Skip to content
Part 22 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

“Karka mun komai don Allah ka ga bana da lafiya.”

Adeel ya ce, “Just Once, koda daga yau ne kadai don Allah zan iya rasa raina nake ji, ni nasan me nake ji,na Tabbatar da cewa yau in har ban samu damar nan ba sai dai in rasa raina.”

Gaaji ta fara kuka.

Tana kara rurrufe jikinta.

“Ke halali nace, ba zan iya aikata abun da ba daidai ba ga wasu matan waje, Ki ba ni hakkina kada ki cutar da rayuwata.” Ya fada cikin wata irin Galabaitacciyar murya, Idanunsa sunyi jajawur.

Yana kara matsawa gareta ta ture sa gefe, ya yi gefe yana rike mararsa yana jin wata irin azaba da bazai iya misaltawa.

Numfarfashi yake tamkar wanda ake kokarin zarewa rai.

A tsorace Gaaji ta tashi bata san yadda a kai ta iya tallafoshi ba.

Cikin Numfarfashi a hankali yake fadin, “kin amince in… In…Please.”

Girgiza masa kai tayi alamar eh tana hawaye.

Cikin wani irin sauri ya fisge wandonsa, ita ma ya cire mata hijabin, wata irin fisga da ya yiwa pant din jikinta sai da ya yage.

Rufe idanunta tayi hawaye na kara kwarara tana fadin, “na shiga uku, Don Allah kar ka mun da zafi, kar ka mun da zafi zan mutu nima in kamun irin na ranar mutuwa zan yi na shiga uku.”

Ba tare da ya saurareta ba, tallafota ya yi yana yin addu’ar da kowanni magidanci kanyi lokacin kasancewa da iyali.

Tana ganin yana kokarin haƙe mata ta kara matse idanunta tana, “Don Allah, don Allah ka ji don Allah a hankali Wayyo ni…Sai kuma tayi shiru kasancewar fuskantar abun da ba tai zato ba duk da cewa taji alamun yana shigarta amman ko kadan bata ji zafin da take zaton ji ba sai saɓanin hakan wanda zata iya dangana shi da jin dadin da bata taɓa samun irinsa ba a rayuwarta.

Shi kuwa Adeel sambatu yake yana fadin, “Ya ilahil alamina na gode maka Zainab na gode, ke kadai ce maganin lalurata bana da wani maganin da ya zarce ke, don Allah kada ki gujeni duk rintsi ki Kasance tare dani, ke kadai ce zaki iya share mun hawaye ki hanasa zuba, ke ce zaki iya warkar da ciwon da ke damuna, Allah… Allah na gode, Allah ya miki albarka, Allah baki abun da kike so… Ya saki a aljanna.”

Kusan 13 minute suna abu daya tukun Adeel ya ji sa daidai, sai a lokacin ya fahimci Ashe Gaaji ta dade da yin shiru ta ƙankame sa tunda ta tarar da sabanin tunaninta.

Tana ganin ya dakata har cikin ranta ji take kamar ta cakumosa ya ci gaba.

Yana kokarin tashi amman rike san da tayi ya gagara dagowa yayi yana kallonta, suna haɗa ido ta yi saurin kautarwa tana sake sa a hankali.

Murmushi ya yi ya kalleta, “Kukan ya kare ne?”

Kunya ta lullubeta tana sunkuyar da kai ƙasa.

Tashi ya yi, ya shiga toilet ya hada ruwa yana fitowa kawai ya sungumeta.

Ya shigar da ita cikin toilet din yana zuwa ya tsundumata a ruwa sai da ya wanketa tas da kanshi kafin ya ce to tayi wankan tsarki.

Tana farawa kafin ta gama ya yi sauri ya fita ya canja bedsheet din gadon ya koma toilet din ta gama kenan ya dauketa ya dawo da ita kan gadon.

Ita dai Gaaji wata irin kunyarsa da kwarjini ya mata ko ido ta kasa haɗawa da shi bare yin magana.

Yana ajiyeta ya yaje Wadrope dinta ya dauko mata kaya ya shafa mata mai sannan yasa mata kayan.

Ya zauna daf da ita yana dago fuskarta ya kalleta ya ce, “Zizi ba za kiyi magana ba?”

Jin motsin shigowar Uwar Soro ne yasa Yareema saurin miƙewa zumbur yana kokarin fita.

Aiko yana fitowa daga dakin suka ci karo.

Kunya ta kama shi ya fara soshe-soshen ƙeya.

“Daman kana nan ne? Na zata ka tafi ai.” Uwar Soro ta fada.

Adeel ya ce, “umm yanzu zan fita daman zamu fita da Adnan ne.”

