Skip to content
Part 25 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Hakan yasa Sarkin Fada saurin fita yana yekuwa.

Gabaɗaya aka taru kan Mai Martaba.

Fulani Babba kasa jure ganin hakan tayi tana zuwa ita ma fadi sumammiya.

Cikin damaucewa Uwar Soro ta kira Adnan ta sanar da shi kan lallai yazo.

A ka kira Dr Habib wanda yake babban likita ga masarautar.

Dr Habib na duba Mai Martaba ya girgiza kai tare da fadin, “Banjin cewa akwai sauran numfashi tattare da shi, sai dai hakuri tare da fatan Allah ya gafarta masa.”

Sai a lokacin Fulani Kilishi ta fada gabansa tana jijjigasa cikin muryar kuka, “Kar ka yi mana haka Mai Martaba Don Allah ka tashi, ba mu hakan da kai ba,ka mun alƙawari tare zamu rayu kuma tare zamu bar duniya,ina kake so insa raina? Ya kake so in iya rayuwa babu kai?”

Jakadiya ta rikota tana fadin, “Sai hakuri babu mafitar da ta wuce ace yanzu anyi masa addua domin ita yake bukata fiye da komai.”

Adnan ya rasa inda zai sa kansa gabadaya ya rasa gane kan Komai Musamman da Uwar Soro ta sanar da shi abun da ya faru a daren jiya.

Ya je gun Sarkin Fada yana fadin, “Ranka Yadaɗe tunda Allah ya yiwa Mai Martaba cikawa ataimaka a bude Adeel ya yi masa sallah.”

Sarkin Fada ya ce, “Adaren jiyan da abun ya faru Mai Martaba ya umarceni da in basa makullin dakin, kuma na mika masa saidai in za a bincika ko za a gani ,domin baza a taba iya bude dakin ba tare da mukkulinsa ba, dakin na dauke da wasu sirika na Mussaman in ban manta ba ma Mai Martaba ya taɓa sheda mun cewa wannan dakin ba zai taɓu buɗuwa ba sai in har yana numfashi ka ga kenan amfani da mukkulin ma a yanzu kila wa kala ne duk da cewa ya zama dole anemo mafitar budewan.”

Fulani Babba kuwa har lokacin bata farfaɗo ba anata kokarin yi mata fiffita.

Adeel da wasu cikin dogarai tare da Shamaki sunyi iya yinsu na ganin sun dubo makullin dakin duhu amman basu samu ba.

Hakan yasa kawai aka fara shirye-shiryen jagorantar yiwa Mai Martaba Sarki Rohaan Sallah.

Liman ne ya shige gaba domin yi masa wanka.

Iahirin Al’umma da ke cikin Garin Mutuwar ta matukar taɓasu wanda ya kawo daukewar duk wata walwala da ke ciki ,daga mutanen cikin fadar har masu kudin waje da talakawa.

Liman da Adeel tare da Sarkin Fada sunata kokarin yiwa Mai Martaba sutura, abun mamaki ana dauko Ninkafani za a rufe shi da shi kafarsa ta fara motsawa.

Idanun Adeel ne suka fara hango hakan cikin sauri ya ce, “Da ran Mai Martaba bai mutu ba wallahi bai mutu ba,ku kalli yatsun kafafunsa suna motsi gasu nan suna motsi.” Ya fada yana nunawa.

Aikuwa abun mamaki da al’ajabi gilmawa kafafun Mai Martaba suke kamar yadda Adnan ya fada, fita ya yi,ya kara kiran Dr Habib ya gwada shi.

Yana gwadawa ya tabbatar da cewa a yanzu yana numfashi amman ya yi ƙasa sosai.

Zai iya farfaɗo wa kuma zai iya mutuwa.

Tamkar doguwar sumace wacce zai iya daukan kwanaki ko watanni kafin ya farfado. Cike da mamaki Dr habib yake jawabin domin gwajin da ya yiwa Mai Martaba a dazu babu alamar ci gaba da rayuwa a tattare da shi,amman da ke Ubangiji mai iko ne kuma mai tattabar da abun da ba a zaton tabbatuwarsa hakan ba abun mamaki bane.

Gyarasa sukai aka sa masa kaya sannan aka mai da shi kan gado.

Dr Habib ya ce, “a cikin wannan halin da yake ciki abu kadan za a iya yi masa sauran numfashin ya kauce,yana matuƙar bukatar kulawa da tsaro wanda inda hali masu lura da lafiyarsa kadai ke da hurumin ganinsa, duk da cewa ban ga alamun wata guba ko wani mummunan abu da ya ci ko ya sha ba, amman tabbas wannan shirine da akayi don hallaka shi, Shi kuma Ubangiji ya nuna ikonsa tare da nuna cewa yafi karfin hakan.”

