Skip to content
Part 8 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

“Soupy!

Soupy!!

Soupy!!!

I’m happyyyyyy, Haroun ya amince zai aureeeeeeeni.”

Da haka ta shiga gidan, cikin ihun farin ciki 

tana kwalama Soupy kira.

A hankali mutanen gidan suka fara fitowa kowa na son sanin abin da ya haddasawa shugabar tasu wannan ihun murnan.

Bata kula da su ba ta yi kan Soupy tana mai riko hannunta, ta fara kewaya gidan da ita tana dariya. Ita ma Soupyn da ba ta fahimci dalilin farin cikin sai ta biye mata suna ci gaba da kewaye tsakar gidan.

Har sai da juwa ta fara kamata, tukunna ta cika ta, ta tsaya a saitin Bitil dake gefe, fuskarta a turbune tamkar haɗowar hadari a haka take hararar Ashanar.

“Aunty Bitil.”

A karo na farko Ashana ta kirata da Aunty.

“Ki share duk abubuwan da suka faru a baya, Ni nan da wata uku ma barin gidan zanyi, komai zai zama naki kamar yadda kika daɗe kina muradi. Ki manta ma anyi wata Ashana da ke yawan ɓata miki rai, ki tayani da murnan na gane me rayuwata take ciki, na gane girman zunubin da nake aikatawa, kema kuma zan so ki gane, ki yarda mu rushe gidan nan, kowa ya koma ga danginsa, hakane kawai zamu ji saukin haƙƙin yaran da suka ɓaci ta silarmu.”

Kallonta take zuciyarta na ƙara tafasa, kamar ba za ta tanka ba, sai kuma ta yanka ɗin.

“Ba zan taɓa barin gidan da mahaifiyata ta mutu a cikinsa ba, aka haifeni a cikinsa, idan ke za ki iya bari to fine, amma karki takura zuri’ar gidan, karki tarwatsa min gida dan kawai ke kin samu abin da kike muradi, karki aikata min wannan babban lefin Ashana!”

Ta faɗa, idanuwanta cike da gargaɗi.

Kafaɗarta ta ɗaga guda ɗaya cikin halin ko in kula, sai kuma ta waiga tana duban mutanen gidan.

“Ban ce ku ji maganata dole ba, na sani ba ni da ikon shiryar da kowane bawa, amma ina kira gareku da ku yi tunani a cikin hankalinku, ku gane abin da muke aikatawa babban zunubi ne da ban san ya zan kwatanta girmansa ba. Ni Quraisha ina umartarku da duk wacce ta gane illar abin da take yi, to ta kama kanta, ta kuma koma ga ahalinta, ta tsarkake tubanta, da sannu za mu samu rahmarsa idan mun yi ne domin tsira daga azabarsa.”

Kus-kus suka fara yi, kowa na komawa baya, alamun ba sa son barin gidan.

Murmushi Bitil ta yi tana kallonta, akai sa’a itama ɗin ta kalleta. Gyaɗa kanta ta yi, duk sai ta ji ranta ya ɓaci, a hakan ta juya zuwa ɗakinta, Soupy na take mata baya.

“Ke ma kina tare da Bitil ko? Ba za ki biyoni mu yi kyakkyawar rayuwa ba, har Allah ya kawo miki miji ki yi aure?”

Ta furta, tana tsare Soupy da idanuwa.

“Maa, ban san me zance miki ba, amma dai da sannu ni ma watarana zan fahimta, yadda kika fahimta ɗin. Karki ji haushi na, ban san me ya sa ba, ina jin kamar zunubi ne barin gidan nan, ina jin kamar idan na barshi mutuwa zanyi, ki yi haƙuri.”

Ta furta, idanuwanta na kawo ruwa.

Shiru ta yi tana dubanta, a hankali kuma sai ta jawota jikinta, ta rungumeta tana shafa bayanta alamun rarrashi.

“Na sani karki damu, ina tunanin akwai kafin da su Mama Kankana suka yiwa gidan, da dole sai ka shekara goman nan za ka iya barinsa, na miki alƙawari da sannu zan lalata komai, bari dai hankalina ya gama kwanciya.”

