Skip to content
Part 15 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

HAMOUD

A hankali ya buɗe idanuwansa, kansa da ya yi gingimeme ya rike yana miƙewa, mamaki yake yadda har tara ta wuce yana nannauyan barcin.

Abubuwan suka fara dawo masa tas-tas suna ƙara tunzura zuciyarsa.

Toilet ya faɗa ya saki shawa, ya fito ya shirya, ya nufi gidansu.

Mamynsa yake son gani, ya sani ita kaɗai ce zai ganta yaji sauƙin raɗaɗin zuciyarsa.

A falon ya tadda ta, tana zaune da Hisnul-muslim a hannunta tana dubawa, a gabanta ya zube yana ɗora kansa saman cinyarta.

Hawayensa ta ji a cinyarta da ɗuminsu ya sata ɗago da kansa tana kallon tilon ɗan nata, tana ganin yadda ya firgice a rana guda.

“Me ya samu jarumina, ina Jarumtar kake kuka kamar mace, me ya saka zubar hawaye Hamoud, wane abu ne me wannan girman, ina kabar tarin addu’o’in da na koya maka na kauda damuwa? Ina ita matar taka?”

“Na sake ta…”

Ya furta, yana jin ɗacin kalmar  a ƙasan zuciyarsa.

Ganin yadda abin ya sata yin shiru, ya sa ya kkranto mata tiryan-tiryan, tundaga ranar walimarsu da yaga ASABE.

Sai dai ya ɓoye abu, abu me girman da ba zai iya duban tsabar idon mahaifiyar tasa ya gaya mata ba, abu mai girman da ke ƙoƙarin sa shi ya yi aman kayan cikinsa.

“Ban san yadda zan iya yafewa Kawu ba Mamy.”

Salati take, tana jinjina lamarin.

“A barshi da mai duka, ko da wasa, kada ka furta wannan zancen ga mahaifinka, ba zamu shiga tsakanin yan uwa ba, mu barshi, da sannu asirinsa zai tono a idon mahaifinka. Ita kuma ka yi daidai da ka sawwake mata, tirr! Da auren irin waɗannan matan. Ka gode Allah da asirinta ya tono ba tare da kayi wata alaƙa da ita ba.”

“Ita kuma wacce ka ce ta faɗa makan yar uwarta ce ne?”

Ɗagowa ya yi yana kallonta, sai kuma ya miƙe da sauri yana goge fuskarsa.

“Mamy bari zan dawo gobe, na tuna abu, na tuna abin da zanwa FAKRIYYA da zan fanshe dukkan damuwata. Za tai nadama wallahi.”

Tana kwala masa kira haka ya juya da sassarfa ya fice.

Jan motar yake yana jin yadda nutsuwa ke sauko masa, yarinyar yake tunawa da Fakriyya ta ce masa REZA sunanta, sunan ya jinjina a ƙasan ransa a karo na farko, tabbas kuwa REZAR ce, da zai yi amfani da kaifinta gurin daddatsa tunanin Fakriyya.

Buga sitiyarin ya yi, da murmushi a ƙasan zuciyarsa, sa’ilin da ya hango kalar kishi irin na FAKRIYYA.

5:30 PM


HAMOUDI

A hankali yake gangarowa cikin layin, ya samu guri me kyau ya aje motarsa. Ya fito yana ƙarewa unguwar kallo.

A kan gidansu Fakriyya ya aje idanuwansa, abubuwa masu tarin yawa yake tunawa da suka gudanar a gurin, asalima a cikin gate ɗin ya fara furta mata kalmar so.

Numfashi yaja ya furzar jin ɓacin ran na ƙara taso masa, a hankali ya fara takawa yana kusantar jerin gwanon gidajen, so yake ya samu yaron da zai tambaya ya nuna masa gidansu Reza, ya sani sarai unguwarsu guda da Fakriyyar.

