. Kalaman da ya watsawa mahaifiyar suka dawo a jejjere cikin kunnuwansa. Da duk wani abu da ya aikata a yau.

Idanuwansa har sun kaɗa, sunyi jawur tamkar garwashi, a haka ya ɗago yana saita su kansa.

“Idan ban kashe Fakriyya ba, wallahil azim ni zan zama silar mutuwarta. Jininta ya halattam Kin san me nawa Mamy kan wannan batun?”

Baya ta yi da tsoro ganin yanayinsa, harta fara tunanin ko Haisam ne tare da shi.

Sautin Soupy da suka ji tana bawa Alhaji labarin rayuwar Quraisha, ya sa shi yin shiru yana ƙarasawa gare su. Ya kasa kunne yana jin labarin da ko a tatsuniyoyi bai taɓa jin kalar sa ba.

Alhaji ya goge kwallar da ta zubo masa yana girgiza kai.

“Allah ya bayyana shi, a ko’ina yake da sannu za ku ga ya dawo. Quraisha ƙarama Allah ya bayyana mahaifinki.”

“Amin,”

Suka furta a tare.

Hamoud ya kalli Soupy, ya juyo kallonsa ga Alhaji.

“Idan san samu ne ina so a ɗaura aure na da Quraisha yanzu.”

Gaba ɗaya suka bi shi da ido tamkar sunga mahaukaci sabon kamu.

“Eh yau jumma’a na so auren ya kasance, yanzu idan aka barshi kamar waccar ta ci nasara ke nan. Yau ɗin nake so na yi auren ko da yana nufin mutuwarta.”

“Haba Romeo, a ina ka taɓa ganin an ɗaura aure tsakiyar dare. Ƙarfe 2:30 fa yanzun? Ka watsattsake kuwa? Ba ma haka ba, Ni ne yayan amarya, dole a sake sabon shiri, ka zo ka nemi auren a hannuna, idan na yaba da hankalinka sai na baka.”

Gaɓa ɗaya suka murmusa.

Soupy ta dube shi.

“Ka yi haƙuri Hamoud har zuwa gobe, yanzu ai jumma’ar ma ta wuce, tunda sha biyu ta gifta. Ka je ka daidaita da iyayenka ka faɗa musu komai. Gobe Sha Allahu sai ka zo a ɗaura aure. Reza ai ta zama taka.”

Shiru ya yi yana gyaɗa kai alamun ba haka ya so ba.

“Shi ke nan bari mu wuce har gobe dai, Hajiya ku kwana lafiya.”

Hammad ya furta yana kallon Soupy.

“Haba ɗan nan, wace irin Hajiya kuma. Hajiya fa irin tiƙa-tiƙan matan nan ne waɗanda ba su da ɗan tofi (pant) daidai su. Duka yaushe akai girman?”

Ta furta tana gyara zaman rigarta, idanuwanta kan Alhaji da ke ta kallonta yana sosa ƙeya.

Suna haɗa ido ya juya da sauri yana jawo hannun Hammad.

Reza da ta kula da su ta ƙunshe bakinta da dariya tana dosar ɗakinta.

Hamoud ya bi bayanta da kallo yana murmushi.

Ya musu sai da safe, shi ma ya rufa musu baya

HAMMAD.

9:35am

Kallon da Alhajin ke masa ne ya sa shi ƙara yin ƙasa da kansa yana juya yatsunsa saman karfet ɗin da yake kai.

“Ka ce ba kai ba ne ka ɗauki jakunkunan. To menene zai tabbatar mini da hakan?”

“Ka ba ni kwanaki ko uku ne, zan kawo maka ko wane ɓarawon, idan ban kawo ba ka mini duk abin da ka so. Amma wallahi duk abin da ya faru ka yarda sharri ne aka mini.”

Shiru Alhajin ya yi yana kallonsa, shi kuwa ko ba shi ba ne akan idon mahaifiyarsa dai ai ba zai iya ɗaure shi ba.akan Duk da ya fi son dukiyarsa fiye da komai.

“To, ka yi ƙoƙarin ganin hakan ya yiwu. Amma na maka iyaka da cikin gidan. Idan ba ɓangare na za ka zo ba, to ka tsaya iya naka. Abu na ƙarshe, karka kuskura na ƙara ganin ka sha wani abu da zai gusar da tunaninka, wallahi ka ji na rantse zan iya kaika mari ka shekara goma ban waiwayeka ba. Shashasha kawai, kai yanzu dan ance ba ka da mahaifi sai ka kama shaye-shaye? Duk ina tarin ilimin naka?”

“Ka yi haƙuri Alhaji, na yi kuskure.”

“Tashi ka ba ni wuri, ni za ka bawa haƙuri ko kuwa Mahallacinka za ka nemi ya yafe maka da ƙetara iyakarsa da ka yi. Ɓace min daga gabana, sakarai kawai, sai tsayi yawa bishiyar dabino, babu komai cikinsa sai rashin hankali.”

“Na gode Alhaji.”

Ya furta yana miƙewa, hannunsa a ƙeya yana sosawa.

Yana buɗe ƙofar zai fice, Hajiya kuma na sawo kai. Ta wara idon mamakin ganinsa, kafin kuma ta dalla masa harara ta wuce shi zuwa cikin falon.

“Alhaji me wannan yake yi anan? Uhm duk na tsorata da rashin ganinka jiya. Sai da na bincika aka ce mini ka bi Hammad ne.”

Wani kallo da ya watsa mata da ya sa ta zaunawa tana jin yadda ƙirjinta ke lugude.