Liman ya ce, “Tabbas Wannan Ikon Ubangiji da karfin IzzarSa ce kawai ke aiki.”

“Indai hakanne kuwa ina tunanin ba za mu bayyanar da cewa yana raye ba, gudun samun wata matsalar za mu bar al’ummar Garin nan da ma na cikin Masarautar nan cikin Duhun cewa ya rasu kamar yadda aka sheda a farko gudun samun wata matsalar don tunda aka fara kawo wannan harin to komai ma za a iya a yanzu kam, za a kulle bangaren nan nasa daga yau daga shi sai masu lura da shi ne zasu kasance ciki, sauran lamuran fada kuma ni zan ci gaba da jagoranta duk da cewa hakan ma tsira za ayi ba amman zanyi kokarin magance duk wani kalubale da zan fuskanta.”

Adnan ya ce, “to yanzu ya za ayi kenan gudun kada su fahimci cewa yana raye.”

Sarkin Fada ya ce, “Za a shirya amfani da wata gawar maimakon tasa muje a binne,na Tabbatar indai aka binne gawa gaban al’unma ba wanda zai ji aransa cewa Mai Martaba na raye ko da kuwa cikin mafarki ne.”

Hakan akayi kuwa Dr Habib ya kirawo Nurses a ɓoye tare da tanadar duk abun da zasu bukata domin lura da Mai Martaba da masu aiki aka rufesu cikin Part din, dake babba ne komai da ake da bukata akwai ciki.

Su kuma suka samu wata gawar suka lullube aka je akayi sallah kowa ya sheda.

Uwar Soro na gun Fulani Babba, ta farfaɗo amman ko magana bata iya yi.

Ban da hawaye babu abun da ke kwarara daga idannunta.

Bayan sun dawo daga kai jabun Mai Martaba kabari Adnan ya shiga Part din Fulani Babba.

Uwar Soro na ganinsa ta ce, “har kun kai shi?”

Adnan ya ce, “Eh.”

“To yanzu ya Maganar fito da Yareema? Ba key kuma koda keynma akwai matukar wahala kofar nan ta bude muddin Mai Martaba baya Numfashi.”

Adnan ya ce, “Allah ne kadai yasan me yake nufi da hakan, Amman a yanzu kam bama da wata mafita sai dai aita addu’a.”

“Hmm to Allah Gamu gareka, Amman tabbas masarautar nan na daf da shiga cikin wani hali.” Uwar Soro ta fada.

Adnan na fita dakin Duhu yaje yana yiwa Adeel magana.

“Prince… Prince….kuna lafiya dai ko?”

Adeel ya ce, “Lafiyar kenan kazo ne?”

Adnan ya numfasa cikin yanayin tausayi ya ce, “Hmm ya Zainab din na ji tana ta wani irin numfarfashi.”

Adeel ya ce, “Eh wallahi, ina ganin silar karshen rayuwarmu kenan kasancewa anan.”

“Mai Martaba bai da lafiya kuma makullin dakin nan na wajensa kuma kasan dakin in ba yana numfashi ba,bazai taba amfanin da za a iya budewa ba, sai dai muta addua har ya samu sauki .” Adnan ya fada.

Cikin damuwa Adeel ya ce, “Innalillahi wa inna ilahir raji’un, Ba lafiya? Me ya samesa? Adnan Don Allah ayi kokari a lura da lafiyarsa inma na fita kasar wajene kayi duk kokarin da zaka yi wajen samar da mafita.”

Adnan da idanunsa suka sauya kala ya ce, “In Sha Allah komai zai wuce zai ji sauki karka damu.”

*****

Jakadiya tsaye ta cukume Fulani Kilishi.

“Wannan makircinki ne, tabbas wannan makircinkine bana kowa ba, wai me kike nufi ne? Me kike nufi na ce miki? Kin manta ni wace ce ko? Wato bazaki daddara dani ba ko?”

Wata irin dariya Fulani Kilishi ta yi, “Au wai ni? Dani kike kenan? Ni me zanyi ma kina nan ke da kike gabana a iya makirci da iya yin gutsiru tsoma.” Ta ƙarasa maganar tana fisge hannayenta da ta rike mata kaya da shi.

