Skip to content
Part 15 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Dakyar Uwar Soro ta ja Gaaji ta shigar da ita daki, ta kwantar da ita akan gado.

Idanunta bude sun fito kamar zasu yi magana amman ko alamar kiftawa basa yi.

Uwar Soro ta jinginata da filo sannan ta ce, “Me yasa kuke son bayyana kanku aduk lokacin da kuka ga Jakadiya, shin baku san hakan zai iya zamtowa matsala bane ga rayuwar Gaaji?”

Wani irin Murmushi gefen fuska suka sake kawai ba tare da sunce komai ba.

Uwar Soro ta ce, “Au baza ku fada mun dalilin zuwan kun ba? To yanzu ku barta don Allah ta dawo hayyacinta ta huta, sannan ina neman alfarmar da karku kara zuwa mana cikin masarautar nan.”

Basu ce mata uffan ba, basa ma da niyar yin wata magana, ganin haka yasa Uwar Soro ta fita taje ta karbo Ruwan Addu’a agun Liman, tana zuwa ta shafa mata a fuska bai fi minti biyu ba idanunta ya rufe tayi atishawa sai barci.

Da kyar Jakadiya ta iya karasawa Dakinta, toilet ta nufa cikin sauri ta kwaɓe zanin da ke jikinta, sai da ta karar da duk wani abu da ke cikin cikinta illa hanji sannan ta wanke jiki ta fito,tana fitowa kan Gado tayi ta kwanta kawai, bata san lokacin da wani gigitaccen barci ya yi awun gaba da ita ba.

Sai da tayi Awa uku cikakku tana barci kafin ta farka, aikuwa farkawan da zata yi taji fuskarta tayi mata wani irin nauyi, a hanzarce ta nufi madubi.

Wani irin kumbura kumatunta dukkanin bangaren da tasha mari suka yi , tamkar lafiyayyan bread.

Hawayene ya fara kwararo mata tana sa hannu a fuskar na kara yi mata radidi cikin muryar kuka ta ce, “Wa innan mutanen lallai so suke su canja mun kamannina, zama bai kama ni ba, dole in wanke kafata in nufi gun Boka Zirru .”

Daukan wani mayafi tayi ta rufe fuskarta yadda baza a ganeta ba a sulale ta fice daga Masarautar, har yanzu a firgice take bata da burin da ya zarce ta ganta gaban Boka Zirru.

Wani ƙasurgumin daji ta shige, shiru ban da kukan tsuntsaye da iskar bishiyoyi ba abun da ke tashi agun,haka ta dunga kutsawa sai can ta tsaya a kofar wata bukka wanda ga dukkan alamu babu wata bukka a cikin Dajin sai wannan.

“Gafaranka dai Boka Zirru kayi bakuwa ko zan iya shigowa.” Tana fada cikin daga murya.

Dariya ya fara sheƙawa wanda sautin dariyar sai da ya amsa ilahirin Dajin Hatta bishiyoyin da tsuntsaye sai da suka girgiza kusan minti guda kafin ya ce, “Ya Ke karamar Munafukar MASARAUTAR BENONI ki shigo da baya tsugune kina jan gwiwoyinki, karki taka mana danmu,in kika taka mana danmu sai kin haifa mana wani.”

Haka ta durkusa ta baya tana jan gwiwoyinta har ta shige.

Tana shiga ya daka mata wata irin tsawa tuni ta kyankyami jikinta, sai kuma ya ci gaba da dariya tukun ya ce, “mun san meke tafe da ke, ba sai kinyi mana bayani ba, Amman kafin komai ina so ki sa aranki cewa yanzu babban aikine gareki, gareku, kuma ga kowa ma dake rayuwa cikin wannan Masarautar ke harma da wajenta.”

Jiki a sanyaye JAKADIYA ta ce, “wannan wacce irin matsalace da zata fi karfin kowa?”

Dariya ya ci gaba da yi kafin ya ce, “Matsalar da tayi kokarin canja miki kamanni da mari mana.” Ya tsaya da magana sai da kara ci gaba da dariyar tasa kafin ya tsagaita ya na buga wani abu ya ce, “Ya zama dole ku tashi tsaye.” Sai da JAKADIYA ta razana.

