Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Auren Sadaka by Safiyya Mukhtar Garba

GARGADI

Ban yarda wani ko wata su juya min labari ta kowace hanya ba yin hakan zai sanya a fuskanci hukunci

SHIMFIƊA

Kaina a ƙasa ban iya cewa komai ba illa sharar hawaye da nake ta faman yi Ina sharewa wani na daɗa biyowa kumatuna, sai da ya gama zazzagemin kwandon masifa da cin mutunci sannan ya juya kansa.

“Kai kuma sokon banza sokon hofi ka ci gaba da zama haka tana rainaka kana zubarda girmanka a idonta tana taka ka tayi yanda takeso ka cigaba da sa mata ido.”

Ya sake juyowa kaina a fusace kaman zai mangareni “maza ki tashi ki wanke tas Kuma ki goge wallahi in har bakiyi ba na lahira ma sai ya fiki jin daɗi”! Yana gama faɗa ya kaɗa Babbar rigarsa yai gaba, yana fita shima yai maza ya bishi yana tsoron kar ya tsaya ya janyowa kansa wani ruwan.

Baƙin ciki kaman zai kasheni wani takaici yana tokaremin zuciya na miƙe na kwashe tsummokaran da ke gabana don bazan kirasu Kaya ba tsummane na kai bakin rijiya na zube ina harararsu kaman su suka yimin laifin.

Sai da na cika Babban baho baƙi sannan
n igiya na haɗa robobin waje guda da share ruwan na ɗauraye ƙafafuna sannan nai ɗaki na kwanta kan katifata wani baccin wahala mai nauyi yai gaba da ni.

Sai wajen La’asar na tashi Ina miƙa na duba agogo har anyi sallah ma na miƙe da sauri don naje nai alwala nai sallah Allah ya so ma ba nice da girki ba da na gane kurena.

Ina idar da sallar na haɗa wuta a dutsen guga charcoal na zauna zaman guga saida na goge kayan tass sukai kyan gani suka ɗan dawo hayyacinsu sannan, na miƙe nai Alwala don an kusa kiran magriba, ana yi nai sallata ban tashi akan daddumar ba sai da akai isha’i nai shafai da wutri sannan sannan na miƙe Ina ninke sallayar ya shigo Simi Simi tamkar tsohon munafiki ya raɓe bakin ƙofa.

Na ɓalla masa wata muguwar harara idona kaman zai faɗo cikin masifa na ce masa “me Kuma kazo yimin nan ka wani shigo ba ko sallama tamkar an jeho ka? Kansa da yake ƙasa ya sake saddawa ƙasan cikin ƙasƙantar da kai da sanyin muryarsa ya ce “Gimbiya kiyi haƙuri nayi sallama baki jini ba ne dama….” Nai maza na katseshi don bana son jin wannan shegen muryan nashi me kama da salamatu na ce “menene tsummanka ko? To gashinan ɗauka maza kafita ka ɓacemin da gani”, ya duƙa yana ɗaukan kayan da na ƙulle a baƙar leda.

Kamar bazai ta fi ba ya tsaya yana kallona duk a tsorace ya ke dani da ma balle yanzu da yasan yayi laifi.

Ya buɗe bakinsa da ƙyar “don girman Allah kiyi haƙuri ba don ni ba….” Na buga masa uwar tsawar da ni kaina bansan na iya ta ba “kutumar uba! To dama ka isa na haƙura don kai ne?! Ka isa?! I say get out!!”.. a zabure ya fice daga ɗakin har yana zabga tuntuɓe na bishi da wani mugun kallo zuciyata Kamar ta faso ƙirjina saboda wutar ɓacin rai sai da naji ƙarar rufemin langa langar ƙofata da yayi sannan na koma kan katifar na zauna jaɓar wani kuka mai cin rai da taɓa zuciya yana tahomin Ina jin kamar ciwona zai tashi.

Na gama na share hawayena ina sheshsheƙar ajiyar zuciya na miƙe don zuwa na ɗaura Alwalar bacci kekensa da ƙwarransa na nan ƙofar ɗakin bai tafi da su ba na bisu da harara ina shigewa makewayin, na gama duk uzurirrikana na fito na shige ɗakin da kullewa na gama komaina na kwanta ina shafa Addua, wani sabon tunanin na fara rerowa a ƙwaƙwalwata tamkar karatu wanda na riga na haddaceshi don in da sabo saba Ina haka har bacci ya kwasheni.