Gyaɗa kai ta yi tana murmushi, tana ƙara jin ƙaunar uwar ɗakin nata na ƙara zauna mata a kirji.

Bayan Wata Uku

A ranar Litinin, wacce ta yi daidai da 17 ga watan Yuli a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da cas’in da biyu (1992) ne aka ɗaura Auren Quraisha Ashana da Haroun Ali.

Sheikh Hariss shi ya zama walinta, Haroun kuma mai masallacinsu ya masa walicci, kasancewar ba shi da kowa, iyayensa sun daɗe da rasuwa, danginsa kuma suna ƙasar Habasha (Ethiopia) bai ma san yadda za ai ya same su ba, kasancewar mahaifansa ba su taɓa zuwa da shi ba, har suka koma ga mahalliccinsu.

A tsakar gidan ta tsaya mamaki take yi take ƙara yi, Haroun ya shammace ta, ba ta taɓa tunanin zai iya gyara gidan haka ba. Godiya kawai take yi ga ubangijin talikai da ya azurtata ta miji irinsa.

A haka ta ji ya rungumeta ta baya, kansa a dokin wuyanta yana shinshina gashinta.

“Mamakin na menene, tunda kika shigo kin kasa ƙarasawa cikin. Da fadlar Sheikh Hariss muka gyara gidan fa, shi ya tambayeni kan ina zan zauna, na ce masa a shagon da nake haya, ya ce to na kama hayar gidan gabaɗaya mana. To shi ne ya ba Ni tasa gudummawar ta hanyar biyan kudin hayar gidan har na shekara uku, ki gode masa Quraisha.”

Jinjina kai ta yi, yanayin jikinsa da ke manne jikinta, ke haifar mata da rashin nutsuwa.

“Kin san me?”

Ta ji muryarshi a saitin kunnenta.

“Ban san na fara sonki ba sai da kika yi wata uku ko hanyar da kika san za mu haɗu ba ki biyo ba, da gaske kin azabtarni, kullum fa ina layin gidanku, ko islamiyyar da kike zuwa akan idona kike wucewa. Sosai nake jinki araina Quraisha! Na roƙe ki da karki barni, komai sauyin da rayuwa za ta zo mana da shi.”

Ya furta, muryarsa ɗauke da wani yanayi me girma dake sake zauna mata a dukkan ruhinta.

“Ban san ta ya ya kake tunanin zan iya barinka ba, tunanin hakan kaɗai na sa zuciyata karaya inji gaba ɗaya rayuwar ba komai ba ce Haroun. Hatta mutuwa ina fatar ta ɗauke mu tare. Ban san yadda zan rayu a lokacin da babu kai ba.”

“Ban san me ke sani tunanin ba, amma dai to na daina, tunda baki so.”

“Ba ka faɗa min ba.”

“Me kuma?”

“Yadda akai kasan sunana na gaskiya.”

“Oh! Daman akwai sunan da ba na gaskiya ba?”

“Please mana, Quraisha fa nake nufi.”

Ta furta tana langaɓe kanta.

“Da me za ki biya ni idan na faɗa.”

Ya furta yana rungume hannuwansa

“Rufe idonka ka ji to.”

Rufewar ya yi, a sannu ya ji saukar tausassun laɓɓanta saman nasa.

Tsigar jikinsa ya ji ta tashi, har bai san sa’adda ya jawo ta jikinsa gaba ɗaya ba.

“Ni ma sai na rama.”

Kwacewa ta yi tana guduwa gefe, hannunta saman fuskarta alamun kunya.

“Ka bari mana, tsakar gida ne fa, wani zai shigo.”

Riƙe baki ya yi yana dubanta, sai ya zame mata kamar mace

“To ba zan faɗa ba, ji wai Ni za ki yiwa wayo.”

“To fara faɗa mini, ka ji.”

“Na ji, amma da sharaɗi, ba za ki damu ba duk abin da zan faɗa miki.”

“Eh na yarda.”

Ta furta, tana mai do da hankalinta gaba ɗaya kansa.

“A tun ranar da kika furta kina so na, na shiga bincike kan dukkan rayuwarki ta hanyar ƙawarki Zenabu.