Jakadiya ta yi tsaki, “ke kika kashe Mai Martaba, na Tabbatar babu wa inda zai iya wannan aika-aikar sai ke,kuma wallahi ki sani da cewa ko ni,ko ke ne cikin Masarautar nan.”

Fulani Kilishi ta kalli Jakadiya sama da ƙasa kafin ta ce, “Uhummm lallai taki na wahalar da me kayan kara,ashe kina tunanin zan iya aikata abun da yafi karfin wanda kike aikatawa? Kina tunanin zan iya rusa miki sharri?”

Jakadiya ta ce, “wannan kuma damuwarkine don ni bana taɓa rasa hanyar ɓullewa duk kofar da aka rufe ni tamkar an bude mun wata kofar boyayyace wacce ni kadai kan iya hasasota, Don haka kada ma kisa aranki cewa zaki mulki wannan masarautar muddin ina numfashi a doron ƙasa.”

Tana fada ta fice.

Wata irin Dariya Fulani Kilishi ta fara mai fidda sautin ban tsoro.

Sai da tayi me isarta kafin ta ce, “karshen dai alewa ƙasa.”

Uwar Soro daukan Fulani Babba tayi ta maidata bangarenta ganin cewa ta kasa samun sukuni sam sam ko kadan.

Hankalin Jakadiya ya matukar tashi fiye da kowa,ta kasa zaune,ta kasa tsaye domin bata san ta yadda zata bullowa lamarin ba, hakan yasa kawai ta dauki Safina suka koma gun bokanta.

Taje ta sanar da shi dukkanin abun da ke faruwa duk da cewa ya farfada mata wasu abubuwan da hasashensa suka hango kafin ta furta.

A karshe ta nuna masa cewa inda hali tana so ta mulki masarautar Benoni da kanta.

Dariya yayi yana fadin , “Hakan ai ba komai bane abune mai sauki tunda dai Shi Mai Martaba ya bar duniya,amman ki sani da cewa indai har yana duniya ba za ki taba mulkar masarautar nan ba koda kuwa cikin mafarkinki ne.”

Jakadiya ta ce, “Ya mutu fa,gabanmu aka fito da gawarsa aka je aka binne kuma ni naga gawarsa ido cikin ido, sannan matarsa Fulani Babba inaso a rufe mata baki ta koma saidai ta ji magana kawai amman ba wai ta iya maidawa ba, sannan ita kuma mai son karawa dani Kilishi abarta in azabtar da ita da kaina yayin da na hau karagar mulki masarautar Benoni.”

“Hahaahaas Shugabar munafukai,shugabar marasa tausayi da tausayawa, shugabar ha’inci da zaƙon ƙasa, zaki iya yin komai don biyan buƙatar ki na sani,amman nima ina so ki sani cewa ina kara sheda miki muddin Sarki Mohammed Rohaan na raye bazaki taba iya hawa kujerar sa madadinsa ba koda kuwa birnin sin zakije gun sarkin Aljanu ya baki laƙani sannan kuma duk da haka tafiyar aikinmu daidai akwai bukatar wannan yarinyar ta rabu da Yareema duk yadda za ayi kisam yadda za ayi shi ya fito watakila ita dauwamarta ciki yasa ta gaji ta mutu don na lura tana da taurin kai na fitar hankali sannan ita kuma Fulanin a yanzu haka bakinta a rufe yake na duba na gani kuma ya rufu kenan har karshen numfashinta”

Jakadiya tayi dariya kafin ta ce, “Yoo ni daman ai dukanninsu ma a yanzu ba wanda nake son kashewa na fiso in kaskantar da su,su zama bayina suna bauta mun, motsina ya zam bugun zuciyarsu cikin sauri,muryarta ta zam mai tsinka masu jijiya, gani na kuwa yasa su ficewa daga hayyacinsu gaba-daya, anyiwa iyaye na kisan gilla ba tare da sun sha wuya ba,amman kuma zan azabtar da su wahala tai silarsu shiyasa na ji matukar bakin cikin mutuwar Mai Martaba ba tare da ya ɗanɗana kudarsa ba, sannan ita kuma wannan figigiyar yarinyar dole zan samo mafitar da zatai saurin zama mushe daga ita har abun da ke cikin nata.”

“Wannan ya Rage nake nidai zanyi abun da yake akwai ne kawai.”

Safina shiru gabadaya jikinta ya gama yin sanyi domin ta tabbatar da cewe Mahaifiyar ta makirace ta mai lasisin bugawa a jarida,duk son zuciyarta da Mugunta ta danneta ta take.