Kallonsa take hannu rike da kirji sai da ya kara daukan Minti guda yana dariya kafin ya ce, “Kamar yadda kika sani…. Kuna da yawa masu kudirin mugunta, yaudara da cin amana a Masarautar nan, wasu sukan nuna nasu a bayyane wasu kuwa ba sa taba bari a gane, kowa ya dage kan lallai sai ya cika burinsa kuma duk akan Mutum Daya, Yareema, Haaaahaaaaahaaaahaaa to kuna ruwa, na ce muku kuna ruwa, haaaaahaaa, Tabbas an samu wacce zata iya tarwatsa shirin komawa waye a cikinku indai baku tashi tsaye ba sai dai kuga lumara na tafiya cikin idanun ku amman baku isa ku aikata komai ba.”

Jiki na rawa Jakadiya ta ce, “Wace ce wannan? Kuma a ina take? Mutum ce ko Aljann?”

Bori ya shiga yi sai can ya juyo ya kalleta ya ce, “Dukka biyun akwai, Mutum da Aljann,kuma suna zaune cikin wannan Masarautar, babu shakka abun da ke fuskarki ba aikin kowa bane sai nasu, kuma indai suna cikin wannan Masarautar ina kara jaddada miki cewa baku isa ku aikatawa yareema komai ba, tamkar kariya suke garesa kuma ba za su taba bari wani abun cutarwa ya riskesa ba, koda kuwa an tura indai suna nan zasu riga Yareema amshewa.”

Muryarta na rawa ta ce, “Bangaren Uwar Soro anan nayi gamo da Aljanun kuma ita bata ganinsu, yanzu inna koma ban da tabbacin cewa suna daki.”

“Wannan Yarinyar duban mu ya nuna zata iya zama Fulani cikin wannan Masarautar, huuuhuuuu, inko ta zama Fulani kashinku ya busheeeeeeeee, koma miye dai na gama nawa yanzu ya rage naki indai kina so komai ya tafi yadda kike so hakan wajibi ne da ki binciko inda wa innan mutane biyun suke rayuwa, Aljanna da mutum, a tare suke, dole akwai su amman ban san inda suke ba kuma wannan ba aikina bane, ni dai zan baki wannan kwallin da ki sanya shi cikin idanunki kije ki riske su muddin zaku hada ido dasu to ina tabbatar miki da cewa basu babu wannan masarautar har gaban abada .”

Karba tayi tana juya kwallin ya yi gyaran murya yana, “in kika yi wasa da damarki wasu suka san wannan sirrin kuma suka riga ki magancewa to babu shakka duk aikin da za a miki ba zai taɓa yi ba, da zaran kin aikata abun da na umarta babu wani jinnu ko bil’adaman da suka isa su kara dake ke ce gaba kan komai, ba Yareema ba, hatta Mai Martaba sai kin juyasa son ranki, haaaahaaahaaa kije, tashi kije,ki tafiiii, haaahaaahaaaa.”

Aguje Jakadiya ta fice tana haki, lallai akwai matsala babba cikin Masarautar nan ai kuwa da wata ta zam matar Yareema duk rintsi gwanda Khalesa ta zama duk da cewa ita ma din ba son kasancewar ta take ba, amman kuma za a iya juyata duk yadda aka so tunda bata da wani karfin sihiri daga ita har mahaifiyarta ta.

Tana saƙe-saƙe a zuciyarta har ta isa Masarauta can dare.

Washegari kuwa da sassafe tana tashi ta saka wannan kwallin ta nufi Bangaren Uwar Soro.

“Koma wace ce wannan mayyar aljanar sai nayi maganinta ko ni ko ita, in tasan wata ai bata san wata ba, za ayita ta kare tunda dai har sau biyu ina ganinta a bangaren Uwar Soro babu shakka anan take yau kam kwananki ya kare eeeyy kwananki ya kare, In Sha Allah bayan kin ganni ido cikin ido nayi maganin ki sai na rama marukan da kika mun.”

Tana tafiya tana sambatun ta kasa kasa.

Ba excuse tana zuwa ta shige bangaren Uwar Soro tana surutai, “Uwar Goyon Yareema na dawo yau za ayi ta ta kare tsakanina da Aljanun bangarenki, ko ni ko su yau kam tunda naga abun nasu iskanci ne ma don sunga ana tsoron sune to yau daidai nake jin kaina da su.”

