Skip to content

Yana buga mata Belt din, sai da tayi wata irin mummunar shiɗewa tsabar zafi tana kankame masa jiki, “Na mutu. Shi kenan na mutuuu. Baffa.”

Kara sake mata ya yi.

Uwar Soro tayi mutuwar zaune, Adnan ne ya yi jarumtar rikewa Adeel hannu yana, “Haba wannan wani irin cin zaline, ko ba komai ai ka tausaya mata kasancewarta na karamar yarinya koma me ta maka.”

Ko saurarensa Adeel bai ba ya ci gaba da kokarin makawa Gaaji Belt tun tana iya kuka har ta gagara tayi shiru kawai.

Da kyar ya samu ya kwaceta aiko yana kwaceta da gudu tayi bayan Uwar Soro shi ko ya fita ya wuce.

Duk ya farfasa mata jiki da ciwo ya yi ruɗu-ruɗu wani gun ma jini yake.

Cikin Muryar kuka a raunane ta ce, “Wannan mugun ba d’igon imani a zuciyar shi, kuma ba zan yafe mishi ba, kuma aradun Allah sai na rama mai kama da bunsuru kawai.”

Uwar Soro ta ce “Wato bakin ki ba zai mutu ba wannan shegen dukan da ya miki kadai bai ishe ki ba, ki dai bi a hankali kar ya illataki a banza.”

Adnan ya ce, “Kin ga in kika kara tsokanosa ba ruwana nikam zan bari ne ya miki dukan da yaso in yaga dama ma ya maidaki wannan dakin.”

Gaaji na share hawaye ta ce, “Cab ya maidani wannan dakin hmm.” Sai kuma ta yi shiru.

Gasa mata jiki da ruwa mai zafi Uwar Soro tayi sannan ta bata maganin da zai rage mata radadi.

Baccin awa uku Gaaji tayi ko da ta farka jikinta bai gama yin kwari sosai tunda daman cen ba lafiya gareta ba, shiru tayi tana tunanin ta hanyar da za ta dauki fansa, tafi minti talatin tana saka da warwara.

Sai da ta tabbatar Uwar Soro ta shiga cikin fada sannan can ta saka dan yatsanta a baki ta ciza ta girgiza kai, zumbur ta mike, lalabawa tayi ta gudu bangaran Prince Adeel, jin ana kiraye kirayen sallar isha yasa taji dadi ta kara sauri ta isa bangaran, dama tuni Prince ya wuce masallaci haka ta lallaba ta isa daining gurin da aka jera masa abincin shi na dare, budesu tayi daya bayan daya, ferfesun kayan ciki ne a gefe sai fried rice sai ruwan tea, murmushin mugunta tayi ruwan tea din ta dube ta shuga waige waige ganin ba kowa sai ta kai bakinta kan flake din ta tofa yawu mai yawa a ciki sannan da sauri ta rufe ta jujuya shi dan ya hade haka sauran abincin da na sha duk tayi fried rice din ce kawai da ta tofa bata motsa ba.

Tsaye tayi tana karewa daining table din kallo tana dariyar mugunta, “Mugu yau zanyi maganinka, gobe ma ka sake dukana saura ma wannan jelar taka ai muna nan sai na yanketa wuƙa zanzo da ita in kana barci aradun Allah in fisgeta maga ta mugunta.”

Har ta juya za ta fice sai kuma ta dawo tunowa tayi da wata muguntar da sauri ta haura sama ta shige dakin shi toilet ta shiga ta yi kashi a kasa sannan ta diba da hannunta ta shashafa jikin bango, ko wankewa bata tsaya yi ba ta fice da gudu sai bangaran Uwar Soro.

*****

Adeel kuwa bayan an idar sallah sai da ya shiga bangaren Fulani ya jira har sarki ya gama zaman fada ya shiga bangaren shi sannan yai mata sallama ya je su ka gaisa da sarki su ka danyi hira tukun ya nufo bangarensa cikin tafiyar isa da izza na jinin sarauta shamaki na binsa a baya, a daining yai wa kan shi masauki ya bubude kulikan da su ke kan daining din farfesun ya diba kadan sannan ya hada tea, tass ya cinye farfesun dan yana son shi sosai sannan ya daura da tea.

