Skip to content
Part 28 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

ALHAJI NAWAZUDDEEN

“Kin gane, yarinyar tana tunanin ni na kashe mahaifiyarta, amma wallahi zan dafa miki ƙur’ani ba ni ba ne, asalima bansan guba ba ce na bata, ba…”

Mikewar da ta yi a firgici tana komawa baya ya sashi ƙara dakatawa yana kallon yanayinta.

Sosai take jin tsoron shi tun da ya furta kisa.

Wato ya ma tashi daga uban shegu ya koma makashi?

‘Tirƙashi’

Ta furta a ƙasan ranta, tana juyawa da gudu tana haɗa matattakalar benen da ba ta san yadda ta samu wannan ƙarfin ba.

Shi ma bai yi wata-wata ba ya rufa mata baya da sauri.

Haamin da Haajir suka fashe kukan tsorata.

Nawaz cimmata ya yi tana shirin buɗe ƙofar ta shige. Da ƙarfinsa ya sa hannuwansa biyu yana danƙo kafaɗunta. Ya juyo da ita saitin fuskarsa. Zahiri yake hango girman tsoronsa da ke mamaye da ita saman fuskarta.

“Ya isa mana! Haba!! Shekararmu nawa tare wai? Menene ba ki sani ba nawa? Duk ina yardar? Dan Allah ki nutsu ki saurareni!!!”

Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin kwace jikinta daga hannuwansa. Ganin riƙon ba na Dattijon banza ba ne ya sa ta nutsuwa tana haɗa kalmomin da take son furtawar.

“Komai nisan zamanin da ka kwashe da mutum. Yarda na iya goge su a cikin sakanni biyun da wannan mutumin zai nuna rashin gaskiyarsa. Tsakani da Allah ban san yadda zan yarda da maganganunka ba.”

“Shi ya sa na ce ki karanta wasiƙar, wallahi za ki fahimci komai.”

“Me ya sa zan karanta abin da masoyiyarka ta aiko? Wai ma ta ya ya kake tunanin zan iya karanta wannan abin da bansan me ya ƙunsa ba. Na gaji da tashin hankalin. Yaran can biyu sun ishe ni, ba sai na ƙara da maganganun uwarsu ba.”

“Farida, da Allah fa na miki rantsuwa babu komai cikinta da ya danganci abin da kike zaton. Mu fa ba yara ba ne, ban san me ya sa kike ƙoƙarin mai da kanki daidai da shekarun Hamoud ba. Ashe ga inda Hamoud ya ɗauki taurin kai, muke ƙoƙarin tura shi ga Yaya?”

Shiru ta yi tana sunkuyar da kanta ƙasa. Tabbas su ɗin ba yara ba ne, sai dai ko waye zai ji kalar labarin nan ba zai san me zai aikata ba. Ita fa gani take na ta rikicin mai sauƙi ne idan ta kwatanta shi da wasu matan. Ƙaramin misali ma ƙawarta Hajiya Rufaida Umar, ace yau ta samu kalar wannan matsalar, tana rantsuwa da Allah za ta iya nakasta mijin saboda zafin zuciya. Allah ya kyauta kawai.

Takardar da ya miƙo mata ta katse tunaninta, ɗago wa ta yi ta kalle shi, daga bisa ni kuma ta karɓa, tana jin yadda zuciyarta ta buga, kayan cikinta suka dunƙule tamkar yaron ciki na naushinta. A haka ta warware wasiƙar ta fara karantawa.

Kanta haɗa karatun ta gama haɗa zufa. Tabbas komai ya bayyana. Fyaɗe aka ma mijinta, ya ilahi, wannan wace irin rayuwa ce? Sai kuma ta ji nauyinsa gabaɗaya ya lulluɓeta. Tana tuna ranar, a sume ta same shi a ɗaki. Sai dai babu wata alama da ke nuna anyi wani abu. Tana tuna yadda ya shafe fiye da wata cikin damuwa, tana zaton kan abin da sukai fashin nan, ashe ga dalili nan, tabbas babu namijin da zai iya furtawa matarsa an masa fyaɗe, duk kuwa girman yardar da ke tsakaninsu.