Da Mamaki Uwar Soro take kallonta ta ce, “Aljanu? Wai har yanzu ganinsu kike a bangaren nan? Anya kuwa ba idanunki ke miki gizo ba?”

“Gizo? Ba wani batun gizo fa, kin ga fuskata ai a gabanki jiya suka sharɓa mun zafafan marukan da sai da na gigitace, amman yau za ki ce babu su?”

Abun dariya ya fara bawa Uwar Soro ma, cikin dariya ta ce, “To inma Aljanunne zaki iya fada dasu ne kina Bil’adama suna jinnu?”

Jakadiya ta ce, “Kwarai ke dai su fito kawai yau kiga abun mamaki zanyi fata-fata da su.”

Uwar Soro ta tsaya kallonta kawai tana bambami har da leƙe-leƙe ganin ba aljanu bare alamarsu yasa ta gaji ta fita cike da takaici.

Aranta tana fadin koma a ina wannan matsiyaciyar yarinyar take saita nemota tayi maganinta ta bar masu masaurata.

*****

Tun jiyan Gaaji bata farka ba sai daidai lokacin da JAKADIYA ta bar bangaren, tana fita Uwar Soro ta ji muryar Gaaji na kwallara mata kira, Ta shi tayi tana

“AlhmduLillah Allah yaso baki farka tana nan ba ni ‘Ya su.”

Murya a sanyaye Gaaji ta ce, “Ruwa,Ruwa zan sha.”

Da sauri ta dauko bottle Water ta dan dagota kadan ta bata ta sha.

Tana gama sha ta ce, “Abokina bai zo ba ? Baaba ki kira mun shi muyi wasa kinji Don Allah ina so in ganshi.”

Uwar Soro ta ce, “Adnan fa yana gun Baffanki Uwata kinji, yana cen yana lura da shi ina ga tare zasu dawo ma In sha Allah yanzu bara in shirya miki kayan wanka sai in miki tunda naga jikin naki ba kwari sai kici abinci ko?”

Girgiza kai Gaaji kawai tayi.

Uwar Soro ta mata wanka ta shiryata sannan ta bata kayan breakfast ta ci.

Ko tafiya da kyar Gaaji ke yi sai jan kafa jikinta ya riga ya gama yi mata tsami, kuma sun rike mata kafa ɗaya walwalarta da ka-kazar duk sun dauke dif sai dai ta zauna tayi shiru tun abun baya damun Uwar Soro har ya fara damunta. Musamman ganin ko shirmen da take ma ta daina saidai ta zauna tayi shiru.

JAKADIYA kuwa kullum cikin safarar zuwa Bangaren Uwar Soro take da kwallinta ko Allah zai sa ta ci karo da Gaaji amman ina, aduk lokacin da zata shiga bangaren Gaaji bata tashi a barci ba har tayi duk abun da zatayi ta gama ta fice.

Hankalinta ya tashi matuka Domin ko Yar gulmace-gulmacen data saba bata iyawa duk tunanin yana kan hanyar da zata bi wajen ganin ta kawar da wacce ta tare mata hanya.

Bangaren su Khaleesa kuwa shirin biki suke ba kakkautawa ita da mahaifiyarta, tunda hakan ke faruwa Nasmah ta shiga ciwo mai tsanani.

1 week latter.

Prince Adeel na zaune a bangarensa yana tunanin anya Gaaji lafiya kuwa? Ko neman fitanar da ta saba yi masa yau kusan kwana takwas kenan bai jin ko duriyarta bare kuma ta shiga bangarensa.

Tun yana jurewa har ya ga hakan ya gagara kawai yana so yaje ya duba shin tana lafiya kuwa.

Hakan yasa ya tashi nan take ya fita.

Uwar Soro ta tafi Fada Gaaji ce kadai kwance adakinta da Teddies dinta ta zura masu ido tana sa masu hannayenta a fuska.

Ganin Adeel tayi kawai tsaye abakin kofa, nan take gabanta ya yi wani mummunan faduwa, tsoron shi taji har cikin ranta,zuciyarta na bugun tara tara, a dari ta tashi zata, Adeel ya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 15Auren Wata Bakwai 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×