Wani ya hango can nesa a kwance saman mota, da sauri ya ƙarasa gare shi, yanayin da yaga gayen a ciki ya sashi dakatawa yana tunanin yadda zai tambaye shi.

“Yaaahhh…Baabah ƙaraso mana…Ya ka tsaya kana min zikiri a saman kai…Na sani kai ma damuwa gareka koh? To zo ka ɗaga kwalbar nan ka kwankwaɗe ka ji yadda za ka na hango kanka a duniyar Mars…”

Gayen ya furta yana ƙara bajewa saman motar, da kwalbar giya a hannunsa ya shanye fiye da rabinta.

Kallonsa yake yi, ga kyawu har kyawu, amma ya zaɓi rayuwar da ba za ta amfane shi da komai ba.

Ya ja tsaki sanin baya fahimtar zancensa.

“Gidansu wata Reza nake nema, a layin nan take, ko ka santa?”

Ɗagowa Gayen ya yi, yana buɗe idanuwansa da suka ƙanƙance da ƙyar.

“Reza mai kaifin baki…Kowa ya hau ki karkace ya taɓe. Kafin ya farga kin yi mar illa. In ji gwani na, ɗan tuna min sunansa mana Baabah…”

“Yawwa! SANI SABULUUU…”

“Ka san fa shi ya haifi kakana na Bakwai ko?”

“Na sani, gashi nan kuna kama, ina gidansu REZAR?”

Hamoudi ya furta da murmushi, yana tura hannunsa a aljihu.

“Idan ka miƙe wancan layin kayi kwana, ka ƙara miƙewa kayi kwana, zaka ga wani ƙatoton Shop, ka ce a baka Reza… Amma da ka tsaya na maka aikin da Rezar za ta maka, Ni ma na iya yankan farce…”

Tsaki yaja me ƙarfi, ya gama ɓata masa lokaci, bai kuma amfane shi da komai ba. Akwai alamun bai gwanance da shaye-shayen ba shi ya sa giyar ta bugar shi sosai.

“Allah ya shiryeka, Ni mace nake nema ba shirmenka ba, ka gyara rayuwarka, sam! Ba ta da ce da kai ba.”

Ya furta yana juyawa.

“Ba ka ji ba Baabah…”

Gayen ya furta yana saukowa daga motar cikin tangaɗi.

“Ka ga wannan jerin bukkokin?”

Ya furta yana nuna ɓarin gidansu Fakriyya.

“Bari dai na ga, ɗaya, biyu, uku, hudu, biyar, yawwa shiga wancan gidan, ina jin za ka ga Rezar.”

Ba tare da ya yarda gidan ba ne, ya juya yana kusantar gidan da ya kwatanta masan.

Madannin jaras ya gani a waje, dan haka ya danna. Bai daɗe da fara dannawarba wata ‘yar kututturar mata ta buɗe.

Ware idanuwanta ta yi sosai tana kallonsa, sai kuma ta buɗa masa hanya, ya shiga cikin farfajiyar gidan.

“Da Allah Reza nake nema, ko tana ciki?”

“Eh zauna, bari na kira ta.”

Ta furta, tana nuna masa fararen kujerun dake gurin.

Ya zauna yana mamakin yadda tsarin gidan yake sak irin nasu Fakriyya, ‘lalle bariki ta daɗe tana kaɗa ganginta cikin unguwar nan.’

Juyawa ta yi da hanzari tana dosar cikin gidan, farin ciki ke damalmala ruhinta har bata san yadda za ta kwatanta shi ba, da haka ta tura ƙofar,

tana zaune gaban mirror da aka gyara aka saka sabon mudubi, ta yi kyau harta gaji da yinsa, bakin nan ya yi raɗau da jambaki.

“Kin shirya a daidai! Hamoud ke zaune waje yana nemanki, meke faruwa ne shi da yake ikirarin bai sanki ba?”

Murmushi ta yi tana cije leɓenta na ƙasa.

“Na sani ai, na san zai zo nemana.”