Riƙo hannuwanta ya yi yana janta suka sauka daga matattakalar benen. Idanuwanta suka sauka kan yaran da ke ta kuka. A karo na farko wani lamari mai girma da ke murɗe da tausayi ya ratsa ruhinta. Tabbas ta su kalar ƙaddarar ke nan. Ita ko me za ta iya idan ba godiya ga Lillahi azza wa jallah ba? Da sauri ta zare hannunta daga nasu ta isa gare su. A karo na farko ta jawo su jikinta cike da so da ƙauna, tana jin girman jinin mijinta da ya haɗa alaƙarta da yaran. Ƙannen Hamoud ne fa! Ɗa ɗaya tilo da ta iya mallaka a gabaɗaya rayuwarta!! Rarrashinsu ta hau yi har su kai shiru. Ƙarshe ma suka fara gyangyaɗii, nan ta shinfiɗe su saman kujerun falon.

Ƙarasawa ta yi kusa da shi ta zauna. Tana ganin yadda ya rame cikin awanni ƙalilan. A hankali ta zare hannuwansa da ya ɗora a kansa. Shi ɗin ma ɗagowa ya yi yana dubanta da idanuwansa da suka ƙara ja. Ya san mai take buƙata, dan haka ya gyara zama dan zuba mata bayani.
*

“Kin sani shekaru goma sha da suka gabata, ba ni da wani babban Amini kamar marigayi Alhaji Saleh Tumbi.

To, watarana ina zaune Ofis ɗi na naga kiran shi, yana nema na da na same shi a gidan gonansa da ke bayan gari. Ban tambaye shi dalili ba, saboda na san ta yiwu wasu sabbin harkokin suka ɓullo. Dan haka na aje komai na tafi.

Na isa a lokacin da shi ma ya iso, muka aje motocinmu a tare. A bayan mun gaisa ne ya ce zai kewaya zuwa can ciki inda kajinsa da tala-talonsa suke, Ni na ƙarasa ciki. Na ce masa to, na ƙarasa ɗin saboda na gaji, ba zan iya binsa zagaye wannan tafkeken gidan gonar mai cin fuloti fiye da goma ba.

Da shiga ta na tadda wata mace zaune a falon. Sallama na mata, ta amsa mini ina ganin yadda take maida a hawayenta.

Na zauna jim, kafin na ji sautinta tana tambayata ni Abokin Alhaji ne? Na ce mata I. Ta ce sunanta Bitil dan Allah in taimaka mata inyi magana da Alhajin ya bata adadin abin da suka yi na yarinyar da suka haifa tare, kuma ya bar yarinyar ta rayu da lafiyarta. Duk tana maganganun nan ne bayan ta sauko daga saman kujerarta ta haɗa hannuwanta cikin hawaye tana roƙona.

Na ɗago da mamaki ina kallonta saboda ban san Saleh yana neman mata ba. Ganin haka ya sa ta ba Ni labarin abin da ya haɗa su. Yanzu kuma yana mata gargaɗin ta ba shi yarinyar zai bawa dodon tsafinsa.

Hankali na ya tashi, saboda ban taɓa sanin Saleh yana tsafi ba, ko alama ban taɓa gani ba. Na san ai kina tuna ranar da na ware wata dukiya mai yawa cikin nawa, na ce akai gidan marayu, ki na tunawa? Har ki na faɗan yaushe na farfaɗo daga karayar arziki da zanyi wannan sadakar? Na miki shiru kawai. To, kinji dalili nan, wannan dukiyar, ta Saleh Tumbi ce da na san na karba muna harka.

To, anan na mata nasiha, na nuna mata duk ita ce ta ja, tun farko ita ta haɗa muguntar ta hanyar hana wacce ta kira da Ashana zaman lafiya harda shirka da Allah duk domin hana abin da ikon sa ne. Ita kuwa mugunta fitsarin fako ce. Sau tari kan wanda ya haɗa ɗin take komawa. Yanzu gashi wa gari ya waya? Sosai jikinta ya yi sanyi. Har ta ce mini In Sha Allah za ta nemi matar ta yafe mata. Za kuma ta tubarwa zunubanta. Yanzu dai na yi ƙoƙarin raba ta da Saleh, na mata alƙawarin hakan, na tabbatar mata ba ma ita ba, ko ni na bar shi ke nan har abada, idan har na masa nasiha bai ji ba.

Anan ta ce na kawo mata ruwa, ta duba fridge din falon babu ruwa. Na fita mu ka yi kicibis da Alhajin yana jikin motarsa. Ban nuna masa komai ba, na ce masa akwai baƙuwa tana buƙatar ruwa. Ina ganin sa’adda ya yi murmushi, ya ce shi ma yanzu yake shirin shigo mana da ruwan aka kira shi. Ya zura hannu a motarsa ya ɗauko wata gora guda ya ba ni. Ya ce mini yana nan zuwa. Ban ji komai ba na karɓa na kawowa matar. Ta buɗe ta sha. Hmm!”