Ita ta faɗa mini asalin sunanki da abin da ya sa kika baro garinku. Ki yi hakuri, na ji na tsaneki a wannan lokacin, yadda har za ki iya baro jaririnki ki kuma cakawa mahaifinsa abin da kika san zai iya mutuwa.

Hankalina bai kwanta ba har sai da na je garin naku…”

Ya dakata ganin ta ɗago da gigita hawayen har sun fara sauka.

“Kin gani ko, zan fasa wallahi, mene na kukan?”

Girgiza kai take yi ta kasa magana.

Ya san me take son ji, dan haka ya dora

“… Da kwatancen da Zenabu ta ba Ni, na gane gidan ahalinki, sun karɓe Ni fiye da tunaninki musamman da suka ji na ce Ni ne zan aure ki, sun yi nadamar abin da suka aikata gareki da ya yi silar guduwarki.

Anan suka tabbatar mini da mijinki bai mutu ba a wannan lokacin, sai bayan shekara biyar ya rasu, tarin Tibi ne silar mutuwar.

Na tambayesu game da yaron da kika bari, suka tabbatar mini ba su san inda yake, tun bayan rasuwar uban, wani ƙanin uban ya ɗauke shi suka tafi birni, ba su ƙara jin doriyarsa…”

Yadda ta ƙanƙame shi tana gunjin kuka ya sa shi dakatawa yana bubbuga bayanta a hankali.

“Ki yi shiru mana, namiji ne fa, zai nemiki duk daren daɗewa.”Ko fa sunansa ban sani ba Haroun, babansa ya mutu yana fushi da ni, ta yaya yaron nan zai yafe mini? Na baro shi tun kan ya san gardin nonon uwa.”na

“Sun faɗa mini sunansa fa, kinji ko Hammad? Ko Hamoud? Kai na dai manta. Amma wallahi na so yana nan, da sai dai ki ganshi a gurina, karki damu, bayan watanni sai muje mu binciki dangin mahaifin, ai sun san inda za a same shi.”

Gyaɗa kai ta yi, a hankali kuma ta ji ya fara mata abin da ta fara hango kanta a gajimare

“Ba fa kuyi sallar isha ba.”

“Wai ke ina ruwanki da ni ne?”

Ya furta yana mata ɗaukar yar tsana zuwa cikin ɗakin.

Ya yi nisa cikin sha’aninsa ya fara jiyo bugun ƙofar, a tare suka miƙe yana ƙoƙarin mai da rigarsa.

“Oh ni, wai mutane ba su san Ni ango ba ne?”

“Dariya ta yi, tana ganin yadda yake ƙunci.

“Oh ni, wai mutum bai san na zama tashi ba ne har gaban abada?”.

Ta furta, da salon muryarsa, cike da tsokana.

Kwafa ya yi, “Bari na dawo za ki sani ne.”

Ya furta yana dosar ƙofar.

“Ba ka ji ba.”

Ta furta, tana ƙunshe bakinta.

“Wai meye ne? Sauri nake fa.”

“Rigar fa a baibai kasa, ga kumatunka duk jambakina, haka za ka fita, yawwa! Ba ka ma fa tsarkake jikin ka ba.”

“Oh ni Allah, wallahi duk kin ruɗani, tsarki kuma me ruwanki, CE miki akai na gama?”

Ya furta, yana ƙoƙarin kwaɓe rigar.

A bayansa ya ji ta, ta rungume shi.

Juyowa ya yi yana kallonta duk ta yi wani sanyi.

“Mene kuma? Kina jin yadda bugun ƙofar ke yawa fa?”

“Kawai ji na yi ba na so ka fita.”

Tsai ya yi, yana dubanta.

“To ko a kyale, idan aka gaji da bugun ba a buɗe ba, an tafi?”

“A’a ba a haka, baka san ko muhimmin abu ba ne, jeka kawai”

Kallonta yake, yana kallon hannunsa da ta riƙe tana cewa ya je.

“Ba ki sake Ni ba, kina cewa in je kuma.”

“Oh, ban kula ba.”

Ta faɗa, tana zare hannun a hankali.

Juyawa ya yi har ya kai zauren ya ji muryarta.

“Na roƙe ka, duk tsananin rayuwa ka da ka bar ni.”

Juyowa ya yi yana kallon yanayinta, ga sautin bugun ƙofar na ƙara ratsa kunnuwansu.

