Dakyar Uwar Soro ta ja Gaaji ta shigar da ita daki, ta kwantar da ita akan gado.
Idanunta bude sun fito kamar zasu yi magana amman ko alamar kiftawa basa yi.
Uwar Soro ta jinginata da filo sannan ta ce, "Me yasa kuke son bayyana kanku aduk lokacin da kuka ga Jakadiya, shin baku san hakan zai iya zamtowa matsala bane ga rayuwar Gaaji?"
Wani irin Murmushi gefen fuska suka sake kawai ba tare da sunce komai ba.
Uwar Soro ta ce, "Au baza ku fada mun dalilin zuwan kun ba? To yanzu ku barta don Allah ta dawo hayyacinta. . .