ALHAJI NAWAZUDDEEN
"Kin gane, yarinyar tana tunanin ni na kashe mahaifiyarta, amma wallahi zan dafa miki ƙur'ani ba ni ba ne, asalima bansan guba ba ce na bata, ba..."
Mikewar da ta yi a firgici tana komawa baya ya sashi ƙara dakatawa yana kallon yanayinta.
Sosai take jin tsoron shi tun da ya furta kisa.
Wato ya ma tashi daga uban shegu ya koma makashi?
'Tirƙashi'
Ta furta a ƙasan ranta, tana juyawa da gudu tana haɗa matattakalar benen da ba ta san yadda ta samu wannan ƙarfin ba.
Shi ma bai yi wata-wata. . .