“Ni dai dan Allah ki koma ciki, ba ki san ko tsuntsaye ba na son suna gane min ke ba, yanzu fa zan dawo.”

Juyawa ta yi tana komawa ciki.

Shi kuma ya ƙarasa yana buɗe ƙofar.

Yaro ne tsaye, hannunsa ɗauke da wani babban Jug.

“Gashi, Alhajin wancan gidan ya ce in kawo maka, hajiya ce ta kawo tsarabar, aka yi harda kai.”

Karɓa ya yi yana kallon gidan Alhajin da yake nuna masa.

Ba yau ya saba aiko masa furar ba indai Hajiyar ta kawo. Sosai mutumin ke ji da shi, kasancewar shi ke biyawa ya’yansa Ƙur’ani.

“To ka ce masa na gode, zan shigo masa gobe. Amma kai bantaɓa ganinka ba a unguwar nan, yaushe ka zo?”

“Jiya na zo, ina bara ne.”

yaron ya furta yana juyawa.

Shi ma komawa ciki ya yi, yana mai saka sakatar ƙofar.

“Kina ina ne? Fito ta samu, kawo mana cups.”

Miƙewa ta yi tana kallon abin da ke hannunsa.

“Me muka samu, har na ji yunwata ta watannin baya ta taso.”

“Fura ce damammiya, idan kika sha sai kin mance kunnenki dan dadi, ina ji harda dabino suke yinta.”

“Dariya ta kama yi ganin yana santi tun kafin ya sha.”

“Ba fa yau na saba sha ba, kike mini dariya, duk sanda suka dama suna ba Ni, kurɓi kiji” 

Ya furta yana miƙa mata

Karɓa ta yi, a hankali takai bakinta ta kurɓa.

Zare ido ta yi, kafin kuma ta fara ƙoƙarin furzo ta, sai dai tuni ta wace cikin maƙogwaranta, ta haɗiye da ƙyar.

Tunda take, bata taɓa shan mummunar fura irin wannan ba, babu daɗi ko kaɗan.

“Ya na ga kina zare ido, dadi ko?”

“Eh”

Ta furta tana ƙumshe bakinta, “sha ka ji.”

Kai Jug din ya yi bakinsa, ya yi kyakkyawar kurɓa irin shan muguntar nan. 

Da ƙyar ya haɗiye yana kallonta yadda take masa dariya.

“Ba irin ta ba ce wannan ai, me ke faruwa ne?”

Ya furta, ganin yadda take dariya ya sa ransa fara ɓaci, a hankali kuma ya ji kansa na juyawa, ya dafe kansa yana zama gefen gadon, bakinsa na ambaton Allah.

Ita ma tsit ta yi, haka kawai ta ga yana zame mata abin tsoro.

Kan ta farga ta ganshi gabanta, ya sa hannu ya keta rigar barcinta har ƙasa, a haka ya fara ƙoƙarin haiƙe mata da dukkan ƙarfinsa.

Ji ta yi ba ta so, duk wata sha’awarsa ta ji ba ta yi, tana kici-kici, tana ce masa bata so, sai dai ina, abu yake yi tamkar baya hayyacinsa, da ta matsa masa ma, yana ruwan cikinta ta ji ya tofa mata yawu a fuska. Da ya gama cimma burinsa ya miƙe cike da kyankyami yana hankaɗata, duk wani sanyin rai, tausayi, ya kau a zuciyarsa.

Itama kallonsa take, bakin ciki ke lullubeta, ita Haroun ya tofawa miyau? Miƙewa ta yi za ta yi magana ta ji saukar hannunsa a fuskarta, ya tsinka mata mari, kanta farga, ya ƙara zuba mata wani.

“Dan ubanki, gidan ubanwa kika kai budurcinki da za ki zo mini a fanko, wa kika taɓa bawa kanki?”

Kallonsa take yi, hawayen na sauka saman fuskarta, hannunta dafe da kuncinta.

‘wane budurci kuma yake nema ita da bata shigo duniya ba ma sai da ta yi aure ta haihu? Me ke faruwa ne?’

Kar ku manta da comment da danna taurarin nan! 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 7Asabe Reza 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×