Kamar an tsikareshu tashi ya yi ya haura sama yana shiga wani uban wari ya daki hancin shi don dama abude Gaaji ta bar toilet din, kawar da kai ya yi ya sake k’utsa kai cikin dakin wari nata k’aruwa rufe hancin shi ya yi ya kufi toilet din dan yasan daga nan warin ya fito, yana shiga idon shi ya fada kan kashin ya rintse ido da karfi ya yi baya sai ji ya yi ya taka abu saukinta daya da takalmi a kafar shi, yana ganin abin da ya taka ya ya fara kakari cire takalmin ya yi ya fice da dan gudun shi wani uban amai ne ya zo mishi da sauri ya sauka kasa kitchen ya wuce ya dinga kwarara amai kamar zai fito da kayan cikin shi.

Kakarin da yake har waje Shamaki ne ya shigo cikin tashin hankali, da sauri yaje bangaran Uwar Soro ya fada mata halin da ya tarar da yarima a ciki, ita ma ta kad’u da ganin yadda ya ke ta kakari ba abin da ya ke fitowa amma bai dadara ba, kama shi tayi zuwa bangaranta, kasancewar dare ya yi, suna shiga yaci gaba da yunkurin amai dakyar Uwar Soro ta samu ta shawo kan shi ta hanyar lallashi da kwantar mishi da hankali har ya daina, “Adeel me ya same ka ne ka ke ta amai kuma na lura yanzu kai ne ka ke neman zuwan aman da kan ka?”

Idanunshi sunyi ja kamar garwashi har wani ruwan bacin rai ne ya taru a ciki, Ya ce “Kisa a kira min dukkanin masu aikin da tsaron bangarena.” Ya fada jikin Galabaitacciyar murya.

“Nop me zasu yi a wannan daren ka dai fadamun meke faruwa, ko wani abune a bangaren naka?.”

Bai ce kara cewa komai ba, hakan yasa ta fita ta nufi Part din nasa.

Bangaran Yareema Uwar Soro ta koma ta shiga har cikin dakin, Mamaki ya kamata “Lallai duk wanda ya aikata wannan kazantar ba karamar kasada ya dauka ba,” komawa tayi taje tasa aka gyara dakin aka fesa turaren wuta kala kala da Room fresheners cikin ‘yan mintuna dakin ya dauki kamshi, ko da ta koma bangaranta ta tarar da shi yana ta ci gaba da kakarin.

Uwar Soro ta ce, “Na sa an gyara amman ina mamakin yadda akayi har aka aikata hakan.”

Adeel ya ce, “Dukansu daga yau sun bar aiki ba zan iya daukan wannan shirmen nasu ba, Part din da Ko Mahaifiyata da mahaifina basu taba shiga ba shine har su zasu iya bari a shiga a aikata mun wannan kazantar?”

Gaaji na gefe tana sheƙa dariya suna haɗa ido sai gwalo tana turo masa harce, can kuma sai ta ce, “Sannu ko, mazaje anji jiki Aradun Allah.” Dadi take ji har cikin ranta domin tasan tunda bai kamata A part din ba mai tunanin cewa ita tayi kuma koda ya sani ma yanzu duk jikinsa ya mutu ba zai iya mata komai ba.

A daren ranar Adeel bai iya bacci a bangaran shi ba duk da kuwa Uwar Soro ta fada mishi ta sa an gyara amma fir ya ki komawa gaba-daya kyankyami yake ji, duk tsigar jikinsa ta gama tashi, karshe a falon Uwar Soro ya kwanata ta gyara masa wata farfadiyar gujera mai kama da gado.

Ta ce wa Gaaji, “Oya to kije kema ki kwanta.”

Tashi Gaaji tayi tana leƙa idanun Adeel, “Oh Sannu kaji an sha ka… Sai kuma tayi shiru tana rufe bakinta da hannu.

Sai da taje daidai kofar dakinta ta juyo tana kallonsa da ta tabbatar ya dago ido ta yi masa gwalo kafin ta shige.

Kautar da kai ya yi, kawai zuciyarsa na saka masa cewa ya tsani wannan yarinyar.

*****

Washegari da asuba Uwar Soro ta tashi sallah tana yi ta fito Parlour domin duba Adeel jiki na karkarwa ta gansa ga dukkan alamu ko sallah bai samu zuwa ba, zazzafi ya yi masa mummunan kamu hatta hakoransa rawa suke “Subhanallah Adeel zazzabi ne a jikinka amma ka kwana haka baka tashe ni ko magani a baka ba?”

