Skip to content
Part 9 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

Ta hadiye wani mugun yawu mai daci tana jin kamar duk wata masifar duniya na sauka saman kanta. 

“Haroun ka manta bazawara ka aure Ni.”

Bazawarar ubanki? Yaushe kika ce min ke bazawara ce munafuka? Wallahi za ki nadamar aure na, ba zan taɓa barinki ba, amma kam sai kin gwammace da ma baki taɓa sani na ba, yar tasha kawai, dabba, Mahaukaciya, me ya da budurcinta a titi.
Ya faɗa yana mai barin ɗakin.

A dandaryar ƙasan ta durƙushe, tashin hankalin da bata san ƙarshensa ba take jinjinawa, me ke faruwa ne? Kuka take sosai tana nadamar komai da ta yi na rayuwarta. Tunda ta wanzu duniya, bata taɓa ganin baƙin dare irin wannan daren ba. A daren amarcinta komai ya ɓaci tsakaninta da mijinta.

A haka ta kwana a zaune, shi kuma yana tsakar gidan anan ya kwanta tsabar ya tsani ganinta.

Rayuwa ta ma Quraisha juyin waina, komai ya canja ta yadda bata taɓa tsammani ba, ta tashi daga Ashana ‘yar kwalisa, ta koma wata halittar daban, harta tufafi gagararta yake tsabar babun da take ciki.

A cikin shekara gudar da ta kwashe gidan Haroun ba taɓa sanin wani abu farin ciki ba, ya hanata hulɗa da kowa, kai ƙarewa a gabanta ya ma Soupy dukan tsiya saboda ta zo wurinta.

Babu abin da ke haɗata da shi, sai idan tashi ta ciyosa ya zo ya haiƙe mata, ya gama ya yi ficewarsa.
Abu ɗaya ke tada mata hankali yadda dukkan ibadarsa ta tafi, yanzu ko sallah ce sai tana faɗa masa anyi sallah fa, tukunna zai tashi ya yi bayan ya gama zageta tas!

Tasha fakar idonsa ta tafi tallar ruwa a lokacin ana kullasa a leda santana, haka za tai ta zagaya tasha ana siya ficika-ficika domin kawai ta samu abin da zata ci abinci.

Tasha zuwa gidajen mutane wankau ko surfe, dan kawai ta rufa ma kanta asiri.

Tasha haɗuwa da abokan harkarta, ciki harda officer suna roƙarta, da ta baro mijinta, ta zo ta ci gaba da harkarta cikin rayuwa me kyau.
Sai dai ina, zuciyarta ta yi imanin da ba zata ƙara komawa zina ba duk tsananin da rayuwa za ta mata, ta yarda ta mutu tare da gallazawar Haroun, ba za ta ma iya barinsa a wannan halin da ibadarsa ma sai an tuna masa ba, tana jin komai ya faru da shi ita ce sila, Haroun ba haka yake ba, akwai sanadin da ya watsa rayuwar mijinta kamar yadda Soupy ta taɓa gaya mata.

Sai dai wanene?

A haka take rayuwa kowacce rana akwai kalar tashin hankalin da zai zo mata.

Har zuwa yau da suke shekara biyu na aurensu, ta gane tana ɗauke da ciki, tana ɗauke da jinin Haroun.

Farin ciki take, tana jin kamar ma damuwarta ta ƙare, motsi kadan sai ta shafa cikin soyayyar abin da ke ciki na zauna mata a rai.

A haka Haroun ya shigo ta doshe shi da batun.

A karon farko tun zamansu tare da ta ga ya kawo hannunsa daidai cikinta fuskarsa cike da murmushi.

Sai dai yana ɗora hannunsa taga ya janye kamar wanda ya taɓa shocking, Fuskarsa a turɓune yana dubanta.

“Na ji, Allah raya, idan ba za ki iya kula da shi ba za ki iya zubarwa, kin sani banda komai, idan ma ina da, ba zan kula da abin da ban san tabbatuwarsa nawa ba ne.”

Ya furta, yana juyawa akan takunsa, ya fice daga gidan.

Durƙushewa kawai ta yi tana dukan kanta a jikin bango, bata taɓa zaton Haroun zai iya haramta cikin da yake nasa ne, wace irin masifa ce wannan, ba za ta yafe ba, ba zata taɓa yafewa wanda ya sata a wannan halin ba.

Haka ta ci gaba da kula da cikinta har zuwa ranar da ta tashi da ciwon da bata taɓa sanin akwai irinsa a duniya ba, Haroun yana kwance take jan ƙafarsa da ya taimaka mata.

Miƙewa ya yi yana dubanta, bai san me ke danne rayuwarsa ba, gaba ɗaya baya ma tuna wanene shi, kallonta yake tausayinta ke son rinjiyar abin da yake ji na danne zuciyarsa, miƙewa ya yi ya kai hannu zai dafa ta, a take ya ji wata irin wutar tsanarta ta ratsa ilahirin jikinsa, tamkar gwaggwan biri haka take zame masa.

