"Soupy!
Soupy!!
Soupy!!!
I'm happyyyyyy, Haroun ya amince zai aureeeeeeeni."
Da haka ta shiga gidan, cikin ihun farin ciki
tana kwalama Soupy kira.
A hankali mutanen gidan suka fara fitowa kowa na son sanin abin da ya haddasawa shugabar tasu wannan ihun murnan.
Bata kula da su ba ta yi kan Soupy tana mai riko hannunta, ta fara kewaya gidan da ita tana dariya. Ita ma Soupyn da ba ta fahimci dalilin farin cikin sai ta biye mata suna ci gaba da kewaye tsakar gidan.
Har sai da juwa ta fara kamata, tukunna ta cika ta, ta tsaya. . .