“Ban gane ba, kinsan da zuwansa ke nan?”

“Kalli wannan.”

Ta furta tana tura mata wani copyn hoton Fakriyya da Disco.

“God!” Ta furta tana wani irin juyi.

“Ba dai wannan kika nuna masa ba, wai! Reza ba ki jin magana, kin min daidai fa, dole anjima na leƙa gidan Linda na masu ta’aziyyar mutuwar auren.”

Ta ƙarasa ƙasa-ƙasa gudun kar Quraisha ta ji su.

“Yanzu sai ki je ai, Allah ya sa da abin ya zo.”

“Haba yanzu duk wannan yatsun nasa da nasha sai ki ce inje? Ce masa barci nake, ya jirani nan da 7:30 idan zai iya. Ba ma fa lallai ya sake ta ba kike ta murna.”

“Yo ai daidai ke nan, ya aure ku duka ku biyun a zuba bala’i, ke tsaya ma, Hamoud ɗin kike cewa ya jira ki? Duk ina haukar son, karfa ki ƙara rasa shi.”

“Ba za ki gane ba ne Soupy, faɗa masa kawai, ki yi kallo.”

Ta furta da murmushi tana tuna Haisam.

Juyawa ta yi ta fice.

Ita kuma ta miƙa hannu za ta ɗau gashinta na doki, sai dai wayam babu, dube-dube ta hau yi, har ƙasan madubin amma babu, yanzu fa ta fiddo shi ta ɗora saman madubin, to ina ya shiga?

‘Haisam’ Ta furta a ƙasan zuciyarta da bayyanan nan murmushi saman fuskarta.

“Ka ba Ni dan Allah, na san kai ka ɗauka.”

Ta furta tana dube-dube, motsi ta ji cikin Toilet da sauri ta ƙarasa, kafin ta buɗe ma ya fito, da gashin a hannunsa.

“Ya Allah! Ta furta tana ƙare masa kallo, ya yi kyau har ya gaji, yana ta walwali cikin Alkyabbar, ga Kambu da aka ɗora a saman kansa wanda aka ƙerashi da ɗanyen Jauhari.

“Yanzu aka gama bikin naɗin sarauta ta, na zo in faɗa miki naga kin fiddo wannan abin za ki saka, na hana fa, babu kyawu, kin kuma sani.”
“Ni dai ka ba ni, daga yau fa shi ke nan, kwalliya zanyi da shi, In jewa Hamoud da ke waje.”

“Hamoud!” Ya furta, launin idanuwansa na canjawa, har sai da ta yi baya da tsoro.

“Na ga zuwansa, amma kin san me?”

Girgiza kai ta yi a hankali.

“Ki daina ambatar sa idan ina guri, Ni ma ba zan shiga rayuwarku ba, ba za ki gane me nake ji ba ne, da ƙyar fa nake tausasa zuciyata, ba dan haka ba, da tuni na daɗe da ɓatar shi a duniyar nan.”

“Amma kai fa ka ce in aure shi? Ka san kana kishina har haka me ya sa ba za ka yadda muyi aure ba?”

“Saboda ba zai yiwu ba, Ni ba azzalumi ba ne. Yanzu dai abar maganar, muje ki ga yadda zan gyara miki gashin, ba sai kinsa wannan abin da ke ƙara kawo mugayen cikinmu rayuwarku ba.”

Ƙarasawa suka yi bakin mudubin, ya ja mata kujerar ta zauna, ya tsaya daga bayanta.

“To rufe idanuwanki, karki kalli mudubin.”

“A’a Ni dai, ka barni naga yadda za ka yimin.”

“Oh to za mu gani.”

Ya furta yana ɗora hannayensa saman gashinta, ya fara tsagawa da mataji.

Hannu ta gani me gashi da cako-cakon farata a jikin mudubin, a hankali takai hannyenta saman nasa tana shafawa, taji babu gashin, ai sai ta rufe idanuwan nata da sauri kirjinta na bugawa.