Haka ta ja hannun safinar suka koma Masarauta cikin dare.

3DAYS LETTER

Gaaji da Adeel sunan adakin suna fama Mussaman Gaaji da ta ke kara zama abar tausayi.

Fulani Babba na nan Adnan da Uwar Soro na faman jinyarta domin ciwo take mai tsanani.

Kamar daga sama suka jiyo hayaniya.

Adnan da Uwar Soro na fita suka tarar da Fulani Kilishi ta tara mutane tana yi masu jawabi.

“Kamar yadda yake,yau kwana uku da Mutuwar Mai Martaba Kuma Fulani Babba babu lafiya,sannan Yareema ma na kulle wanda ba asan ranar da zamu iya fidda shi ba, haka kuma masarauta ba za taba tafiya babu jagoranci ba,wanda a yanzu nauyin ya koma gareni,ya zame mini dole ni zan jagoranta wanda nake son yanke hukuncin cewa Auri Waziri Domin ya zam Sarki mai jogarantarmu duka,wannan shine hukuncina kuma babu ja ga hakan.”

Kallon kallo aka shiga yi, Mussaman Magajiya da ta kurawa Waziri ido tana mamakin jin hakan.

Wata irin fusata Jakadiya tayi tama kasa rike fushinta ta ce, “Wallahi karya kike,nice nan na cancanci rike masarautar nan a yanzu domin nice wacce aka haifa ciki kuma ta girma ciki dukkanin abubuwan naɗin saurauta suna ƙasana don haka baki isa ba kuma baza ki taɓa isa ba.”

Fulani Kilishi cikin fushi ta ce, “Ke har awa? Kin isa? Ina magana kina magana? Meya hana lokacin da kike masarautar tun yarinta Mai Martaban bai aureki? Ko ki iya bakinki ko kuwa ki jawa kanki tashin hankalin da ba kya zato, tsaf zan iya tsige ki daga sarautar Jakadiyar da kike taƙama da shi.”

Jakadiya ta ce, “Ke da gani na kinsan nafi karfin sauraren shirmen batutuwanki amman kisa aranki cewa bazaki taba mulkar wannan masarautar ba domin kuwa a yau ni zan maye gurbin Mai Martaba.”

Tana fada ta wuce cikin Fada kai tsaye taje zata hau kan kujerar,takunta ga carpet din farko gabanta ya yi wata irin mummunan faduwa kafin ta ankare jinta tayi an daga sama an dirar a waje.

Fulani Kilishi tayi dariya tana kadai kai.

“Daman taya za ayi kujerar milki ta amince da tsintacciyar mage? Ai sai mu da muka zame mata jini a cikin jiki.”

Ta ƙarasa maganar ita ma tana kokarin zuwa gun.

Ko kafarta bata daura kan carpet din ba ta fara jin saukan duka ta ko ina a jikinta,ita kam ma sai da akai wullo da ita kafin aka dirar.

Nan Jakadiya ta tashi tana dariyar ƙeta.

“Masu jinin kenan? Tabbas ni da kujera ko babu kujera ni zan jagoranci wannan masauratar ko Anki ko anso.”

Dukkaninsu binsu da kallo suke kawai Mussaman Uwar Soro,Adnan, Shamaki da Liman tare da Sarkin Fada basu ce ƙala ba.

A karshe ma fita sukai suka barsu a wajen.

Daga Jakadiyar kuwa da Fulani Kilishi dukkanin su kowacce tayi alwashin sai ta mulki masarautar Benoni da karfi koda babu kasancewa cikin Fada.

Daga ranar kuwa suka fara mulkar masauratar kowa na kokarin nuna ikonsa da izzarsa.

Fulani Kilishi da Waziri sunata kokarin shirin yin aure yadda a tunaninsu in anyi auren dole Jakadiya ta hakura ta durfana gabansu kasancewar sa namijin da zai yi jogaranci.

Jakadiya ce ta sanya akira mata Fulani Babba tazo, Uwar Soro ta sheda mata cewa bata da lafiya bata ma cikin hayyacinta.

Cikin fushi ta umarci cewa koda kuwa Gawace ita sai ta taka tazo gareta.

Haka Uwar Soro ta riketa suka je.

Tana zuwa ta sheda mata cewa daga yau sune zasu dunga share-share da wanke-wanke a Masarautar gabadaya.

Uwar Soro ta ce, “Ranki Ya Dade Don Allah kiyi mana aikin gafara ni zanyi komai amman ita amata uzuri ko magana bata yi kuma bata cikin hayyacinta ma.”

