"Ba zan taɓa barin ki ke kadai ba, koda kuwa hakan zai iya zama silar rayuwata,na gwammace in sadaukar ke da abun da ke cikinki ku rayu, ba abun da zai sameki kinji ki daina kuka,ina jin kukanki har cikin raina,zubar hawaye daga idanun ki tamkar zubar jinin jikina ne,haka kuma bayyanar damuwa aranki hakan kashe mun zuciya zaiyi, Please Zizi ki nutsu Kinji gani nan na ce miki ina tare da ke."
Ya karasa maganar shi ma yana rikota tare da shafa mata baya cikin tashin hankali, laluben fuskarta yake yana kokarin share mata. . .