Ya yi shiru yana murza goshinsa da yake jin tamkar zai rabe biyu. Ita ma a zakwaɗe ta riƙo hannuwansa tana masa kallon me ya faru?

” Guba ce a cikin ruwan Farida, guba mai ƙarfin da ban san ya zan kwatanta miki ba. Kurɓa biyu kawai ta yi gorar ta suɓuce daga hannunta ta faɗo ƙasa, tana riƙe maƙogwaronta, tana nuna Ni da hannu alamar Ni na yi poisoning nata, jini yana fita ta hancinta.

A daidai lokacin da zan ƙarasa gare ta cikin tashin hankali, na ji motsin mutum jikin tagar da ke duban wata duhuwa. Ƙarasawa na yi gurin da sauri na duba ban ga kowa ba. Dawowa na yi gareta, a kallo guda na gane har rai ya yi halinsa, hannuwanta na nuni da saitina a haka ta mutu. Ta mutu da burin neman gafarar shirkar da ta yi. Ta mutu da burin neman yafiyar matar da ta ɓatawa, duk da ban san ta ba, tabbas maganganunta sun nuna girman yadda ta saduda. Ashe lokaci ya ƙure mata, me zance? Me ya sa zan amsa ni na kashe Bitil? Ban sani ba ni ma.

A firgice na fito daga wurin, na tafi ina kallon gawarta da idanuwanta ke ƙafe kaina. Har gobe na kan yawan yin mafarki da ita.

Ban tadda Saleh Tumbi ba, sai dai motarsa, da sauri ni kam na shiga tawa motar na jata zuwa gida. Na kuma ba ki labarinta, sai dai bance miki ta mutu ba, ki na tuna ai ranar har kika ce na mata ƙoƙari kan Alhajin.

Ban san ya suka ƙare ba, ban kuma ƙara yin magana da Alhajin ba kasancewar na tafi Ethiopia, sai ma mutuwar sa da na ji a bayan wata biyu da faruwar lamarin.

Sai dai a yau na gane. Tabbas motsin nan da na ji na wani makusancin matar ne. Ta yiwu ya ga lokacin da na bata ruwan. Kin ga ke nan zai ɗauka ni na kashe ta. Ita kuma yarinyar da take yarta, take ɗaukar fansar mutuwar uwarta kaina. Shi ya sa ta shigo har cikin gida na a ci mini zarafi, ta kuma auri ɗa na, yanzu kuma take sonsa a bayan ta haihu da ni take so ta haihu da ɗa na ma ke nan? Kan hukuncin da banda haƙƙinsa.
Sai dai, abu guda nake mamakinsa har yau, wanene ya faɗa ma yarinyar ina da waɗannnan abubuwan da suka zo fashinsa? Ina jin ko wanene jinina ne. Sa’annan Hamoud kawai ya san na mallakesu da kuma inda suke.”

“Kawu Auwal ma ya sa ni.”

Ta furta da sauri, sai a bayan ta furta kuma ta riƙe kanta.

Kallonta yake yana jin yadda zuciyarsa ta buga. Auwal dai ƙaramin Ƙaninsa?

“Me kike nufi Farida, ban gane ba.”

“Ka yi haƙuri. A gaskiya mun dade da sani kawai mun ɓoye maka ne. Kuma yarinyar da Hamoud ɗin ke shirin aure yanzun ta faɗa masa, kasan suna da alaƙa da uwar yaran nan. Auwal shi ya turo su su zo su yi fashin. Ita kuma ta samu damar da take son samun. Mun ɓoye maka ne saboda gudun shiga tsakanin ‘yan uwa.”

Bai san ma mai zai ce ba. Tashin hankulan sun ishe shi haka nan. Ji yake kamar ya tarkata iyalinsa ya tafi ƙasar da ba za a ƙara jin ɗoriyarsa ba, ɗan uwansa fa, jininsa ke masa hassada? Har da turo yan fashin da sanadinsa duk wani abu da ke faruwa ya farun. Ya fi ƙarfin minti ashirin cikin wannan halin ya gaza magana.

Ita ɗin ma shiru ta yi hannuwanta saman kuncinta tana tunanin ya rayuwar za ta yi da su gaba? Cikin wannan duniyar mai cike da ruɗa ni. Duniyar da idan ta shimfiɗa maka tabarma nemi gefe kawai ka zauna. Saboda idan ta tashi naɗewa hantsilewa take yi. Ba za ta ce ka gyara za ta naɗe ba. Idan kuwa ka zauna tsakiyar ta, za a naɗe da kai ke nan. Ka yi zuwan asara, ka kuma koma da asarar.

