Skip to content
Part 24 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

“Ba zan taɓa barin ki ke kadai ba, koda kuwa hakan zai iya zama silar rayuwata,na gwammace in sadaukar ke da abun da ke cikinki ku rayu, ba abun da zai sameki kinji ki daina kuka,ina jin kukanki har cikin raina,zubar hawaye daga idanun ki tamkar zubar jinin jikina ne,haka kuma bayyanar damuwa aranki hakan kashe mun zuciya zaiyi, Please Zizi ki nutsu Kinji gani nan na ce miki ina tare da ke.”

Ya karasa maganar shi ma yana rikota tare da shafa mata baya cikin tashin hankali, laluben fuskarta yake yana kokarin share mata hawaye duk da cewa shi ma hawayen ke ambaliya a fuskar shi.

Cikin Muryar Kuka ta ce, “Ni ban dau komai ba,banma san abun da suke tuhumata da dauka ba, wallahi bansan mene ne abun ba, ban san shi ba,bani na dauka ba.”

Kara shigar da ita Jikinsa ya yi,yana fadin, “Na sani, na sani ba ke kika dauka ba ma zaki taɓa dauka ba, ban san wata mafita ba a yanzu illa cewan Allah baya barci kuma shi ba alzalumin kowa bane, Don haka Ubangiji na tare da mai gaskiya a ko ina da zai tsinci kansa,hakan jarabacewa gareni da ke kuma kila yanzu aka fara bamu ma fuskanci komai ba,kisa aranki za mu karbi duk wata jarabawa da Ubangijinmu zai mana kuma bamu fidda tsammanin samun rahamarsa anan gaba ba mijinki na tare da ke duk rintsi.”

Ban da kuka babu abun da Fulani Babba take, idanunta sun canja kala sun koma jajawur , Uwar Soro na zaune bangarenta ita ma din dai kukan take tana bata hakura kan komai zai daidaita In Sha Allah.

“Wannan abun ba komai bane face shiri don kawai a tozarta Yareema duk kulle kullen da ake masa baiyi ba sai sun haɗa da Wani kuma Zainab ba ɓarauniya bace, Ita ce matar Yareema ba wai Safina diyar jakadiya ba, Zainab ce asalin matarsa wanda liman ya daura masu aure cikin Masarautar nan ba tare da sanin kowa ba, babban tashin hankali na a yanzu cikin da ke jikin Zainab ka da silar hakan ta je ta rasa ranta ina matuƙar jin tsoro.”

Fulani Babba na jan numfashi ta ce, “Me yasa? Me yasa tun farko bazaku sanar da cewa akwaita ba? Me yasa tun farko ba a sanar da Mai Martaba kan ta ba, kunyi kuskure , kunyi kuskure babba ya tabbata yanzu an shiga tsakanin Adeel da Mai Martaba tunda ya ajiye duk soyayyar da yake yi masa gefe.” Ta karasa tana fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya wanda kowacce Uwa na iya riskan kanta ciki yayin da wani kaddararren al’amari ya sami Ɗanta.

Uwar Soro ta dafata tana fadin, “In Sha Allah ni da Liman da Adnan zamu je mu sanar da shi gaskiyar komai kuma ina sa ran cewa zai fahimta duk da cewa gudun samun hargitsa yasa muka biyewa Yareema ba tare da sanarwa ba,amman yanzu dole mu nemo mafita.”

Jakadiya da Safina na zuwa ɗaki suka fara sakin tsakin takaici.

“Wai shi wannan Yareeman naku gaulon ina ne? Ana ce masa nan ne yana cewa can ne, yanzu ya bita fa kenan wai da gaske.” Cewar safina.

Jakadiya ta ce, “hmm tun tuni inata kullawa da kuncewar nemo mafita na ji matukar mamakin da har ya iya bude baki ya ce matarsa ce , ban taɓa zaton faruwar hakan ba, A Yareeman da na sani kau da kai zaiyi tamkar baya wajen ma ga faruwar hakan,amman kuma ya goge mun hadda yau,ya rusa mun shirina,ya tarwatsa mun shirina a yadda naso da an kaita dakin nan kasheta zansa ayi ammam yanzu kuma taya? Ta ya ma hakan zai faru ta gama asirce shi wannan tsinanniyar yarinyar amman babu komai daga ita har cikin da ke jikinta baza su taɓa rayuwa cikin Masarautar nan ba,ko ince duniyar ma gabadaya muddin ina raye.”

Safina ta ce, “Ni Sarkin ne ma ya ban haushi wallahi yana maganar nan kamar in damƙo shi in shaƙe don takaici.”

