Ajiye wayar Adnan ya yi ya gyara kwanciya don tuni Gaaji tayi nisa a barcinta.
Washegari
Da Asuba Adnan na dawowa daga masallaci sai ji Gaaji tayi ya saɓeta, a hankali ta bude idanunta suna kallon juna, murmishi ya sake mata yana kai bakinsa daidai kunnensa cikin raɗa a sanyaye ya ce , "Morning Beauty."
Gaaji ta taɓe baki , "Umm ni kasan ai bansan me kana cewa ba kuma."
"Oh Sorry, Ina Kwana Kyakkyawata ko ince Boddi Am." Ya karasa maganar yana shigar da ita toilet din.
Gaaji ta ce, " Yaya Me zaka mun? Ka barni zanyi alwalar. . .