Bai san me ya sa ya ji hawayen na sauka akan kuncinsa ba, wani abu ke ingiza shi da ya tafi, ya tafi kawai, ya yi ta tafiya inda ba zai sake ganinta ba, a haka ya fara ficewa yana kallonta, tana hawayen azabar naƙudar, yana hawayen da bai san dalilin zubarsu ba, a haka ya fice daga gidan, yana nausawa inda dukkan zuciyarsa ke ingiza shi.

A tunaninta mutane ya tafi kawo mata, ganin har sa’o’i biyu sun shuɗe bai dawo ba ya sata fara tunanin neman mafita, adaddafe ta miƙe jin ciwon ya lafa mata, Soupy take son Kira, Dan haka ta fice cikin talatainin daren, tana bin bango, tana durƙushewa, tana miƙewa, a haka ta ƙarasa
Titin, ta daɗe a durƙushe kafin ta samu ɗan taxi da ya dauketa zuwa gidan.

A tsakar gidan ta zube jin ciwon ya ƙara taso mata, bakinta na kiran sunan Soupy.

Fitowa mutanen gidan suka fara yi, ciki harda Bitil rungume da ɗiya a hannunta da ba za ta gaza shekara ɗaya ba.

Soupy ta yi saurin ƙarasawa tana tallafarta, ta ɗago tana kallon Bitil da ke tsaye ko gezau.

“Asibiti fa za a kaita, naƙuda take, da alamun ba za ta iya haihuwa da kanta ba.”

Ta furta, idanuwanta akan Bitil.

Yarinyar Hannunta ta dire a ƙasa, ta tashi tana tsayuwa saitin Ashana.

“Amma kinsan dokar gidan nan, idan mutum ya bar sa, babu wata alaƙa da za a sake yi da shi ko? To ba za a kaita ba, uban wani ya kaita yin auren?”

“Amma kinsan wannan larura ce ko, ki duba ga Fakriyya nan kema kin haifa, na sani kin san zafin haihuwa da shi kan shi ɗan. Me ya sa ba za ki ji tausayinta ba…”

“Soupy!”

Ta furta a kausashe tana zare idanuwanta.

“Fakriyya da na haifa waya san ubanta? Ita kuwa wannan da take naƙudar ai yana da uba, kuma haƙƙinsa ne, ki rufe min bakin ki anan kafin na sauke miki abin da ke kanki, magana ce na gama, asibiti ba za aje ba, In za ta iya ta haihu anan to, so nake ita ma ta ɗanɗana zafin da na ji ya yin da take shugabancin gidan nan, alhalin Ni ya kamata in gada.”

“Maa a tausaya mata, kalli yadda ruwa ki zuba ta ƙasanta.”

“Linda!”

Ta furta a tsawace.

“Ki rufe min tsattsaman bakinki anan, tausayin ne bana yi.”

“Ku kuma duk wanda ya sa hannunsa a haihuwar Ashana, akwai irin hukuncin da zan masa, ku bace min da gani.”

Ta faɗa tana sunkutar ‘yarta ta koma ɗaki, sauran ma sum-sum suka fara watsewa.

Gurin ya rage daga Soupy sai Linda.

A hankali Linda ta matso kusa da Soupy, a daidai kunnenta ta faɗa mata abin da za ta yi. Ta juya ita ma zuwa cikin ɗakin.

Kwantar da Ashana ta yi a tsakar gidan, ta fice da sauri zuwa gidan matar da Linda ta kwatanta mata.

A take sai gasu sun dawo, sai dai kafin su maida ta ɗakin, naƙudar ta taso mata da wani irin ƙarfi, kan ka ce me ne wannan sai ga kai ya fito, da taimakon matar aka ƙarasa jawo babyn.

Hawaye Soupy ke yi tana kallon kyakkyawar ɗiyar.

Ashana ta kalla dake ta sauke numfashi.

A idanuwanta ta gane tana son sanin me ta haifa.

Diya ce gata nan, ke da Haroun duk kun bayyana a siffarta.

Murmushi ta yi da ƙyar tana cije bakinta.

“Ji nake kamar ana daddatsa bayana Soupy, ciwo nake ji kamar tafiya zanyi in da ban zan sake wanzuwa…”

Shiru ta yi tana mai da numfashinta da ke kakkatsewa.

Soupy na hawaye haka take girgiza mata kai tana sake ƙanƙame jaririyar.

“Ki riƙen amanarta Soupy! Duk rintsin rayuwa karki barta ta aikata abin da na yi, karki barta ta yi zina dan Allah, ki maida mata sunana, ki kirata da Quraisha Haroun Ali, idan kinga mahaifinta ki basa ita, ki faɗa masa jininsa ce, ya rayu da ita domin ta tashi tana gujewa zina…”

<< Prev | Next >>

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 8Asabe Reza 10 >>

1 thought on “Asabe Reza 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×