Taxi ya tare da sauri ya shige Adnan ma ya shiga, cikin tashin hankali Adeel ke magana, "ka yi sauri, Don Allah ka yi sauri mu karasa asibitin nan,in wannan yarinyar ta rasa rayuwarta nima zan rasa tawa." Yana maganar yana kara jijjigata.
Duk da cewa Adnan ma na cikin damuwa amman ganin yadda Adeel ke bayyanar da damuwarsa ƙarara ga halin da Gaaji ke ciki ya basa mamakin da ya kasa dauke idanunsa da kallonshi.
Har suka isa asibiti Gaaji na jikin Adeel, kasa jure sakewa nurses din ita ya yi sai da ya bisu suka shige Dakin. . .