“Me ya sa za ki ce ya auri Humaisa? Duk ina alƙawarin da kika mini za ki rufe sirrin nan har zuwa sa’adda zan furta masa da kaina? Me ya sa ma za ki ce mahaifiyarsa ce ta kashe ubansa. Yanzu gashi nan kin saka shi a mummunan hali ya fara shaye-shaye.”

Ƙoƙari ta yi ta danne dukkan tashin hankalinta, kafin kuma ta miƙe tana dawowa kusa da Alhajin. Cikin salon da ta san tana gamawa da zuciyarsa ta fara magana.

“Ka yi haƙuri Alhaji, hankali na ne ya tashi na ganin yadda yarinyar ke sonsa, ka sani ta san komai tun ranar da ta ji muna zancen da Hajiya Babba. Sannan maganar na faɗa masa Mahaifiyarsa ta kashe ubansa, ai kaima ka faɗa. Yanzu dai ayi haƙuri. Damuwata ɗaya, me yake yi anan shi da ya kamata ace yana Prison yanzu?”

“Mun samu mahaifiyarsa…”

“A ina!?”

Ta furta tana ƙoƙarin rasa nutsuwarta.

“Can wata unguwa take zaune A Watse Quarters. Ina karuwan nan Ashana da aka taɓa yi a Lagos?”

Gyaɗa kai ta yi da sauri..

“Ina jin labarinta lokacin muna ‘yammata, yanzu kam ai ta mutu ku, shekarun da yawa fa.”

“Tuba ta yi, ciwo ya kwantar da ita, ba ta mutu ba, haka ita ce mahaifiyar Hammad. Quraisha dai da kike jin labari ita ce ta koma Ashana…”

Da ƙyar ta haɗiye wani yawu muƙut! Jin yadda maƙogwaronta ya bushe. Girgiza kai take, inaaa! Aiko Humaisa za ta mutu ba za ta auri jinin karuwa ba. Dama ganin duk dukiyar Alhajin na ƙoƙarin zama tasa ce ta yi sha’awar haɗa auren. Yanzu kam ta haƙura, za kuma ta yi koma menene ganin Hammad ɗin ya bar gidan, ya koma can gurin mahaifiyarsa su ƙarasa rayuwar tare.

“…To saboda haka ne ya sa na dawo da shi gidan. A idon mahaifiyarsa ba zan iya ɗaure shi ba. Idan na gama bincike zan ɗau matakin da ya dace kan lamarin.”

Kalmomin Alhajin suka datse sauran tunanin da take. Ta ɗago tana saita idanuwanta kansa, kamar ta faɗa masa abin da ke ranta, na ya bar Hammad ga Mahaifiyarsa. Sai kuma ta haɗiye, a ƙasan zuciyarta tana tunanin abin yi.

*

Fitowarsa ke nan ya hangi fitowar Humaisa cikin gayunta za ta makaranta. Kau da kai ya yi tamkar bai ganta ba ya juya yana nufar ɓarinsa.

Da sauri ta ƙara takunta akan takalminta me shegen tudu ta sha gabansa.

“Yaya Hammad…”

Shiru ta yi tana ƙissima adadin kwanakin da ta yi bata ganshi ba. Fiye da wata guda ba inda ba ta je nemansa ba, haka cikin abokansa babu wanda ba ta tambaya ba.

“Ka yi haƙuri.”

Ta furta, idanuwanta na cikowa.

“Me kika min na ba ni haƙuri, ki wuce karki makara ko ba lecture gare ki ba?”

“Komai ya faru ni ce sila, ban san na yi wauta ba sai da na bar ganinka. Amma wallahi ni ban san lokacin da na fara sonka ba, duk abin da na faɗa maka a lokacin sun fito ne daga lungun zuciyata…”

“Ina wasa da ke ne Humaisa?”

Ya furta yana ƙara takunsa zuwa gabanta, sai ta zama ‘yar firit, duk da kuwa takalmin da ta saka ya taimaka wurin ƙara tsayinta iyakar ƙirjinsa.”

“Yaushe kika san zuciya har wani lungu gare ta? Karatu kike yi ko kuwa koyo kalaman fitsara? Ta ya ya kike zaton kallon da nake miki matsayin jinina zan iya canja shi zuwa wannan shirmen? Ba zai yiwu ba. Ki kauda tunanin nan kinji ko, akwai Abokina yana sonki, ki ba shi dama ya zo ku daidaita.”

Girgiza kai take yi alamun ba za ta iya ba. Hawayen suka zubo tasa bayan hannu tana share su.

“A’a, ba zan iya son wani bayan kai ba, ka kaini makarantar dan Allah…”

“Za ki wuce ko kuwa? Kinga motata anan ne, Ni kaina tunanin inda na barta nake. Me kike so ma wurin ɓarawo? Ina ce ba dake aka haɗa baki ana cuta ta ba.”

Ware ido ta yi sosai jin wani tsoro da ya shige ta. Ko da hasashe yake yi dole ta faɗa masa iyakar gaskiyarta ya san babu ita cikin lamarin. Dama ba dan an mata mugun gargaɗi ba da tuni ta faɗa wa Abbanta.

“Ban taɓa cutarka ba Yaya, Hajiya ce ranta ya ɓaci shi ne…”

“Humaisa!!! Me kike yi anan?”

Gaba ɗaya suka juya suna kallonta.

“Wuce ki tafi, ba na san sakarcin banza.”

Ta furta, tana dannawa Hammad harara.

Sum-sum ta juya ta tafi tana maida hawayenta.

Shi ma juyawar ya yi ba tare da ya ƙara kallon saitin Hajiyar ba. Tunda ya gane ba mahaifiyarsa ba ce, duk wani girma nata da ya rage cikin idanuwansa ya tsiyaye.

<< Asabe Reza 21Asabe Reza 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×