Jakadiya ta ce, “Ya Shammaci tunani da hasashena matuka duk da cewa nasan yana da tsauri kan dokinkinsa zai iya yiwa koma waye hukunci kamar yadda muguwar zuciyarsa ta sanyasa yin ajalin iyayena,amman tabbatar da cewa bazai taɓa iya kashe Ɗansa ba, kar ki damu da hakan duk ma fa indai nice fitilace ai mai haskaka sharri, don haka zan iya haskawa kowa hanya watakila ma shirinmu ne ya fara aiki kan Mai Martaban amman yanzu dai mu zubawa Sarautar Allah ido, Fulani Kilishi da kaina na dauko Sarkokinta na kai na aje cikin kayan wannan yarinyar sauran kuma na daure mata a hijabi, sannan na sa Fulani Kilishi yin kwazazzabon kuka da kwareroton cewa an sace mata sarkonkinta na gado wanda yake mallakin mahaifiyar Mai Martaba Mohammed Rohaan ne ta bar wasiyan rabawa Surukanta kuma akan wa innan sarakunan Mai Martaba zai iya komai kansu domin tamkar wani bangare ne na wannan masarautar hakan yasa na yi amfani da su.”

Magajiya zaune cikin yanayin damuwa, Rumaiysa ta kalleta, “Mamma lafiya kuwa?”

Ta numfasa kafin ta ce, “Abubuwan mamaki da sarƙaƙƙiyar wannan masarautar tun basa bani mamaki da tsoro har sun fara bani, na san da cewa bakisan dalilina na cewa lallai sai kin Auri Yareema ba, kulle-kullen da ake kullawa ta kowanni saƙo nayi tunanin cewa zan iya magancewa amman ashe yafi karfina, zuwan yarinyar tabbas duk shirine,haka kuma wannan yarinyar ma da aka laƙawa sharri shi ma shirrine mai zaman kansa, tunda har Yareema ya bude baki ya kirata da sunan matarsa ya tabbata cewa ita ce Matarsa, in zaki lura tunda ake maganar waccer dayar yarinyar amsa guda ya taba badawa na ya santa amman daga nan bai ce komai ba, Rayuwar Masarautar nan na matuƙar bani tsoro , yanzu ina so ki bani goyon baya duk yadda za ayi mu nemo mafitar warware wannan lamarin .”

Rumaiysa ta ce, “Ni tun farko ban yarda ma da wannan Jakadiyar ba sam sam wlh matar bata mun ba,bare kuma yanzu da wannan yarinyar tazo ake cewa ‘Yarta ce, duk yadda za ayi In Sha Allah zamu nemo mafita.”

Hajiya Rabi ban da jirga-jirga babu abun da take yi tana cixon yatsa.

“Wai me abubuwan nan suke nufine? Da farko jakadiya da ‘Yarta yanzu kuma wata yarinya kuma yareema na kiranta da sunan matar shi? Suna so su juyarmun da kwakwalwa in fara daina gane komai.”

Khaleesa ta ce, “ni ban damu da zuwan kowa ba,duk yadda za ayi kawai a kashe wannan yarinyar ita ma yar jakadiyan mu kasheta har ma da Jakadiyar Don ni wallahi Allah in ban Auri Yareema ba zan iya mutuwa.”

Hajiya Rabi ta rike kirji cikin firgice ta ce, “Mutuwa? Rufamun Asiri, yanzu kika fara rayuwa ma,kuma kisa aranki kamar kin mulki mutanen cikin Masarautar Benoni da kewayenta, ko da kuwa ace hakan zai ja mun matsala ne,ba ji ba gani yanzu za a fara asalin fito na fiton,kin ga wannan yarinyar jakadiyan ta kanta zan fara ni don nafi ganin matsala tattare da ita fiye da kowa.”

Bangaren Hajiya Maimuna ma daren yau hakan take ta kasa samun Nutsuwa tsabar takaici hakan yasa ta gagara zuwa bangaren Fulani Babba.

Nasmah ta ce, “Yanzu shikenan dai ba zan taɓa samun Yareema matsayin miji ba? Ga safina ga waccer yarinyar? Gaba kuma bamu san me zai faru ba ko ince bamu san wace ce zata zo ba.”

Hajiya Maimuna tayi ajiyar zuciya, “Bari kawai, duk zagon ƙasan da nake shiryawa yana kokarin tashi a banza kenan amman duk da hakan ai hanya bata taɓa kulluwa ga wanda ke dauke da makulli a hannu Don haka ki kwantar da hankalinki indai na amsa sunan mahaifiyarki to zan cika miki burinki.”