Da wannan saƙe-saƙen na sun suka ga an turo ƙofar falon da ƙarfi ana ƙwallo da wani baƙin matashi. Sai da ya danganta shi da tsakiyar falon tukunna ya dakata, ya ɗaga kafarsa ya ɗora saman bayan gayen ya take. Ya ɗago yana kallon iyayensa da idanuwansa da ke cike da fitina. Kawu Ishaq, Kawu Husein, Kawu Auwal. Suka shigo a bayansa.

“Kai, kai, na ce ka kyale shi a haɗa shi da yan sanda kake ta tamaula da shi kamar ka samu kwallo ko, zuciya fa ba ta kai mutum guri mai kyau.”

Kawu ya furta yana takawa kusa da yaran da ke kwance. Da ƙarfi ya buga salallami yana kallon Nawaz da ya miƙe tsaye tun shigowarsa.

“Ikon Allah, Allahu Akbar Kabiran. Wallahi babu in da suka barka sa’ar da kake kamar su. Wannan yarinya wannan yarinya Allah ya tsine mata.”

Ya ƙarasa yana zama saman ɗaya daga cikin kujerun.

Nawaz da Farida da suka gama fahimtar komai suka zauna suma.

“Yanzu Hamoud ya je mini, ya faɗa mini dukkan abin da ke faruwa har abin da kai ba ka sani ba. Shi ya sa muka zo gabaɗaya don a tsaida magana guda.”

Hamoud gaya musu labarin da waccar ɗin ta baka.

A hankali ya ba su labarin duk abin da ya faru gidansu Reza. Yana gamawa Nawaz ya faɗa musu wanda ya faɗawa Farida.

Sun daɗe suna jinjina girman lamarin, kafin Nawaz ya dubi Hamoud Gayen da Hamoud ya take da ƙafarsa, ya ma daɗe da suma.

“Wannan fa?”

“Abba shi ne munafukin da Fakriyya ke aiki
da shi yana jiyo sirrikan gidan nan. Da shi ne kuma munafukan cikinmu ma suka taɓa amfani da shi. Bio sunansa.”

Ya furta yana sauke idanuwansa ɓarin da Kawu Auwal yake.

Ta ke ya sha jinin jikinsa, ya sadda kai ƙasa.

“Auwal! Ka ga abin da ka ja mini ko? Me za ka ce game da waɗannan yaran?”

Kakkausar Muryar Abba Nawaz ta ratsa falon.

“Ban gane ba, me Auwalun ya yi?”

Kawu ya furta ɗa rashin fahimta.

“Hmm! Shi ne silar komai da ya faru, shi ya fara kawo su cikin gidan nan…”

A hankali ya kwashe komai ya faɗa masa da matsalolin da ya yi ta samu a ƙasar da ya je duk dalilin fashin.

Kawu yana ta salallami, yana kallon Auwal da ya yi tsumu-tsumu.

“Tashi ka fita, daga yau ka fidda kanka cikin danginmu.”

Da ƙarfi Auwal ya miƙe yana ƙarasowa kusa da kawun. “Dan Allah ku yi haƙuri, sharrin shaiɗan ne.”

“To tunda ka ƙalawa shaiɗan sharri ka aje mini duk wani takadda ta Company da ka san Ni na ba ka. Ɓace mini da gani!”

“Yaya a bi a hankali dan Allah a yi hakuri mun san ya yi kuskure…”

“Husein, ba sai ka nuna mini Gyatumarku ɗaya ba. Idan hukuncin bai maka ba kai ma tashi ka bi shi.”

“Ba haka ba ne yaya.”

“Au to, na CE daga yau Auwalu ya fita daga zuri’armu, na kuma gama magana.”

Juyawa ya yi yana kallon yayansa Nawaz, a hankali kuma ya karasa yana ficewa daga gurin cike da tarin nadama.

Ganin ya fita ya sa Kawu sauke numfashi cikin takaici. Kafin kuma ya miƙe sosai saman kujerar yana haɗe yatsunsa.

“Yanzu Hamoud kamar yadda na maka alƙawari a yau ɗin za a ɗaura auren. Ita kuma uwar yaran ba dan ka nuna mini a barta ba da ina da damar da zansa a ɓatar da ita ma cikin Prison. Sai dai ta ci darajar waɗannan yaran biyu da ta kawo. Ta kuma ci darajar amintar da ke tsakanin ubanta da naka. Dan haka ka kira Hammad ɗin da ka ce muje a samu shi Kawun yarinyar komai ma ya ƙare. Ko kuna da magana?”