Ya ƙarasa maganar da sauri yana ficewa, Murmushi kawai ta yi ta wuce ita ma.

Yana fitan kuwa sai ga kiran Adnan kan cewa yana mota yana jiransa.

Adeel ya ce, “Bara na dan yi wankan wait For a minute please.”

Adnan ya ce, “Kamar ya? Wanka da tsakar ranar nan yau ba kai wanka bane?”

“Eh.” Kawai ya fada yana katse wayar.

Da sauri ya shiga ya yi wanka ya shirya ya fito.

Kallo ɗaya Adnan ya masa ya ce, “yau Nikam wani albishir aka yi ma ne gabadaya yanayinka ya sauya kai kadai sai sakin Murmushi kake.”

Adeel ya kara yin murmushi yana gyara zama ya ce, “Ashe haka so yake?”

“Ban gane haka so yake ba kamar ya?” Adnan ya fada.

“Umm Allah ina son yarinyar can sosai kuma ban taba kawowa araina zan taɓa jin son wata ‘Ya mace ba,bare kuma ita.”

Adnan ya yi dariya, “Ah kace mun Murmushin yau na Fulani Gaaji ne ina ga dai tana daf da canja mana Prince Adeel daga miskilanci da rashin murmushi .”

Adeel bai ce komai ba sai Murmushi, haka suka tafi.

*****

Fitowa Parlour Gaaji tayi ita ma kallo ɗaya mutum zai mata ya tabbatar tana cikin farinciki, bata san Adeel ya ci karo da Uwar Soro ba, hakan ya bata damar baiyyanar da tsantsan farin cikinta a fili.

Taje ta kwanta a jikinta fuska dauke da fara’a.

Uwar Soro ta shafa mata kai tana fadin, “Wannan farin cikin fa?”

Gaaji ta ce, “Ba komai Babata kawai dai na jima ban ji dadin jikina kamar na yau bane.”

Uwar Soro ta ce, “Umm to Allah kara sauki kin ga ya kamata ma ki fara zuwa awo aje kuma ayi scaning tunda cikinki na ta kara girma.”

Gaaji ta ce, “Umm ni kar su mun allura ba na son zuwa asibitin nan.”

Uwar Soro ta ce, “aiko dai dole kiyi hakuri sai anje.”

*****

Jakadiya Zaune da Safina gaban Mai Martaba.

Jakadiya ta ce, “Ranka Yadaɗe batu na gaskiya Safina Cikin jikinta na Yareeema ne amman kuma ba yadda ake tunani ba, domin kuwa samuwar hakan ya faru ne bayan sunyi aure a boye wanda daga ita har shi suna tsoron bayyanar da hakan ne Musamman ma shi, ita kuma ganin bata da wata mafita Shiyasa ta zo ta sanar da cewa ya mata ciki kawai a gudun kada tace sun yi auren sirri ya zam mata matsala, sannan tunda tazo cikin Masarautar nan cikin kalubalen take tana fuskanta ana ƙoƙarin kai mata hari tare da tursasata kan cewa lallai ta bar Masarautar nan ko a kasheta wasu kuma suce lallai sai dai tazo gabanka ta musanta faruwar hakan kamar yadda aka kai mata hari shekaran jiya, Mai Martaba kuma daman kamar yadda na fada a farko na sam cewa Yareema ba zai taɓa aikata wannan aika-aikar da aketa tunani ba, kuma yanzu tunda abun ya kasance na gida Alhmdu Lillah ai ina ga kawai inda hali sai a shirya shagalin bikin a sabumta shi sai ta haihu a dakin mijinta inaga zaifi ko?”

Mai Martaba ya gyara zama kafin ya ce, “To a gaskiya dai na ji matukar dadin jin hakan samun mafita kan mummunan abun da muke zato gashi kuma abun ya kasance kan ta gida, amman duk da haka baza ayi shagalin yanzu ba akwai abun da zan bincika musamman masu kai mata harin nan, ta zauna a wajenki har Allah ya sauketa lafiya tukunna.”

“Maddallah Da Sarkin BENONI godiya muke Allah ya tabbatar da alkairi.” Jakadiya ta fada suna fita da Safina.

Jakadiya ta ji dadin amincewar da mai martaba ya yi sosai amman sai dai taso ace kafin Safina ta haihu za ace za ta tare da Yareema.

Suna shiga daki Safina ta kalleta tana dariya ta ce, “Yanzu wai har ya yarda kenan ni matar Yareema ce? Kuma ya amince kenan fa.”