Washe gari gidan namu ya tashi a rikice ana hargitsi don dama kwana2 ba a bawa hammata iska ba, Ina daga ɗakina ina jiyosu suna ta bala’i ana Auno ashar galan galan, wannan kuwa abune me sauƙi a wajensu don in da sabo sun saba wanan ɗan mitsitsi kenan daga cikin aikinsu zasu aikata ma fiye da Haka basa shakkarta uban kowa.

Wai Umman Nura ce ta cinye kuɗin adashe an bata nata tun baya akazo zubin na gaba ta ce bata da kuɗi kusan zubi huɗu Tana ƙinyi gashi ta haɗa kuɗin jamaa ta cinye shi ne fa uwar adashen ta ɗebo mata ƴan sanda akazo tafiya da ita shi ne aketa zage zage abin nasu dai ha sauƙi sai na Allah aka sata a Mota akai police station da ita ƴan gulma Kuma an cika gidan ana maida yadda akai,

Na jiyo ƙarar buɗe langa langar ƙofata na miƙe da sauri Ina gyara ɗaurin zani na na fita a masife na zata ƴan damben ne suka shigomin sai naga saɓanin Haka mai gidan ne da kansa.

Yana sanye da ɗaya daga cikin tsummokaransa da na wanke masa jiya ya samu wata shegiyar hula ya buga tamkar ɗan dako kodayake bashida banbancin da su don ni a gani na GYARTAI ai ɗan uwan ɗan dakon ne.

Ya ƙarasa shigowa yana cangala shanyayyar ƙafarsa ta hagu da hannunsa na hagu da shima yake a shanye, ya ɗan duƙa kaɗan cikin muryarsa mai sanyin hali yana gaisheni a ɗar,
Ban amsa ba illa riƙe ƙugu da nai Ina jijjiga jikina Ina masa banzan kallo mai cike da tsana, jin shuru ban amsa ba yasa ya ɗago shanyayyun idanunsa ya zubominsu, ganin shi nake kallo Ina auna masa hararara yasa ya maza ya sake sadda kansa yana duƙar da shi ƙasa, naja tsaki, “meye ka shigomin kana wani tsatstsareni Kamar na ci bashi!? Eyeee ko wata uwar kake jira na maka?”

Jin tsawata ya sa ya diririce yama kasa magana illa bakinsa da ke motsi ya kasa maganar yana nunamin akwalan kekensa da nake tsaye kusa da shi.

“Au wai ni kake nufi na miƙo maka ko Yaya?
Da rawar baki Ya ce “aa ɗauka zanyi naga kina tsaye a kusa shi.”

Na ja gefe, ya janyo ƙafarsa ya ɗauki ƙwarran (ƙwarya), da kayayyakin cikin wani tsohon buhu ya ɗora a kariyar keken ya ɗaure da igiya sannan ya ja keken ya fita da shi, yana cemin sai ya dawo dukda yasan ba amsawa zanyi ba ya faɗa ne kawai don yaji daɗin bakinsa ya fi ce a gidan yana kallo har yanzu masu hayaniyar basu gama ba ana ta yi, yai musu addu’ar neman shiriya ya murɗa kan kekensa ya gaba yana tallata sana’arsa

“GYARTAI gyartai gyaran ƙwarya gyaran duma gyartai yazo a kawo”, yana ta kurɗawa layi layi duk me gyaran ya kawo. Yana fita na saye langa langar na koma ɗaki da nufin na kwanta sai naji na kasa kwanciyar ma gaba ɗaya.

Na miƙe don nayi ƴan gyare gyarena na fara ɗage katifar dake ƙuryar ɗakin na share dandamalin kasa don ɗakin ko Albarkacin ledar tsakar ɗaki babu haka yake dandaryar suminti na share na mayar da katifar na gyara zanin gadon da filon na gyara ƴan buhunhuna na na kaya dama su Kenan a ɗakin sai gefe robar ruwa ce ƙatuwa Kusada ita Kuma randar ruwan sanyi sai ƴan Abubuwan da baa rasa ba na sha re tas na sa tsumma na goge ɗakin ya fes kaman ba shi ba na kunna turaren wuta na tsinke na saki labule na fito na fara aikin tsakar gida shima na gama na wanke makewayina tas naga gurin ya min kyau sannan na zauna ina hutawa.

Na bayar aka siyomin koko da ƙosai zan ƙarya da shi don bazan iya cin wannan gantalallen ɗumamen nasu ba na wahala jiransa ma aikine yanzu haka ma sun cinye su da bataliyar ƴaƴansu nai tsaki a raina ina daɗa tsanar rayuwar gidan da basuda tsari sam!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.