Ya furta yana sauke idanuwansa kan Mamy.

“A’a Kawu. Wallahi ni ma tunanin da nake ke nan, tun da auren nan ba ta so, to ta jawo dalilin da ya sa ma za a yi shi a yau ɗin. Sannan ka ce ita Quraishar ta yi alƙawarin mai da yaran nata da kai. To me ya fi wannan halicci? Macen da ba za ta bari a tozarta iyayenka ba ai ita ce mace. Ko ya ka ce Abban Hamoud?”

“Hakane, Allah ya dafa mana.”

Ya furta, duk da yana jin tsoron kalaman da ke cikin wasiƙar nan a ƙasan ransa. Bai san me ke ɓoye cikin ran yarinyar ba.

“To shi ke nan, bari muje, kai Nawaz yi zamanka. Kai kuma Hamoud kira yaron ya gayawa Kawun nasa za mu zo.”

Tafiya suka yi gidan Alhajin Hammad. Kafin su je ma har Hammad ɗin ya riga su isa, sun gama shirya sitting room din.

Ko da isar su take Alhajin ya karɓi komai kasancewar Hammad ya masa bayani.

Ana idar da sallar maghriba suka zauna
cikin masallacin da wasu ɗaiɗaikun mutane. Kawu ya dubi Hamoud.

“Jeka ka kawo goro da alewar da ke bayan motata.”

Yana jin yadda Hammad ke zungurinsa. “Kai Romeo ina ka sheƙa, ance ka kawo goren ɗaure Juliet.”

“Ka gane mana, wai kunya nake ji, je ka kawo Please…”

Ganin Kawu da ke can gefe suna ɗan ƙus-ƙus dinsu zai ɗago. Ya sa shi juyawa cikin rawar jiki yana ficewa daga gurin.

Ba ɓata lokaci ya dawo. A take aka ɗaura kan sadaki dubu Hamsin.

Addu’a suka ƙara yi kowa ya miƙe cikin farin ciki. Hamoud ma sai yanzu ya fara dariya, da gani yake kamar wani abu zai ƙara faruwa.

A haka suka fito shi da Hammad, yana ta tsokanarsa ya bari ya fara gayawa Juliet an ɗaura musu aure.

Alhajin Hammad ma ya ɗauki ƙullin goronsa ya yi gida.

Tana zaune a falo ya same ta, aje kayan hannunsa ya yi ya zauna kusa da ita. A daidai lokacin kuma kiran Soupy ya shigo wayarsa. Idanuwanta suka sauka kan hotanta gefenta kuma Alhajinta ne, wato ma a sunanta hotansu ya saka.

Yana shirin kai wayar kunne ta yi wata sufa ta warce wayar. Ta ƙara kallon hotan. Dattijon Mijinta ne da wata kututturar mata take gani.

“Kanbabban bala’innan. Abban Humaisa wace ce wannnan?”

Murmushi ya yi ya miƙe tsaye, ranar da yake jiran zuwanta ke nan dama.

“Matar da zan aura ce, ita ce wacce na faɗa miki tana kula da Maman Hammad…”

Sakin wayar ta yi ta fadi ƙasa, da sauri ta dafe kujerar da ke gefenta ganin wata juwa na shirin zubar da ita.

“Karuwa? Karuwa za ka aura?”

“Ke ahirr! Ta daɗe da tuba wannan.”

“Amma Alhaji ji bi fa yadda ka ke kashe Selfie da ita, tsofai-tsofai da kai. Saboda ALLAH me za ka yi da wannan guntuwar matar?”

Ta furta, hawaye na sauka har dokin wuyanta

“Ni ma fa guntun ne, kuma haka ki ka gani kika aure ni, dama guntu ai sai guntuwa. Tsufa kuma dama can ke kaɗai kike ganin tsufana.”

“Dan Allah ka yi haƙuri, na san dan na maka wancan lefin ne kake son hukunta ni. Ka yi mini kowane irin hukunci ne, amma ban da kishiya.”

“Sai ki yi kuma. Ni fa auran nan gobe ma za a ɗaura shi ko jibi. Karki damu ba gida guda zan aje ku ba. Ki gode Allah da ba Ashanar na ce zan aura ba, koma sa’ar Humaisa.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 27Asabe Reza 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×