Jakadiya ta ce, ” Na san zai yarda ai da abun da na fada masa, amman dai naso ace ya amince ki tare acen ki haihu amman duk hakan ma wata babbar dama ce da zamu lalubo wannan yarinyar, sannan aiki na biyu dake gabanmu shine rufe wa Mai Martaba da Fulani Babba baki, koda wasa ka da su ji cewa hakan ba daidai bane ko kuma wani wasi-wasi a zuciya, duk da cewa shi Yareema kam na gama da shi amman zamu kara kaimi tunda na fahimci cewa ba nawa kudirin kadai ke shawagi cikin Masarautar nan ba ke duk wani mahaluki da ya nuna kokarin kawo mana matsala zamu rufe masa baki inko hakan ma yaki zamu kawar da shi ta karfi.”

Safina ta shafa cikinta tana dariya, “Lallai akwai shagali Matar Yareema kuma Uwar Yareema.”

Jakadiya ta ce, “kin ga ina zuwa ma tukunna, bara naje nayi wani kashedi wa Fulani Kilishi.”

Ta fada tana ficewa da sauri, bangaren Fulani Kilishi ta shiga kai tsaye.

Tana zuwa kuwa ta ganta cikin yanayin damuwa, koshigarta yasa ta miƙewa zumbur.

Jakadiya ta kalleta ta kyalyale da dariya.

Jiki a sanyaye Fulani Kilishi ta ce, “Ina fatan dai baki sanar da mai martaba abun da muke aikawatawa.”

Jakadiya na dariyar mugunta ta kalli Fulani Kilishi tana zagayeta sai da tayi dariya me isarta ta ce, “Ban sanar ba amman zan sanar muddin kikai kokarin hanani aiwatar da abun da ke raina, In kin amince da shirina kila ma har ki samu tsira daga ciki, in ko kika kuskura kika nuna aa ummm kwanakin ya kare cikin Masarautar nan.”

Fulani Kilishi ta ce, “Don Allah ni dai kada ki tona mun asiri ki fada ko me kikebso zan baki, daga sarkar zinare da duk wani abu dana mallaka, inma makuden kudade ne duk zan baki koda kuwa duk abun da na tara ne indai zaki rufamun Asiri.” Ta karasa maganar tana durkusawa gabanta.

Jakadiya ta kara sake dariya har tana rike ciki ta ce, “Oh Allah wai yau Ni Fulani Kilishi ke yiwa biyayya har da durkusawa gabana? Lokaci kenan ya fara zuwa tun yanzu, Umm ki saurare ni da kyau kuma ina so ki bani goyon baya dari bisa dari.”

“Zan baki, zan baki wallahi na amince koma mene ne.” Fulani Kilishi ta fada cikin sauri.

Jakadiya ta ce, “shikenan tashi ki zauna muyi magana.”

Tashi Fulani Kilishi tayi tana mai zaƙuwa da son jin abunda Jakadiya zata furta.

Jakadiya ta dafa kafadarta tana fadin, “ba wani abu bane fa mai wahala, da farko dai ki tsaida duk wani shirinki da kike shirin yi, sannan kada ki kuskura ki tambayeni dalilin yin abun da zan fada miki, Safina zata Auri Yareema duk da cewa kudai ba hakanma kuka so ba, to zata aure shi a yanzu ma abun da ake ciki shine cikin jikinta da aure ya mata shi ba wai ba aure ba,bsun yi auren sirri ne wanda suke tsoron sanarwa don haka bakinki kanin kafarki daga ke har Wazirin ki sanar masa don ni bana da lokacin bunsuru kamarsa in kunenku yaji, jikinku da rayuwarki sun tsira in ko akasin Hakane tabbas kuna cikin hatsari don ki sani duk makircinki da wani kulle kullenki atafin hannuna suke zura ido da goyan baya dukkan kudirina shine naki.”

Tana fadan hakan ta fice tana dariya.

*****

Adeel ya saba duk dare sai yaje bangaren Uwar Soro ya ga Gaaji ya kuma bata su ice cream dinta amman yau kam bai je ba.

Kamar wasa yau har dare ya tsala ba Yareema babu alamunsa.

Ita kuma Gaaji ta kasa barci ko da ta rufe idonta kwanta kasawa ta yi ta dunga juyi.

Karfe 12:00pm na daren kawai ta tashi ta fice ganin da gaske dai ba barcin zata iya ba.

Shi ko 11 ya dawo ganin dare ya yi gashi kuma ya gaji hakan yasa kawai ya yi wanka ya kwanta.

Har ya yi nisa a barci, tana shiga taje daf da shi ta ƙanƙamesa ta kwanta tana shakar kamshin jikinsa harda ajiyar zuciya.

Jin alamun mutum ya yi a bayansa hakan ya sa shi saurin razana.

<< Auren Wata Bakwai 22Auren Wata Bakwai 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×