Tana jin sautin dariyarsa. “Ai na faɗa miki dama.”

“Yawwa kin kuwa duba tabon ƙunanki na cinya?”

Girgiza kai ta yi tana son dubawar.

“Me ya same shi? Rufe idonka to in duba karka gane mini jiki.”

Murmushi ya yi mai sauti, ya rufe idon.

A hankali ta yaye cinyar ta ta dake cikin jar rigar data saka.

Dubawa take sosai amma bata ga tabon ba.

“Yana ina to? Buɗe idon naka na gama dubawa.”

“Na goge shi jiya dana ɗauko ki daga kogi. Yanzu ke kawai dan na ce miki na ƙone sai ki ƙona kanki? Bama ruwa ne ya ƙona Ni ba fa, garin yawona na ratsa ta gidan wani malami, ban san me ya kafa a gidan da ya ƙona Ni ba, shi ya sa ranar da muka je gidan malamin nan naƙi shiga, saboda na ji tururin abin daga sa ƙafata cikin gidan. Kai bantaɓa ganin halitta mai taƙadiranci irin taku ta mutane ba.”

Dariya ta yi sosai, har yanzu idanuwanta a rufe.

“Ka san ranar da na ga auren Fakriyya har fasa bakin Soupy na yi. Cewa ta yi a sato Hamoud a kashe. Kai Ni kaina ban san me ya sameni lokacin ba…”

“Buɗe idonki to ki gani.”

Ya furta da ƙoƙarin kauda zancen, bai san dalilin da ya sa take yawan ambatonsa ba, lalle soyayyar tasa ta yi tsuntsuwa zuwa kan Hamoud, yana jin yadda ransa ke baçi, haka yake ambaton Allah a zuciyarsa, yana roƙansa da ya sauƙaƙa masa.

Ta buɗe ta kalla, sai kuma ta mike da sauri tana dariya.

“Wow! Kalli fa yadda ya zama kamar na sarauniyar England.”

“Ita ce ai, a birnin zuciyata fa.”

“Gaskiya ka dinga min irinsa, ya zama kamar fa hula na saka, ashe Ham bulukin nawa ya iya adon mata.

Ɗal! Ta ji an ɗalle mata baki.

Riƙe bakin ta yi tana dariya.

“Wai kai me ya sa baka so ace maka baƙi?”

“To ke Ni baƙin ne? Ko a garinmu babu baƙar fata fa, ina lefin ki ce min kalar Habashawa.”

“Amma ka san me? Kuna da bambamcin dabi’a da Ham…”

Ta kasa ƙarasawa, ta riƙe bakin tana kallonsa.

“Wane irin bambanci?”

Ya furta yana kauda kallonsa daga kanta

“Shi ya faye zuciya, da fushi, ga rashin fahimta, kai ko dariyarsa ban taɓa gani ba. Kai kuwa sanyi gareka, ga fara’a, ga girmama ɗan Adam.”

“Hmm! Ni Kam bari ki ga na wuce kafin ki idasa tarwatsa min zuciyar. Ki je gashi can yana jiranki sai doka tsaki yake”

Ya faɗa da murmushi yana dosar Toilet ɗin.

Juyawa ta yi tana ƙara kallon kanta a mudubi, wani dogon takalmi ta zaro za ta saka.

A daidai nan Soupy ta shigo tana harararta.

“Haba ki duba lokaci fa, maghriba ake shirin yi, ki je ki ji da me ya zo mana…” ta yi shiru tana kwalalo ido, 

” To, ikon Allah! Ke tsaya ma, wannan style ɗin dake kanki fa? Yaushe kika fita zuwa saloon? Ba ma haka ba, anya akwai irin wannan gyaran a Naija?”

“A YouTube na kalla”

Ta furta, tana zira takalmanta.

Sakin baki Soupy ta yi tana kallonta, a haka har ta ratsa ta gabanta ta wuce.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 14Asabe Reza 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×