Wata irin tsawa ta daka musu saida Fulani Babba ta razana.

Ta ce, “Na fada babu canji babu ruwana da rashin kasancewarta cikin rashin lafiya ina jadadda miki koda ace ita gawa ce wannan aikin ya wajaba akanta.”

Haka suka shiga kitchen suka dugun zuma aiki gabadaya ta maidasu bayi, hatta su hajiya Maimuna,Hajiya Rabi da magajiya.

Cln karen su suke yi babu babbaka, shiga cikin Masarautar ma sai sun zaba mai shiga,duk zuwan da Adnan zaiyi Fulani Kilishi ta ce indai shine kada a taba bari ya shiga domin ta lura munafukine.

Haka kuma ta hana ana bawa Adeel da Gaaji abinci saidai Uwar Soro ta saci sauran abinci a kitchen in sun gama aiki ta kai masu a boye.

Wata guda kenan ana abu Ɗaya Gaba-daya Fulani Babba ta gama fita a hayyacinta ta dawo asalin baiwa cikin bayin ma wulakantattu domin kullum cikin wahala take.

*****

Cikin Dare suna zaune rabe da jikin Juna Jakadiya taje ta kori Shamaki ta tura masu Maciji cikin Ɗakin.

Tana turawa Gaaji tayi wata irin ƙara can kuma hannunta ya damƙo macijin ta rike duk da cewa cikin duhu ne amman shigar macijin dakin kawai jikinta ya bata.

Bata san yadda akai ta damƙa ba kuma batasan yadda akai ta rike da hannunta ta rabashi biyu ba kamar sanda.

Adeel ya fara lalubenta yana, “Mene ne ya faru? Kina ina ne wai? Don Allah ki dawo jikina duk abun da zai sameki ya samemu tare.”

Sai ta yayyakan Macijin gunduwa gunduwa kafin ta ce, “Macijine kuma ya tafi Shikenan.”

Ta lallaba ta lulubosa suka kara rungume juna.

Kamar an tsikareta can anjima ta fara kuka tana rike Adeel, “Zan mutu inaga mutuwa zanyi ji nake abu zai fito daga jikina, Wayyo wayyo Allah…. innalillahi wa inna ilahir raji’un zan mutum… Mutuwa zanyi….. Tana maganar tana kara kankamesa tare da cizon baki.

Nakuda ce gadan gadan tazo mata wanda a yaune cikin jikinta ya cika wata bakwai cif.

Adeel ya gama rudewa ga rashin haske gashi shi bai ma san yadda ake karban haihuwar ba.

Adeel Ya ce, “ki yi hakuri, ba mutuwa zakiyi ba,ina tare da.

Kafin ya rufe baki ya fara jiyo kukan jariri.

Kara birkicewa ya yi ya lalubo kofar Dakin yana so ya yi magana.

“Waye ne a kusa Don Allah wane ne a kusa? Muna neman taimako ataimaka Don Allah ataimaka mana.” Ya fada daidai lokacin da Shamaki ya dawo.

A hankali ya ce, “Ranka Yadaɗe lafiya? Gani nan ina kusa.”

Adeel ya ce, “Don Allah ka taimaka mun da haske yanzu akwai matsala.”

Duba ko ina yayi da ya tabbatar babu kowa,Torch light din sa ya tura masa ta kasan inda ake tura masu abinci.

Adeel ya janyeta da sauri.

Yana haskawa yaga kan yaro na kokarin fitowa.

Haka yasa hannu ya zarosa, ya ajesa yana juyowa ya kara ganin wani kan Kuma haka ya kara janyowa Gaaji wahala tayi wahala hawayene kawai ke zuba ga jini da ke kwarara.

Wani galan-galan ya gani a gefe ya dauka ya dinga dirza cibiyar yaran saida ta fara dagargajewa kafin ya samu yanke su da kyar.

Ya cire wandonsa daga shi sai gajeren wando ya lullubesu ciki.

Komawa ya yi gun Gaaji tana wani irin Numfarfashi ya ce, “Sannu Kinji ,sannu.”

Gaaji ta ce, “Kila na shigo rayuwarka ne kawai don in haifa ma su kuma na gama aikina ina ji a jikina mutuwa zan yi zan mutune.” Tana fada tayi wani irin numfashi Shikenan ta daina gabadaya.

Adeel ya yi wata irin kara yana jijiigata, saida masarautar ta amsa karar ta ko ina Mai Martaba ma saida ya yi wata irin farkawa a firgice.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 25Auren Wata Bakwai 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×