Ta hadiye wani mugun yawu mai daci tana jin kamar duk wata masifar duniya na sauka saman kanta.
"Haroun ka manta bazawara ka aure Ni."
Bazawarar ubanki? Yaushe kika ce min ke bazawara ce munafuka? Wallahi za ki nadamar aure na, ba zan taɓa barinki ba, amma kam sai kin gwammace da ma baki taɓa sani na ba, yar tasha kawai, dabba, Mahaukaciya, me ya da budurcinta a titi.Ya faɗa yana mai barin ɗakin.
A dandaryar ƙasan ta durƙushe, tashin hankalin da bata san ƙarshensa ba take jinjinawa, me ke faruwa ne? Kuka take. . .
Wow great writer