Kamar yadda kowa ya kasa runtsawa cikin Masarautar haka ma Fulani Kilishi zaune take gefen gado duniya tayi mata daurin huhun goro.

“Shirina kawai in bata rayuwar Yareema ya yi wa wara mace cikin shege ne ta yadda ba za a karaa samun wani daga jikinsu da zai mulki masarautar Benoni ba,in Auri Waziri mu mulka amman reshe na kokarin komawa ga mujiya? Tabbas zan ci gaba da yiwa Jakadiya biyayya amman ba zan taba fasa shirina a ɓoye ba,yanzu ya kamata in kara rike damtse inyi duk wani abu da zai sa in samu Nasara koma mene ne.” ta karasa maganar a zuciya ta na wani irin Murmushi wanda ita kadai ta san dalilin hakan.

Gaaji da Adeel yadda su ka ga dare haka suka ga safiya, duk da cewa su basu ma san yaushe safiyar tare ba,tunda cikin duhu suke wanda ko kansu basa iya gani bare gane wani abu.

Cinnaku da sauro ta ko ina cizon su yake, Mussaman jikin Gaaji har ya yi mata ruɗu-ruɗun kuraje ana taɓawa ana jin girmansu.

Jikinta ya kumbura ta ko ina daga fuska har kafafu,tsabar wahala idanunta a rufe suke duk da cewa koda ta budenma babu abun da zata gani,amman tsantsar wahala da azabar cizo yasa kumburan idanun da sukai suka rufe da kansu.

Adeel cire Rigar jikinsa ya yi,ya rufa mata a jikinta, don tun tana kuka har ta gagara ban da ajiyar zuciya babu abun da take yi,ga azabar zafi ga yunwa da take ji ga rashin samun nutsuwa gabadaya ta birkice ,tun tana sa hannu tana koran saurayen da cinnaku tare da kyankyasai da manyan kudaje har ta gagara kawai ta kwanta jikin Adeel ta ci gaba da ajiyar zuciya tamkar numfashinta zai fice.

Shi dai neman duk hanyar da zai bi ya kareta yake baya ma ta kansa ko kadan, tausayinta yake ji har cikin ransa wanda ga ciki ya tsufa WATA BAKWAI lokacin da tafi bukatar kulawa da taimako ga shi yazo mata cikin wata sigar wahala.

A sanyaye ya ce, “kina jin yunwa ko?”

Gaaji ta ce, “Eh.” Da kyar ta fito.

Ya saki numfashi.

“Kiyi hakuri watakila in safiya tayi za azo a kawo abinci sai kici ko.”

Bata ce Komai ba domin maganar ma wahalar fita take yi mata.

Jakadiya Uwar Soro ta gani tana sauri dauke da kwanon abinci ta nufi dakin Duhu, da sauri ta tare tana , “Jakadiya ina zaki kike sauri haka?”

“Umm Wallahi yareema zan kai wa abinci da yaron nan na kwana yadda naga dare haka naga safiya Shiyasa nace bara in kawo masa.” Ta fada.

Uwar Soro ta mika hannu tana, “Ayyah aikuwa kin kyauta ki kawo zan bada abashi domin sarkin Fada ya sanar da ni cewa Mai Martaba ya ce kada abawa kowa damar zuwa sai shamaki Don haka zan bashi ya kai.”

Jakadiya bata so ba ta mika mata ta tafi tana , “Shegiya karamar munafuka mai hana ruwa gudu, adai kai masan ai Shikenan.”

Uwar Soro na ganin jakadiya ta tafi tayi sauri ta zubar da abincin ta dauko wani a part dinta ta bawa shamaki ya kai.

Shamaki na tura abincin da sauri cikin rububi Adeel ya janyo yana mikawa Gaaji.

Shi yana bata ita ma tana kokarin ci da kanta kusan rabi da kwatan abincin a kasa ya zube,shi baya ma ta cikinsa burinsa dai ta ci.

★★

Har karfe Tara Mai Martaba Sarki Mohammed Rohaan bai fito Fada ba.

Hakan yasa Sarkin Fada zuwa bangarensa domin dubasa.

Shigarsa ke da wuya ya tarar da abun da ya gigitashi.

Mai Martaba kwance daidai bakin Kofar Part dinsa ba Numfashi ga dukkan alamu ya gama shiri kenan zai fita wani lamari ya afku.

Jijjigasa Sarkin Fada ya fara yana fadin sunansa.

Amman babu alamar numfashi a tattare da shi…..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 24Auren Wata Bakwai 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×