Shi dai baya jinta, babban bargo ta dauko ta rufe shi sannan ta fita ta je bangaran masu aiki ta kira direba da taimakon shi da shamaki su ka sa shi a mota sai asibiti.

Sai da gari ya yi haske sannan Uwar Soro ta kira Fulani ta sanar mata halin da Adeel ya ke ciki, fatan samun lafiya, nan take hankalinta ya yi matuƙar tashi.

A asibitin ya yini sai da yasha ruwa leda uku sannan da dare ya matsa a basu sallama ba zai kwana a asibitin ba.

Mai Martaba kuwa ya kagu yaga yadda jikin Adeel din yake, yana jin an basu sallama a ranar tun kafin lokacin tashi fada ya shiga cikin gida ya zauna zaman jiran zuwan yaron shi.

Kamar kuwa Adeel ya sani suna shiga masarautar ya ce a kai shi bangaran mahaifin shi, ko da ya je dukkanin yan Masarautar sun hallara a babban parlourn.

Bayan sun gama yi masa sannu da jiki.

Jakadiya ce ta yi gyaram murya tana fadin, “Allah dai ya tsare gaba ya kiyaye mana kai Yareema, amman ka ga da ace ka daure ka yi aure ai da komai zaifi zuwa da sauki, kuma na Tabbatar da cewa hankali kowa zaifi kwanciya Mussaman mai martaba, ina ganin lokaci ya yi da za ace an aura maka Yar Uwarka Khaleesa.”

Nan take gaban Adeel ya yi wani irin mummunan faduwa.

Jakadiya ta ci gaba da fadin, “tun dai na lura kun fahimci juna kuma kuna son junanku mene ne na bata lokacin?”

Parlourn ya dauki shiru na yan wasu daƙiƙu kafin Mai Martaba ya yi gyaran Murya “Lallai kam nima ina da tunanin hakan, ya tabbata kenan kun fahimci juna da Yar Uwarka? Mai Martaba ya fada yana kallon Yareema.

Shiru ya yi kansa kasa ba tare da ya ce komai ba.

Karaf Jakadiya ta ci gaba da fadin, “Ranka Ya dade ai kasan shi da kunya ba zai iya bada amsa ba amman na Tabbatar da cewa akwai fahimtar juna tsakaninsu.”

Hajiya Rabi da Khalesa suka hada ido suna sakin Murmushi.

Hawayene ke kokarin gangarowa Nasmah Hajiya Maimuna ta kalleta ta sake mata wani matsakaicin murmushi da nunin ta rike kanta kada ta bari kowa ya fahimci wani abu.

Fulani Babba kam ban da Murmushi ba abun da take bayyanar wa.

Magajiya da Waziri suka haɗa ido suna kallon kallo.

Mai Martaba ne ya katse su da fadin, “Lallai za ayi abun da ya dace nan ba da jimawa ba, kana bukatar hutu yanzu Yareema kuje ka kwanta ka huta.”

Yareema na kokarin tashi kenan Jakadiya ta ka da baki tana fadin, “lafiya kuwa naga goshinka da ciwo kuma Yareema?”

Kallon kallon Uwar Soro da Adeel suka fara sai can kuma tayi saurin fadin, “Eh fa lokacin da yake Amaine kafin Shamaki ya shiga dakin ya buge kai da bango.”

Jakadiya tasa hannu a haɓa, “amman dai wanna ciwon kamar bana buguwa ba.”

Tashi Yareema ya yi kawai ya fice, Uwar Soro da shamaki suka bi bayansa.

*****

Gaaji na kwanciya barci tayi mafarkin Adeel ya kamata yana kara yi mata abun da ya mata ranar.

Banda numfarfashi ba abunda take.

Tuni ta mike tana zufa duk ta jike gabadaya da ruwa tamkar a zahiri hakan ke faruwa.

Cikin dare ta nufi kitchen ta dau wuƙa tana, “Aradun Allah sai na yanke masa jelar nan watau abun ma har cikin mafarki, daga yau ma inna yanke ai shikenan naga abun da zaina ishkanci da shi.”

Ta ƙarasa maganar tana ficewa a hankali.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×